Free chapter · Read without an account

Episode Sixty: Amina

by Maman Maama · Maimoon

Kadan ya rage dariya bata kubce min ba saboda ganin reaction din fuskokin su. Sam ba haka suka yi tsammani ba, su a tunanin su babu matar da za'a gaya mata irin wannan maganar ta hadiye sannan ta bayar da amsa irin wacce na bayar. Hajiya tace "kin sani? Kina nufin ya gaya miki exactly wannan maganar?" Ita kanta tasan cewa nasan karya suke yi, Nace mata "eh ranki ya dade ya gaya min, ai baya boye min komai. Ya gaya min komai na labarin sa har labarin asalin fara shan giyarsa" a take naga kalar idonta ya chanza, murmushin fuskarta ya kau. I got her exactly where I wanted her. Na gyara zamana na harde kafafuwa na irin zaman da Sultan yake yi, na cigaba da cewa "nasan komai akansa, nasan duk abinda ya aikata a baya nasan kuma wanda bai aikata ba, nasan kuma abinda zai aikata nasan kuma abinda bazai aikata ba" Daya matar tace "kuma duk kinsan halayensa kika yarda kika aure shi? Shi fa aure ba abu ne na wasa ba, in kika auri mutum kamar kin zabe shi ne ya zama uban 'ya'yan ki" nayi mata murmushi nace "ai in kana so kasan mutum, ranki ya dade, ba wajansa zaka kalla ba, ko kuma abinda mutane suke fada akan sa ba. Abinda zaka kalla shine his inner self, deep down waye shi. Sultan deep down is a good person, very good person, na gani kuma nayi niyyar fito da wannan goodness din nasa waje yadda kowa zai gani. Alhamdulillah, na fara samun nasara, dan duk wanda yasan Sultan shekara daya data wuce in ya ganshi yanzu yasan da akwai banbanci. Wata rana ina fatan kuma zaku ganshi kamar yadda nake ganinsa." Sai a sannan Khulsum tayi magana bayan tayi tsaki tace "tana magana kamar wata psychologist" na juya na kalle ta nace "but I am a psychologist, I have a first class degree in psychology from the second best university in the world. I know exactly when someone is lying to me, and I also know when someone is hiding or trying to hide something, ni kuma in na san haka sai curiosity ya saka in fara binciken gano menene ake boyewar. Tun farkon ganina da Sultan na san cewa he is hiding a very dark secret dan haka na fara bincike, yanzu so far nasan abubuwa da yawa a kansa, wasu abubuwan da na sani ma shi kansa bai sani ba". Na bi fuskokin su da kallo, kamar an tsiyaye musu jinin su daga jikinsu, na hango kiyayyata karara a rubuce akan fuskokin su. Kusan minti biyu babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu. Hajiya ce ta kirkiro murmushi tace "ku tashi mu tafi, mun bar ango yana ta jiran amaryarsa" Khulsum ce ta fara tashi ta fita ba tare da ta kalli inda nake zaune ba. Har mota na raka su ina ta nanata godiya ta a gare su bisa ziyarar da suka kawo mana da kuma albarkar da suka saka mana a auren mu, na daga musu hannu sannan suka tafi. At least nasan yanzu tsakanin mu is clear, babu munafunci babu yaudara. Ba zasu sake zuwa su ce zasu gaya min wata magana akan Sultan ba, amma kuma nasan na kunno wata wutar kuma. Na gaya musu nasan secrets din su dan haka na kara wutar kiyayyarda suke yi min. But I was ready, Allah yana tare dani and I was not scared. Na yarda da Allah na yarda da kaddara, nasan su basu isa suyi min komai ba, duk abinda ya same ni daga Allah ne ba daga gare su ba. Kuma komai nisan jifa kasa zai dawo, duk kuma abinda ka shuka shi zaka girba, in khairan khairan in sharran sharran. Ina komawa cikin gida na koma part dina nayi wankan da ban samu nayi ba, ba fito na shafa special mai na, na kuma fesa turaruka daban daban. Na jima ina neman kayan da zan saka, daga baya na dauko wata rigar bacci deep red, wadda akayi da lacy material, tsahon ta bai karaso rabin cinyata ba, tana da hannun bra da kuma matching panties amma babu bra. Ni kaina dana kalli madubi sai da naji kunyar kaina, kalar ta kara fito da haske da kuma kyan fatar jikina. Na dauko deep red lip stick na shafa a lips dina. Na dauko dogon hijab har kasa na saka, sannan na fita. A palourn sa na ciki na tarar dashi, yana kashingide da fararen singlet da gajeran wando a jikinsa, ya kunna TV ya rike remote a hannunsa amma kuma ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani yana kallon sama. Na jima a tsaye ina kallonsa amma bai ma san na shigo dakin ba. Na dan daga murya nace "wanne film kake kallo ne?" yayi sauri ya kalle ni sannan ya kalli TV din, ya daga kafada yace "I don't even know me suke yi. Baƙin naki sun tafi ne?" Ban bashi amsa ba, ya fara kokarin chanza station, na chire hijab din jikina a yar a gefe nace "pss" ya juyo da sauri yana kallona, a hankali remote din hannunsa ya zame ya fadi kan carpet, ina kallon idonsa naga duk wani tunani da wata damuwar sa suna disappearing har sai da ya zamanto babu saura. Ya saki ido da baki da hanci duk yana kallona, a hankali ya furta "ya Ilahi save me, wannan yarinyar so take ta haukata ni" sai kuma naji kunya nadan rufe idona kadan da hannayena wadanda suka sha jan lalle tun na biki na, ni kaina bansan lokacin da na zama marar kunya har haka ba. Yace "come here" babu musu na tafi gabansa na tsaya, ya fara kallona tun daga yatsun kafa ta har zuwa kitson kaina, na sake jin kunyar sa na daga hannuna zan rufe fuskata sai ya rike hannayen duk biyun ya jawo ni na fado jikinsa, na boye fuskata a wuyansa ina sake jin kunyarsa, ya saka hannu daya ya dago fuskata yana kallona da idanuwan da suka fara juyewa zuwa tsantsar sha'awa yace "please, ki gaya min gaskiya, anya ke mutum ce kuwa?" Nayi dariya tare da lakuce masa hanci, sai ya bata rai "okay dariya ma na baki ko? I mean how can someone be as beautiful as you are? Kwakwalwa ta ta kasa dauka. Kin rikita ni gabadaya kin zauta ni, saura kadan inyi loosing sanity dina". Na daina dariyar da nake yi na zagayo wuyansa da hannu daya dayan kuma ina shafa sajen fuskarsa ina jinjina irin girman soyayyar da nake yi masa, nace "I may be good looking, duk da dai ba kamar yadda kake fada bane ba, but I don't think I am as good looking as you are. Ban taba gani ba, ko a mafarki ban taba ganin namiji like you ba, you are special and you deserve special treatment, and that's what I am planning to give to you my husband" Yayi murmushin daya kara kawata kyakykyawar fuskar sa, sannan ya saka dan yatsansa yana zagaye lips dina idanuwan sa a akan su yace "and I am planning on treating you as the queen you are". Daga nan ya hade bakin mu, in his kiss wanda har yau yake draining senses from my brain, taking my breath away and feeling my heart with love, Sultan's love. A mintocin da suka biyo baya muka manta da duk abinda ya faru a ranar, babu Takawa and his threats, babu Hajiya and her hypocrisy, babu Khulsum and her food, a lokacin hatta Mommy da Daddy basa gabana, Sultan ne kadai a gabana, only him existed in my world kamar yadda shima ni kadai ce a tasa world din. Sai da akayi first round aka zauna break sannan na bashi labarin yadda mukayi dasu Hajiya, ban boye masa komai ba na gaya masa duk abinda suka ce min da amsar dana basu. Kamar yadda nayi tsammani, bai nuna damuwar sa koya tada hankalinsa ba sam, sai nuna min jin dadinsa da yayi akan yadda nayi tackling maganar da kuma trusting dinsa da nayi. Daga nan muka bar maganar muka cigaba daga inda muka tsaya. Hint ga matan aure, irin wannan time din shine best time na discussing sensitive issues da mai gida, especially mai gidan da yake da temper ko kuma wanda baya daukan shawara, a lokacin he is relaxed, in body and in spirit, kan sa is fresh, and he is very excited, da wahala ki fadi abinda zai bata masa rai a lokacin. Amma fa bance ayi using time din wajan roko ba, ko kai tsegumin kishiya ba, gwara ayi amfani da time din gurin bawa mai gida shawara mai kyau wacce zata kara kafa miki fadar ki a gurinsa. Washegari kamar yadda Sultan ya saba, in ya tafi masallachi baya dawowa sai gari ya waye, wanda na lura yana zama ne acan yayi karatun al'qurani, ni kuma wannan time din nake using in gyara dakunan sa, mostly daga nan bacci muke koma wa amma yau kitchen na tafi na barshi, yana ta mita wai shi bai ga amfanin in ce sai na koyi girki ba, tunda dai shi zan ke yiwa girkin nan kuma yace baya so ba shikenan ba sai in hakura. Ina shiga kitchen na tarar already Asma'u tana ciki, yau ma cewa tayi in cigaba da watching and learning, tana yin komai tana yi min bayani, ni kuma na bude kaina sosai ina fahimta, in naga abin tambaya in tambaya, har muka gama komai muka jera a dining sannan na tafi zanyi wanka. Ina shiga dakina wayata tana fara ringing na duba naga Daddy. Duk da cewa tun da nazo gidan kullum sai ya kirani ko kuma ni in kira shi mu gaisa amma yau sai da naji gaba na ya fadi. Nayi bismillah na dauki yawar, muryarsa naji wasai babu alamar damuwa a cikin ta, na sauke ajjiyar zuciya na gaishe shi, mun jima muna hira yana gaya min gobe zai tafi England kuma zai dan jima kafin ya dawo, nayi masa addu'ar fatan alkhairi. Sai da muka gama maganganun mu sannan yace "jiya da daddare ai nazo palace, mai martaba sarki ya kira ni akan maganar ku, ya nuna min wasu pictures da suka taba zuciya ta, amma ina so inji daga bakin ki, Maimunatu mai ya hada ki da bindiga?" Yanayin da yayi min tambayar kawai na san cewa abin ya taba zuciyarsa sosai, musamman sanin da nayi na yadda Daddy yake da son ƴaƴan sa. Sai da na hadiye wani abu a makogwarona sannan nace "I was trying to stop Sultan from doing something bad, something very bad, and I succeeded" sai kuma nayi shiru, bana son in fadi wani abinda zai kara tayar da hankalin sa. Jin nayi shiru sai yace " ban san menene ya faru ba Moon har ya kai ki ga daukan bindiga, amma abinda na sani shine na yarda dake, tunda har baki kira ni kin gaya min menene ya faru ranar nan ba hakan na nufin kina ganin zaki iya handling koma menene, amma ina so ki sani, as much as I like Sultan I like you more, amma hakan ba wai yana nufin bana son Sultan ba, ina sonsa sosai kuma ina alfahari da abinda kike yi a rayuwarsa, but be very careful my daughter, your picture with a gun almost gave me a heart attack, ina so ki saka a ranki a kodayaushe cewa you are not alone idan kinga abin yana kokarin yafi karfin ki just give me a call, ko ina kasar nan ko bana kasar nan I will always be there for you. Idan wani abin ya same ki a dalilin auren nan I will never forgive myself, saboda ni na amince na saka ki a ciki duk kuwa da sanin sarkakiyar da take ciki. Zan yi waya da Sultan din shima zamuyi magana dashi." A hankali nace "to Daddy, nagode. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" yace "Ameen" Na jima a zaune a gurin bayan mun gama wayar, kawai sai naji hawaye suna zubomin bansan dalilin su ba. A duniya mutum bazai taba samun mai sonsa ba sama da iyayensa, kuma babban dace a duniya bayan kasancewarka musulmi shine samun iyaye na gari. Iyaye na gari sune ginshikin samun rayuwa ta gari. Amina's POV Tun ranar da tabar gidan Moon kullum sai ta kira number din Ibrahim l amma har yanzu bai dauka ba. Wani lokacin sai ta ji haushi ta jefar da wayar tace yayi wa kansa, amma kuma in ta huce sai ta kuma dauka ta kira shi, still ba response, kuma karin jin haushinta shine number din tana shiga dauka ne ba'a yi. In tayi tunanin ta rabu dashi kawai sai kuma ta yi tunanin to ko bashi da lafiya ne, he might be dying on a hospital bed ko kuma alone a gida for all she knows. Ranar dai da akayi kwana biyar ta shirya da niyyar yau dai zata yi finding out ko ma menene ya same shi. Ta shirya tsaf ta hau sama dakin Mommy ta gaya mata zata fita tana son siyan wasu 'yan kaya, Mommy ta bata kudi tace kuma ta dauki driver amma kar ta dade. Tana shiga mota ta gayawa driver sunan supermarket din Ibrahim, tasan dole zata samu labarin sa a gurin staff din gurin. Tana shiga ta danyi 'yar siyayyar ta kadan tazo gurin cashier ta biya sannan tace "please manager dinku kuwa yana nan? I am a friend of his ina son ganinsa" matar ta danyi jim tana tunanin me zatace sannan tace "eh yana nan ma'am, amma I don't know ko zai ganki, in kina da number dinsa ki kirashi mana in yace ki shiga kinga shikenan" Amina tace "ai number din nasa bata shiga ne, I would have called him, just ki je kice masa Amina tazo tana son magana dashi" matar tayi saurin girgiza kanta "am sorry ma'am, bana son inyi laifi" Amina tace "OK, just show me ina office din nasa yake sai inje ni kadai" nan matar tayi mata kwatance. Ta hau saman benen da aka nuna mata tana kallon kofar offices din da suke a jere, a kofa ta uku taga an rubuta "manager" sai data sauke ajjiyar zuciya sannan tayi knocking, babu response, ta sake yi sannan ta murda hannun kofar, ga mamakin ta sai ta ji kofar a bude, ta tura ta shiga da sallama. Yana zaune akan kujerar sa yana danna laptop din gabansa. Looking as handsome as ever. Ya dago lumsassun idanunsa ya dora akanta, sanyin ACn office din ya saka ta dan rungume hannayenta tana shakar daddadan kamshin sa. Bai ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanu. Ta dan kirkiro murmushi ta karaso gaban desk din sa, tace "Can I sit down?" Nan ma babu amsa sai idanu da yake binta da su, ta dan zauna tana kallon haduwar office din, ta na feeling nervous, a ranta tace damn you Moon da kika saka nayi miki wannan alkawarin. Kamar daga sama taji yace "What do you want?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa, babu dariya sam a fuskarsa, zuciyar ta taji ta fara tafasa, a ranta tace "what am I even doing here? In Moon tana son ta san halin da yake ciki she should come by herself" ta mike tsaye cikin zafin rai tace "am sorry I bother you" da sauri ta fice daga office din kamar zata tashi sama. Har ta fara sauka stairs din sai kuma tayi wani tunani, wannan mutumin kar fa ya dauka wai ta damu da shine ya saka take ta kiran sa a waya kuma har tazo office dinsa, da sauri ta koma saman, ba tare da sallama ba ta kuma bude kofar ta tsaya a bakin kofar tana kallonsa tace "ba wai dan na damu da kai nake kiranka a waya ba, ba kuma wai dan na damu da kai nazo office dinka ba har da zaka wulakanta ni. Moon ce ta roke ni inyi haka, har kasa ta durkusa akan guiwoyinta sannan na yarda zan yi, dan haka save your arrogance for her not me, ka tattara duk wani guntun wulakancin ka and shove it up your handsome face" Tana gama fadin haka ta buga kofar da karfi ta juya ta tafi tana murmushin jin dadin ta rama wulakancin da yayi mata, sosai taga yadda expression din fuskarsa ya chanza sanda ta ambaci sunan Moon, ita wannan soyayyar mamaki take bata. Ji tayi ya bude kofar da sauri ya biyo ta, bata waiga ba taci gaba da sauka stairs din yace "Amina wait please" ta juyo tana kallonsa tace "saboda me? Saboda kaji nace sakon Moon ne zan gaya maka? Wait, ya akayi ma kasan sunana? Ka yiwa kanka ai, zan koma in gaya mata kace baka son jin komai daga gareta" ta juya ta cigaba da sauka, tana jin sa ya biyo bayan ta yana kiranta amma bata waiga ba, tana gama sauko wa tayi hanyar fita, sai da takai bakin kofa sannan ta juyo, bai biyo ta ba, the mighty manager ba zai zubar da ajinsa a gaban yaran sa ba. Ta fita ta shiga mota suka koma gida. Tana ta tunani a ranta, wannan wacce irin soyayyace haka, wanne irin so ne Ibrahim yake yiwa Moon, duk da cewa kiri kiri Moon ta zabi Sultan, duk irin abinda ya faru ranar nan amma har yanzu mare ambaton sunan ta ya chanza masa lissafi. Ita kam bata jin zata iya yiwa wani irin wannan son. Ta fara tunanin abinda ya faru ranar da aka kai Moon, bata taba tsammanin wai maganar zata wuce shikenan kamar ba'a yi ba, amma Moon wai ko Daddy ta hana a gaya wa, wanne irin so ne haka itama Moon take yi wa Sultan?. Tana shiga gida ta dauko wayar ta, 6 missed calls from Ibrahim. Dariya tayi a bayyane, she got him right where she wanted him, sai ta rama duk abinda yayi mata, sai ta ja ajinta san ranta. Kwanan su biyu a haka, ya turo messages sunfi a kirga, ya kira ta sau ba adadi amma bata kula shiba. Ranar kwana na ukun dai ya gaji, zuciyar sa tana ta yi masa sake saken menene sakon Moon din da Amina zata bashi? Is she OK? Kar dai ace wani abun ya faru da ita ranar nan bayan tafiyarsa. Yana tashi daga office ya biya ta restaurant ya ci abinci daga nan gidan su Moon ya wuce, direct ya doshi gate din gidan yayi horn, mai gadi ya leko ya ga motar bai bude gate din ba ya fito ya taho gurin sa, ya sauke glass din sa yana kallon mai gadin yace "Amina tana na kuwa" mai gadi yace "eh tana nan" ya cigaba da kallonsa, Ibrahim yace "zan iya shiga in ganta ko kuma in tsaya anan za'a kirawo min ita?" Da sauri mai gadin yace "a'a bara a bude maka ka shiga ciki" still amma yana kallon Ibrahim, sai kuma ya dan yi gaba kamar zai tafi ya kuma juyowa ya kalli Ibrahim, sai ya dawo da baya, yace "ni kuwa bawan Allah kamar kaine ka taba zuwa nan a shekarun baya ka bani sako in bawa Maimunatu" Ibrahim yaji yawun bakin sa ya bushe, yace "eh nine Baba, ashe baka manta ni ba" baba Habu ya washe baki yace "yauwa har naji dadi, ai bana manta fuska, in dai naga mutum ko mai tsahon shekaru ina iya gane shi" ya danyi shiru sannan yace "abinda yasa kaga na tambaye ka shine, bayan na bata sakon, lokacin zasu tafi England, ta bani wata katarda tace in baka. Tunda kuwa suka tafi kusan kullum sai ta kira ni ta tambaye ni kazo? Daga baya ni nace mata ta hakura ta daina kira, in kazo da kaina zan kira ta in baka ita kuyi magana" Ibrahim ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya runtse idonsa yana jin zafi a ransa, Baba Habu ya cigaba da cewa "ina fatan dai ba wajan ta kazo yanzu ba, saboda anyi auren ta satin daya wuce" Ibrahim ya bude idonsa yace "No, ba wajanta nazo ba, wajan Amina nazo, nasan anyi bikinta. Amma baba takardar da ta baka tana nan kuwa har yanzu?" Baba habu ya danyi tunani yace "ai shekarun ne da yawa, amma zan duba maka, inna ganta kafin ka tafi sai in baka" daga nan ya bude wa Ibrahim gate ya shiga sannan ya tafi kiran Amina. Tun da Ibrahim yayi packing idonsa yake rufe yana jin ɗachi a ransa. She trusted that he will come back shi yasa har ta bayar da letter tace a bashi idan yazo, amma bai zo din ba, he imagined her pain, calling day after day tana tambayar ko yazo? Amma kullum amsar shine bai zo ba. Tace masa five years tayi tana jiran sa, a cikin five years din nan bata taba yin ko da saurayi ba, shi take jira duk kuwa da tasan cewa shi yayi aure. Ya dafe kansa da yaji yana sara masa. Ya bude ido yana kallon gidan, wannan shine karo na biyu daya shigo gidan nan, ya tuna abubuwan da suka faru a zuwansa na farko, a karshe ya juya ya tafi ya bar hawaye yana zuba a idon Maimunatu. Ji yayi duk ya tsani kansa. Ta madubi ya hango ta ta fito tana kalle kalle, gabansa yaji ya fadi, she looked so much like Moon, but she isn't Moon. Ya danna horn ta juyo ta kalli inda yake, tana zuwa dai dai window dinsa ta bata rai ganin shine, ta rike kugu tace "what do you want?" Exactly abinda ya gaya mata a office dinsa, bai bata amsa ba ya turo ko fa ya fito, ya jingina da motar ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zuba mata ido. Sai kuma ta kasa kallonsa ta juya tana kallon gefe, sai da ya gama tsare ta da ido sannan yace "na horu haka, ayi min afuwa, nayi kuskure ba zan sake ba" ta juyo tana kallonsa tace "me kayi?" Yace "laifuffuka na ai suna da yawa, na farko I used you to get into Moon's home, na biyu I ignored your calls, na uku I treated you badly a office dina" Ta dan so tayi murmushi amma ta maze tace "shine abinda ya kawo ka? Ai na dauka kazo kaji sakon da Moon ta bani in gaya maka ne. To tunda ka gama fadar abinda zaka fada ni bara in koma gida" yayi sauri ya tari gabanta yace "to ai baki ce kin hakura ba" ta murguda masa baki ta sake yin gaba, sai kuma ta juyo "au ba zaka tambaye ni sakon Moon din ba" ya girgiza kansa yace "just tell me if she is OK" ta danyi murmushi tana kallonsa tace "she is more than OK. Amarya ce fa ko ka manta" daga haka tayi komawar ta gida. Ya danyi murmushi yana jin dadi a ransa, at least Maimunatu is OK, she loves mijin da ta aura, abinda ya faru ranar ya tabbatar masa da haka, abinda ba shi da tabbaci a kai shine idan shi mijin nata yana son ta kamar yadda take son sa, idan zaiyi treating dinta right, bindigar da ya bata a hannunta a ranar ya kuma doubling doubt din Ibrahim akan kasancewar sa miji na gari.. Ya koma motar sa ya tayar ya koma bakin gate, yana zuwa Baba Habu ya kawo masa wata 'ya karamar envelope, fuskar sa cike da alfahari yace "ka ganta kuwa na gani" ya karba yayi godiya ya debo kudin da bai san adadin su ba a aljihun sa ya mika masa amma sai yaƙi karba yace "Maimunatu tafi karfin haka a gurina" Ibrahim bai bude letter din ba sai da yaje gida ya gama duk abinda zaiyi yayi shirin kwanciya sannan ya dauko takardar ya bude; Dearest Ibrahim I may not be around when you come back. Please give the man who gave you this letter your new phone number and I will call you. I miss you Maimunatu. Ya ajiye takardar ya dafe kansa da hannayensa biyu yana jin garin yana juya masa. Ya tuna yawan zurga zurgar da ya ringa yi zuwa unguwar su Maimunatu, amma Allah bai taba bashi ikon karasawa gurin mai gadin su ba, all this while wannan wasikar tana ajjiye, da ace ya karasa gurin mai gadin ya karbi wasikar ya karanta da duk wata karya ta Amira ta kare. Ba Amira ce ta raba shi da Maimunatu ba, Allah ne ya raba su, saboda ya riga ya kaddara cewa babu aure a tsakanin su. Ya jingina kansa a jikin frame din gadon for some time, sannan ya mike zaune ya dauko wayarsa yayi dialing number din Amina, ga mamakin sa sai yaji ta dauka, bata gaishe shi ba tace "what do you want?" Yace "har zan kwanta na tuna baki ce kin yafe min ba har yanzu" tace "to sai na fada? Tunda kazo gidan mu kaga na fito ai na hakuran kenan ko" yace "thank you" tace "good night then" yace "wait. In really kin hakura can we be friends then?" Ta danyi shiru sannan tace a hankali "am not Moon" yace "I know" tace "ok, friends then" yace "to kiyi min dariya mana inji sai in yarda mun zama friends din" tace "I don't have dimples" yace "I know".

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.