Free chapter · Read without an account
14
Free Book.
*14*
Fullo tasa hannu ta goge hawayen dake fuskarta, ta ɗaga kai tana bin wayar dake ringing da ido, tunani take yi akan ta je ta ɗaga ko ta bari, ɗaya ɓari na zuciyarta ya rinjayeta akan ta je ta ɗaga ɗin.
Saboda haka ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta a mace, bata ma ko iya ɗaga ƙafa sai janta take yi har ta ƙarasa inda wayar take manne a bango.
Ta kai hannu ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina ta kaɓe abin da ke jikin zaninta sannan ta ce,"Fullo".
Jin muryarta a cikin wayar yasa Fullo saurin saita natsuwarta, sai da ta gyara muryarta sosai sannan ta amsa kiran.
"Na'am Maama".
Hajiya Madina tamkar tana kallonta ne a lokacin, don tana jin muryartata tunaninta ya bata kamar da wani abu, apple ne a hannunta a lokacin, amma cikin wani irin zullumi ta ajiye tana tambayar Fullo,"Kuka kike yi?".
Fullo ta haɗiye wani abu sannan ta ƙara gyara muryarta tukunna ta ce,"A'a Maama".
Hajiya Madina ta ce,"Amma ya aka yi na ji muryarki wani iri, wani abu ya faru ne? Ko ba kya jin daɗi?".
Ta jero tambayoyin ga Fullo muryarta na fita da sautin dake nuna damuwa da kulawa.
Kamar tana gabanta ta girgiza kanta ta ce,"A'a Maama lafiya lau".
Ta faɗa cike da mamakin yadda aka yi Hajiya Madinan ta gane kuka a cikin voice ɗinta farat ɗaya, dan har sai da ta kai ga ta kalli wayar, to ko dai tana kallonta ne.
Hajiya Madina ta ƙara cewa,"Tiles ɗin nan suna da tsantsi sosai, I forgot to tell you that. Allah yasa ba faɗuwa kika yi ba wajen yin mopping?"
Duk da cewar bata fahimci ɗan guntun turancin ba amma ƙarashen maganar ya fahimyar da ita dukkan maganar.
Ta ce,"A'a Maama nayi takatsantsan, har na gama ban zame ba".
Hajiya Madina ta ce,"To yayi kyau, kin gama aikin?".
Ta ce,"Ehh yanzu nake shirin rufe ɗakin".
Hajiya Madina ta sake cewa,"Mai amsar saƙon da na baki ya zo yana ta jiranki, ki je ki kai masa sannan ki ƙarasa aikin. Mu ma mun kusa dawowa muna jira Boɗejo ta shirya ne tare zamu taho".
Ta ce,"Tom Maama Allah ya dawo da ku lafiya".
Da haka wayar tasu ta katse, Fullo tabi wayar da kallo tana jin son Hajiya Madina har cikin ranta, a iya ɗan zaman da tayi ta gama karantar matar, zata rantse duk wanda ya faɗi aibun Hajiya Madina to ɗan hassadarta ne.
Macece da bata da ɗagawa ko kaɗan, bata tunƙaho da arziƙinsu, bata wulaƙanta talaka, bata da ƙasƙanci, kowa nata ne, kowa ganinsa take ɗaya suke, kowa sonsa take yi, mutumta duk wanda yake tare da ita take yi babu tozarci.
Ƙasa ta duƙa ta tattara takardun ta mayar cikin file ɗin da suka faɗo, sannan ta mayar cikin wata drower daban da wadda suke ciki da.
Ta fita daga ɗakin jiki a saɓule, da ƙyar ma take yin tafiyar tamkar mai ƙarancin jini a jiki, tana saukowa daga upstairs ɗin ne cikin tsautsayi ta gurɗe ƙafa.
Bakinta ya furta bismillah kafin ƴar ƙarar da ta saki ta biyo baya. Cikin jin zafi da raɗaɗi na lokaci guda ta riƙe ƙafar tana cije fuska.
Gurɗewar ba ƙarama ba ce, dalilin da yasa idanuwanta suka cika da tarin hawaye kenan, wani sabon kukan ya ƙaru akan wanda zuciyarta bata gama yinsa ba, sai da ta ɗauki kusan minti huɗu sannan ta tashi ta sakko da ƙyar sai ɗingisa ƙafar take yi, sai da ta kashe light na parlon tukunna ta bar side ɗin.
A ƙofar ɗakin mai gadi ta tarar da mutumin, baƙi ne kamar yadda Hajiya Madina ta sanar mata, yana da curar ƙasumba, fuskarsa kuma sam babu fara'a. Mai gadi dake jin radio ganinta yasa shi yin murmushi, ta rissina ta gaishe shi ya amsa mata yana tambayarta ya aiki, ta amsa masa da lafiya.
Sannan ta tsuguna a gaban mutumin da ko inda take bai kalla ba tun zuwanta, bata sani ba ko haka yake ko kuma ita yakewa hakan don ta ɓata masa lokaci oho.
"Ina yini".
Ya kalleta ta wutsiyar ido, kamar ba zai amsa ba can kuma ya ce,"Lafiya".
Ta fito da hannunta daga cikin hijab wanda ke ɗauke da file ta miƙa masa ta ce,"Ga shi wannan ta ce a baka".
Sai da yayi mata wani kallo kafin ya warta, ba zata kira hakan da karɓa ba sai dai warcewar, hakan kuma ya ɓata mata rai, ta miƙe cikin ɗaurewar fuska.
Tafiyarta zata yi, ba zata ƙara ko da ɗigon minti anan ba, cewar ita ƴar aiki ce hakan ba yana nufin a dinga wulaƙantata ba. Ta sani ita ba wata ba ce, ba ƴar wani ba ce, amma wallahi tafi ƙarfin wulaƙantawar kowanne kalar mahaluƙi, talauci ai ba hauka bane, dan haka yanda bata wulaƙanci haka ba zata yarda a wulaƙanta matsayinta ba ko da wasa, ita ƴar mutunci ce kuma da darajarta, aiki suke ake biyansu ba wai roƙo suke ba.
Saboda haka yanda ya warce bai karɓa da arziƙi ba, haka itama zata bar wajen ba tare da ta jira nasa saƙon ba in ma yana da shi, ai dama ce akai kawai ta ba shi, to idan ma yana da wani abin faɗa sai ya jira Hajiyar ta dawo ya bata, amma ba dai ita Fullo ta jira karɓar nasa saƙon ba.
Abin da bata sani ba a wannan lokacin shine, tun yunƙurawar da tayi zata tashi shi kuma ya bar wajen, saboda haka ko da ta kalli inda ya zauna taga babu shi bata yi wani mamaki ba, tayi tsammanin faruwar hakan.
Ta ce da mai gadi,"Baba kayi haƙuri dan Allah ban miƙo maka abincinka ba, wallahi ina cikin aiki ne sai yanzu na samu sarari amma bari na je na kawo maka yanzu".
Tsohon ya washe bakinsa da duk haƙoran da suka ɓaci da goro ya ce,"Laa babu komai ƴar nan, karki damu".
Juyowar da zata yi kawai taga mutum tsaye a bayanta ya harɗe hannaye a ƙirji, da tsananin mamaki take kallonsa from head to toe, baki buɗe ta kasa rufewa, ya zata kira yanayin da ta shiga a yanxu? ta san dai gefe ɗaya farin ciki ne ya lulluɓeta, to amma ɗaya yanayin fa?.
Idan ta ce ba ta kewarsa tayi ƙarya, idan ta ce bata yi murnar ganinsa ba tayi ƙarya, idan ta ce bata son ganinsa ta yaudari kanta.
Cikin wani irin emotions da take jin kanta tayi saurin saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta, murmushi kawai take yi, irin murmushkin nan mai faɗi da ke fallasa kyawun fuska, wani daɗi ne kawai ke ziyartarta, ji take yi tamkar an mata albishir da kujerar makka.
Tana son ganinsa, tana ta so ta kasance da shi amma babu dama, lokaci yayi mata ƙaranci tun da ta fara wannan aikin, rabon da ta saka shi a ido tafi sati uku, har Kaka ta gama ciwonta basu haɗu ba, duk da cewar kullum sai ya zo dubiya, sai dai idan ta koma Kaka ta bata sallahun saƙon gaisuwarsa da ya bar mata.
Allah ya sa ni sai yanzu da ta gansa take jin tamkar ta ɗauki shekaru bata gansa ba, kuma Allah ya sani a yanzu ji take yi kamar ta rungume shi don tsananin farin ciki, ta ya ya? Ta ya ya zata nuna masa irin jin daɗin da ta yi na ganinsa?.
Ta ramin yatsunta take hango fuskarsa da gaba ɗaya babu walwala, lokaci guda tasha jinin jikinta, wanne irin bayani zata yi masa ya fahimta? Ko me zata ce ba lallai ya gane ba, abu ɗaya kawai tasan yana ransa shine yanzu ta fifita aiki akansa.
Sai kawai jikinta yay sanyi, still hannunta na rufe da fuskarta tayi ƙasa da kanta tana jin kamar tayi kuka. Bata yi aune ba ta ji faruwar al'amarin da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu ita da shi, hannunta ya ruƙo, wannan hannun nata da bai taɓa riƙewa ba tsawon lokacin da suka ɗauka tare, me zata yi yanzu? Zata sakar masa hannun ne ya sauke kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi ko kuwa zata hana hakan? Domin gani take kamar ba zata iya haɗa ido da shi ba, kunyarsa take ji sosai, kunyar riƙe ma ta hannu da yayi, tana ganin tamkar sun aikata wani babban alfasha ne.
Idanuwanta suka ciko da ruwa, ta shiga ƙiftasu a hankali, dai-dai lokacin kuma da ya sauke hannun nata daga kan fuskarta, kallonta yake har yanzu, ya kasa ko da ƙiftawa, ji yake kamar ya ɗauketa, ji yake kamar ya sureta ya kaita duniyar da babu kowa aciki daga shi sai ita.
A ƙoƙarinta na zame hannunta daga nasa ta ɗago ido tana kallonsa, kamar ruwa take gani a nasa idon shima? Kamar yana so yayi kuka ne? Kamar rauni ne take gani a ƙwayar idon nasa? Kenan shima yayi kewarta har irin haka?.
Shi kuwa kallon da take yi masa gani yake kamar tana masa kallon tuhuma ne, me yasa ya zo nan? Me yasa ya biyota? Me yasa bai tambayi izininta ba?
Ai tun kamin ya zo ɗin sai da ya shiryawa amsa waɗannan tambayoyin, ya kuma san zata yi masa rangwame ko da zata hukuntansa.
Ya rumtse idanuwansa tare da ƙara riƙe hannunta sosai yana murzawa sannan ya ce,"Ki yi haƙuri, na kasa ci gaba da jurewa shi yasa na biyo ki".
Cikin sanyayyar murya ta ce,"Hannuna".
Sai ta ji ya ce,"Ba zan iya saki ba Halimatu, wallahi ba zan iya ba. Don Allah ki barni".
Ba tare da ta ɗago kanta daga sunkuyen ba ta raba hannayen na su, sannan ta ce,"Me yasa to baka tambaye ni ba kafin...".
Bata ƙarasa ba ya katseta,"Naga zan mutu shi yasa, kuma bana so na mutu ban mallakeki ba, ba kuma na so na mutu ba muyi sallama ba. Ina ta son ganinki, ina ta so nayi magana da ke, amma wannan aikin yabi ya toshe kowacce ƙofa, ita kuma zuciyata sai zafi take tana kukan rashinki, shisa yau na ce babu abin da zai min shamaki da ganinki ko da ace fadar sarkin gombe kike aiki yau sai na shigeta na ganki, daga nan kuma nima sai na nemi taimakon a ɗauke ni aikin muke yi tare ina rage miki, ta yanda zanke samun ganinki ko da yaushe. Na zo da complete takarduna, please ki yi min iso ko Allah zai sa a dace".
Ta kalleshi tana murmushi, da gaske yake babu wasa a maganarsa neman aikin ya zo. Ta kalli takardun ta ƙara kallonsa tukunna ta ce,"Ni babu takardun komai aka ɗauke ni".
Ya ce,"Arziƙin Kaka kika ci shine dalili".
Ta juya idanu sannan ta ce,"Ko da babu Kaka ni banga ana ɗaukar mai wanke-wanke da shara da takardu ba".
Ya ce,"Kuma dama na iya wanke-wanke sosai ba".
Ta saki dariya sosai tana ɗora bayan yatsunta akan bakinta. Yana kallonta har yanzu fuskarsa bata gama saki ba ya ce,"Dariya na baki? Allah da gaske na iya wanke-wanke, kuma ki tambayi Inna ki ji, idan na wanke kwano har ƙyalli yake ya dawo kamar sabo, kuma na tabbata na fiki iyawa. Saboda haka na san idan suka ɗaukeni a kwana ɗaya za su bani ɗaki a gidan nan, wataƙila ma ke su kore ki, kuma dama haka nake so dan wallahi bana ƙaunar wannan aikin".
Tayi wani murmushin ta ce,"Ka ga ni kuma ina sonsa, tun da da kuɗin muke rufawa kanmu asiri. Yanzu haka ma Kaka ta kusa siya min ƙaramin fili da kuɗin da ake ajiyewa".
Ya ɗan kauda kai gefe sannan ya dawo yana ƙara fuskantarta.
"Sau nawa kike aikin ruwa?".
Ta juya idanu sannan ta ce,"Ya danganta, ina wanke kwanuka kuma zanyi girki idan Adda Zaytuna bata yi ba, sannan kuma in wanke banɗaki guda shida, shikenan".
"Shikenan! Wannan yawan aikin shi zaki kira da shikenan Halimatu?".
Ya maimaita kalmar da mamaki.
Ta ɗaga gira,"Eh, ai babu wahala tun da ba ɗauda suke yi ba, nan da nan nake kammalawa na tafi ɗaki na huta. Saboda haka ka bar damuwa watarana sai labari".
Ya ce,"Balle ma kin kusa ki daina, very soon in sha Allahu. Na yi mafarki na zama ɗangote".
Ta waro ido tana kallonsa, ya ɗaga kai ya ce,"Da gaske, wai na koma Ɗangoten Gombe, na aureki mun bar ƙasar gaba ɗaya, muka ajiye Inna da Kaka a saudia mu kuma muka wuce London Honeymoon".
Tayi far da ido ta maimaita kalmar, "Honeymoon, kamar na taɓa jin wannan kalmar amma na manta a ina".
"Zaki ma santa ne lokacin da muka yi aure, Allah Halimatu na aureki da Uwar kuɗina a yawon shaƙatawa kawai zamu ƙare rayuwarmu, wani banzan aikin gida duk ba za kike yi ba".
Tasa hannu cike da kunya ta rufe fuska,"Ni fa yarinya ce na ce ka daina faɗa min kalmar aure".
Yayi mata harar wasa ya ce,"Kin manta ɗazu kika zo duniyar. Ai na tabbata a karatun aure babu wanda baki sani ba sai dai ki raina min wayo, sai ka ce ba aminiyar Maijidda ba".
Ta danne dariya ta ce,"Me kake nufi da Maijiddan?".
Ya ce,"Oho".
Haka su kai ta hira ba tare da sun san lokaci ya tafi ba, Fullo sam ta manta ma a inda suke, sai da mai gadi ya ankarar da su. Cike da kunyar mai gadin ta bar wajen dan idan ta biye ta Amir ba zasu tafi haka ba, yana faɗa mata wai yau subscription zai yi.
Bin ta yayi a baya yana ta murmushi, tsaye ya sameta a gate ɗin da zai shigar da kai ɓangaren ma'aikatan gidan, tana ta jan yatsun hannunta kamar yanda hakan yake ɗabi'arta ne.
Ya jingina da ƙofa yana kallonta yance,"Wai kuɗi kike lissafawa a jan yatsun nan ko me?".
Idonta na ƙasa ta jinjina kai,"Ehh kuɗin ɗangoten Gombe nake ƙirgawa".
Yayi murmushi ya ce,"Allah ya amsa".
Itama ta ce,"Amin". Sannan ta kalli yanayin garin da magriba ta ƙarato ta ce,"Mu yi Sallama su Hajiya na kan hanya, kuma akwai sauran aiki gabana".
Ya ce,"Aikin me?".
Ta ce,"Adda Samha ta bar min guga kuma tana da yawa, gata bata da sauƙi mafaɗaciya ce".
"Barkono ce ita?".
Ta ce,"Kafi barkono in ka ji ana faɗa".
Ya kalli agogonsa ya ga har ƙarfe shida da minti goma, ya sauke numfashi sannan ya ce,"To sai yaushe?".
Daga yadda yayi maganar sai yayi mugun bata tausayi, itama ba dan tana so za su yi sallamar ba, lokacin da bata fara aikin ba ai babu ruwanta da wani kallon lokaci, ko zasu kwana suna shan soyayyarsu babu mai katse su.
"kawai zan ce banda lafiya kaga zan huta ranar".
Ya ɗan zaro ido waje ya ce,"A'a bana so ki yi ƙaryar ciwo, kawai dai zan ƙara dawowa".
Ya faɗa yana jan ɗan cif-cif ɗin gemunsa. "A'a ni kam ban yarda ka zo ka ban kunya ba".
Ta faɗa tana kama gefen hijabinta.
Ya ce,"Ohh kina jin kunyar kar su ga saurayinki ba ɗan gayu ba kuma talaka ko? Alhalin ke mai kyau ce".
Tayi saurin girgiza masa kai yanayin fuskarta na sauyawa,"Ko kaɗan ba haka bane, dan Allah karka ƙara wannan tunanin Amir, ba zan ji kunyar nunaka a koma ina ne ba wallahi, kai nake so ba gayunka ko kuɗinka ba, kuma so nake maka na tsakani da Allah".
Tayi maganar kamar zata yi kuka.
"Ban ce ki zubar min da hawayenki ba, kin san suna da tsada. Na faɗa ne dan na zolaya, ki yi haƙuri".
Tayi knodding kanta kawai, kamar ba za su yi sallamar ba, sai da tayi da gaske tukunna su kai sallamar ta juya ta tafi, kuma tana cikin tafiyar ne ya dakatar da ita da tambayar me ya sami ƙafarta, dan a ɗazu bai lura ba sai yanzu.
Ta ce masa babu komai tsayuwar da su kai ne yasa ƙafar yin tsami, ba don ya yarda ba sai dan karya takura mata ya ƙyaleta.
Sai bayan isha'i mutanen gidan suka dawo, bata ma san sun dawo ba saboda lokacin tana ɗakin ƴan aiki zaune cike da kewar Kakarta, yanza basa yini tare ko kaɗan, da dare yayi sai safiya ta taho aiki.
Tayi zurfi cikin tunani ta ji wayar ɗakin na ƙara, tana ɗagawa ta ji muryar Zaytuna na cewa da ita,"Kina ina ne?".
Ta ce,"Laa Adda kun dawo".
Zaytuna ta ce,"To ki zo".
Ta ajiye wayar ta miƙe tana jan ƙafar dan sam bata so a gane ciwon dake ƙafarta.
Boɗejo kawai ta samu a parlon, ta ƙarasa ta tsuguna ta gaisheta. sannan ta tashi zata hau upstairs, Boɗejo ta tsayar da ita.
"Kinga ke ƴar nan zo kai min idon baturen nan nawa ɗakin kwana na".
Fullo ta rissina ta karɓa, Boɗejo ta kalleta ta ce,"Ke kuma zuwan yaushe?".
Ta ce,"Ban jima ba".
"Allah sarki, to sannu Allah yayi miki albarka".
Fullo ta ce,"Amin".
Boɗejo ta sake cewa,"To ɗakin nawa kin sani ne?".
Fullo ta girgiza kai alamar a'a. Boɗejo ta ɗora ƙafarta kan tumtum ɗin dake ƙasan carpet ta ce,"Can ɓangaren ƙarshe na ke kusa da su Turaki, nan suka wullani wallahi daga ni sai halina, kamar ba saurauniya ba ada".
Ta jefa wata choculate a baki ta ƙara cewa,"Ai da mijina shine sarkin garin nan, to da ya rasu ne kuma ɗana Habibu ya hau kan kujerar. Kin ganni kamar ban haɗa jini da sarauta ba ko? Wallah bata dame ni ba in faɗa miki ƴar nan, banda ma dai Allah ya ƙaddara hakan ai ba zata faru ba, sarauta ko wahala, shi yasa ko ƴar izzar nan ma ta masu sarauta banda ita, sha'anina kawai nake ba zan iya takura kaina ba wallahi, ina dalili. Mai gidan nan ai ni ya biyo, idan kika gansa ba kyace Yarima ba, shi dai Habib ɗin dama da kin gansa kinga wanda sarauta ke yawo a jininsa, ai shi wannan Yaron na gidan nan yayo, umm Turaki ba wallahi kam. Sauran yaran Ibrahimu da Samir za ki gansu kamar ƴaƴan tsintuwa".
Fullo dai murmushi take tayi, ta ji sosai tsohuwar ta burgeta.
"Ba kya magana ne?".
Fullo ta girgiza kai ta ce,"A'a ina yi Hajiya".
Boɗejo ta ce,"Au yo ni fa nace ai da an banu. Ba ki da magana dai ina ce ko? Dama ai ba kiyi kama da sauran ƴan aikin ba iyayen zuba kamar sabuwar kanya, wallahi na faɗa miki su nan suke zubewa su sakani gaba inta basu labarin masarauta wai suna so, ita surukar tawa tayi ta jin haushina, itama wannan ƴar Samha tai ta ɓata rai wai ita ba haka ƴan sarauta suke ba, to ni dai basu ishe ni kallo ba ma, dan bana bi ta kansu, ina dalili ka takura kanka akan wata banzar aba sarauta".
Fullo tayi murmushi mai sauti still dai bata ce komai ba, haka kawai ta ji tana so ta ɗauki lokaci tare da tsohuwar suna hira. Sai yanzu Boɗejo ta bata glass ɗin dake cikin box ɗinsa ta ce,"Idan kin je sai kin kunna fitilar ɗakin dan ba lallai bane an kunna min, tun da mai ta'adin Sameer baya nan can muka baro shi gidan Hakimi. Akan mudubi kawai zaki ɗora min shi kin ji, ki riƙe da kyau kar ya fashe, na huɗu kenan da Habib yasa aka yo min shi daga dubai, da yake acan ake duba min lafiyar idon".
Fullo ta ce,"To Hajiya".
Boɗejo tana kallonta sosai ta ce,"A'a wallahi sunana Rumana ko kuma ki ce min Boɗejo kamar yanda jikokina ke kirana. Ina wani batun Hajiya anan salon dai a ƙarawa mutum jin kai, ai da Hajjah suke ce min, Mai Martaba na rasuwa na rufe ido na ce ko Rumana ko wani sunan, to shine fa baturen yaron nan ɗan gidan sarki Habib ya saka min Boɗejo, da ike shi ne jikana na farko, kai izza acikin yaron nan kamar ba zai taka ƙasa ba".
Tana faɗar baturen yaro Fullo ta gane Yarima Abbas take nufi.
"Kema ɗakin kwanan masu aikin kike?".
Ta girgiza kanta,"A'a wurin Kakata nake".
"Can da nisa ne kenan?".
"A'a Boɗejo nan ɓangaren ma'aikata, nan muke da zama".
Boɗejo ta ce,"Au yo ce min zaki tsaffin bayina ne ku, to ai shikenan dama ce nake nan kike kwana na ce to ki zo ɗakina mu kwan tare dan sosai na yaba da hankalinki wallahi".
Samha ta faɗo ɗakin rai ɓace, tana jifan Fullo da wani irin kallo ta ce,"Ke dan Uwarki ina aikin da na saka ki?".
Maimakon bata amsa sai kallo da Fullo ta bita da shi, cikin ranta tana maimaita dan uwarki, kalmar da ta jima bata ji an faɗa mata ba.
"Ba magana nake miki ba?".
Fullo ta rufe ido tana jin zuciyarta na suya sannan ta buɗe ta ce,"Adda Samha ai nayi".
"Kika yi a gidan uban wa? Ban ce miki acikin trolly za ki jerasu ba, gobe da asuba zan bar ƙasar".
Sai taja tsaki ta ce,"Ni ba'a taɓa bagidajiyar ƴar aiki ba sai akanki wallahi, to minti uku na baki ki je ki kammala shiryan kaya tun ban nuna miki other side of me ba".
A sanyaye Fullo ta ce,"Ki yi haƙuri don Allah, zan gyara yanzu".
Ta faɗa tana barin parlon, guntun hawayen dake maƙale a idonta ya sauko, a rayuwar nan ko mene zaka yi mata kayi amma karka sako mahaifiyarta aciki, bata so, bata so ko kaɗan.
Kuma ɗazun sha'afa tayi gaba ɗaya, ta gama gugar sai ta zuba cikin wadrobe tana ta sauri saboda ƙafarta da ke mata zafi, amma tana ta alla alla kafin su dawo taje ta gyara.
Boɗejo ta kalli Samha ta ce,"Ki dai dinga bin duniya a hankali, ni wallahi duk ke ce mai ɗaukan duniya da zafi, su dai su Zaytuna ba su ɗorawa kansu wannan masifar ba. Yo Samha kuɗin ubanki ɗin me? Shi ya bawa kansa? To in gaya miki nan da kika ganni kafin Babana ya zama wazirin Sarki kika ganmu sai kin tsartar da yawu, to amma yau fa? Matar wa na zama kuma yanzu uwar su wa na zama? Kuma wane irin matsayi na taka?. To wallah kaɗan daga cikin ikon Allah ki ga ƴan aikin nan da kike narkawa uwar tsawa da zagi sun lula sama ke kuma kina nan ƙasa".
"Wallahi ba amin ba, wannan ai mugun baki ne Boɗejo".
Samhan ta faɗa tana wucewa ta haye sama.
Abakin side ɗin su Turaki, Fullo ta zo wucewa zuwa part ɗin Boɗejo, Khalil da ke balcony a tsaye yana waya idonsa ya sauka akanta, ya lura da yanda take ta ɗingisa ƙafa tana tafiya da ƙyar.
Ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli adadin minutes ɗin, sannan ya ce,"please hold on 2minutes".
Daga haka ya aje wayar nan kan table ya fito.
"Fullo". Kiran sunan nata ya dakatar da ita daga tafiyar, muryar Kalil ta ji, amma ko da ta juyo maimakon ta gansa sai taga Turaki na tunkaro inda take.
________________
Ina Masu sana'a su ke? Kuna so business ɗinku ya shahara ya kai inda baku yi zato ba?
Kun shirya mu taimaka maku ku isa ga dubban abokan ciniki?
Pages ɗinmu na isa ga sababbin mutane a kullum!
🎯TSARIN ADVERT/ ADVERT RATE...
▶ YouTube Channel
Advert a kowanne episode - ₦3,000
▶ TikTok Page
Advert - ₦2,000
▶ WhatsApp Status
Advert na 24 hours - ₦1,500
📚 ADVERT A PAGES NA NOVEL.
📌 Saman Page - ₦1,000
📌 Tsakiyar Page - ₦800
📌 Ƙarshen Page - ₦500
Ku tuntuɓe mu kai tsaye ta wannan lambar...***
Mai talla shi ke da riba. Ku tallata business ɗinku a yau don samun ciniki mai girma.
*Halima.hz✍🏻*
***