Free chapter · Read without an account

12

by Sumayya Usman · MENE NE ABIN YI..?

  *Page 12*


    
    
    "Yauwa Dad d'in Shuraimah,dama so nake inga ka d'an samu natsuwa sai muyi magana akan abin da ke faruwa a cikin gidannan komi sai k'ara lalacewa yake ,kar ma ita Shuraimah yarinyarnan tazama tamkar zautacciya komi nata a firgice take yin sa".
  "Kar dai kice min kema hankalinki ya fara karkata akan buk'atar da tazo da ita?".
    "Bahaka bane ba,inajin tsorane kar wani abu ya sameta,ka duba kaga halin da take a ciki kamar wata firgitacciya ko wacce aljanu suka shafeta".
    "Nima abin yana damuna sai dai girma da tashin hankali abin da ta d'auko ya wuce tunaninta da kwakwalwarta ma gaba d'aya,shiyasa  na kasa goya mata baya".
    "Eh na fahimci hakan nima tunkafin ta tunkareka da maganar,ganin halin da take ciki a yanzu yasa nafara zargin wannan kuraman banzan".
    "Kamar ya ban gane ba?".
    "Shigowarsa rayuwarta ne ya sa komi nata ya lalace ta rasa aikinta,natsuwarta,kwanciyar hankalinta,walwalarta hatta da arzikin da muke dashi da wanda itama take dashi duk ta daina amfani da su,intakaice maka komi na rayuwarta bashi da amfani ,in ba shi ba to tayaya bazan zargeshi ba ko inga laifinsa?".
    Kai³ ku dai mata akwai ku da tsirfa kala da kala,amma in banda haka wannan yaron ina ruwansa?,dubi irin rayuwar da yake yi ko acikin gidannan,kofa acikin kurame y'an uwansa shi abin tausayi ne duk hayaniya,rashin hakuri da rashin yarda ta kurman mutum shi ba ruwansa taya zaki jefeshi da irin wannan munmunan zancen?".
    "Nifa ba wannan maganar da kakeyi ne a gabana ba,duk wani abu da ya shafeshi matsalarsace can,ni babu ruwana dashi bai shafe ni ba ko kad'an,ni matsala d'aya d'iyata Shuraimah da abin da ya same ta".
    "To naji bata shafeki ba,yanzu fad'a min abin da kike so,sai dai kar ki manta k'udirin Shuraimah ba abune mai sauk'i ba,ni narasa yaushe kika fara damuwa da lamarin y'ar taki ba har haka?",ya k'arasa zancensa cikin sigar zolaya.
    "Gani nayi rayuwarta na neman salwanta a aikin banza shiyasa na aje kawaici da kara a gefe guda".
    "Kai haba,taya yarinya na  ceton rai sai ke kuma ki kira shi da aikin banza?".
  " Wlh wannan ba ceton rai bane ba cutar da kai ne kawai gwarama ka sallamesa ya bar gidannan,in yaso in ta daina ganinsa gabad'aya ko hankalinta ya dawo jikinta mu samu sauk'i".
"Subahanallahi lalle naga alamar ba so kike zancennan yak'are ba,so kike ya k'ara lalacewa gabad'aya,a yanzu ma tana ganinsa suna rayuwa a wuri guda ana samun irin wad'annan tarin matsalolin shine kuma zaki kawo wannan zancen to kar in k'ara jin makamantansu".
   
    "Allah Dad d'in Shuraimah ban yarda da wannan kuraman banzan ba,da akwai wani abu acikin zuciyarsa,nakasa yarda dashi acikin zuciyata".
        "Na fad'a miki kar ki k'ara tarata da irin wannan maganar,ki natsu ki nemo mafita tunkafin lokaci ya k'ure maki ,don bazaki had'a kai dani a aikata irin wannan ta'asar ba",yana gama maganar da zai yi ya juya mata baya gami da Jan duvet ya lullu'be jikinsa.
   Tsuru Mom tayi tana kallonsa zuciyarta a cunkushe take tana ta sak'a mata abubuwa da dama wanda ita kad'ai tasan meye acikinta,ta d'auki lokaci mai tsawo kafin ta kwanta sai dai tana kwanciya ta mik'e ta d'auki waya kamar zatai making call sai ta fasa tayi hakan kusan so ukku amma ta kasa kiran,daga k'arshe dole hakura tayi ta kwanta amma koda ta kwanta ta kasa barcin sai motse-motse kawai take.

    Washe gari Mom da Dad suna dinning room suna break fast Shuraimah ta fad'o ciki kamar wacce aka turo,kusan duk sai da suka firgita cikin yanayin fushi Mom ta dubeta tana cewa,"wai uban me yake damun ki haka ne Shuraimah ,ko so kike da k'arfi da yaji sai kin haukata kanki kin koma mahaukaciyar gaske,sannan hankalinki zai kwanta?".
    "Mom na duba kaf gidannan tun jiya da daddare banga Nadeen ba ,alamu sun nuna ma bai kwana a cikin gidanan ba".
    "Kamar ya bai kwana gida ba?",cewar Dad a tak'aice.
    "Wlh Dad tunjiya da daddare na shiga d'akinsa naga baya ciki sai nayi tunanin ko yana bathroom,yau kuma ina tashin k'ara koma sai dai yanda nabar d'akin a jiya haka na iske sa hasalima a bud'e d'akin yake,kuma na duba ko ina acikin gidannan amma ban ganshi".
    "Taya haka zata faru bayan a daren jiya ba abin da ya faru ko wani kwakkwaran motsi banji ba".
    "Har gate keeper sai da naje na tambaya ko yaga fitarsa amma yace min tun safiyar shekaran jiya rabon da yagansa,kuma tare dashi muka duba shi kaf fad'in gidannan bamu ganshi ba ".
    Duk wannan zance da'ake Mom zaune take tamkar wacce ruwa ya cinyeta ,ta kasa ko kwakkwaran motsi balle tasamu damar furta wata kalmar, maganar Dad ce ta dawo da ita daga mutuwar zaune data risketa na wucin gadi,cikin tsawa yak'ara mai-maita mata abin da yace wanda har sai data kai ga firgita, "me kika sani game da 'batan yaronnan?". 
    "Am..... uhmmmm....wlh..... Allah......ban san komi ba game da 'batansa......,hasalima nima yanzu nake jin labarin 'bacewarsa a bakin Shuraimah"......
    "Ki bud'e baki kiyi mana bayanin dazamu fahimta ba wai kiyi ta kame-kamen banza da na wofi ba",cewar Dad a d'an zafafe.
    "Dad ban gane me kake fad'a ba, kar dai ace abin da kunnena yaji kuma na fahimta shine gaskiyar abun da yake faruwa?".
    "Ki tambayi mahaifiyarki wata k'ila in kece dakanki ki ka tuhumeta zata iya baki gamsarshiyar amsa".
    Cikin hanzari na juya ina fuskantar Mom don son fahimtar asalin gaskiyar dake faruwa akan fuskarta,abin da na gani yayi matuk'ar ta da min hankali zallar rashin gaskiya da kuma tarin danasani kawai na gani kwance akan fuskanta,kasa amincewa nayi da abin da idanuwana suka nuna min har sai da na kai ga tambayarta domin samun tabbacin daga gareta,babban fatana shine in ga wata alama komi k'ank'antarta da zata k'aryata ko nuna akasin abin da nake gani kwance akan fuskakarta,sai dai Ina ban ci wannan nasarar ba domin daga k'arshe ma duk'ar da kanta kasa tayi batare da ta sami damar kallona cikin ido ba balle in saran jin wani abu daga gareta wanda hakan ya tabbatar min da gaskiyar abinda Dad ya fad'a,cikin matsanancin bak'in ciki gami da tarin damuwa da na k'ara tsintar kaina a ciki nasa hannuna na d'auki car keys tare da mayafina nayi waje ba tare da nasan ina na dosa ba.............✍✍✍✍✍
    
    
    


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.