Free chapter · Read without an account
Chapter 27
(The acceptance) Parlor shiru kake ji se sanyin AC din dake ratsa ko ina a parlor wanda yagauraya da daddan turarurrukan da aka kunna na room humidifier da ake amfani dasu a parlor koda AJ ba maxauni bane koda yaushe ma'aikatan gidan cikin gyara farm house din sukeyi sbd kusan indai AJ na kano nanne gurin hutun sa anan yake xama in stress yamasa yawa bakowane yasan wnn gidan ba ma se ita dimple din da bawani guri da popsy kexuwa yalabe inbayason jama'a wanda bata saniba sbd wani lokacin da ita yake tafiya suyita rayuwa su biyu abinsu batareda damuwa dakomai ba, sameer AJ yakalla kafin yace "yanxun sameer kaima tareda dimple kake ko kuna matakin kammala high school," yace "hakane" yana gyada kai kansa aqasa murmushi yay yana furta "Sameer I know everything about you all the part time job's dakake yi nasansu" dagowa yay yana kallonsa cikin dan mamaki se kuma yatuna ai aysha xata iya fada masa duk da ita kanta bawai komai tasani nasaba har yanxun komai na alaqarsu gani yake yana faruwa cikin wani irin sauri wanda Allah kadai yabarma kansa sanin dalilin wnn gaggawar ace har sunkawo stage din babanta yasani saura nasa iyayen,murya Alh yatsinkaya yana furta " sameer kasan part time job's bazasu riqemun yarinya ba ko" kunya ce yaji kmr xe nutse agurin wai baban Aysha kemaganar riqe masa ya aurefa kenan at his age ina his not ready,yace "sameer kudin yarane har yanxun kuma naga sincerity cikin idanuwanku gaba daya akan san dakukema juna,' yadago suka hada ido yamai murmushi kafin yadora "kaida Aysha have a Bright future together bi ixnillah,sbd akwai quruciya atare daku alqawari daya xakumin kaida ita cewar soyayya baxata saka kuyi getting distracted daga karatu,sannan xanyi magana da mahaifinka idan munga yakamata mukai alaqar ku next stage ma duk xakaji" wani daram zuciyarsa tace " yasan bashida matsala da baffa SAM AMMI,Ammi yake ji ta irin tashin hankalin daxe fuskanta idan taji labarin wnn soyayyar tasa," yace "toh alh duk yajja kace but me and dimple ai bayanxu ba koh" yafada yana dan langabar dakai,sosai Alh yake hango quruciyar da xa axuba awannan soyayyar duk da ya yaba da nutsuwar sameer adan xaman dasukai yafuskanci bashida rawar kai da gigi irin na dimple da qawayenta he's very calm, yace "ba yanxun ba sameer abinda nakeso guda daya ne kai qoqari kasamu abinyi katsaya da qafafuwanka kafin ku kammala high school kuna kammalawa xanyi muku baiko" sunkuyar dakai yay yana smiling shima Alh yakasa dena murmushi haka kurum shauqin abin keshigarsa yanason yaga auren diyarsa dimple haka kawai yakeji idan becika wnn burin nasaba kmr wani abu xaifaru dashi mara dadi daya kasa gane menene,dimple ce tashigo tana rafka sallama tareda chef Aiman yana riqe da qaton tray yajero copy da light snacks ya ajje saman dining din, "thanks" Aysha tace bayan ta ajje ma popsy americano dinsa datasan yana matuqar so kallon sameer tai tana furta "kaifa wanne kake so," bedago yakalleta ba sbd bayason tasashi rashin kunyar kafeta da ido gaban babanta amma yanajin idanuwanta akansa seda tasake maimaita tambayar sannan still kanshi aqasa yake "fadin I'm OK," tadan qarawa idonta girma tana fadin "popsy kajiko wnn fillon kai yake kunya fa" tafada tana ajje masa hot cappuccino agaban shi tana furta "it's my favorite try it," tana saka griddlecakes saman plate din da chef ya ajje gabansa tana furta "oya maxa kacinye yanxun," popsy riqe baki yay yana mamaki yau dimple dinsa ke serving plate din wani ba nataba tabbas yaga sauyi sauyi mafi girma arayuwar diyarsa wato nuna kulawarta gawani wanda bashi ba, ahankali sameer yadago yana mata wani kallon qasan ido itama shitake kallo tadage masa gira daya tanai masa alamar yaci, dauke idonsa yay yana furta " you start first" popsy yi yayi kmr bega mesukeyi ba yana tina tasa quruciyar yana murmushi,dimple ce tafara kai cup din baki tai sipping ahankali tana furta "popsy wato coffee din chef Aiman namusammman ne ko shekara nawa xanyi ina shan cappuccino bayamun kmr na Aiman," tafada tana sha tana limshe ido popsy ma sipping coffee dinsa yake ahankali kafin kwatsam yace "sameer ka kwasan ya sheik ubaydullah shi din kmr yaya yake gurin mahaifiyar ka koh," smiling sameer yay yana tinawa da farin dattijon cousin din su ammi ne kuma wayake uwa daya uba daya da mahaifiyarsu Aysha,yace " eh Alh nasanshi" yace " Allah sarki agurinsa na nemi auren mahaifiyarsu dimple karo nabiyi bayan dan uwan mahaifiyarka moddibo yarasu allah yajiqan rai kakwasan cewar dimple dakai kunada alaqa tabangaren mahaifanku mata," ya girgixakai yace "xumuncin xamani kenan kaga ita hudallah duk tasan yan uwanta sbd mahaifinta da mahaifiyarta tuwona maina akai yan maxa xar suke haka walijam da bint kobaka taba saniba kaima,sudin aminan junane nagaske tun quruciya" yagirgixa kai yana furta "shidai yasan ammi tace hudallah yar dan uwanta ce bata taba cemasa komai akan mahaifiyar ta ba" yajinjina kai yana jaddada rashin xumunci irin na bint bawani dan uwanta na xumunci datake ja ajiki idanba mahaifiyarta ba bata da yan uwa dasuka fito ciki daya duka yan uwanta yan uba ne shiyasa tunda ta aura me arxiqi kodacan tafi qarfinsu kallon kowa daidai take balle yanxu da ita kanta attajirar kanta ce, ya sheik yayan ta ne ubansu daya shine babban malamin da Alh ke tambayarsa shawara akan abubuwa da dama narayuwarsa musamman bangaren iyalinsa,idan abu yashigema Alh duhu nan rugarsu yake xuwa duk da yayi yayi yadauke sheik din daga rugar yasiya masa gidaje kala kala acikin garin gombe da wajan ta amma yaqiyarda yadawo seda Alh yagajiya yasiya masa mahaukacin fili yagina masa qaton gida da babbar makarantar tsangaya dayake gudanarwa wanda yakeda tarin almajirai cikin makarantar, dimple haka kawai taji ranta yasoma sosuwa meyasa popsy xetasa sameer sufara labarin gombe inda tatsana dangin ummi da hudallah dabata santa ko sunan gombe tatsana a anbata domin bata manta irin axabar data sha acandin mafarin qiyayyar ta da yar uwarta hudallah har yau idan tatuna setayi kuka abun yafaru shekaru biyar dasuka wuce amma har yanxun tanajin xafinsa cikin ranta coffee din takesha da zafi zafi batai auneba tai choking (kwarewa)tafara wani irin tari cikin tashin hankali popsy yamiqe kan yaqarasa kanta sameer yariqeta gam yana furta "subhanallah aysh, sannu meyasameki aysh are you OK sannu sannu" tari takeyi ba qaqqautawa yafara bubbuga bayanta saida duk yabi yarude gaba daya popsy ne yamiqo masa ruwa yana furta kabata ruwa koxe sassauta girgixakai yay yana furta "she can't drink water," daga nan beyi wata wata ba kawai yamiqar da ita hawaye daya nabin daya akuncinta tama kasa magana,yariqeta around the waist yana pulling inwards and upwards above her belly button Allah daya temaka guntuwar rigar t shirt ce jikinta da dogon wandan plazo, wani irin dogon numfashi takeja lokacin da yake Thrusting abdominals dinta popsy dai yatsaya yana kallonsa ahankalin tarin yatsaya chak tana maida numfashi sameer ma sauke ajiyar zuciyar yake yana sauke hannunsa daga jikinta luf tai ajikin shi kanta nakan qirjinshi se jera mata sannu yakeyi, Dimple sannu ko lemme call a doctor se alokacin sameer yatina a inda suke kuma a yanayin dasuke sannan tareda wa suke wata irin kunyar popsy tasake lullubeshi yabude idanuwansa ahankali yasauke kan dimple da har lokacin tana ajikinshi ne popsy yaji yana furta "it's an emergency kayi sauri she choked,ina railway farmhouse," yadatse wayar yana qarasawa yatallafo aysha daga jikin sameer yana furta "mamana are you ok" kai kawai take iya daga masa yace "bari kawai mutafi hospital I can't wait" dasauri ta girgixa masa kai tana sake maida numfashi kafin cikin sanyi ta iya fadin "I'm OK popsy," ruwa sameer yadauka yana fadin "xaki iya sha yanxun" popsy ne yakarba yana samata abaki aiko tasha ruwan dakyau tadago aranta tana furta "dimple kije ki kashe kanki sbd baqinciki na hudallah itakam batada asara sema dadi daxata ji," miqewa tai muryarta nadawowa daidai tana fadin "bakune kuka dameni da hira mara amfani ba kuka saka nakware" tafada tana tabe fuska, sameer da mamaki kan fuskarsa yake kallonta mahaifin nata take cewa yadameta da hira mara amfani inshi tace she sa antane but be kamata tafada ma popsy hakaba ai koba komai yahaifeta, kallon popsy yay wanda sarai yagane inda tadosa rigima takeso tayi masa kan yayi xancen hudallah da sameer, dawo kixauna yafada yana gyara mata kujerar data miqe akai kafada tamaqe tana tura baki kmr qaramar yarinya tace "a ah baxan xaunaba tunda......" bata qarasaba sukaji anturo qofa Mr bunyamin ne riqe da brief case irin ta likitoci bayansa wani dattijon doctor sanye cikin baqar tom suit me kyau da tsada, qarasowa sukai yagaisa da Alh yana furta "long time no see Alhassan Abu jandal," murmushi shima yay yana sakin hannunsa dasukayi masabaha yace "Dr Aryan kadai gujemu ka barmana Sahara," yace "toh ya xa aiyi Alh aikasan munamu kasuwancin ba irin naku bane," yaqarasa yana kallon dimple "ba magana princess kin kwacemin mata koh," smiling tai tana fadin "barka da yamma uncle doctor" yace "xomu gani garin qaqa kikai choking" yana mata nuni data qaraso inda yake tace "uncle doctor bafa Seka duba niba sameer yabani first treament na abdominal thrust so you don't have to worry," qarasawa yay yana bude case dinsa da Mr Bunyamin ya ajje masa ya dakko wani abun gwaji yana furta "nida ba injection xanmiki ba meye natsoro I just wanna make sure numfashinki yadawo daidai" kallon popsy tai tana qara yamutsa afuska domin itada Dr Aryan din mijin doctor sahara bawani shiri sukeba kmr yajja suke da matarsa sbd ko bacin rana idan takwanta sahara bata gari shiyake dubata kuma burinsa yay mata allura shiyafi ganin sauqinta akan magani kuma ga zafin hannu gareshi ba kmr sahara ba ko allura xatai mata seta soma lallashinta tayita bata baki sannan take yarda ayi mata, qarasawa tai taxauna gefen kujerar da ya ajje case din nasa sameer harde hanuwa yay yana kallonta, haka doctor yagama duddubata yana furta "lallai ja'ira kyasamu bakin magana sbd qalau kike" yajuyo yana furta "Alh ai already abinda xanmata anmata" yaqarasa yana maida kayansa ciki,Alh yakalli sameer yana fadin "all tnx goes to him," "Dr Aryan meet sameer S Fulani Dimple's" seyadan tsaya yana smiling dasauru takarbe tana fadin, "boyfriend he's my boyfriend uncle doctor," dariya both AJ da Dr Aryan sukai Dr Aryan yan furta "Dimple,dimple so he's your boyfriend" yaqarasa barin da sameer yake yana miqa masa hannu akwai wayewa me tarin yawa atattare da Dr Aryan din wanda baruwansa da shiga rayuwar wani balle yatambayi meyasa dimple keda boyfriend da qananun shekarunta,yace "nice to meet you Mr sameer" yana miqa masa hannu don suyi masabaha shima nasa hannu yamiqa suka gaisa yana masa murmushi shi abin mamaki yaketa kalla anya kuwa xe iya rayuwa da aysha duniyar sa datasu akwai banbanci meyasa so xemasa haka tsorone yake neman darsuwa cikin xuciyarsa tsoron da tinawa da soyayyar dayakema ayshan yay saurin dokesa,muryar Dr Aryan yadawo dashi daga dan tinanin daya lula, "you saved her life Mr sameer we are greatful for that" "domin datasha ruwa kmr yajja mutane dayawa kebama wadanda sukai choking ruwa a situation dinta she would have hard a serious attack," Aj ne yaqaraso yana rungume sameer, "I'll forever be indebted to you banidaa abinda xanbaka sameer kaidin kaxama savior din princess dina" yadago yana dan bubbuga kafadan sa yana furta "Allah yasaka maka da mafificin alkhairi nan yake bama Dr Aryan yajja abun yafaru har saving dinta daga ruwa dayayi yake fadama Aryan din yajinjina irin soyayyan da sameer din kema ayshan duk da ya lura shi ya iya danne abinda yakeji sbd kunya da yakana irin tasu ta fulani sabanin aysha wacca tatashi cikin sangarta da tarbiyyan bayyanar da duk wani abu datakeji akan koma waye ko so ko qi intanayi bata iya boyewa," Saida akai kiran sallar magrib sannan Dr Aryan yay sallama da AJ yatafi sameer da aysha kuwa ganin AJ dayasamu tsohon aboki suna tattaunawa aysha tajashi wajan farm din gidan tana nuna masa shuke shuke kala kala suna hira cikin nishadi da qaunar juna suka fada ma juna irin kewar juna dasuke abindai gwanin birgewa, kiran sallar ne shima yasa cema aysha xewuce suka koma ciki don yay sallama da popsy aikuwa popsy yace "yabari suyi sallah tare se ayshan tarakashi" aikuwa se murna takeyi ance xata raka sameer,yace "bake dayaba keda Mr bunyamin xakuje" turo bakitai tana fadin "pls popsy I'm not a kid," yace "I know for security reasons inkuma baki xuwa dashi seki xauna" dasauri tagirgixa kai tana fadin "xataje xataje" bayan sun idar da sallar cikin sahu daya a daya daga cikin qananan masallatan dake unguwar dakyar AJ yasamu fitowa daga cikin jama a maqota dasuka dan sassansa duk yawanci masu hannu dashuni ne se barka akemasa na auren muhsin wanda basu samu halarta ba ana masa fatana alheri, hannunsa riqe cikin na sameer daya kasa sakewa har lokacin suka shigo shibesan AJ ba idan har yace yakarbi abu ra ayinsu da halayyarsu kusan iri dayane da dimple da xuciya daya yaji qaunar sameer tasamu gurbi axuciyarsa sbd yar kulawar dayaga yabama diyarsa awannan rnr darajar sameer tahau cikin xuciyar AJ da bawanda ya isa ya kankareta har numfashinsa na qarshe, duk da sameer yayi yayi subar rakiyar xe iya tafiya dakansa qiyawa sukai dimple harda saurin shigewa mota tana fadin "kanka akeji," sameer yakalli Alh yafaramai godiya bisa amince masa da yay yacigaba da dating dimple sannan da irin karamcin dayay masa yamasa alqawari in sha Allah xe kula da ita yariqe alqawarin qaunarta duk rintsi duk wiya until infinity, yaqarasa yana furta "Alh my love for her is eternal,she is my eternity,till jannah reunite us I'll always be there for her,baxaka taba dana sanin amincewa dani ba in sha Allah" sosai Alh yakeji yacike wani gurbi mefadi na rayuwar dimple daya dade yana so yacike,kama hannunsa yay yana furta "not Alh, call me popsy kmr yajja yarana kekirana your part of them now," yaqarasa yana wani bright smile,shima murmushi yamayar masa yana fadin "popsy,popsy" yamaimaita,popsy yace "jeka karkuyi son karkuyi dare," gaban motar yashiga yana kallo aysha, na hararansa wai yadawo baya inda take kawai yasaki wani smile da ita kadai take gane ma anarsa alamun kunya yakeji baxe iya xama kusa da itaba agaban popsy, Mr Bunyamin ne ke driving suna tafe motar tai tsit kafin aysha tana matso gaba kmr wata qaramar yarinya tadafa kujeran daya ke tana fadin, "wai sewani shareni kake yi tun daxun ko," yadan waigo tayi daf dashi da yana iya shaqar qamshin sassanyan turaren jikinta mai dadin gaske,yace "sharri ko,niyaushe na shareki," tace "aikasan ba sharri nake makaba wai kai kunya koh toh indai popsy ne seka gaji kadena dakanka," Yace "hakadai kikace nibaxan iya rashin ta ido gabansa ba," tace "ainasani kunyarshi kakeji ku fulanin nan duka gulmanshi...........," saikuma tai sauri ta toshe bakinta tana dan cije harshe alaman tasaki baki yace "ehen qarasa mana gulmammu ko," yafada yana dage mata gira daya dan basarwa tai tana ja dabaya tace "nifa ba haka xanceba karka fassarani," yace "1-1 nima bayanxun kikace ina shareki ba kuma inkin xagi fulani kema your part of them don haka harda kanki," turo bakitai gaba tana furta "nidaiba bafulani bane ba,meya hadani daku," yace "your mom she's original fula,right,even your sister your part of us too," batason yagane rashin jituwarsu itada mahaifiyarta tun yanxun badan tasan abinda take badaidai bane a'ah saidan kawai tanajin takaicin sanar masa wacece mahaifiyarta, murmushi kawai tai tana dan canxa maganar lokacin datake fada masa xasu wuce UAE hutu kuma kafin su dawo qila sai anyi resuming school duk jikinshi yay sanyi yana tinanin irin yajja xeyi kewarta, agaban Mr bunyamin suke firan soyayyar su ayi fada ashirya haka abunnasu gwanin birgewa harsuka qarasa anguwar su sameer din bayajja aysha batai dashi kan akaishi har qofar gidaba yaqi sbd yana gudun surutu yafison shi dakansa yafadawa iyayansa maganar alaqarsa da Aysha basuji bakin wasu ba kuma unguwar tasu akwai yan sa ido nagaske, shiyasa yace su saukeshi bakin titin rumfar shehu haka suka sauke shi saida suka shafe kusan rabin awa gefen titi suna hira kafin ya lallabata dakyar tashiga mota suka juya xuwa gida saida motarsu tabace sannan yajuya yanufi hanyar nasu gidan cikeda nutsuwa yake tafiya har yaqaraso bakin layinsu gurin kmr rana sbd hada hadar jama a gashi daman sunada wutar lantarki a unguwar sosai, inda baba rabi ke suyan awara yaga dandaxon samarin unguwar ankafa majalisa shi mutum ne marason hayaniya balle kuma yawan mu amalla da mutane iya kacinsa da sauran samarin unguwar gaisuwa sbd rabin rayuwarshi yanayi ne amakaranta idan kuma yasamu hutu ko yadawo weekend ba inda yake xuwa se kwari yataya mahaifinsa xaman shago ana tasowa kuma se ashiga makarantar dare ananne ma yake dan haduwa da matasan anguwar yawanci shike karantar dasu suna matuqar ganin girma da qimarsa dayake baya shiga sha aninsu koda yake dayawa acikinsu sungirmeshi amma sbd kama kansa dayake yi ko cikin sa anninsa baya shirme shiyasa hatta da manyan unguwar suna yaba nutsuwarsa sosai. gaisawa sukai da jama ar gurin yacire dari biyu cikin aljihunsa ya miqa abashi awara naduka tace "toh babban mutum saidai ba asoyaba ko xakaje kadawo ne?" don tasan kotace yatsaya ba tsayawar xeba sbd tarin jama ar gurin dadai da yamma ne farkon fitowar ta yakan tsaya har hira suyi don mutuniyarsa ce sosai,yace "kawai tabashi danye xeje gida asoya" tace " to ai shikenan" tunda ta dade dafahimtar yamafison danyen yafi siyansa indai shi xeci inkuma moon xe siyawa ne takecewa ita baxata iya wahalar suyaba koma meye yasiyo mata danyan domin Moon bata fita inka ganta awaje toh makaranta amma ko aike indai yananan shiyake xuwa inkuma bayanan kamal yasamoma ammi almajiri daxata ringa aika domin daga shi har sameer din wani mahaukacin kishin Moon din sukeyi sosai, shi sameer badan komai yay hakanba sedan kare tarbiyarta matsayinta na gudan jininshi,ba ranar da Moon xata fita anguwa ko biki ko suna se anbiyota anaso shiyasa abun kedamunsa yana iya qoqarinsa gurin kare tarbiyyan ta daga samari barkatai, shikuma kamal daman matsayinsa na wanda xata aura dolene yay kishinta Allah Allah yakeyi kawai tai graduation ayi auretaxama tasa domin kalar alhaxawan dake son Moon na bashi tsoro, amma kuma inyatina da irin son da Moon da iyayanta kemasa hankalinsan nadan kwantawa sbd yasan abun duniya baxetaba rufe musu ido ba su canxa ra ayi akansa,shiyasa shida sameer suka samata takunkumin fita, Toh wannan kenan danyar awarar taxuba masa yay mata godiya yataho yana kwankwasa qofar gidansu yaji ana kiraye kirayen sallar isha'I hakan yasa hudallah na bude masa qofar yamiqa mata awaran yana fadin "kisoyamin pls,kisaka kwai xanje mosque," betsaya jin mexata ceba ya juya xuwa masallaci,alwala yayda daya daga cikin famfunan dake bayan masallacin yana idarwa yashige mosque aka tayarda sallah,bayan an idar yadan xauna yana azkhar yaga Alh dikko yashigo tareda abdussamad da kamal wadanda sukai missing sallar suka qara binsa akaiwani sabon jam'in sukai tasu sallar yana xaune sewani tinani yashigo masa duk duniya bawanda baffa keganin qimarsa da darajarsa kmr amininsa dikko, daya baya gayawa daya magana yatake yasan yanajin kunyar yaje yatare baffa damaganar Aysha kmr yajja popsy yabuqata,yasan baffa yanada hangen nesa gakuma Ammi Agefe dabesan me aysh tamata ba yatabbata Alh dikko ne last option dinsa indai har yanason baffa ya amince masa cikin sauqi,bayan an idar da sallar yaqarasa gurin Alh dikkon yana furta "daddy barka da dare kmr yajja yaransa ke addressing dinsa shima haka yake cemasa domin Alh dikko kmr uba yake agurinsa," yace "ah ah babban mutum,daxu na leqa akacemun kaje unguwa har kadawo kenan," yace "eh daddy" yace "toh masha Allah ainaga mejiki dasauqi har yana cemun xefito karatun dare yau nace a ah daliban nasa ma duk nakira nasanar musu sunce suna mai yajiki Allah qara sauqi," yace "ameen ameen daddy" suna qarasa fitowa daga masallaci kamal ke qarewa sameer kallo irin adon dayaci yadaisan sameer nadason gayu shidin dan gayune amma haka kawai baxesa babbar riga yay yawo da itaba inba wani muhimmin abun xe halarta ba,smiling yay yana tina Moon tace masa aysha na tana kano fa, kenan gurinta yaje dan gyaran murya kamal yay yana fadin, "S fulani inane kaje wai haka dodan gida ko kace naxo narakaka" harara ya auna masa kafin yace "Daddy daman inada magana idan kasamu lokaci senaxo gidan nafada maka," Yadan juyo anitse yana fadin "babban mutum yanxun me nakeyi muqarasa gidan ko daman naji haj saratu nata jajanka kwana biyu kamata yaji," smiling yay yana fadin "ai xanleqa in sha Allah," kamal dan xaro ido yake yanawa sameer alamar mexe cewa daddyn kardai yaqara xuwa yasa adaga bikinsa da Moon domin wancan karan sameer ne yaje yacewa Alh dikko bekamata ayi bikin kamal da Moon ba batareda tagama secondary school ba gara tagama inyaso koda nangaba ne Moon xata iya amfani da kwalinta intai sha'awar cigaba da karatu, yay na am da shawarar sa lokacin kamal har gaba yay da sameer yadena kulashi yace baqincikin shiga daga ciki yake masa, shikuma har ga Allah yafison Moon tasamu ingantaccen ilimi kmr yajja kowacce ya kesamu, aurenma dan anfi qarfinsa ne,toh yau gashi a thesame tight sport da Moon da kamal keciki har gara kamal yana da shekaru dakuma abinyin daze iya riqe mata sama da daya sannan moon ba yar kowa baceba,tabbas ita aysha akwai banbanci Moon tasan babu aysha bata sani ba,kuma he's ready to face any challenge domin beson iya kacin halin daxe shigaba in akace xa'arabashi da ita, yana wannan tinanin har suka qarasa sitting room din Alh dikko, abdussamad ko shigowa gidan beyiba yatafi majalisar su shikuma kamal danjin kwaf domin yasan sameer din kansa tsaye yakeyin abubuwa tsaf xece wannan karan abari Moon tai degree, Alh yakalli kamal bayan sun xauna yana fadin "kaikuma lafiya kabiyomu," dan sosa qeya yay yana fadin "Daddy daman ai," yakalli sameer yana fadin "ko tare kukene" dasauri yace "a ah daddy," kamal yakalleshi yana cije baki,Alh dikko yace "bamu guri toh," miqewa kamal yay yana kallo sameer namai dariya qasa qasa yafice, Yadago yana fadin "Daddy........." sekuma yay shiru yanajin nauyinsa sosai balle kuma baffansa, yace "babban mutum talk inajinka," "Daddy daman akwai wata yarinya ne....," se yakasa qarasawa yasunkuyar dakai, murmushi Alh dikko yay irin nasu na manya yace "ehen inajinka," Yace "daddy daman inason tane da aure" Sameer yadago yaga Alh dikko yakafeshi da ido baya ko kyaftwa yakasa gane emotions dinsa, Yadorada "daddy bayanxun bafa nake nufi kawaidai inason kusan da itane sannan mahaifinta ma ya amince yace yanason magana da baffa shinema yace infada masa,daddy pls karkuce nayi qanqanta Daddy I can't do without her," smiling Daddy yake ahankali kafin yace "jaa numfashi mana sameer bantaba gani karasa natsuwarka irin yauba,kanaji na" kunya ce kuma takamashi yace "Daddy I'm I'm....." yakasa qara sawa, Alh dikko yace "babban mutum yar wace kuma a ina take datake neman susuta maka natsuwarka da lissafi haka" qasa dakai yasake yi yana cire hular kansa data dameshi da xafi, Yace "qanwar hudallah ce," yace "wace hudallah din wacca dai nasani daman moddibo yara biyu gareshi bansani ba," yace "ah a daddy mamansu daya"afirgice alh dikko yamiqe yafara xagaye parlor kafin yajuyo yana fa din " kasan wacece mahaifiyar hudallah kuwa Dr Bint AJ kuma nasan hudallah ce kadai diyar da bata haifa da AJ ba sameer karkacemun abinda yafi qarfina kaje kadakko min a ina makasan yar AJ," qasa dakai yay yana fadin "sunanta aysha she's he's only daughter sauran yaran maxane," juyowa yay cikeda mamaki yana fadin 'kasan wacece ita kenan ma ko sameer ayajja nasanka da hankali da hangen nesa ai banyi tinanin xaka kawomin shirme haka ba dadai waccan sokonne" yana nufin kamal, yace "Daddy itadin yar makarantar muce a Abuja class dinmu daya daddy" yace "and sameer AJ baxe baka yarsa ba sbd matsayin mu dana su akwai banbanci sameer kanemi wata kawai kowacce xan tsaya maka amma karka kaimu inda bamukai ba nasan tunda aka haifeka komai naka na musamman ne sameer kaidin badan kowa bane but kasamu privilege din samun ingantaccen ilimi darayuwa cikin environment maikyau kana Karatu tareda yaranmasu hannu da shuni sameer hakan baya nufin kaxama daya daga cikinsu,kasani koni dakake gani AJ yafi qarfin yay ma magana dani balle har inganshi ido da ido xan iya iya qoqarina gurin ganin kasamu duk abinda kakeso amma banda wannan, sameer sufyan baxe amince dawannan yarintar takaba shekarunka goma shatakwas aduniya yanxun you can get over her tunkan kai nisa kadakatar da wannan soyayyar sbd banida qarfin gwiwar daxan tsayamaka wnn karon,AJ ba sa an karawana bane," yace 'yanason yay magana da baffa kuma yasan alaqar dake tsakanina da aysha shi Alh AJ din," Maganar data daki dodon kunnen Alh dikko kenan,yaxauna jikinsa duk amace yadaisan sameer baya qarya amma kuma besan sanda yakoyi narrating tatsuniya kmr haka ba, yace "sameer dago ka kalleni nan,AJ dinne yasan kana soyayya da yarshi kuma ya amince daman ina wasa dakai ne bansani Alh alhassan abu jandal fa shi kake nufi," jinjina kai sameer yay kwalla nataruwa a idonshi yace "Daddy baxan taba yimaka wasa irin hakaba kasan baxan taba qirqirar qarya nafada maka ba,he's ayshas father kuma yabani amanarta,yace mun we have a bright future together kuma xannemu abinyi wanda xesa na iya riqeta,I'll sure you daddy I'm worthy of her, kowa yana cewa tafi qarfina amma shi yacemun naxama kmr dansa yanada kirki ba kmr yajja kuke kallonsa ba," maganganun sameer sun taba masa zuciya yaji cewar bekyautawa sameer ba yakawo masa matsalarsa wacca yakasa tunkarar mahaifinsa dashi shikuma memakon yaqarfafa masa gwiwa seyayi qoqarin dakusar dashi amma still maganar yitake yi kmr tatsuniya akunnansa,ko waccan satin seda ogan alh bala Harka yace "masa yagaji daneman appointment da xuwa Abuja kimanin watanni uku kenan yanason yaga AJ yakasa samu sbd he's always busy yanaso yakaimasa wani business proposal ne amma yama kasa ganinsa ba irin form din dabe cikeba amma besamu ba amma yanxun sameer kesanar dashi yaga AJ" yace "ina sauraronka sameer nayarda kanasonta kuma AJ yasan dahaka yanxun mekake so ayi" yace "daman inason kai convincing Baffa xan fadama ayshan seta sanar dashi ranar daxakuje kuhadu dashi tunda kunga mune masu nema ko daddy muxamu sameshi ko" yafada yana langabar dakai sbd kansa yasoma masa ciwo wannan doguwar maganar dayake tun dazun yasa duk bakinsa da kansa ya fara ciwo, yace "babban mutum karatunka fa,kanaga xeyiwu da maganar aure karka biyema Samar mana," yace "ba abinda xaisamu karatu na in sha Allah," yace "shikenan Babban mutum in sha Allah xanwa sufyan din magana xuwa gobe in Allah yakaimu," yace 'toh Daddy nagode sosai" yana sakin murmushi, yace " lallai najinjinama wannan yarinyar babban mutum haka tasace mana zuciyar ka" rufe fuska yay da tafin hannunsa yana dariya zallar quruciyar tabaiyana kanta Alh dikko ya girgixa kai yana fadin "yayan xamani kam sesu gara mu auraddaku duka muhuta se yanxun kasan dakunyar" dariya yay yana fadin "daddy Allah yaqara girma zanshiga cikin gidan yanxu" yace "aidaman kagudu tunda kagama abinda yakawoka" dariya shima Alh yake kmr yajja sameer keyi har yafice cikin gidan yashiga suka gaisa suka dan taba hira da haj saratu kafin yamata sallama tanata qorafin tun yanxun xetafi bejima ba, yace "akwai abinda xeyi agida" yawuce batareda yabari sun hadu da kamal ba don yasan titsiyeshi xeyi seya fada masa meyacewa daddy din, Moon ce tabude masa qofa sbd tunkan yaqaraso yakira wayarta taxo tabude masa qarfe goma da rabi yashiga cikin dakinsa kayan jikinshi yatube yasanya towel ganin mama tashige ciki bame masa qorafin yacire, domin tace qato dashi yadena mata yawan tsiraici wai, Wanka yaje yafesa yafito se alokacin yatina yana jin yunwa kitchen yashiga yasan ba lallai ma ya iya cin abinci awannan lokacin me nauyi sbd kwanciya xeyi,bubbude food plask din yay yaga white rice ne,dayaji veges se stew din kifi ya lumshe ido yanajin qamshin farfesun har cikin cikinsa yasan aikin hudallah ne wnn farfesun kifi nadaya daga cikin abubuwan dayake matuqar qauna a rayuwarshi itakuma takan yimasa aduk lokacin data samu dama don tafaranta masa rai, yarufe yana fadin "Allah yamiki albarka my cousin" dayan qaramin ball din yabude yaga awararsa ce tasoyata ta taji kwai yaqara smiling, daga baya yaji ance "daga ina kake?" juyowa yay cikin mamaki don beji shigowarta ba, yace "ahm ahm amm--- daga gidan Daddy nake yanxun," tace "bayanxun ba tundaxu da yamma dana shiga wanka akacemun kashirya kace kafita daman kana fita baka sanar dani inda xakaba sameer,yaushe kafara boyemun abubuwa ne nicefa ammin ka," tafada cikin karaya duk seyaji badadi dabe sanar da itaba kafin yafita domin shammatar tama yay saida Yatabbatar tashiga wanka yay wuf yacewa Moon tafada mataa yafita don yasan tabbas xata iya hanashi inya fada mata gaskiya, riqo hannunta yay yana fadin "ammi pls ba boyemiki abubuwa nakeba don Allah kiyahaquri in abinda nai miki yabata miki rai pls" tace "dole yabatamun sameer kadenajin maganata ai ansanar mun dakomai cewa wannan fitsararriyar yarinyar me ido har tsakar ka itace diyar taxo garinnan kuma itadin diyar bint ce daman nadade daxargin hakan wannan idanuwan na bint dake tattare da ita baxan taba mantawa dasu ba dasune tacuci dan uwana yafada tarkonta bata barsaba harseda taga takasheshi tahuta,itace sanadin rayuwar dan uwana moddibo natsaneta natsani duk wani abu daya alaqantu da bint sbd bint bala i ce zuriar bint datawa baxata qara gaurayawa in sha Allahu" runtse ido sameer yay yanajin dacin bacin ran dayasa mahaifiyarsa ciki duk da yarasa gane inda maganarta tadosa amma yanada tabbacin akwai wani babban rashin jituwar dake tsakanin mahaifiyar su aysha dahar yau besani ba dakuma amminshi yana fatadai kar fast dinsu yaxo yaxama sanadin rushewar future happiness nasu shida Aysha, dakyar ya iya lallashin ammin nasa yakasa sanarmata inda yaje sbd yanada tabbacin setamai fata fata yau intasan abinda yaje yafadama Alh dikko,kuma dikko kaifi dayane idan yace xeyi xeyi inyace baxeba baxeba ne yasan tunda Alh dikko yafahimcesa shawo kan baffa bawani abu bane amman yanxun farko yanason amminsa taqaunaci Aysha tasota yanason hudallah da aysha su gyara alaqarsu yasan hudallah ce makullin zuciyar mahaifiyarsa domin ammi nayiwa hudallah sonda kosu yayan cikinta bata Masu shi tabbas idan hudallah taqaunaci dimple ammin sama xata sota, har parlor yarakata bayan yamata qaryar ba abinda ke tsakaninsa da dimple duk don taji dadi dadi, tawuce tabarshi xaune saman carpet yaxubo farfesun kifin amma yaji yarasa appetite gaba dayansa,wani iri yakeji dukansa yarasa sukuni miqewa yay xefita a parlor hudallah tafito riqe dawani novel tana duddubawa,tsayawa yay chak yana ganin lokacin kawomata maganar yar uwarta yayi yama manta da laifin dimple din ga hudallah so hana ganin lefi, dagowa hudallah tai suka hada ido yasakar mata murmushi yana fadin "good evening sis,sannu kuma da aiki," dariya tai tana zama akan daya daga cikin cushions din qaramin parlor tace "kagama borin kunyar taka kadawo daga tadin dan sosa kai yay yana fadin nifa ba tadi najeba kunje kun xugamin mahaifiya ko," tace " sameer kenan daxan zuga ammi akan dimple dayau babu me barci agidannan sbd rigimar daxan tada maka,daga kai har ita ba akaina kuke ba amma dai kabani mamaki aduk matan duniya karasa wacca zakaso se dimple" dan batarai yay kafin yace "meyene da Aysh din" straight takalli idonsa tace "bata dace dakai ba," yace "yanxun kikace ba akanki mukeba meye kuma nafadan haka," kallon plate din hannunsa tai tana fadin "bakaci abincinba kenan,' yakalli plate din daya dauka da niyyar kaiwa kitchen,tace "idan tacikama cikin naka da soyayya kasaka a freezer domin kasan bakyau al mubazzaranci ko inkuma inda kaje abinda suka koya maka toh bansani ba," ajje plate din yay aqasa yaxauna gefen hudallah ya kama hannunta ahankali yana fadin, "bansan dawana ido xankalle ki ba,bansan mexance miki ba bansan irin bullying dinki da dimple taiba bansan wane kalar rashin jituwane atsakaninku ba amma nasan deep inside kedin kina qaunar ta sosai sbd takasance jininki itace sakuwanki daman ana fada ashirya yanxun kikalleni nida Moon we fought alot amman muna shiryawa shi bound din sibling daman haka yake you guy's are just being childish," dakatar dashi tai da tahanyar daga masa hannu tace "she is childish nataba cutatar da ita ka tambayeta shin nataba cewa banasonta ka tambayeta shin nida dimple maqiyane katambayeta,kowa xaka tambaya a household din AJ yasan cewa dimple hates me bata qaunar bude ido taganni shi always troubles me......,kasani ba baka sani ba all this year's anan nake samun peace of mind idan naxo gareku,gareka biyayena, if you tell me how much I mean to you inaji kmr I'm at the safest place in this world akwai dukiya da rayuwar jindadi maitarin yawa gidan AJ but I choose here sbd anan ake nunamin nima dan Adam ce kmr kowa,taqarasa tana fashewa dakuka wani irin tausayinta ne yashiga zuciyar sa ahankali yake fadin "I'm sorry if my words hurt you,naji nayarda cewar aysh ke cutatar dake but you know what Aysh Will change xata canxa, I'll help her change" kukan taqara qarfinsa tana maijin takaicin sameer har qasan ranta wato yakasa dosar inda take buqata yaje, amma dole wnn tausayinta dayake ji yaxama daya daga cikin makaman daxatai yaqi gurin ganin tacusa masa tsanar dimple din acikin ransa yaushe tai sakaci aysha tasamu wnn gurbin me girma azuciyarsa, amma afili saitace "sameer nan din dana kexuwa nasamu sassauci kanaso kadakko ta kasata arayuwar mu tsundum sameer ina tsoron kaima kadena sona sbd dimple tafiye makani," yace "shshsh that will never happen kinaji matsayin ki danata baxe taba xuwa daya ba kowa danasa inason kidena hada kanki da ita pls she's who she is and you're who you are,xan gyara wnn alaqar in sha Allah one day keda ita xaku xauna a inuwa daya ku qaunaci juna kmr ba abinda yataba raba kanku" cikin shashsheqa take furta "dawannan rnr xaixo dana fi kowa farinciki aduniya," amma axuciyarta dariya da takaici yaciyota tace kayi kagama wllh nida dimple baxamu taba jituwa ba sbd baxan taba sauya halayena ba ita kuma baxata taba qaunataba indai har bangyara ba.
AYSAM It's Fatoums Passion's Love,passion,hatred,betrayals and power between two different world's.