Free chapter · Read without an account
12
Free Book.
*12*
Bayan ta gama jera komai a dining ta zo ta tsuguna gaban Hajiya Madina.
"Maama komai ya kammala". Sunan da yaranta ke kiranta da shi itama da shi ta ke kiranta, Hajiya Madinar ta faɗa mata haka a watarana, sanda take ce mata.
"Fullo ban taɓa ƴar aikin da nake jinta tamkar ƴar cikina ba irinki, saboda haka daga yau Hajiya ya fita daga bakinki, ki dinga kirana da Maama kamar yadda kika ji ƴaƴana na ce min kin ji".
Hajiya Madina ta shiga kallonta ta wutsiyar idonta ba tare da ta amsawa maganarta ba, Fullo kuma dai har yanzu tana nan durƙushe bata motsa ba, kuma tunaninta bai bata ko Hajiya Madinar bata ji ba ne, a'a ta san ta ji kawai dai a jininsu ne basa amsa maka nan take sai sun ɗan ɗau lokaci.
"Oak tom, ki je ki zuba naki ki ci".
Abin da Hajiya Madina ta ce da ita kenan. Ta miƙe ta wuce, sannan suma suka nufa dining, by the time Turaki har ya gama nasa, yana zaune wajen yana aikin danna waya.
Suna cikin yin breakfast ɗin ne wayar Nihal tayi ƙara, ganin sunan da ke yawo jikin screen ɗin wayar gabanta ya faɗi, jikinta na rawa ta kai hannu tana gyara zaman medical glass nata, ta cikinsa ta ke kallon Hajiya Madina wacce ta dakata da cin abincin tana yi mata wani duba ta ƙasan ido.
Duk ta dabarbarce, tsoronta Allah tsoronta kar ta ce ta miƙa mata wayar.
Saboda haka tayi saurin kai hannu tayi mute na ringing ɗin, sai dai kamin ta ɗauke hannunta daga kan wayar sabon kira ya ƙara shigowa. Babu shiri ta haɗiye wani dunƙulallan yawu tare da rufe ido.
Kuma kamin ta buɗe maganar Hajiya Madina ta shiga cikin kunnuwanta.
"Give me the phone". Kamar zata yi kuka ta ɗauki wayar hannu na rawa ta miƙa mata.
Hajiya Madina ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta miƙawa Khalil, ya karɓa ya saka a aljihunsa.
Har suka kammala breakfast ɗin babu wani wanda yayi motsi na hira ko kuma tsokanar juna kamar yadda suka saba da mahaifiyar ta su, saboda yanayin da ta tashi da shi yau sun kasa gane kanta, ga shi Nihal ta ƙara dagula musu ita.
Samha ta ɗaga landline en dake gefensu ta kira wayar ɗakin ma'aikata. Bugun da bai wuce biyu ba Fullo da ke can ta ɗaga.
"Ke ki zo mun kammala". Abin da ta ce da Fullo kenan ta kashe wayar. Wanda a ɓangarenta azamar tashin take yi saboda tana lissafe ne da lokaci, su kan ɗauki minti ashirin a dining, kuma buƙatarsu da zarar sun kammala da shi ayi clearing wurin.
Tana shigowa parlon Hajiya Madina na shirin hawa upstairs, ta kalleta ta ce mata.
"Idan kin gama ki sameni a ɗaki".
Fullo ta amsa da,"Tou". Sannan ta shiga gyara wajen.
Komai nata cikin sanyin jiki take yinsa amma kuma nan da nan take gama abu, tana gama wanke-wanke bata tsaya ɗora lunch ba tun da ta san basa nan kuma bai wuce su yo takeaway na dinner ba idan sun tashi dawowa.
Zata wuce ɗakin Hajiya Madina Khalil dake parlon a zaune shi ɗaya ya tsayar da ita.
"Sojan rana zo nan".
Ta tsaya daga hawa saman ta juyo da murmushi fuskarta, abun da ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus ɗin irin na sauran ƴan aikin da suka yi a baya.
Har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce,"Hamma Khalil ga ni". Ta faɗi sunan nasa kamar yadda ta ji ƙannensa na faɗa masa.
Ya ce,"Ai nayi zaton ko kina ciwon baki ne". Ya faɗa da salon zolaya.
Ta murmusa da cewan,"Ciwon baki kuma?".
Ya ce,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi".
Ta saki murmushi mai faɗi da cewar,"Hamma Khalil to ai kai ne kake faɗin sunan da ba nawa ba, shisa sai na yi zaton ko bada ni kake ba".
Shima murmusawar yayi kafin ya ce,"Yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana mai zai yi zato? Kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne".
Murmushi kawai tayi bata ce komai ba.
"Anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?".
Furucin da yayi yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa.
"Bana zuwa makaranta ai".
Da mamaki ya kalleta,"Gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?".
Ta ɗaga masa kai tabbacin hakan.
Ya girgiza kansa,"To islamiya fa?".
Ruwan hawaye ya cika idonta kafin ta ce,"Nayi islamiya kamin Ummi ta rasu, kuma itama tana yi min a gida".
Ya ce,"Wace Ummi?".
Sai da tasa hannu ta goge hawaye tukunna ta ce,"Mahaifiyata".
Lokaci ɗaya tausayinta ya kama shi. "Allah ya jiƙanta".
Ta amsa da,"Amin na gode, Allah yaja da ran su Baffa".
Shima ya amsa da,"Amin na gode. amma kuma idan baki je makarantar boko ba ta ya aka yi ranar nan kika karanta saƙon da Maama ta bar miki?".
Ta ja yatsanta na tsakiya bata ce komai ba. Ya katse shirun,"Tambayarki na ke".
Murya a hankali ta ce,"Wanda zan aura ne ya fara koya min yadda zanyi karatu, kuma daga baya sai muka daina saboda ayyuka da suka yi masa yawa".
Kalmar wanda zan aura ta ba shi mamaki. To amma sai dai aure wa ƙaramar yarinya kamar wannan a wajen ƴan ƙauye ba wani abu bane, wataƙila da ace ba anan suke zaune ba yanzu haka tana da ƴaƴa. Ya sauke numfashi ya ce,"Yayi ƙoƙari shi wanda za ki aura ɗin. Yanzu yaushe ne bikin?".
Ta ce,"Ba'a tsayar ba tukunna amma dai da an kusa wani dalili yasa aka ɗaga".
Ta faɗi hakan idonta na kawo ruwa sosai, kuka take son yi a lokacin amma saboda Khalil ɗin ta hana kukan samun ƴancin fita daga bakinta, domin bata so ya gano wani ciwo da rayuwarta ke ɗauke da shi.
Ya ɗaga kafaɗarsa ya ajiye wayarsa sannan ya fuskantota gaba ɗaya.
"To kin san menene? Mu a gidan nan idan mutum zai yi aiki dole sai yana karatu, ki je ki tambayi duk wanda ya taɓa aiki anan, haka tsarin Baffa yake. And dalilin da ya sa ma ina ga Maama bata yi miki zancen ba kwana biyu aiki ya sha kanta ne, amma yanzu idan kin je ki tuna mata, akwai Malamin da yake zuwa yana yi muku karatu".
Ta ɗago ido tana kallonsa, kamar bata fahimci me yake son cewa ba. Ya ɗaga mata gira,"Ehh idan kin je ki cewa Maama ke ba ki yi karatu ba".
Ta gyaɗa kai kawai sannan ta miƙe zata wuce. Turaki ya shigo parlon a lokacin yana waya. Ta gabansa ta wuce tana ji yana cewa,"Me zan yi da yarinyar da bata waye ba, ka bar wannan batun she is not my type. Imfact ni babu aure ma a lissafin rayuwata".
Hannuwan Fillo suka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta buɗe, tayi sallama amma ba'a amsa ba. Hakan yasa tasa kai zuwa ciki ƙafafuwanta na luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin dake malale a duka ɗakin tun daga bakin ƙofa, kai ka ce cikin auduga kake sanya ƙafa saboda tsabagen taushi.
Tayi tsaye daga nan bakin ƙofar bayan ta maida ƙofar ta rufe, jikinta take takurewa saboda yanda sanyin ac ke ratsata. ta kusan minti uku tsaye sannan Hajiya Madina ta fito daga wata ƙofa da idan ba sani kayi ba, ba zaka ce ƙofa ba ce. Da sauri ta durƙusa a ƙasa tana kama gefen zanenta ta riƙe. Dalilin wani abu da yayi duka acikin kanta sanadin furucin da ta ji Hajiya Madina tayi acikin wayar da ta ɗauka yanzu da aka kira.
"Asiri fa kika ce Lubna, wa ya faɗa miki?".
Abin da Hajiya Madinan ta faɗa kenan cikin muryar razani, amma ita a wannan lokacin kalmar asirin ce ke ta maimaituwa acikin kwanyar kanta, lokaci guda kuma hankalinta ya gushe daga cikin ɗakin ta lula wani wurin can daban da tunanin abin da ya danganci asirin.
"To shikenan Allah dai ya kyauta. Ni ma kinga zamu je gidan Alhaji Babba ne akan lamarin Hammansu, sam yaƙi aure kuma ko zancen auren baya so ayi masa, mun rasa kuma dalilinsa dan ko jiya sun fi awa shi da Baffansa kan ya sanar masa da dalilinsa ya ce shi babu komai haka ɗaya, sannan babbar matsalar duk wannan nacin ibadar tasa yanzu ba yayi, sai ki ga ko sallah ake yana zaune. To shine Boɗejo ke ganin abun kamar ba lafiya ba".
Hajiya Madina ta faɗawa ƙawarta Lubna da suke wayar.
Daga ɓangaren Lubna ɗin ta ce,"Subhanallah, gaskiya kam dai wannan labari ba lafiya ba a tashi a nemi magani, namiji har namiji kamar Turaki ace baya son aure, ai lamarin akwai duba. Allah dai ya kawo komai da sauƙi".
Hajiya Madina ta ce,"Amin ya Allah. Shikenan sai mun ƙara yin waya, dan Allah karki manta da saƙon nan ki bayar akai musu".
Daga ɓangaren Lubna ta sake cewa wani abu, sannan Hajiya Madina ta ce,"Ina ta ƙoƙarin yin hakan. Sai dai ina tsoro Lubna, ban san mutanen da ke bibiyar rayuwarsa ba, haka ban san wanne irin shiri suke yi akansa ba, dalilin da yasa na dage akan cewar ya haƙura da kowanne irin aiki zamansa a gida shine kwanciyar hankalinmu, haka kuma shima a nasa ɓangaren wannan ne kaɗai tsaron da zai samu. Wallahi ba ki ga munin last accident ɗin da yayi ba, Lubna sai da na gama cire rai da shi tukunna ya farfaɗo. Amma akan maganar wannan company ɗin da Baffa ke cewa zai buɗe musu wataƙila na yarda ya zama jagoran ciki in har bai ɗara daga state ɗin nan ba, amma muddin wani gari ko wata ƙasa ce can daban hakan ba zai yiwu ba".
Haka suka ci gama da tattaunawa tsawon mintuna kafin suyi sallama. Ta ajiye wayar tana mai cewa da Fullo,"Buɗe wancan closet ɗin ki ɗauko min wasu takardu daga sama".
Ta miƙe dan cika umarninta, tana ɗauko takardun tana mamakin irin jama'ar da Allah ya bawa Hajiya Madina, ko da yaushe acikin yin waya take, inda take gani da ita ce gaskiya ba zata iya ba, domin idan kunnenta bai ciwo ba to bakinta zai yi. Yanzu fa ta gama waya ko minti biyu ba'a ƙara ba amma har an kuma kiranta.
"Zan bar su a gida, akwai yarinya idan ka zo zata baka".
Abin da take cewa da na wayar kenan, kuma lokacin da Fullon ta ƙaraso ta durƙusa ta bata takardun.
"Alright sai ka zo".
Daga haka wayar ta su ta yanke, ta dubi Fullo ta ce da ita,"Gobe za ki fara ɗaukar karatu a gidan nan, ba ke ɗaya ba ce akwai wata sabuwar ƴar aiki da za'a kawo anjima za ku ci gaba da aiki tare. Bana son fitina Halima, bana son kuskure, ki kula da hakan. Karatun boko da arabiya zai ke yi muku. Ki tsaya ki maida hankali, domin akwai aikin da nake so ki yi min, aiki ne na masu ilimin boko, idan kin mayar da hankali, idan har kinyi nasarar samunsa Halima za ki sha mamakin yarda zan mayar da ke, duniyarki zata sauya, za ki zama abar kwantance, bayanki zai zama tarihi, idan kuma akasin hakan, tabbas ina mai tausaya miki da asara mafi girma da za ki yi a rayuwarki".
Fullo so take ta ɗago ta kalleta amma ta kasa, jan yatsunta kawai take. "Ungo wannan".
Sai a sannan ta ɗago tasa hannu biyu ta karɓi takardun.
"Ki adana su, zuwa ƙarfe biyar na yamma akwai wani zai zo ya karɓa, baƙi ne dogo yana da ƙasumba. Ba shi kawai na ce ki yi, ki je masa da fuskar mutumcinki Halima. Na san kin gane lissafina".
Kan Fullo a ƙasa ta ce,"Tom Hajiya".
"Bani lafayata fara".
Fullo ta miƙe ta ɗauko ta kawo mata. Ta cikin mudubi Hajiya Madina ke ta kallonta, zuciyarta na mai jin so da tausayin yarinyar.
Bata bar kallonta ta cikin madubin ba ta ce,"Zo ki saka min wannan fil ɗin".
Fullo ta matso zuwa bayanta ta karɓi fil ɗin a hannunta sannan ta saka mata kamar yadda taga Zaytuna nayi mata a duk sanda ta saka lafaya.
Ita ta ɗaukar mata jakarta suka fito a ɗakin, suna saukowa take faɗa mata,"Akwai key ɗin ɗayan bedroom na Hammansu acikin drower na mirrow, idan mun fita ki je ki gyara masa. Don Allah ki yi gyara mai kyau, ki kaɗe duk wata ƙura".
"Tom Maama, sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya".
Har bakin mota tayi mata rakiya, Khalil ne zai ja motar dama, ta shiga tana tambayarsu.
"Ina Hammanku da Nihal?".
Sameer ya ce,"Hamma ba lallai ya san mun fito ba, amma na ga Nihal tayi wajensa da nake fitowa".
"kira min shi".
Sameer ya ɗauki waya ya kira shi, sai dai kamin ta kai ga yin magana ma ya ce ga shi nan fitowa.
Fullo kuwa tana komawa key ta ɗauka ta fito ta wuce ɓangaren Turaki, ɓangarensa dake jikin na Baffa. Tana shiga parlon ta ji maganarsa na tashi a parlon.
Tayi saɗaf ta ɓoye ta wajen wani corrido, dan har ga Allah ita ba so take suke haɗuwa ba saboda bata son wannan tsawar da yake sakar mata, yana sakata tana tunawa da moment ɗin da bata son tunawa da shi ta ke ba.
Kuma har zuwa wannan lokacin tana ƙyale shi ne kawai saboda darajar mahafiyarsa, banda haka da tuni ta nuna masa tafi ƙarfin ya dinga zaburar da ita dan kawai tana aiki ƙarƙashin arziƙinsu.
Shi da Nihal ne wadda ta ji tana roƙonsa akan dan Allah ya bawa Maama haƙuri. Maganar take tana karyewa saboda kukan dake fita daga bakinta. Ta leƙo ta ga Turakin na tsaye ne ya harɗe hannayensa ta baya yana fuskantar gabas, kansa a sama kamar mai tunani. Ita kuma Nihal gwiwoyinta na zube a ƙasa a gabansa. Kafin ya juyo gareta ya ci gaba da magana bayan shirun da tayi.
"Arziƙi da talauci duka na Allah ne, idan Allah ya baka arziƙi ba yana nufin ka fi kowa bane a cikin bayinsa, kuma ba wai an baka dama ba ne dan ka wulaƙanta wanda bai da shi ba, shima idan Allah ya so yana iya ba shi nasa rabon, ko kuma ya ƙwace daga hannun kai da kake wulaƙanta talaka ya bawa wanda ka raina. But kin san me nake so ki fahimta?".
Nihal ta ɗago da kanta tana kallonsa, sannan ta girgiza kanta alamar a'a. Shi kuma ya ci gaba,"Maama uwa ce da yau ba zata so ace ƴarta ta shiga gidan da zata wahala ba, wannan haka yake ga kowacce uwa. Burin iyaye ne ace ƴaƴansu sun yi aure sun zauna a inda za su ji daɗi, dan haka Maama bata hana alaƙarki da shi ba ne saboda yana talaka ba...".
Tun bai kai ga ƙarasawa ba ta katse maganarsa,"Allah Hammah ta ce makusarsa a wajenta shine talaucinsa, banda haka babu abin da zai hana ta barina mu'amala da shi. Kuma ni wallahi Hammah ina sonsa, shi kaɗai zuciyata ke da muradin aure".
Ya kai hannu ya shafo wuyansa yana mai lumshe ido ya buɗe. "Ba za'a hanaki aurensa ba dan kawai yana talaka, idan har na gari ne to ba shi da wani aibu a idon Baffa. Saboda haka ki kwantar da hankalinki, ta shi muje".
Ta miƙe ya kama hannunta suka fita. Fullo ta sauke ajiyar zuciya, duk yacce take tunanin mutumin nan ba haka yake ba. Shi ɗin mai kyau ne, kuma ta fahimci yana da kyan zuciya.
Halima.hz✍🏻
***