Free chapter · Read without an account

Page 23

by AISHA YUSUF HANWA · Gaba Kura

GABA KURA


AISHA HANWA


***

PAGE 23






 Duk yadda Munari ta yi tunanin Baba zai haƙura idan ta lallaɓa shi ya gagara karshe ma korar ta ya yi a wurin. Dawowa ɗaki ta yi tana kuka ita kuma Mama bata ce mata ta tafasa sauke ba, illa ma takaici da Munarin ta dinga bata, a ganinta ai abun farinciki ne ma ganin za"a rabata da wannan auran alaƙakai ɗin.

Abu kamar wasa sai ga shi abu na so ya tabbata tana ji tana gani Babanta ya shiga ya fita aka raba auranta da Baban Sani, a lokacin ana neman wurin wata biyar da ɓatan shi, tun ana cigiya har an haƙura an zubawa sarauta Allah idanu.

Ko da kotu ta bata takardar ta bai rabata da ƴan uwan shi ba, kusan duk sati take zuwa duba Baabar shi wanda hawan jini ya rigada ya Kaita ƙasa.


 Kullum ta yi sallah sai ta roƙi Ubangiji ya bayyana shi ya kuma bashi kariya a duk inda yake.

Su Amina sun zo sun jajanta wa juna kuma ita da Inna Hauwa suka kwaso mata kayanta a gidanta tsab.

Makwafta aka yi ta koke koke saboda an saba kuma Munari mutum ce har da rabin shi ma, babu ruwan ta da kowa harkar ta kawai take yi ba sawa babu hanawa.


 Tun da ta dawo gida bata zauna ba sana'arta ta kama. Ta san zaman ba zai mata ba, gidan dai ta bari shi ne ta dawo mawa ta san komai dole idan kana so sai ka tashi ka yi kamar kana yi.


Babu wanda ya hanata domin watarana ma a hannunta Mama ke samun kuɗin da take ƙarawa a na cefane.

Rayuwar gidan kadaran kadahan babu mai zaginta ko samun hantara daga ƙanni kamar yadda sauran zawarawa ke yawan ƙorafi, hasalima ita girmamawa ce a tsakaninsu.

Ta kwashi wata goma cur a gida, kuma har a lokacin ba labarin Baban Sani babu dalilin sa, abubuwa da dama sun faru ciki har da dawowar Muttaƙa cikin manema da sunan kome.

Allah Ya temake ta shi Uban gayya ya mashi tas ya kuma ce 'Har abada mun raba hanya da shi" Saboda jin ciwon abunda ya mashi lokacin da ya sake ni, cikin kunya ya ja ƴan matan ƙafafuwan shi ya bar kofar gidan.

Ba ƙaramin daɗi ta ji ba da abunda ya yi ma Muttaƙa ba,ko banza ya nuna mashi ba neman kai yake da ita ba, tana sane da duk labarin gidan shi, dayake yayi gini ya tashi a gidan gandu, unguwar su Inna Hauwa ya koma duk wani motsi na su ta sani, gida ne sun maida shi kamar sansanin yaƙi ya kara aure ga yara kusan goma sha da ka gansu kasan babu isasshen kulawa a gidan ko dakin arziki wanda zai saka matar babu amma yake ƙokarin maida ta.


Bai san yadda Malam Musa ya ƙulla ce shi bane akan ce mashi da ya yi Munari na da farar ƙafa duk lokacin da magana ta tashi sai ya maimaita maganar nan da faɗa mashi.

Ya turo dattawar unguwa ya kore su har abun ya so ya zama masu faɗa, su suna ganin ya wulakanta su, shi kuma ya ce idan har rashin ba Munzali Munari ne ya ji ya ya yi wulaƙancin su yi abunda za su yi.

Aka rabu dai rai duk babu daɗi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.