Free chapter · Read without an account
*🪻SAWUN KEKE...🪻*
Matashi ne wanda bai wuce shekara Ashirin da Biyu kacal a duniya ba, Fari ne tas tamkar da an taɓa fatarsa wurin zai yi tabo, Allah ya yi masa baiwar kyawu irin na musamman ɗinnan, ya na da dogon hanci siriri kamar ya yi magana, sai idanunsa dara-dara fararen cikinsu karr suke sai kwarjini kamar na Namijin Zaki, bakinsa ɗan madaidaici ne a tsuke tamkar bai taɓa buɗe shi ba ma bare ya yi magana ko cin abinci, fuskarsa a ɗaure tamau kamar wanda aka yiwa Albishir da wuta.
Sanye yake cikin Farar Jallabiya tass wadda ta yi matuƙar karɓarsa kyawunsa ya ƙara fitowa tamkar balarabe. a memakon aski sai wani tumemen kitso ne ƙwalli ɗaya tal kamar rai akan nasa, zanen hannu biyu ne an ɗauke shi tin daga gabannin goshinsa har sai da ya sauka a bayansa, ya saƙu ya yi kyau sai ƙyalli da walƙiya yake, dukkan yatsun hannunsa biyar idan aka haɗa da na ɗaya hannun goma sanye suke da wasu arnakun zobuka wanda su ke wani irin sheƙi da walƙiya gami da ɗaukar idon me kallonsu, wasu sirara wasu kuma manya.
Gaɓoɓin yatsun kuwa jajir suke da jan lalle sun yi kyau kamar a sace a gudu, ko na wata macen Albarka.
a ɗan nesa da shi ta tsaya cikin muryar kuka ta ce "Akhiee! Sheikh Auwal na kiranka"
Ko gezau bai yi ba wai da sunan anyi masa magana, ta san ba zai ce uffan ba don haka ta ci gaba da tafiya.
Wata ƴar hula wadda ake kira taɓani ka ji hadisi ya zaro a Aljihunsa ya kife kansa kana ya fara takawa saɗaf-saɗaf kamar me tsoron ƙasa.
Lokacin da ya gama ƙalelejinsa ya je kiran tuni dukkan malaman da aka kira sun halarta saura shi kaɗai ake jira.
Ba tare da shakka ba ya ratsa tsakaninsu ya wuce ya dangana da Sheikh Auwal sannan ya durƙusa ba tare da ya ce cikal ba.
Girman kansa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke fusata kowa da shi, ganin yadda ya zo ya durƙusa ba tare ya ko kallesu ba ya ƙara dugunzuma Sheikh Auwal.
"Ba ka iya gaida manyanka ba?!!" Sheikh Auwal ya faɗa cikin tsawa.
tamkar dutse aka yiwa magana haka Akhiee ya yi.
Yasayyadi Jameel ya dubi Sheikh Auwal gami da cewa "Alagafarta Malam me ya faru ne?"
"Gashi nan ku tuhume shi, kisan kai ya aikata"
Sheikh Auwal ya faɗa bakinsa har rawa yake sabida tsabar ɓacin rai kamar ya fashe da kuka.
Akhiee kuwa jin wannan furucin ya sa shi saurin ɗago gwarazan idanunsa ya zubawa Sheikh Auwal ba tare da ko ƙiftawa ba, Murtukekiyar Dorinar bulalarsa ya zara cikin rufewar ido na ɓacin rai ya shiga zabga masa ta ko ina ya na faɗin ''Dena kallona mara kunya!!!, har sai yaushe na za ka shiryu ka dena abinda ka ke yi??" ya zuba masa kyawawa aƙalla goma shabiyar a jere sannan ya tsagaita ya na huci tamkar an watsawa garwashi ruwa.
Ko uffan Akhiee bai furta ba haka kuma baiyi ko motsin kirki ba, sai dai ya yi ƙasa da idanunsa saɓanin da da ya yi wa Sheikh Auwal ƙiri-ƙiri da su.
Sheikh Auwal ya na ja baya, Sayyadi Muhsin ya ƙara ararsa, dukansa yake ba ji ba gani tamkar ba ɗan mutum ba, sai da daka iyayinsa ya gaji kana ya yi gefe, Shima Yasayyadi Jameel ya zabareshi.
Duk yawan malaman ba wanda bai dake shi ba sai dai wani ya fi wani yi da yawa.
Duka suka yi masa wanda in wani aka yiwa ba zai iya miƙewa daga gurin ba sai dai a ɗebe shi, in an ɗebeshin sai Asibiti don sai ya yi jinya.
Ba don sun huce takaicinsu ba dole su ka ƙyale shi don in su ka ci gaba da dukansa ma su za su ci gaba da shan wahala.
Akhiee kam ya na durƙushe a inda yake bai yi yunƙurin guduwa ko ramawa ba haka bai buɗi baki ba bare ya ce su yi haƙuri, ba za a ce dukan baya shigarsa ba duba da yadda fuskarsa ta yi wani irin jaa, idanunsa kuwa sun rikiɗe sun canja kala sunyi murtuk, farar Jallabiyar jikinsa ta sirka da jan jini sabida farfasa masa fata da su ka yi.
Mutanen aji kuwa tamkar ba a taɓa halittarsu ba, sun yi tsitt wasu na kuka wasu hawaye wasu kuwa da yake sun saba gani ba su yi kukan ba sai dai jiki ya mutu liƙis.
Cike da kyara Sheikh Auwal ya ce "Tashi ka fice min daga aji ba na son ganinka!!!"
miƙewa ya yi tangargar kamar ba shi aka yiwa wannan mugun lahanin ba, bai ce kanzil ba ya fice daga ajin, inda ya ke tsaya da ya koma ya tsaya idanunsa a ƙasa, zuciyarsa na wani irin tuƙuƙi da ruri tamkar za ta tarwatse, hannu ya sa cikin aljihunsa ya zaro haɗaɗɗiyar Wiwinsa tare da leta, ya bata wuta ya fara zuƙar abarsa ya na fesarwa cikin salo da ƙwarewa.
Sheikh Auwal ya ma rasa abin yi don haka ya yi wa ajinsa addu'a cikin gaggawa ya tashe su.
Husnee wadda take kuka kamar an sanar mata mahaifinta ya mutu ta miƙe da ƙyar ta na jan ƙafafunta da su ka yi sanyi su ka maƙale ta nufi hanyar fita, a tsawace Sheikh Auwal ya ce "Keh!!! kukan me kike wa mutane??"
Kasancewar tsoronsa ya gama kafa sansani a zuciyarta ba ta san lokacin da ta tsayar da kukan ba, cikin sauri ta ce "ba komai"
"Dawo ki zauna dokar makarantar nan ba a fita ana yi mana kuka, ko kuma ki tafi ajin sama a ci gaba da karatu da ke."
baki na rawa ta ce "Zan je saman" a cewarta da ta zauna tare da wannan azzalumin gwara ta je ajin saman ta ci gaba da karatu.
Ƙafafunta na karkarwa ta hau sama, ta zo giftawa kenan hayaƙi gami da warin wiwi su ka ziyarceta, cakkk ta tsaya ta zuba masa ido cikin tsananin tausayinsa, ta yi zurfi a tunani ba ta san lokacin da ta fara cewa "Bawan Allah me yasa ka ke yi musu laifin da za su yi maka irin wannan dukan?? meyesa su na gama yi maka faɗa ka ke ƙara maimaita wani kuskuren? nan fa Islamiyya ce ka ke shaye-shaye a cikinta" ta yi maganar cikin sigar nasiha da lallami.
idanunsa masu barazanar kauda ganin duk wanda ya kallesu ya zuba mata har na wani lokaci sannan ya kauda kai ba tare da ya ce kanzil ba.
Rausayar da kai ta yi za ta ci gaba da magana ya yarfa hannunsa gami da yin taku biyu ya matsa gefe.
Tsillll!! ta ji wani abu tamkar kibiya ya soki ƙwayar idonta ɗaya, ta yi saurin dafe idon tare da yin ƴar ƙaramar ƙara, Akhiee ya sake kallonta ya kauda kai ya ci gaba da busa hayaƙinsa.
Murza idon ta fara yi sai ta ji zafin ya ɗauke kamar cirar ƙaya sai da wani irin hawaye sharr!!! sharrr!!! da ya fara zuba daga iyakacin ido ɗayan kamar almara.
Ta kuma ɗaga ido za ta kalleshi ta ji an finciketa, wani aji da babu mutane Zara ta ja ta, sai da ta ɗan sarata kana ta ce "Kar ki kuma zuwa kusa da wancan, kin ga ya lahanta miki ido ɗaya idan ki ka ƙara kallonsa zai lahanta ɗayan, ke kinyi sa'a ma wata ana kiranta Husaina Isah wallahi makantata ya yi dulum, sanadin dena zuwanta makarantar nan kenan, amma daga baya ta warke, ki yiwa kanki arziki kar ki ƙara yi masa magana kar ya cutar da ke a banza."
Husneee ba ta ɗauki batun Zara da gasken gaske ba a cewarta ta ya daga kallonsa zai makanta mutum? kuma tayaya ma za a ce shine ya lahanta mata ido bayan ko kusa da ita bai zo ba hasalima sai ƙara matsawa can ya yi.
a halin yanzu tausayin Akhiee shine a gabanta don haka ta ce "Ni ba na son ƙarya, haba don kun tsane shi sai ku yi ta yi masa abinda kuka ga dama? wai shin shi ba shi da ƴan uwa da iyaye ne da malamai ke yi masa wannan dabban dukan??"
Murmushi me tafe da hawaye Zara ta yi sannan ta ce "Sheikh Auwal, Yasayyadi Jameel, Yasayyadi Usman, da kuma ni kaina da ki ke tunanin ƙazafi na yi masa, duk ƴan uwansa ne, ni ƙanwar Akhiee ce su kuma yayyensa ne, dalilin da ya sa ma muke ce masa Akhiee sunan Babanmu ya ci, amma wasu za ki ji suna kiransa Muhammad Muhammad, wallahi ina son ɗan uwana ba zan iya yi masa sharri ba da gaske nake shine ya makanta Husaina, ina gaya miki ne ba don komai ba sai don kar ki kai kanki inda za ki illata, Akhiee haɗari gare shi fiye da zaton masu zato."
Cikin takaici Husnee ta ce "Amma kun ji jiki wallahi, ashe ku ne ƴan uwansa amma kuke masa wannan abin?? to ni ba zan taɓa yarda shi ya makantata ko kuma shi ya tsokane min ido ba har sai na gani da idona ko kuma ya faɗa min da bakinsa."
Rausayar da kai Zara ta yi ta na shirin yin magana su ka ji jiniyar ƴan sanda, durummm!!! zuciyarsu ta buga a tare, Husnee ta yo waje cikin sauri, ta na fitowa ta tarar Akhiee...