Free chapter · Read without an account

Chapter 26

by Fatima Rufa'i Nasidi · AYSAM

(Blood sisters) Kasa daukar baqaqen maganganun da Moon take fada akan ayshar kwakwalwarsa tai duk da yasan wasu mugwayen halayenta da yawa tunba yauba na ayshan wanda yasan xata aikata duk abinda Moon din kecewa tana yimawa hudallah kmr yajja taji abakin hudallah amma se kwakwalwar sa tagaxa fahimtar meyasa dimple din taxama haka ashe apart from school kids datake bullying harta da yayarta ma xalunta takeyi acikin gida yasan yana matuqar sonta da qaunarta but yawa kansa alqawari son dayake mata baxe bari taringa fadawa halakar xaluntar wani dan Adam aduniya ba dan Adam dinma hudallah jinin jikinsa domin shida hudallah jiyake tamkar uwa dayace tai nakudarsu damuwarsa tatace haka itama damuwarta din tasace yasha qoqarin ganin taxauna atareda su agidansu sbd yajja take fadamusu ana maltreating dinta gidan AJ din, amma setaxe baxata iya nisa da mahaifiyarta ba wanda betakura mata akan haka ba sbd shima beson abinda xe nisanta shi da amminsa koda nasakan gudane, akwai shaquwa da soyayya tajini meqarfi tsakaninsa da hudallah wanda yayi alqawarin kawo qarshen tashin tashinar dake tsakaninta da yar uwarta matsawar yanason yay keeping dinsu both arayuwanshi, Moon kuwa ganin sameer din baida niyar tanka mata ko tayata xagin dimple din yasa tajuya tafice adakin tana yar mitarta qasa qasa, wayar sace tasoma ringing ya dauka yana duban mai kiran Aysh ce shin yadaga yace mata me yanajin haushinta shekara da shekaru kan abinda take ma hudallah yar uwarsa kokuma yasanar da ita irin axabtuwa dakewarta da yayi natsawon lokacinda basa tare,daga wayar yay daga daya bangaren yanajin yajja tasauke numfashi tana fadin, "SAM" Ayajja ta kirayi sunan nasa yamanta da duk wata damuwarsa taduniya ciki ko har abubuwan da moon tagama sanar dashi kan rashin kirkin ayshan,kmr tana gabansa take fadin "SAM are you OK?pls say something yajikin baffa kuna hospital ne xanxo naganshi Sam,Sam I'm worried Sam say something," smiling yay kmr yana gabanta kafin yace "Aysh lemme answer the first question before acigaba ko,irin wannan jera tambayoyi haka," turo bakitai kmr tana gabanshi ganin yana neman maida abin wasa,tace "SAAAAAAM," yace "Aysssshhh" yana kwaikwayon muryar nata,tace " Allah Sam nidai kafadamin ina kake inason naxo naganka natabbata you are not OK" Tarar numfashinta yay yana fadin, "I'm OK,I'm alright kuma jikinsa baffa dasauqi domin yanxun haka muna gidama ansallamemu," tace "are you sure?" yace "aysh karfa kifara rashin lpia sbd tinanin halin danake ciki i can hear it from you're voice," tace "Sam I'm just worried Moon nata kuka last night I'm scared bansan halin dakake ciki ba,kuma Moon ma seems sick yatake dftn tadaina kukan ko," aranshi wani irin sanyi yaji ganin tadamu da damuwar yar uwarshi wacca ko minti bata gamayi da debe mata albarka agabansa ba har yanxun yanason yasan asalin real side din ayshaa tabangaren halaye one moment tai acting kmr wata Lucifer the next moment you'll call her an angel wannan mix halayentan suna bashi mamaki da tsoro at the same time mutum nada halaye guda biyu dole akwai wanda take faking wanda banata ba abinda yakeso yagane kenan, haka suka dau tsawan mintina suna waya kafin suyi sallama tana mejadda da masa xefa ganta taxo duba baffa wanda dakyar yashawo kanta domin ayajja Moon tadau xafi akanta bekamata suhadu ba balle hudallah wanda yasan straight xatace yagoya bayan aysha akanta sbd shima yafisonta toh yana buqatar time wanda xe shirya yafuskanci matsalar datake tsakanin su biyun,koda wasa dimple bata kawo masa mgnr hudallah ba shima kuma hakan domin koda suke school bata taba mentioning tanada wata sister ba agabansa saidai brothers wato wanda take uba daya dasu sukadai yake jin labarinsu abakinta, hudallah dake labe bakin qofar tana sauraron wayar sameer din dayagama jin yataho daf daqofar yasa taisaurin komawa bakin rijiya tana xura guga daniyar xata debo ruwa, labulen dakin yadaga kafin yafito duka yana naxartar yajja take jan ruwan dakyar kana gani kasan rigimace kawai ba iyawa tai ba dagowa tai tana smiling kafin tace " yauwama ai naxata kobaxa ka fito bane shiyasa kuma rana nayi bamuda ruwan amfani," qarasawa gaban rijiyar yay yana sake naxarin face din hudallah tana masa murmushi shima mayar mata yayi yana tina kamanni tsantsar dasuke da dimple dinsa, saidai jar fatar da hudallah xata nuna mata shine yake boye ainahin kamanninsu da suke da mahaifiyarsu sak,tace "biyayena(Dan uwana) wannan kallonfa sekace yau kafara ganina tana dan tsokanar sa," smiling yay lokacin dayaga tadan dage masa gira alamar yadena kallona,yace "har wannan ma abun dakikaimin irin natane sak sede yafi mata kyau" cikin dan mamaki don bata kawo xemata maganar dimple din cikin sauqi hakaba sbd yajja taji bewa dimple din tata maganar,tace "wakenan?" tana kicin da ido,atakaice yace "your little sister," gaba daya annurin fuskarta ne yadauke tadauka after all bata Daren datai jiya tana sanar da Moon mugwayen halin dimple don tatabbatar xata sanar da sameer xataga qiyayyar dimple a idanuwansa amma setake ganin sabanin hakan,me hakan kenufi biyayanta bin bayan dimple xeyi kome ye domin baxata taba bari wannan damar data samu kaitsaye tawuce taba wajan ganin taraba dimple da abinda take so arayuwarta akaro nabiyu,muryarshi tatsinkaya yanafadin "hudallah she's young nagano bacin ranta axuciyarki dakwayar idaniyarki,amma kisani everything will be fine sameer is here for both you and aysh baxan bari daya yakuma cutatar da daya acikinku ba" yaqarasa yana janyo gugan daya debo ruwa yana tarawa ababban daron gidan naruwa, beqara cemata uffan ba sema da yagama jan ruwan nasa yadauraye qafafunsa da hannayansa yana fadin takoma ciki rana tayi shixai shiga yadanyi barci before akirayi sallar azhar,tanaji tana gani yashige yabarta atsakar gidan,takaicinsa ne yacikata kafin tace " inkasan wata aibakasan wata ba" tashige parlor,quryar daka takoma tana dube dube koxata ga Moon jin shiru yasanya tace "qila tawuce tahfix ne" tadau wayarta tana latsawa tana smiling. Dimple kuwa bayan gama wayarta da sameer still hankalin ta bekwantaba tanason tagansa tabiye masa kan tahaqura daxuwa ne kawai don kada yacigaba da insisting akan kartaxo din a safiyar yau kuma Alh AJ datashi tawagar suka sauka suma ajihar kano babban mother's eve yaya hauwa tashirya awani babban event center dake jihar kano din, wannan karon Alh dakansa yasaka muhsin da abokanansa su Arsal xuwa gurin party domin ayajja yakega yaya hauwa nabashi labarin ba abinda yahalarta a abuja anan abin magana xe xame musu ga dangin doctor bintu dasuka qaraso suma daga gombe kowa naji dakansa dakudi manyan motoci keta parking tako ina aharabar babban gidan qarshedai su muhsin ma da abokanansu se daya daga cikin guests din popsy dake nasarawa akabude musu tun yana nuna qin abun har yasoma sakin jikinshi bayan MUHASSIN yatabbatar masada inhar yaqi qara xuwa wani event din toshi xai shirya yahau matsayin sa kuma yasan bame ganewa amma tsananin kishin muhsin akan abinda yake nasa yasaka yahana MUHASSIN din xuwa kowana event wai yajera da wacca xata xama matarsa ina baxe yiwuba, qarfe biyar daidai Aysha tasato hanya tafito daga gurin event din tana haki domin dadan gudu gudu sauri sauri tabaro gurin kakarta tagurin mahaifiya daadar gombe kenan wacca tasata agaba tanata nunawa matan yan uwan babarta ita waiga dodanniya mara san xumunci tagama yatsine yatsinen fuskar domin gaba daya gurin bikin bemata ba al umma sunyi yawa duk dadai antsara abun yatsaru amma itakam takasa jurar wani tsayawa se angama wannan taron kafin taje taga sameer harta lace din jikinta cixonta yakeyi domin itada kayan gargajiya sam basa wani shiri kota saka bata wani jimawa take tubewa wai xafi, @360 tafigi motar meenah wacca dakyar ta lallaba ta tabiyota suka taho tanayi tana mita haka suka baro gurin taron yaudin basuyi kwalliya afuskar suba hakan yasa straight tasaita map din wayarta xuwa address din gidansu sameer, meenah kam bakinta kmr xefado harda yiwa dimple din wa'axin wai tacika xama clingy tacigaba daqin jin mgnr kowa akan sameer seya yaudare ta yadena sonta indai xata cigaba da nuna masa her world revolves around him, qiiiiii kakeji wata mota hummer qatuwa tasha gabansu da sauri aysha tataka burki tana dafe qirji, wani irin tsitsinkewa zuciyarta keyi sbd tsoro adaidai qarqashin gadar kabuga manya manyan motocin suka xagayeta meenah ba abinda take se zare ido kafin tace "dimple kodai kidnapping dinmu za'ai hakafa akeyi afinanai, dimple I'm scared dimple insunxo kifada musu ni babana bame kudi bane sojane me dan qaramun albashi,dimple ke suke nema you are Miss AJ kinsan babanki ne billionaire karki bari su hada dani" cikin tsawa da hassala da maganganun meenah din take fadin "would you shut up,let me think straight wadannan motocin securities din popsy ne, why are they following me like this?" taqarasa tana yunqurin bude murfin motar riqe hannunta meenah tai daqarfi tana fadin "noooo,karki soma haka nagani anayi awannan film din na terrorist sunyi shigar mutanensu don suyi drawing attention dinmu mufito su sacemu" tafada tanasake rarraba ido daya daga cikin manya manyan motocin akabude mutumin da takewa kallon sani yafito yana gyara xaman suit dinsa kafin dayanma yafito Mr bunyamin da uncle sooraj qanin mahaifinta baban xahra tamanta rabon data sanyashi a idanuwanta shine sukaxo sukai mata over taking haka dawani abun yafaru takasa tsayawa fa, ahassale tafito cikeda rashin kunya take fadin "meye haka xakuxo kuwani sha gabana meye xammaku meyasa kuke bina," wani mugunkallo uncle sooraj din kebinta dashi kafin yakoma motar datafi fito batareda yace mata qalaba meenah kuwa ganin yashigo motar yasa taisaurin fitowa amotar tana raba ido domin uncle sooraj irin murdaddun mutanen nan ne masu bantsoro yanada tsayi gajiki uwa uba ga baqi irin na yan asalin baqeqen niger dinnan, xaro ido tai tana sakin baki ganin uncle sooraj din yafigi motarsu sunmatsa masa yayi gaba da ita tajuyo kan Mr bunyamin wanda yakasa hada ido da ita domin kwarjinin datake masa irin yajja yakeyi gaban megidansa AJ haka yakeyi agaban ta,tsaki taja tana yarfar da hannu tace "what's all this Mr bunyamin explain yourself," yace "sir ne yabamu umarnin mubiki sbd you are not safe in this city daxu akai attempting sace yar uwarki xahra wanda kowa yatabbatar kece real target dinsu amma basuyi nasaraba aka kamasu so Sir yace daga yau kada kisake fita kekadai harse kin koma Abuja, yaturomu muyi escorting dinki xuwa duk inda kikeso,dan xaro ido tai waje tana fadin kmr wata mara gaskiya duk inda xani sekun bini i don't like this muje naji me popsy din xecemin" bude mata murfin babbar motar bullet proof yay tashiga meenah nabinta tana sauke ajiyar xuciya,ganin yajja convoy din motoci kibinsu abaya yasanya tasauya ra'ayi domin ba xataje gidansu sameer da wandannan qartinba masu xubin adawa tafirgita jama'a. Ababbar farfajiyar gidan tatarar dasu popsy dasu Arsal sunyi cirko cirko suna jiran dawowarta sbd yajja popsy yadaga hankalinsa bayan qoqarin kidnapping xahra da akai yau awajen gurin taron suka nemi dimple suka rasa Lilly kuwa saida tasha tafi hannun Arsal sbd ya tambayeta tace itama batasan sanda dimple din tafice ba ganinsu duk cikin damuwa yasanya jikinta sanyi , mr bunyamin yabude mata bayan motar tunkan taqarasa fitowa popsy ya isa da sassarfa yana rungumeta ajikinshi yana sakin ajiyar xuciya ahankali ahankali nutsuwarsa nadawowa gareshi, dakyar ya iya raba hug din yanajin kmr idan yasaketa wani abun na iya faruwa da ita, se shafa fuskar ta yake kmr yaudin yafara ganinta duk setaji tausayin mahaifinta yakamata ita shedace akan irin tsananin son dayake mata itama kuma tana qaunarsa baxataso abunda xeke daga masa hankali akanta dawannan shekarun nasaba, "popsy I'm alright kakalle ni ba abinda yacixar maka ni calm down" smiling yayi fadan ma dayaso yamata kan fitarta bada sanin kowaba se yaji yakasa se muhsin ne yafara balbaleta yana fadin "dakika fice batareda sanin kowaba gidan ubanwa xaki ke kullum baki son axauna lpy ko yanxun da hussain bega da motar dakika fitaba da shikenan bamusan inda kikaiba wakika sani akano wanda begun taron salon tsabar fitina kikadau mota kika fice ba tambayar ixinin kowa," ga mamakinsa seyaga ta toshe kunnuwanta alamar bama ta sauraron abinda yake cewa kenan tacusa kanta jikin popsy tana fadin "xefasa kaina yamun ciwo," kamo hannunta popsy yay yana wucewa bangarensa da ita doctor bint dasauran mutan gurin sukai kasaqe ciki kuwa harda yaya hauwa wacca tadauka ayaudin AJ xenuna koda kadanne cikin bacin ran da dimple tasaka sa aciki domin kafin xuwantan bawanda bewa tas ba akan yabarmusu amanar yarsa sunyi neglecting wanda har ta iya satar jiki tafita har sau biyu jiya dayau har mugwaye sun ankare, idan wani abun yasameta he won't spare wani cikinsu amma yar tadawo yakasa koda yimata kwakkwaran tsawa, daadar gombe ce da Jama'arta suka wuce bangaren doctor bint tanata sallallami kan abinda AJ din yakeyi bai kyautawa wato shibama tawacca aka satar yakeba tawacca akai niya amma ba aiba yake nuna damuwarsa, bangarensu yaya hauwa dai gutsiri tsomace taringa tashi kan yajja AJ din benuna kara sam sam akan sha'anin dimple din. A bedroom din popsy din taxauna tana bashi baki akan itafa batayi haka donta dagawa wani hankaliba musamman ma shi " she just wanna go and meet SAM xata dubo babansa bashida lpy," kafeta da ido AJ yayi yana fadin, "dimple" directly kafin yariqo hannunta, "sunan wannan yaron inason yafita abakinki tunkafin mubata nidakene,nataba nuna miki bacin raina," sosai taxaro ido waje tana kallon mahaifinta tunda take betaba mata magana da kakkausar murya irin hakaba,hannunta tadamqe cikin nasa kwalla natarar mata a ido dasauri yarintse ido domin idan akwai abinda yatsana wanda xe iya salwantar da dukiyar sa daya tara gabadaya akansa shine hawayen diyarshi dimple, kwantawa tai jikinshi tana fadin "popsy don't do this I love him,zuciyata namuradinsa cikin rayuwata popsy don't do this kasan kaidin rayuwata ne pops,baxan iya jurar katsana sameer ba" Dagota yay ajikinshi yasoma goge mata kwallar dake fitowa a idanuwanta kafin yace "don't love too much,because that too much can hurt you so much,kinsan baxan taba qin koda dabba kika kawo kikace kina soba,balle mutum dan Adam Princess dina ina tsoran kada sameer dinnan yay hurting dinki sbd idan hakan tafaru bashi kadaiba duk wani abu daya alaqantu dashi nima xanyi destroying nasa," yafada yana shafa gashinta tace " i promise popsy he'll never hurt me,he love's me too koda xaka tambayeshi dakanka," yace " dimple kinyarda na tambayeshi dakaina" dagada kai kmr wata yarinya yar shekara biyu tana turo baki cikeda shagwaba yace "gobe bayan daurin aure kice masa yasameni awannan address din" yafada yana sakamata wata takarda ahannu karba tai tana bude haqoranta duka dimples dinta na lotsawa kafin tace "saidai kuma kaga shine yake kulada dad dinsa baxe iya xuwaba har seya warke ko," yace "Allah yabashi lpy but inason before kuwuce UAE Yatabbatar yaganni indai yanaso nabashi chance," tace " xexo ma in sha Allah,popsy don't be too harsh on him dan Allah," smiling yay yana fadin " i will be harsh sbd kedin princess dina ce banason wanda yaxama prince ya sameki sbd kedin maitsada ce wanda xeyi treating dinki like a real queen nakeso nasamar maki," smiling tai tanajin soyayyar mahaifinta naratsa duk wani sassa najikinta shikadai ne mutumin dake fahimtarta yasan ciwanta yasan farincikin ta kuma ashirye yake yabatawa kowa sbd ita, bayan tafito daga bangaren popsy dole tabiya tadubo xahra domin koba komai sanadinta aka kusa saceta kmr yajja taji ana fada tamata sannu da Allah yakiyaye gaba. tawuce nasu sashen tana xuwa tatarar da Lilly tsaye gefen window tana tsumayin shigowarta tadago tana watsa mata harara kafin tace " wllh dimple kinbini bashin mari,yau sbd ke qaton gardincan yadaga hannu ya mareni sbd tsabar taurin kai daqinjin magana irin taki" zaro ido dimple tai tana qarasawa kusa da Lilly sosai tace "I'm sorry dear yaya Arsal dinne yamareki," "Meyasa xeyi haka," qoqarin shafa kuncinta take Lilly takauce tana furta "bakisan waye Arsal ba kenan har yau idan yayi fushi nidai ba abinda xance se Allah yasakamin" taqarasa tana hayewa kan bed,sosai dimple taji ba dadi kan abinda Arsal yayiwa Lilly din meye kuma namari banda tsabar mugunta,tana kallo Lilly tarage wutar dakin takwanta itakuma tafada toilet tawatsa ruwa me dumi tafito sallar da bataiba tafara gabatar wa kafin ta idar tashafa addua tamiqe tana tina dramarsu da meenah daxu lallaima yarinya nan movies suncika mata kai yanxun da kidnappers dinne ma tanads courage din cemusu su saceta subarta sbd ita babanta beda kudi se yanxun abun kebata dariya kiran wayar tane yadau hankalinta taduba dasauri tana sakin wani qayataccen murmushi sameer ne, tadaga tana amsa sallamar cikeda nutsuwa da zagin sautin muryar da take dashk,bayan sun gaisa tasake tambayarshi yame jiki ya amsa mata sundade suna waya kafin suyi sallama akan cewar se in Allah yakaimu gobe cikinsu bawanda yakawo mgnr hudallah musamman dimple datake ganin kmr hudallah bata isa taxama wani abu daxai iya dakatar da ita daga samun soyayyar sameer ba alaqarsa daban da ita shima kuma tasa da ita daban. Washegari gidan biki yakacame baqine suketa ciccidowa tako ina kowanne bangare sunyi busy kasancewar yaune za'a daura auren dan fari kuma babban da ga billionaire AJ da nafarko daxai aurar daurin auren yasamu halartar manyan mutane iri iri da yan siyasa kala kala kowa yana xuwa don taya Alh farincikin samun qaruwa cikin iyalinsa tun bayan incident din da yafaru da xahra ajiya da daddare Alh yaqara tightening security na ko ina agidan dakuma duk wani gurin da yasan jama'a zasu taru, sbd nauyinsu daya rataya akansa, ango kuwa duk inda kaganshi for the first time bakin muhsin abude yanata faman answer gaisuwar Allah yasanya alheri daga mutane mabanbanta uwa uba ga abokanan mahaifin sa dasuketa cika masa asusunsa da kyaututtukan su naban girma wanda yaxama kmr al adarsu ce tamanyan abokan nasa,duk dan wanda xeyi aure toh za'a tara masa dukiya taban mamaki,anyi taro lpy angama lpy wunin bikin guda biyu akai dana doctor bint da tawagarta wanda sukai ababbar harabar gidan AJ din sekuma wanda akai na uwar amarya ita kadai anasu gidan, qiri qiri popsy yahana aysha da aminanta xuwa wunin gidan mamadams sbd tsoran kada wani abu yafaru da ita afitar da xatai tagama xumbure xumburen bakin nata ba'asamu tasakko ba saidai mutanenta na IMPERIAL Suka qaraso su Samar da Abbas domin suna son suyi attending dinner din daxa'ai awashegarin rnr wanda su dimple da kudrat suka shirya domin waccan ta Abuja muhsin din besamu damar halarta ba,taso tace sameer ma yaxo gurin bikin amma setaga rashin dacewar hakan sbd tasan baxe iya tafiya yabar jinyar mahaifin saba sbd wani biki. Doctor bint naxaune tsakiyar wasu alajoji aminanta da kuma mahaifiyarta daadar gombe kenan fitarda gwala gwalan daxasuyi amfani dasu suje gurin taron tariyar muhsin din sukeyi wandsa za'ai a Abuja wani satin,daadar kefadin "niwaccar me nauyin nakeso yarnan sbd naga hauwa da qaramar ta inaso nanuna musu mune na Alh ba abinda Alh baxe kasheba don ya farantamana mudangin matarsa," qawar Doctor bint ke fadin "aikuwa dai daada yakamata bintu tanuna ma wancan yar uwar mijin nata matsayinta bakiga yajja take wani shashshama mutane qamshiba, wai ita yayar AJ abinda munsan uba daya kawai suka hada kuma dan ubadai dan ubane," doctor bintu ce cikin ixxa dagadara take fadin, "hjy salma ai nikuma nagama da hauwa tunda har tayarda diyarta tashigo cikin ahalina amatsayin suruka xataji yajja akeji alokacin da xansaka muhsin yatoxartar da yarinyar nan badai burinta takawo yarta agidannan tadandana arziqi ba xataga mexe biyo baya indai muhsin ne," daada ce take fadin "ga waccan sarqar bintu kidaukarma hudallah ita domin ita naga kayan arziqinnan bawani damunta yayi ba," dan murmushi doctor bint tai kafin tace "Allah sarki daughter daada komai na hudallah na musamman ne kinsan wadannan abubuwan ba damunta sukai ba", sallamar hudallah ce takatse mata mgnr datakeyi tadago cikin farincikin jin muryar diyar tata sanye take cikin wata tsadaddiyar atamfa ammata dinkin bubu kasancewar tanada dan jiki yasanya dinkin matuqar hawanta hannunta riqe da wayarta tana musu murmushi,gaisheda dattijan gurin tai duka kanta aqasa takasa hada idanuwa da kowa cikinsu hjy salma kefadin "a'ah fulani ashe kina tafe daga ina haka kmr kinsan maganar ki muke' murmushi tai tana rufe fuska da tafin hannu taqarasa gefen kakarta tana yimata ya gajiyan taro,tace "aini bakida abinda xaki fadamun nasaurareki hudallah,tunda kinnuna min dangin ubanki sunfimu agurin ki ace auren muhsin guda kikasa halartar kodaya aikyasa maqiya suyi mana dariya ko," kama hannunta hudallah tai tana fadin "ayi haquri daada natuba baxan sakeba",tace "dadina dake kenan akwai hankali da saurin fahimta ba kmr waccan tabuxuxun yar uwar taki ba,yanxun dai dftn kindawo kenan," dan dagowa tai tana kallon umminsu kafin tace "daman naxone kawai naimuki Allah yasanya alheri ne kafin kukoma," ummi miqewa tai don talura da kmr mgn abakin hudallah tace "muje ciki inji mekikeson cewa" dadi taji ganin saqonta a isa kwakwalwar mahaifiyar tata tamiqe hjy salma na tsokanar ta " ko suruka take da ita dabaxata iya mgn agabanta ba tunkan ma tace tabata dan nata take kunyarta" sunkuyar dakai tai tana bin bayan mahaifiyar ta xuwa quryar daka tana shiga kuwa tadatsa makulli tana sauke ajiyar xuciya,ummi tace "daughter lpy meyake faruwa keda kikace baxaki xoba meye ne kuma yacanxa miki ra'ayi" tace "ummi akwai babbar matsala" tace "me matsala kuma tamecece," tace "yarinyarnan mana Aysha tana neman Dakko ruwan dafa kanta," tace "what meyasamu dimple din," xamatai gefen gado tana jinjina kai,toh wnn kenan. Anyi dinner nagani nafada na auren muhsin da kudrat dangi da abokan arziqi sun samu halarta tako ina,agajiye su dimple suka dawo daga gurin taron kowannensu ansha rawa anyi shagali wanda baxe lissafu ba,amotar Arsal tabiyo suka dawo gida daga shi sai ita cikin motar suna tafe tana masa hira kadan kadan yana murmushi,yace " honey kinsan me" tace "a'ah saika fada" yace "baxan bari ki ringa gajiyarmun dakanki hakaba da aurenmu baxan yarda kiyi wannan wahalar ba" dan xaro ido tai tana kallonsa kafin tasheqe da dariya tana fadin "idan kaine mijin aise kahana yaya," yace " dimple wai don Allah menene atare dani wanda bakyason sa nasauya dimple I really wanted to make you mine," yafada adan sigar lallashi da lallami tace "yah Arsal pls nifa kunya nakeji idan kanamun irin wadannan maganganun kaifa yaya nane fa kuma i already told you nabawa wani xuciyana," yace " dimple shirmene waccan kisani baxaki taba auren wancan yaronba sbd ke ba sa'ar sa bace," tace "for real" tana tura baki "aini ba aure nacemaka xanyi yanxun ba we are just dating kanaji kuma we both have a bright future together sannan popsy already approved it so kaga bakada wnn yancin fadin i can't be with sameer," yace "dagaske popsy ya san kina alaqar soyayya dawani" jinjina kai tai alamun "eh of cause" cikin son canxa salon xancen yamaida wasa yace "toh ai shikenan ni imbanda abuna ma mexanyi dake wata yar qarama me qaton kai" kicin kicin tai da fuska tana fadin "nadaiji badai nasonka nima" duk lokacin data furta kalmar batasansa tana matuqar cixo da qona masa xuciya amma bayajja xeyi dole yacanxa taku yabiyo mata tawani salon daban dole tacigaba da trusting dinsa yaxamana yakasance shine bangon neman shawararta tunda yaga tayi nisabata taba jin kira indai akan wancan yaronne sameer. Qarfe bakwai nasafe sameer keta juyi atsakiyar katifar gadonshi yana runtse ido shin dagaske Aysha take mgnr data fada masa jiya da daddare wai popsy dinta nason ganinsa toh me hakan kenufi yasan alaqarsu kenan shidin he's not ready yafuskanci babban mutum kmr AJ amatsayin masoyin yarsa shida yasan ba xe taba aure yanxunba aurenma da Aysha taya xe iya riqeta meyake dashi daxai bata, yasan cewa xuciyarshi tariga data rudeshi tagama tunxurashi gurin fadawa gurbin dabai dace tafada ba yanajin har cikin xuciyarshi wnn kiran na AJ ba lpy ba qilama gargadi xeyi masa akan yarabun masa da yarinya kodai wani abu,but ayajja yaji mgnr Ayshan Yatabbata wani abun farinciki ne because she sounds excited, amma shigashi tun daren jiya yakasa koda rintsawa a idanuwansa akai kiran assalatu kuma yaje masallaci yadawo still barci yakasa xuwar masa sbd qarshen abinda xuciyarsa dabaxata gaxa dauka ba shine ace yarabu da Aysha besan itadin taxama wani bangare narayuwarsa ba saiyanxun dayake ga kmr kullum nisa take sake masa, xeje domin baxe iya qin answer kiran mahaifin Aysha ba amma kuma xuciyarsa baya tinanin tanada qarfin karbar abinda Alh AJ din xece masa. Yan biki sunsoma hada inasu inasu tun daren jiya kowa yafara kama hanyar garinsu gidan tsit kakeji yanmatan nata barcin gajiya, doctor bintu kexagaye atsakiyar parlor ta tana kallon lokaci,ita kadaice acikin mahaukacin parlor wanda yasha kayan alatu kai kace ba akano kake ba, Alh ne yashigo da dan sassarfa ganin kiran gaggawar datake yimasa tuntuni, batajira yaqaraso ba ta nufesa dasauri tana fadin "yauwa Alh kafito kenan," cikin dan mamaki yake fadin "bint lpy inada tarofa kin tsayar dani dftn dai kowa lpy ko," tace "Alh ba klau ba," yace "menene bint kisanarmin kona samu nutsuwa cikin xuciyata," tace "dimple ce," yace "what dimple meyasamu dimple din is she OK,ciwanne," riqo hannunsa tai ganin yana qoqarin juyawa yafice tace "ba abinda yasameta xedai samane," dagowa yay cikin bacin rai yana mata kallon tuhuma tace " dimple ce ke soyayya da wani matsiyacin yaro dan gidan qanwar baban hudallah kajifa mutanen nan kota ido basuda shi wai kmr yarka ce xatai soyayya da xuri'ar moddibo," cikin dan mamaki yake fadin "daman abinda kika kira kisanar min kenan kika batamin lokacina," tace "au Alh shi wnn abin bashida mahimmanci inace already yarinyarnan tanada miji ga yaran qawayena da dama wanda suke jira tabasu dama sugwada mata soyayya irin ta yan gata inda yake kwarya tabi kwarya kuma nidai indai ina raye baxan taba bari wata alaqa makamanciyar haka tashiga tsakanin diyata da dan walijam maqiyata cefa," tsaki Alh AJ yayi yana fadin sena dawo yajuya tana yunqurin fita sake dakatar dashi yawatsa mata wani mugun kallo yafice, amota ma kawai tsit yay yana tinanin harnawa ayshan nasa take da ake daukar mgnr wata soyayyar datake da mahimmanci kuma bint wato baxata taba canxawa ba ita lokacin data aura moddibon ai batasan kwarya tabi kwaryarba batasan maqiyanta bane gashi harta hada jini dasu, kuma baxata taba iya goge hakan ba yasan moddibo sosai duk da koda yana raye ba abinda yataba hadasa dashi sai takarar neman auren bint din betaba qullatarsa ko yariqe shi amaqiyi daidai darana daya ba koda kuwa bint tarabu dashi takoma masa yadau hakan amatsayin jarrabawar da Allah yarubuto masa kuma idan dai har sameer yatsallake jarrabawar dayake shirin yimasa toh tabbas baxe damu da mallakawa yarsa abinda take soba kmr baruwansa da duk abinda kowa xefada farincikin dayake gani a idanuwanta yakeso yacigaba. Aqofar katafaren farm house din AJ na railway Gra aka saukeshi yaciro kudi yasallami me napep din da ya kawoshi yaja napep dinsa yay gaba, qarewa qofar gate din kallo yake itakanta abin kallo ce kaikace da xinare aka qerata securities sekai kawo suke hular kansa yadan tura baya yanajin wani xaxxabi na keto masa tako ina,wani babban mutum ne yabude qofar gate din yafito fuskarsa bayabo ba fallasa yamiqawa sameer din hannu suka gaisa cikin mutunta juna yace " mishi yashiga Alh naciki yana jiransa yayi mamaki kwarai domin he's30 minutes earlier da yajja sukai da aysha xeje," bude musu gate din akai suka shiga sameer rashin nutsuwa tasama yakasa tsayawa qarewa tsari da haduwar gidan fargabarsa daya kada Alh yarabashi da yarshi awannan gabar, Saida suka tsalleke faluka uku kafin suqaraso wani madaidaicin parlor da Alh keciki shikadai sanye yake da wata maroon jallabiya wacca yay sallar la'asar da ita yana dandanna laptop din dake gefensa, da sallama mr bunyamin yashigo tareda sameer abayanshi idonshi aqasa yama kasa dagowa sbd kwarjini da cika idon da AJ yakeda shi a idanuwansa, har qasa yadurqusa ya gaisheshi ya amsa fuskarsa adaure babu alamar fara'a atattare dashi saida yay kusan minti goma atsugunne kafin Alh yabashi ixinin xama,qasan tattausan carpet din gurin yaxauna yana tattare babbar rigar data qaramasa kamala da cikar haiba da yasanya tamusamman, shiru sukai daga Alh har sameer din bawanda yace wani abu,Mr bunyamin ganin haka yasa yamiqe yana fadin "Sir bari naje daga waje," daga masa kai kawai yayi yana fita a parlor duka,Alh ture laptop din gefe guda yayi yana xubawa sameer din idanuwansa gaba daya kafin yace masa "meyasa kakeson dimple,? betaba expecting wnn question din daga garesa ba,besan sanda yaji xuciyarsa tayi qarfi bakinsa yafara furta, I love her for no reason,dan dage gira aj yay cikin mamaki yake fadin "those that make sense" Wani irin qarfin hali dakwarin gwiwa sameer yatattaro yana bashi answer da if you love someone for a reason,when that reason is gone,you're heart can change too,i love her for who she is I love her without any reasons sir," Alh sosai jikinshi yamutu da maganganun yaron tabbas idan har kanada dalilin son wani abu toh wata rana wnn dalilin xe gushe kuma wnn abin dakakeso xaka dena sansa sbd wnn dalilin yaqare wani irin sanyi da gamsuwa answer yaron tabashi amma afili benuna masa komai ba illama tabe baki dayay,kafin yace "naji wannan,kaidin yarone qarami dan shekara goma shatakwas nasan kokai waye nasan suwaye iyayenka nasan burin rayuwar ka,nasane blood group dinka nasan genotype enka,nasan lokacin barcinka nasan natashinka, nasan haxaqar ka nasan rauninka kuma ayajja naibincike akanka baka daya daga cikin yara marasa wayo daxasu sadaukar da mafarkarsu sbd soyayya mara tushe da asali ta yarinta irin wnn ba," Saikuma yanisa sameer yaji mamakin binciken aj akansa matuqa kenan yadade dasanin alaqarsa da aysha aj ne yadago yana fadin "inaso nabaka option guda biyu" yafada yana dan komawa ya kashingida yana rufe ido bayason abinda xeyi but yaxamana dole yay testing love din diyarsa nafari,nisawa yay kafin yace "xanbiya maka kudin makaranta ma'ana xandau nauyin karatunka gaba daya base kayi wiyar xana jarrabawar IGCSE ba wanda baka da tabbacin xaka samu gurbi nafarko idan ma kaxanan kenan,kana karatu xanbaka empty cheque karubuta iya adadin da xasu isheka har ka kammala karatunka a US sannan xanbaka share na dukiya metarin yawa adaya daga cikin companies dina dake can idan ka kammala karatunka,da sharadi guda daya daga kasa qafar ka kafita agidannan kamanta da diyata dimple bakai ba ita baxan amince da distraction arayuwar taba," xuciyar sa yaji tafara tsitsinkewa kmr ana dibo garwashi anawatsa masa a qirji yakasa dagowa yakalli Alh,anitse Alh ke noticing duk wani hali da sameer din yake shiga ya dorada "idan kuma kace xakai declining wnn gwaggwabar damar toh xan fada maka daya option din xan dauke yarinya ta nabar qasar da ita gaba daya kuma xansaka idan kacigaba da bibiyar ta abatarmun dakai da duk wani makusancin ka I'll make sure nayi destroying everything you work hard for," sai alokacin sameer ya iya dago kai yakalli Alh kwalla nasakkowa daga idonsa yasa hannu yana rufe kuncinsa gaba daya yayi jajir, Yace " kaya haquri Alh baxan iya karbar offer dinka ba sbd nasan matsayina nasan mutuncin kaina dana iyayena,kaidin mahaifin aysha ne kuma natabbatar duk abinda xakai baxaka taba cutatar da rayuwarta kotawa ba sbd nasan irin qaunar dakake mata,xanje nacigaba da rayuwata kmr yajja nasaba baxan tabaso nai sanadin daxai raba Aysha da farincikin ta ba wanda nasan kaine Alh,alh koda baka kafamun wadannan sharuddan ba idan kabani umarni nime daukane sbd ina mutunta ka amatsayinka na mahaifi ga wacca nake qauna,riqo qafafuwansa sameer yayi ahankali cikin ficewa hayyaci domin shikansa besan soyayya dayake yiwa Aysha yakai irin wannan matakinba, I can't do without her sir,falling in love with someone like her was the best thing that ever happen to me,there is no price to level my love for your daughter Sir,all I need is for her to stay happy wanda tabbatar kana bata dukkan farincikin datake buqata,I wish her all the best" yafada yana miqewa,sosai zuciyar AJ takarye sbd yaga fiyema da abinda yakeson gani atareda sameer din irin wutar qaunar datake ruruwa axuciyarsa nafargaban one sided love da yarsa keyi yakau,wannan yaron yasiye ba iya xuciyarsa ba hatta da ruhinsa yatafi yayi imanin bawanda xeso dimple din kmr sa bashida wayon daxa ace kodan abin duniya kowani abu yakeson yarinyar tabbas xe tsaya musu sumorewa rayuwar soyayya da quruciya su sameer yagama faranta masa xuciya ayau, juyawa yay xefita a parlorn duka kama handle din qofar yay xemurda yaji anturo tawaje kadan yarage basu hade dajuna ba dimple ce kmr wacca aka koro tana haki tana murmushi kmr wacca akebi dasauri tadan juya tana cigaba da murmushi sega Mr bunyamin yabiyota shima hakin yake Allah sarki bawan Allah tasaka shi gudu da girmansa, Alh ne yataso yana fadin "subhanallah lpy mamana mekikeyi anan? daga ina" ido tadago tana maida numfashi kafin chak taji bugun xuciyarta yakusa tsayawa ganin sameer tsaye idanuwan nan nasa blue sun qanqance sunyi ja hatta da face dinsa tayi wani jajir abinka da jar fata kana kallon sa kasan yayi kuka,wani irin tsitsinkewa taji xuciyarta nayi cikin dan kwanakin datai bata ganshi ba setaga kmr anqara masa kwarjini da dangirma ma a idanuwanta,cikin sarqewar murya tamaida dubanta ga popsy wanda ke tambayar Mr bunyamin lpy? Yace " hjy dimple ce taxo kuma kacemin kar abari kowa yashigo nasanar da ita haka setace toh" ina juyawa ta shammaceni takwaso aguje shine nabiyota danna dakatar da ita nakasa cimmata saida taqaraso aimun afuwa Alh," popsy yakalli dimple cikin fada yake fadin "kebadai kyason kulawa dakanki koh princess meyakawo kinan bana hanaki gudu ba kaikuma Mr bunyamin kmr wani yaro meye nabiye mata data riga taxo base kabarta tashigo ba kasandai banada uxuri aduniya wanda xehanani ganin dimple koh," Mr bunyamin cikeda girmamawa yake fadin "I'm sorry Sir baxan sake ba in sha Allah," yace " bakomai jeka kawai" yana masa nuni da inda yafito sunsun yawuce abinshi, kan dimple yakoma xeyi har xemata magana yafasa ganin irin kallan datake masa na tuhuma, kafin cikin sarqewar baki tace " popsy meyafaru anan mekayi wa sameer,popsy he cries meka fada mishi" tana qoqarin saita numfashi kasa cemata komai yay ganin xallar qaunar yaron nan cikin idanuwanta ta juyaga sameer tana fadin "meyacema tell me sameer kayi magana" tafada cikin qaraji,tana jijjiga kanta daya sara mata tafaraddaya,popsy ne yaxo xe kamo hannunta taai saurin kwa cewa tana fadin "meka fada mishi pls say something popsy," kama hannunta yakuma yunqurin yi tafuxge tana qarasa shigowa tsakiyar parlour kafin tajuyo tana facing dinsu duka su biyun tace "tun agida nakejin something is wrong cewar i should come shiyasa na lallaba yaya Arsal yakawoni nan din amma mexan gani haka kunmin shiru duka," sameer dayake kallonta cikeda tausayawa shauqi da zazzafar qaunar ta nafixgarsa jiyake yi kmr yaqarasa yay hugging dinta ya rarrasheta yakwantar mata da hankali amma ina baxe iya ba baxe iya bijire ma wnn dattijon dake gabansa ba sbd duk duniya yasan bawanda yakaishi qauna da sanin ciwon dimple kuma idan dai har kasancewarsa arayuwar dimple xexama barazana ga alaqarta da mahaifinta tabbas xebarta bari nahar abada juyawa yay xe fice "sameer" yaji anfurta cikin kakkausar murya yadakata yana juyowa ,popsy ahankali yay masa nuni da yadawo gefensa kmr ba laka ajikinshi haka yafara takowa yana karanto duk wata adduar dake fadowa cikin ransa,beyi auneba kawai yajishi jikin popsy yarungumeshi yana shafa masa kai ahankali yana murmushi qamshin turaren popsy nashigewa kowana saqo da lungu nacikin xuciyarsa yana haifarmasa dawata nutsuwa da kamewa dimple ce dake gefe wani irin smiling tasaki tana kawar da duk wani xargi data darsa na popsy xe iya wulaqanta sameer cikin zuciyarta tasan popsy dinta he's a good man yana son happiness dinta taqaraso itama tana fadin " oh popsy wato kasamu son kamanta da daughter ko nima ayi hug din dani" yaxama yarungume sameer tagaba itakuma tarungumeshi tabaya abun gwanin sha'awa kafin yadago yana kallon sameer din kwarjinin sa nadada cike idonsa yay saurin qasa dakai,yace "sameer nabaka amanar xuciyar diyata aysha nahar abada,nagasgata qaunar dakake mata kuma ni ina qaunar duk abinda takeso dagowa yay farinciki yakasa boyuwa afuskarsa," Alh ma murmushi yake masa kafin ya sakko da bakinsa daidai kunnan sameer tayajja aysha baxata jiba yana fadin "saura kuma kasanar da ita barazanar dana maka just pretend like nothing happen daman ina gwada kane kuma kacinye jarrabawar" wani kyakkyawan murmushi yasubucema sameer besan awana gurbi xe saka farincikin dayake ciki ayanxun ba gwadashi ma'ana duk abinda yafada baya nufin har hakan axuciyarsa popsy ne ya gyada masa kai kamar yasan meyake saqawa yace "kaine xabin dimple kuma xabin dimple shine na popsy ko" yafada yana kallonta dan bata fuska tai kafin tace "popsy meye ka rada masa aina ganka banjiba kafadamin" yajja tai maganar yasa daga shi har sameer dariya lokaci daya,ta tabe baki cikeda shagwaba take fadin "nidai sekun fadamun mekukace popsy yakalli sameer yana furta kaji rigima ko wnn sirri ne tsakanin uba da danshi ko" yakama hannun sameer xuwa dining area madedeci na parlor shidai har lokacin yakasa sakewa dimple ce tabiyo su tacigaba wa popsy tabaran nata yana biyemata yana qara kunnata,daga can yace "taje takira masa chef a kitchen yakawo mishi coffee," tace " toh " tana miqewa tana kallon side din sameer suka hada ido ta farfara masa idon tai gaba dasauri yaduqar dakai kmr yanitse dan kunya ganin popsy na kallonsu ita aysha baruwanta,batasan wnn ba.

AYSAM Its Fatoums Passion's Love,passion,betrayal,romance,hatred and power between two different world's.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.