Free chapter · Read without an account

Page 5

by Aisha Nalado · DAMA TA BIYU

Yau kimanin wata daya kenan da faruwar wannan lamari, zuwa yanzu gida ya dawo normal kamar babu abinda ya faru. Ba'ki na nesa duk sun wuce , mutanen gidan kuwa yaransu da manyansu sun dauki dangana a kan lamarin da ya wakana, ko maganar babu wanda ya sake tayarwa , sun mayar da abin kamar ba'ayi ba.

Asmah ma da suke tunanin zata shiga damuwa sai suka ga akasin hakan , don ka a jikinta, saima walwalarta data dawo sabanin da, da take cikin qunci.

Ta bangaren Aslam da'ker ya samu ya shawo kan iyayen shi suka daina fishi da shi suka yafe ma shi, domin, sai da Alhaji baba ma yasa baki, duk da haka ba wani sake mai fuska su ke yi kamar da ba, daga mummy har daddy. Shi dai tunda ya samu sun yafe mai suna amsa gaisuwar shi shikenan, sake fuskar ma ya san zasu yi a hankali.

Domin shi har yanzu bai ga ya aikata wani kuskure ba, a kan sakin da yama Asmah , ko so daya bai tabajin nadama akan hakan ba , shi yama manta da wata Asmah ya shafe babinta a rayuwarshi ,don tuni ma har ya gayawa Zainab ta sanar ma iyayenta iyayen shi za su zo nema masa aurenta next week,.

Tsabar farin ciki Zee kamar ta shiɗe jin cewa iyayen Aslam za su zo neman aurenta,

Duk da tasan akwai qura a gabanta hakance kuwa don tana sanarma mahaifinta take ya ce shi bai shirya aurad da ita yanzu ba ,.. Kwata kwata shekararta nawa da zata ce amata aure , to shi bai shirya ba idan Aslam zai iya jira nan da shekara bakwai to, idan kuma bazai iyaba to ya haqura kawai,... Zee dama tasan hakan zai kasance don haka ta riga ta shirya, babu gudu babu ja da baya

Rigima sosai a kay i ta dage aure takeso kuma da Aslam , yayinda shi kuma mahaifinta yace ba yanzu ba Mom kuma ta goyama mijinta baya , Zee ganin wankin hula na neman ya kaita dare, yasa ta dauki waya ta kira wan mahaifinta dake Nigeria, Wanda dama koda mahaifinta ya amince wurinshi za a nemi auren nata , shima dai dan bokon ne kamar Daddy'n Zee harma ya take ƙanin nashi domin shi duk abinda y'ay'anshi suke so shi yake mushi, ya kuma basu dama su yi duk abin da suke so da rayuwarsu ancinsu ne a cewarsa, to banbancin shi da Dad mahaifin Zee kenan.

Cikin kuka ta sanar da abinda ke faruwa.

Nan ko yace ta ce iyayen Aslam din suzo gurinshi, zai daura mata aure da duk Wanda takeso, karta damu , kuma zai kira dad dinta ya mishi magana cikin jin dadi tace "to Daddy na gode" yace "karki damu y'ata abinda kikeso shi zan miki"

Alhaji abdurrahim wan mahaifi zee ya kira dad ya kuma nusar dashi ilar hanata auren tunda dai ita ta kawo mijin tace tana so, Shiko dad duk da haka bai gamsu da maganar wan nashi ba, karshe dai saida aka kai ruwa rana ya amince ganin zainab din ta dage kai da fata, itako zee tayi hakane saboda tasan hakan ne kadai mafita a gareta inba hakaba kuma tabbas zata rasa Aslam dinta, abinda kuma zuciyarta bazai taba dauka ba kanan wato rashin Aslam.

Ya kasance weekend yan matan mummy ne zaune a main falon mummy sai fira suke yi anata shewa kamar yadda suka saba, ko wacce ta sheqa wankanta tayi shiga irinan zaman gida domin shan iska ,dukkansu qananan kaya suka sa amma ba mai bayyana jiki ba, zahra ce kawai ta saka dogon rigar material mara nauyi , safiyace don gama yin breakfast dinsu kenan suka dawo falo suna kallo suna hira,

Ya kamal ne yayi sallama a qofar falon tare da shigowa fuskarsa dauke da murmushi kamar ko yaushe ,yasha kwalliya cikin qananan kaya shima sai zuba kamshi yakeyi , kusan hada baki sukayi gurin amsa mishi sallama tare da fara gaishe shi , amsa musu gaisuwar ya shigayi da sakin fuska kamar yadda ya saba musu , zaida kallonshi yayi akan zahra kasancewar yafi d'asawa da ita yace "sisto me zan samu a nan ne na breakfast" ya fada yana shafa cikin shi alamar yunwa, yaci gaba da cewa"wai tea suka sha, ni kuma wlh na gani da tea dinnan " Murmushi zahra tayi tace "aiko ya kamal kai kai taki sa'a yau dan yau Asmah ne ta mana masan nan nata mai shegen dadi da shi muka karya , kuma naga akwai saura bari zubo maka " murmushi kamal yayi jin abinda zahra ta fada sosai yake daukin cin masan badan masa ta dame shi ba saidan jin cewa Asmah ce tayi masan, . ...don wannan karon ya shirya tsab ba gudu ba ja da baya , bazai qara maimaita kuskuren daya , bazai yarda ya sake aikata iri sakacin daya aikata a baya ba, duk da cewa har cikin zuciyarshi baiji dadin abinda Aslam ya aikata mataba , amma shi a ganinshi wata dama ta biyu ne ya sake bashi akanta , kuma bazai yi wasa da damarshi ba , ... Zahra ce ta katsemai tunani ta hanyar ajiye mai filet din masan datayi serving dinshi a gaban shi, kamshin miyan taushen da yaji naman rago, hade da kamshin soyayyen Masan shinkafa ya daki hancinshi lumshe ido yayi tare da budesu akan Asmah sake zaune kushin din dake kallon nashi, filet din Masan ya daga sama yanaci yana Kallonta a fakaice , yana jin wani irin soyayyarta na qara narkar da zuciya, yayinda ita gaba daya hankalinta baya kanshi, yana kan amira da batool daketa musu akan wani Indian series da take haskawa a TV tashar Bollywood...

9:00am dai dai Aslam ya farka daga baccin safen daya koma bayan asubah, miqewa yayi ya shiga toilet yayi wanka , shiryawa yayi cikin jeans da t-shirt baqaqe masu kyau , main falo ya sakko yana shafa cikinsa yana yamutsa fuska alamar yunwa na sakad'arsa, frige ya bude ganin babu wani abun tabawa yasa dole ya fito direct kuma part din mummy ya nufa , daidai lokacin da kamal ke cin masa yayinda yan matan mummy ke zaune suna.

Gaidashi su zahra suka shiga yi, a daqile yake amsawa ganin haka yasa Asmah qin gaisheshi,...kamal ne ya miqa mishi hannu suyi musabaha da'ker ya mika hannunshi sai wani babbata rai yake, haka kurum yaji yana jin haushin kamal din, ...shiko baima San yana yi ba ci gaba da cin abincinshi yayi, yana yi yana kallon sahibarsa,.....

Sake maida kallonshi yayi kan Asmah ganin kowa na gaishe shi ita ta dauke kanta kamar bata ganshi,..gyaran murya yayi "uhummm" dago kai tayi ta sauke idanunta cikin nashi , dukansu saida gabansu ya fadi , ...rabonshi da ganinta tun ranar da yasa mummy ta turo mishi ita part dinsu, gabanin Bikin nan ranar da ya mata warning da wuqa , da idanun shi ya mata alamar kallon fa, dauke kanta tayi daga kallon shi ta mayar kan tv still bata gaishe shiba, a zuciyarta tana cewa "wlh wannan ba Asmah da ka Sani da bace , eheeee wannan wata sabuwar Asmah ce da take daidai da rashin mutuncin ka, wacce kana ce mata kule zata ce maka cassss, don yanzu ba tsoranka nakeji, don duk wani girmanka a idona ka zubar ni kuma nasa qafata na taketa" duk wannan a zuciyarta take fada ,...shiko Aslam mamakinta ne ya kamashi ganin yadda ta dauke kai daga kallon shi kamar taga wani banza, ba wannan rawan jikin da tsoron shi dayake gani kullum a tattare da ita , shi sai yake ganima kamar kallon tsana take jifanshi dashi ma, ...kwafa yayi yana girgiza kai ya nufi dakin mummy ganin bai ganta a falon ba, ,a zuciyarshi kuwa yana aunawa Asmah zagi, mayya kawai mai idon mayu kurwata kur wlh, haka kawai da sassafen nan tasa gabana nata faduwa,.shiga dakin mummy yayi bai ganta ba. falon ya sake dawowa,batool ya kalla tare da cewa "kee mummy fa" da sauri batool ta amsa mai da tana part din daddy , hanyar fita falon yayi tare da ce mata "ki kawo min abinci part dina yanzu" ya fada fuskar nan a murtuke cike da isa, ya fice a falon, bai cewa kowa komai ba, batool ce ta mike cikin zumbura baki ta nufi kitchen, ta hado mai koma da komai a tire ,... Dukkansu basa son zuwa aikensa , saboda sunsan ba,a wanyewa dashi lpy karshenta mutum yasha rankwashi ko mari, yamafi Aiken amira duk cikin su, a cewarshi tafisu hankali da nustuwa ,... Ajiye Tiren batool tayi a kan table din dake tsakiyar falon, murtike fuska tayi exactly yadda Aslam ke murtuke musu fuska , gyara tsayuwarta tayi ta fara irin tafiyan shi, d'akin mummy ta nufa cikin kwaikoyan irin tafiyanshi, duk ido suka bita dashi yuuu suna kallonta, fitowa tayi daga d'akin mummy tana ciccin magani kallon zahra tayi tace "kee mummy fa" tana 'kwai'kwayan muryan shi, aiko gaba d,aya suka kyalkyale da dariya jin yadda ta kaurara murya irin na bosawa wai ita tana kwaikwayan muryan Aslam, itako batool bako alamar murmushi a fuskarta ta dake abinta, qara kallon zahra tayi dake kwasan dariya , ta sake cewa cikin 'kwai'kwayan Aslam "ki kawomin abincina part dina yanzu "ta fada exactly yadda ya fada tana mai fita a falon cikin irin takun shi , amira cikin dariya tace"Allah yasa kina leqawa Ku had'a ido" aiko dai tana leqawa ta hangoshi , Allah yasota ya juya baya bai ganta ba , da gudu ta kwaso ta dawo ciki tana haki tace"wlh amira bakin kai shegen kaifi gare shi "dukkansu qara kwashewa sukayi da dariya zahra tace"yar banza ga tsoro ga mugun aiki" ...."eh din "batool tace tare da kinkiman tiren tayi hanyar waje don kai mai abinci,....kamal daya gama shan dariyar diraman batool ya miqe tare da kallon Asmah yace "sister anjima da yamma zaki rakani shopping , inason inma budurwata shopping , kuma kinga ni bansan kan kayan mata ba ," ya fada yana langwabar da kai yayi fuskan tausayi don kar tace baza taje ba , murmushinta mai narkar mai da zuciya ta sake tare da cewa "to ya kamal Allah ya kaimu anjiman, zan sanar ma mummy inta amince"... Amira tace "Allah sarki ya kamal zanje nima" zahra tace "nima haka ya kamal don Allah" harara wasa wa watsa musu tare da cewa "Allah ya kiyaye wa zai fita da Ku, yara sai shegen rawar kai kaman ana kadaku da ruwan hanji, Ku bari gobe bello ya kai Ku," ya fada yana ficewa a falon don karma su qara hada shi Allah,... Yana fita Asmah ta tashi tana kwaso shoki tana musu gwalo, filon kujera amira ta dauka ta bita dashi, kwasa tayi da gudu hanyar qofa , saiga mummy ta sawo kai saura kadan suyi karo Allah ya kiyaye, ...mummy tace"ya haka amira mekefaruwa "langwabe kai amira tayi tana turo baki cikin shagwaba tace "mummy gwalo fa take mana " mummy tace"gwalo akan me" zahra ce ta labartawa mummy abinda ya faru,... gwalesu mummy tayi da cewa "aikam dai kamal yana da gaskiya, inya kwasheku ai sai kusa aje ata nunashi ana dariya, tsabar rawar kanku gara dai yaje da Asmah don itace ma dan dama dama a cikin ku'......

Da misalin qarfe hudu da rabi yan matan mummy ne dukkan su a cikin makeken dakinsu dake part din mummy , daki ne babba mai dauke da madaidaitan gadaje har guda biyu, iri daya da kuma maka makan wardrobe mai qofa shida shida shima har biyu , da kuma madubi babba guda daya shaqare da kayan kwalliya na mata da turaruka masu tsada kala kala, wannan duk aikin mummy ne,...

Komai na dakin pink and milk colour ne idan ka cire fridge da kayan kallo da suka kasance baqaqe, hatta painting dakin pink and milk ne, dakin ya hadu sosai gwanin birgewa ,.

.duk da wadan nan kayan dake dakin still akwai space sosai a dakin, domin ba qaramin babban daki bane,dukkan su a kwance suke akan rug carpet kowa na abinada take so batool na karanta novel, amira da zahra na charting a wani WhatsApp group dinsu na yan mata, Asmah kuma da fitowarta kenan a toilet tana tsaye a gaban dressing mirror tana kwalliya ,saboda shopping din da zata raka ya kamal, ...hoda ta shafa tare da zizara kwalli a idanunta , sai maskara data qara ma dogon eyelashes dinta,jambaki ta dauka pink ta shafa kadan akan pink lips dinta , sai gira da tayi amfani da brush na tage gira ta gyara , kallon kyakkyawan fuskarta tayi a madubi, ita karan kanta tasan cewa ita kyakkyawa ce koda kuwa ba Wanda ya taba fada mata hakan , balle kuma tasha jin hakan a bakin daruruwan mutane,...fari tayi da kyawawan idanunta da sukafi komai fusgan mutum idan yana kallonta ,murmushi ta sakarwa kanta tare da cewa "idon mayu",a hankali yadda ita kadai taji meta fad'a, batool ce ta dago ta kalleta jin kamshin turarenta ya cika mata hanci tace"waike malama Ina zakije ne da yamman nan kike wani kwalliya "kasancewar batool bata nan sanda kamal yace zata rakashi shopping yasa bata San da maganar ba , amsa tayi da "zan raka ya kamal shopping ne wai zaije yama budurwa shopping ". miqewa batool tayi zaune tare da cewa "kutumelesi shine bazakice nazo mujeba kiketa shiri ke kadai, bari kiga na watsa ruwa nima muje" ta fada tana shirin miqewa ,Asmah tace "kinga malama koma ki kwanta kici gaba da karata novel dinki, don su O,O ma dazu ba yadda basuyiba zasu yace bazai je da su ba sun fiye rawan kai"ta fad'a tana kallon side d',insu zahra ,Allah yasa basu jitaba , hankalinsu yayi nisa , komawa batool tayi ta kwanta tana cewa "nayi shiru"taci baba da karanta novel dinta ,.....wani dogon rigan atamfa chiganvy mai kyau ta zura, bayan ta saka inner wear dinta , rigan irin mai pocket dinnan da ake yayine ya kamata daga sama daga qasa kumaya bude sosai, wani fashion Dan kunne da abun wuya ta saka, parking din gashinta mai tsayi da laushi baqi sidik tayi, ta kashe daurinta zahra bihari bayan ta saka abin daurin dankwali a ciki ,mayafi golden color ta dauka qaramin kasancewar akwai golden color a jikin atamfar, ta yafa , pos ta dauka mai siririn hannun cen da takalminshi , suma gold color ne sunji Stone sai shining sukeyi ,qara fesa turare tayi a jikinta , sannan tace yan mata sai na dawo mai zan siyo muku, zahra ce ta dago kai ta watsa mata harara taci gaba da chatting dinta , don har yanzu haushi takeji ance baza,aje dasu ba sun fiye rawan kai ,batool ce tace ki siyomin rufaida yoghurt mai banana pls sis, karki damu tace mata tare da ficewa daga dakin ganin call din ya kamal na sake shigowa wayarta.......

Zaune suke a compound din gidan a wani Dan rumfar bunu mai dauke da kujeru da table na katako mai kyau, Aslam ne tare da abokinshi Dr bashir , abokin shine tun na yarinta Wanda sukayi karatun boka Dana islamiyya tare a Jami,a suka raba jaha kasancewar shi Dr bashir pharmacy ya karanta shi kuma Aslam ya karanci businesses, Dr bashir baya qasar jiya ya dawo tunda ya tafi karatu qasar waje koda ya gama saiya kama aiki acan yakan zo ganin gida jefi jefi

fira sukeyi inda Aslam ke sanar dashi ran Sunday gobe kenan, su Abba zasuje nema masa auren zee, a gurin wan babanta alhaji abdurrahim, kasancewar yasan komai game da soyyanshi da zee din,

Zaro ido Dr bashir yayi yace"kace wallahi ". Harara aslam ya watsa masa tare da cewa "kasan na saba maka qarya, ai dole kace na rantse". Dariya dr bashir yayi, tare da cewa"ai abun ne da mamaki, ban taba zaton su Abba zasu sakko da wuri haka ba " tabe baki Aslam yayi tare da cewa" zasu sakko mana tunda wancen kinibabben tsohon yasa baki",Dr bash yace "amma baka da mutunci alhaji baba ne kibabbe" yace "kwarai ma kuwa, ko zaka je ka gayamai ne " bash yace "a,a ni bashi zan gayama ba daddy zan gayama", zaro ido Aslam yayi yace"ka rufamin asiri na samu daddy ya fara amsa gaisuwata da'ker" ......

Dai dai lokacin Asmah ta fito daga part din mummy ,cikin takunta mai Jan hankali , sai zuba kamshi takeyi, direct parking lot ta nufa inda ta hango motar ya kamal , ta bude gefen shi ta shiga tazauna , kamal ne yace "sister barka da yamma " a kunyace ganin ita ya kamata ta fara gaishe tace"yawwa ya kamal , sorry na shanyaka a mota ko, wlh naje yima mummy sallama ne ta aike ni kitchen, shiyasa na dade"murmushi kamal yayi tare da cewa "ba komai sister bari muje yamma naqara yi" ya fada tare da tada motar yayi ribass ya fice daga gidan,

Sai lokacin lokacin Dr bash da yayi mutuwar zaune tun fitowar Asmah ya sauke wani wawan ajiyar zuciya tare da juyowa ya kalli Aslam,....

Aslam Wanda kanshi ke duqe yana lallatsa phone dinsh, sai lokacin ya dago kanshi, tun fitowarta daga part din mummy kallon daya ya mata ya dauke kai, ganin ta shiga motar kamal, ta'be baki yayi ya daga kafadunshi alamar I don't care dinnan,, Dr bashi yace"yace Aslam kardai kace min su yan biyu ne suka girma haka " girgiza mai kai yayi yace"no nasu bane". "To amira ce "Dr bash ya sake tambaya "ba ita bace" ya bashi amsa Dr bash ya sake "cewa to wacece wannan mai kyau din". Hade rai Aslam yayi jin Dr bash ya kirata da mai kyau haka kawai ya tsinci zuciyarshi dajin haushin Kalmar, cikin dan hasala yace"kai dalla wani bin kai banza ne wlh,kan wannan qaramar mara kunyan rayinyar duk ka wani rude kanata jeromin tambaya kamar wani sabon dan jarida, maimakon Dr bash yaji haushin ihun da Aslam ya masa , amma sai ya kasa,qara qasa yayi da murya tare da cewa "Aslam Dan Allah wannan din itama yar gidan nan ce"

share shi Aslam yayi bai bashi amsaba , murmushi Dr bash yayi yana shafa girjinshi dai dai gefen heart dinshi yace"ta sace zuciyata a gani na farko , kyawunta, nutsuwarta , kamalanta , masu Jan hankali ne ,kuma insha Allah naga matar aure" . qara hada rai Aslam yayi yana watsawa bashir wani banzan kallon,zuciyarshi ta dauke zafi sai tafasa takeyi haka kawai, shi karan kanshi bazaice ga abinda ya tunzira shi ba, cikin bacin rai yace "amma wlh ka bani mamaki kuma kaji kunya bashir " miqewa yayi yana tartare wayoyin shi manya guda biyu dake ajiye kan table din wajen ,juyawa yayi ya nufi hanyar part dinsu, ko qala bai qara cema Dr bash ba, Shima bashir bai damu ba don yasan halin abokin nashi , yanzu haka zaice zai jawo mai raini ne gurin qannen shi , shiyasa ya hasala haka , miqewa yayi ya nufi motar sa ya shige ya bar gidan da qudirin gobe zai dawo ya samu mummy Dan jin wacece wannan mai kyau din.

Wani babban shopping mall sukaje , shopping sukayi sosai na kayan kwalliya da turaruka masu kyau da tsada , sai kayan kwalama dangin su chocolate, sweet, biscuit,dadai suransu,

Juyowa tayi ta kalli ya kamal dake tura mata Dan kwandon da take zuba siyayyarta a ciki, tace "Ya kamal mu barshi haka , wad'an nan ma nasan zasu birgeta. "

Kamal yace"kin tabbatar sun isa kuwa" tace "eh" yace "kodai mu hada mata da suttura haka". Tace"eh to saidai ko abaya" ok yace "muje shagon da ake saida abayas din saiki zabar mata"....

Kai kayan da suka saya suka yi akayi musu packaging dinshi kamal ya biya suka bar mall din,

R.U all store sukaje dake nan kan titin bosso road. Babu kalan abayan da babu a wajen,

Har tasa hannu ta fara dubawa dai kuma ta juyo ta kalle shi tace "ya kamal zo ka zabar mata kaga ni bansan size dinta ba , tunda ban taba ganinta ba "

Murmushi yayi yace "ki daukar mata size dinki, don inaga a tsayi da jiki zata kaiki"

Dan Jim tayi tuna dazuma data tambayeshi colourn skin d'inta dan ta zavar mata mai da powder, cewa yayi ta daukar mata irin wanda take amfani dashi Dan haskensu zaizo daya, yanzu kuma yace size din jikin su daya.

Kawar da wannan tunanin tayi tare da zaban wasu ubansun abaya's masu shegen kyau da tsada , kala biyar dai dai jikinta nuna mai tayi yace "sunyi kyau kuma daga gani ba qaramin kyau zasu mata ba" murmushi kawai tayi cewa yayi itama ta dauki abinda take so, girgiza kai tayi tare da cewa"ni babu abinda nakeso saidai naga irin turaren alhaji baba zan daukar mishi " "OK" yace,

Turaren ta dauka guda biyu ta daukar ma hajiya mama ma nata,yoghurt da ice cream din rufaida ta daukar musu ita da kawayenta, kamal ya biya suka fito,

Daidai parking lot wani mutum da dukkansu suka lura da bibiyarsu da yakeyi tun dazu , ya musu sallama , Amsa mishi sukayi kamal ya miqa mishi hannu sukayi musabaha, tare da tambayarshi lafiya dai ko,

Murmushi mutumin yayi yace"lafiyarce ta kawo ni, ni suna na Ali m Ali, inason nayi magana da sisterka ne inba damuwa "hade rai kamal yayi jin abinda Ali m Ali ya fad'a, yace "haba bawan Allah ya daga ganin mutane zaka tsare su haka akan titi baka San ko su waye ba , to wannan da kake gani matar aure ce kuma tare take da mijn ta" .

Murmushi Ali yayi yace "Mallam wannan ba matar aure bace kuma kai ba saurayinta bane, don naji da ya kamal take kiranka, don haka nake roqonka ka bani dama numbar wayarta kawai zan amsa , ya fada yana hade hannu alamar roqo🙏 pls ya kamal"

Qara hade rai kamal yayi yace "nan ba shine wajen daya dace kayi magana da ita ba, in kana son yin magana da ita gida zakabita,"

Kallonta tayi yace "muje" ba musu ta bude mota ta shiga ko kallon ali dake binta da mayen kallo batayi ba, kamal ya figi mota da karfi, furkar nan a hade kamar bai taba dariya ba, a zuciyarshi yace "haka kawai yazo ya batamin mood d'ina [1/31, 8:07 AM] Sis Aysha: 🌀 *DAMA TA BIYU* 🌀

By Aysher Nalado

*Ni na ma manta na yi shela, sai da y'an ba jira suka fara ankarar da ni, to akwai complete fa hajiyoyi ku zo mu sasanta ta pc, kafin alƙalamin ba zai gagara ba. ****

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol