Free chapter · Read without an account

Episode 16

by Shamseeya Rabi'u Garba · KOMAI YA YI FARKO

16

Hunaif na kwance a gefen Zee dake sharar bacci abinta, kamar ba itace ta gama yi masa ƙaramin hauka few minutes back ba, kallonta ya ke yi yana tunanin wacce irin macece ita ɗin.

Wayarsa ya ɗauka ya sending mail wa Football club ɗinshi, yana neman su ba shi leave, domin at this point yana tunanin ba wa Zee space is the best thing to do.

Car keys ɗinsa ya ɗauka ya fita neman abinci saboda kukan yunwa da cikinsa ya fara yi.  
A hanyar fitarsa daga eatery ya ji wayarsa ya vibrate a aljihunsa, amma sai ya ignoring ya shiga mota abin shi, instead of ya koma gida sai kawai ya wuce gidansa na da da ya fara zama kafin ya siya wanda suke ciki yanzu.
Sai da ya kai gida ya ci abinci kafin ya ɗauki wayar, yana kunna ya gan Mail ne daga club ɗinsa, sun granting masa leave da ya nema, amma only for one week, saboda nan da kwanaki goma suna da babban match, taɓe baki Hunaif ya yi, yace; "Not bad, at least I will clear my head."

Washegari da asuba bayan sallah ya tafi main house ɗinsa, hoping Zee ba ta farka a bacci ba, a hankali ya danna password na ƙofar, ƙofar ta buɗe masa a hankali ya shige, bedroom ya shige being extremely careful not to make any sound, kamar yadda ya zarga Zee na kwance tana kan bacci, girgiza kai yayi cike da takaici wai ƴar musulma amma sallah na ba ta wahala, ya shiga closets ya ɗauki tarkacen da zai buƙata ya bar gidan.

Farkawa kawai Zee ta yi ta gan babu Hunaif a gefenta, hakan na nufin bai kwana gidan nan ba kenan, don da ya kwana gida dole zai tasheta sallar asuba, “To ina ya tafi babu ko kiran waya? Zai ko dawo ya same ni." Zee ta rinƙa ayyanawa a ranta daga kwancen da take.
A hankali ta sakko da ƙafafunta ƙasa tana miƙa, bathroom ta shiga ta yi brush ta fito, wayarta ta ɗauka don kiran Hunaif, tanna kunna wayar da message ɗinsa ta fara cin karo; 'I wouldn't be around for a while so take care of yourself, you can use my card if you need anything, gashi na ajiye miki a gaban mirror.'
Murmushi ta yi bayan ta gama karanta message ɗin, tace; "Idan ka gan dama you should be away forever, so far katinka na wajena ma fi mishkila." Sai ta kwashe da dariya kamar mahaukaciya, bathroom ta koma sharp-sharp ta yi wanka ta fito, simple gown ta saka, ta ɗauki keyn dayar motar Hunaif da ta gani a drawer, ta fita daga gidan, zagaya garin ta rinƙa yi har ta samo babban shopping mall, parking ta yi ta fito daga motar, tana taku ɗaiɗaya har cikin mall ɗin, layin kaya ta fara shiga ta jido kaya kamar ba gobe, kafin ta tafi babban eatery ta siya varieties of abin ci da drinks ta zuba duka siyayyan a backseat ta shiga motar ta ja.

Wani haɗaɗen park ta tafi with the help of bincike ta online, ta yi using Google map har wajen.
Wajen da aka tanada for VIPs only ta zauna, ta zauna, ta ordering fresh juice, tana zaune tana kallon yara dake wasa da iyayensu har aka kawo mata juice ɗinta, ta sha tayi hotuna ta ɗora a social media platforms ɗinta, kafin ta tattara ta koma gida.

A gajiye lis ta shigo gidan, tana shiga ta faaɗa akan gado, ta janyo wayarta tana kallon yawan likes da comments da aka yi a hotunan da ta yi uploading.

Hunaif na kwance a ɗakinsa na guest house ɗinsa yana ƙoƙarin siyan ticket a lokacin debit alert na siyayyan kayan da Zee ta yi a mall ya riske shi, kallon alert ɗin yake yi da mamaki, he can't believe cewa Zee ba ta iya ɗaukar waya ta kira shi ta ji ko lafiya ba amma ta iya ɗaukar masa kati ta je ta yi siyayyar over one million naira, bai gama mamakin wannan ba ya ƙara ganin alert ɗin one hundred and fifty thousand, bayan few hours sai ga alert ɗin hundred thousand.
Mamaki ya kusan kashe Hunaif a zaune, tunani yake yaushe Zee ta zo garin da har ta san wajen tafiya kashe kuɗi haka.
Yana tsaka da tunanin wayarsa ta yi ringing, kamar ba zai ɗauka ba saboda yadda zuciyarsa ke tafarfasa, amma no matter the condition he is in ba zai iya ignoring kiran Mami ba, picking call ɗin ya yi, ya saka wayar a kunne, bayan sun gaisa sai Mami tace; "Hunaif you don't sound alright, Allah ya sa lafiya?"

Murmushin takaici Hunaif ya yi, yace; "I'm fine Mami, kawai dai ki yi ta yi min addu'a Allah ya sa ban yi kuskure wajen zaɓen mata ba."

"Ban fahimceka ba Hunaif."

Girgiza kai kawai Hunaif yayi kamar yana gaban Mamin, sai yace; "Babu komai Mami. Ina su Inaya?" Ya tambaya yana kawar da zancen farkon.

"Sun tafi madarasa." Mami ta bashi amsa.

Hira suka ɗan taɓa kaɗan kafin suka yi sallama suka katse kiran.

Mami ta riƙe wayar a hannunta tana tunanin ko me ZEE take yi wa danta hoi, daman tun zaman da Zee ta yi a gidan na kwana biyu kafin ta tafi Brazil ta fahimci ita ɗin ba mace ce da za a ji daɗin zama da ita ba, amma sai ba ta yi saurin furtawa ba, she decides to give her time and observe her more.

A lokacin Zee ta tafi gidansu Hunaif mai aikinsu ba ta da lafiya tana asibiti, haka ammi da twins za su tashi da safe su yi dukka ayyukan gida Zee na bacci, su kuma dafa abinci su kai mata har ɗaki, idan ta ci abincin ma sai dai su zo su kwashe kwanukan a ɗakin, tsakaninta da Mami kuwa sai kusan karfe goman safe kafin take zuwa gaisheta, bayan gaisuwan nan kuma idan ta shige ɗaki to sai wani safen, tun twins na shiga wajenta a ɗaki ko za su tayata hira har suka daina don ba ta ba su fuska ba.
Tun a wannan lokacin Mami ta shiga damuwa na irin matar da Hunaif ya aura, amma ta daure ta bar komai a zuciyarta, tana tunanin tunda suna son junansu za su zauna lafiya ba za a samu problem ba, amma jin furucin Hunaif yau ya sakar mata da gwiwa, he doesn't sound happy, he sounds very worried.
"Inalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Ya Allah ka kawo wa dana sauki a duk abinda ke damunsa, it's barely one month da aurenshi but he's sounding depressed already." Mami ta faɗa tana goge hawayen da ya gangaro mata.
Wayarta ta ɗauko ta yi wa Hunaif ɗin message; 'Ka tashi ka yi sallah raka'a biyu, ka roki ubangiji ya kawo maka saukin duk abinda ke damunka tunda zurfin ciki ba zai barka ka sanar dani ba, nima a nan I will include you in prayers In Sha Allah.'

Yana kwance yana tunanin duniya sakon ya shigo, yana gani kuwa ya miƙe ya shiga banɗaki ya ɗora alaula, ya fito ya shimfiɗe darduma ya hau.
Bayan ya iddar da sallar sai da ya shafa more than an hour a kan darduman yana kai kukansa ga mahallicinsa.
A kan darduman ya kwanta ya yi bacci kafin lokacin flight ɗinsa ya kai.

________

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya wa Humaira, ya daɗi gobe babu, amma a duk yadda ta same kanta ta kan godewa Allah sannan ta move on da rayuwarta, ta ƙara yawan ibada, ta kuma daɗa zama miskila. Su Laurat na matuƙar ƙoƙari wajen ganin sun ja ta a jiki kamar ƴar uwarsu, Umma A'i kuma ta zame mata tamkar uwa. Ƴan uwanta a can Dala suna yawan kiranta akaiakai su ji lafiyarta su kuma daɗa ƙarfafa mata gwiwa.
Kamar yadda ta yi wa kanta alƙawari, ta cire duk wata damuwa a ranta, duk da tabon da aka yi mata ba zai taɓa warkewa ba amma tana ƙoƙari wajen ganin ta kai da kanta daga tabon, yanzu karatunta ne kawai ta saka a gaba, shi tafi ba wa muhimmanci.

Samarin unguwar kuwa sun yi caa a kanta amma ba ta kula kowa a cikinsu, ɗaya daga cikinsu mai suna muttallab ne ya zo har gida ya sami malam Sadi da maganar sonta, shine Mallam Sadi ya yi magana da Abbanta, Abban Humaira yace idan har Malam Sadi ya yarda da tarbiyarsa ya ba shi dama, zuwansa na farko kuwa Humaira ta yi masa kora da hali, ta faɗa masa akan ita ɗin victim ɗin fyaɗe ce, ai kuwa tunda ya bar gidan bai ƙara waiwayanta ba, kamar ya faɗawa sauran samarin anguwar, duk suka daina kulata, ita kuwa hakan ma ya fi mata daɗi, besides she's just seventeen, kuma tunda Kamis ya rabu da ita ta fidda rai a aure, ko lokacin da ta kula Alhaji Sani saboda kirkinsa ne, yanzu tunda shi ɗinma ya barta to ta closing chapter ɗin soyayya ko aure a rayuwarta.

HUMAIRA na zaune a masallacin department ɗinsu tana duba handout ɗinta na last paper da take da shi, wata friend ɗinta da ta fara kulawa sanadiyyar haɗuwa a Library da exams ya ƙarato mai suna Ameena ta taɓata, tace; "Tashi mu tafi gaban hall, kar mu zauna a nan a fara shirya mutane a hall ba mu sani ba, ƴan ajinmu kuma ba kiranmu za su yi ba tunda suka mana tambarin masu girman kai."

Taɓe baki Humaira ta yi, tace; "Su suka sani. Meenat Ni maganar mutane ba ya damuna wallahi."

"Yo me zai sa ya dameki, ai idan kika ce za ki rinƙa saka maganar mutane a ranki sai zuciyarki ta fashe. Tashi ke dai mu tafi."

Humaira ta tashi suka fita daga masallacin. Suna doso exam hall ɗin kuwa suka gan invigilators a gaban hall ɗin sun fara duba course form da exam cards ɗin students suna shiga ciki.
Meenat tace; "Kamar na sani."
Humaira tace; "Suna son su yi proper arrangements ne yau saboda last paper ɗin mu kenan for the semester shiyasa suka hallaro da wuri haka."
A kunne Humaira ta raɗawa meenat; "Idan kin san kin riƙe chokes ko waya ki rufa mana asiri ki fitar da shi, don it seems their will be strict invigilation today."

Ture mata kai Meenat ta yi, tana harararta tace; "Me kika ɗaukeni ne?"

Humaira na murmushi tace; "Ai ke ɗince kin fara ba Ni tsoro tun maganarki na jiya."

Dariya Meenat ta kyakyale dashi, tace; "Ke nifa I was just kidding, I never meant what I said."

Jiya suna karatu a Library, Humaira na complaining akan wahalar course ɗin, sai Meenat ta Ciro paper, tace; "I think mu yi jotting some things down mu shiga exams da shi, don gaskiya course ɗin nan ba sauki."

Wani kallo Humaira ta yi mata, irin kallon Are you for real, sai ta mayar da papern jakarta tana dariya.

Meenat ce ta fara fita daga exam hall ɗin don exams ɗin was not as hard as she thought would be.
Tana zaune a ɗaya daga cikin garden da suka saba zama da Humaira a department ɗin friend ɗinta Fahad ya fito yayi joining ɗinta, suna zaune suna hira a wajen for over twenty minutes sai ga Humaira ta ƙaraso, tana murmushi tace; "How was the paper?"

Meenat ta yi murmushi tace; "Alhamdulillah, duk abinda mu ka karanta shi ya fita."

Ɗan kallon Fahad Humaira ta yi tace; "Ina wuni." Sannan ta miƙe tace; "Bari na tafi gida, yamma na yi, I will try to visit you before going back home."
Meenat ma ta miƙe, tace; "Mu je Fahad ya dropping ɗinmu." Ta kalle Fahad ta langwaɓar da kai tace; "ka taimaka please."

Murmushi yayi, yace; "I will gladly do that."
Humaira ba don ta so ba, amma saboda kar su Meenat su feeling bad ta bisu zuwa inda Fahad ya yi parking motarsa.
Saida suka fara dropping Humaira a gida kafin suka wuce tasu unguwar, Meenat da Humaira ƴan unguwa ɗaya ne, few houses ne a tsakaninsu.

Washegari da sassafe Humaira na wanke-wanke kwanukan da suka yi breakfast, Laurat na ɗauraye mata, suka ji sallamar Ya Kabir kamar daga sama.
Humaira juyowa tayi don tabbatar ko kunnenta ya ji daidai aikuwa idonta ya sauka akan Kabir da ya shigo bayan Umma A'i dake tankade a gefe ta amsa masa, da gudu ta tashi taje ta rungumeshi.
Murmushi yayi ya rungumeta shima yace; "Humairan Inna, na same ku lafiya?"

"Lafiya ƙalau alhamdulillah, ya hanya?" Humaira ta faɗa cike da farin cikin ganin wani daga gidansu bayan watanni huɗu.

Kabir ya ƙarasa ciki suka gaisa da Umma A'i, ya shiga falon Abba da bai riga da ya fita ko ba suka gaisa, sannan ya sanar dashi yazo ya tafi da Humaira ne, saboda jibi In Sha Allah za ta je garinsu Ummanta.

Abba ya girgiza kai yace; "Kun sangarta Humaira sosai fa, ace yarinyar dake jami'a ba za ta iya tafiya gida da kanta ba sai an zo daukanta?"
Kabir ya sunkuyar da kai yana murmushi bai ce komai ba.
"TOH ka faɗa mata ta shirya ku tafi. Ga wannan ku ƙara kudin mota don ba lallai idan kun tashi tafiya ina gida ba." Malam Sadi ya faɗa yana miƙawa Kabir dubu biyu da ya ciro daga aljihunsa.
Ƙin karɓa Kabir ya yi; "Yace da ka bar shi Baba kar hidimar ta yi yawa."

A gurguje su Laurat suka taya Humaira haɗa kayanta, suka raƙasu har ƙofar gida suka shiga adaidaitan da zai kai su tasha, suna ɗaga musu hannu har suka fita daga unguwar, HUMAIRA ta kalle Kabir tace; "Ba ka faɗa min yau zaka zo ba."

Yana kallon titi yace; "Ba sai na faɗa miki in zan zo ba."

"TOH what if da ka zo ban gama exams ba?"

"Ai na san kin gama shi yasa na zo ɗin, ko kin manta kin faɗa min cewa jiya za ki gama?"

Hannu tayi alamar ta manta, ta buɗe zobon da Umma A'i ta ba ta, ta fara shan abinta tana kallon titi.

KAR FA ZEE TA ƘURE HAKURIN HUNAIF 

FINALLY HUMAIRA HAVE MOVE ON 

JIKARGARBA 
***


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.