Free chapter · Read without an account
TRAILER
TRAILER 🎬
"Lokacin da su ka je Doll factory ɗin nan abin da su ka gani a wajen shine ƙwarangwal ɗin mace a yanda binciken likitoci ya nuna musu. Sannan ba za su taɓa sanin ƙwarangwal ɗin wacece ba, to ka gani mun tsira. Sannan ka yarda da ni a kan haka, cewa babu wanda zai taɓa sani wacece wannan matar har abada"
"Amma karki manta cewa tun farko kin faɗa min Leen ta na da wata hujja da ta samu game da wannan doll factory ɗin, to idan kuma wannan hujjar ta yi sanadiyar tonuwar asirin mu ni da ke fa?"
Juyowa ta yi ta fuskance shi ta ce "Tsakanin lokacin da Leen za ta samu wannan hujjar da zuwa lokacin da za ta kai shi zuwa kotu ka yi tunani me zai same ta. Ko ka na tunanin zan barta haka ne?" Ya ce "Ana ba ki kina ƙi, ki fahimci wani abu mana idan aka ce an samu wata hujja a cikin wannan ƴar tsanar to tabbas babu makawa recording ne, kuma recording ɗin na muryoyinmu ne. Kin san da cewa a daidai lokacin da abin ya faru bayan Lateef da ni da ke ne kawai a cikin factory ɗin"................
******************
Wani shu'umin murmushi ta yi ta ce "Na daɗe da sanin cewa ɗaurin rai da rai a gidan yari ba zai taɓa dacewa da ni ba, shiyasa ban taɓa shirya zuwan shi ba. Kafin Leen ta samu wannan ƴar tsanar sai na tabbata na riga ta samun shi a hannuna"
"Don Allah ki yarda da ni Leen, ba zan taɓa cutar da ke ba" Dafa hannun shi ta yi ta ce " Ban san abin da ya faru a factory ɗin nan ba, ban da masaniya a kan dalilin da ya saka ka ƙona wajen nan. Sannan haka zalika kuma ban san ya aka yi kisar nan ba.
Sai dai abin da na sani guda ɗaya shine ba za ka taɓa iya kashe rai ba" Cikin hawaye ya ce "Amma ɗana, jinina ya yarda na aikata hakan. Ina buƙatar na wanke kaina amma ta ya hakan zai yiwu?" Kamar wanda ya tuna wani abu cikin sauri ya ce "Leen wannan ƴar tsanar! Wannan ƴar tsanar ta na ina?"............
**********************
Kusan minti biyu yana tsaye cak kamar an dasa shi a wajen, wani irin sarawa kanshi ya ke mishi amma cikin dakiya da nuna isarsa na asalin cikakken namiji ya sake hannun mahaifiyarshi da ya riƙe gam ya juyo yana fuskantar mahaifin na shi ido cikin ido sannan ya ce "Ka yi kuskure malam saboda ni mahaifina shekara ashirin kenan da mutuwar shi" Yana gama faɗin haka ya ja hannun mahaifiyarshi su ka wuce....
*******************
"Ya Allah me yake shirin faruwa ne haka? Bayan shekaru 20 yau Abie zai haɗu da su, Ya Allah ka sa su wanye lafiya" Humairah ta ce "To wai ma a ina Afeef da Asad suka haɗu ne har ya san yana asibiti?" To ko dai dama suna haɗuwa ne a ɓoye?"
"Kai ina hakan ba zai yiwu ba, an yiwa duka ahalin gidan nan iyaka da su, sannan bayan haka ma mahaifiyar Asad ɗin ba ta son sake haɗa wata dangantaka da ahalin mu" Haka zalika muma a gidan an haramta mana duk wata alaƙa da su"
****************
"Irin wannan ƙananun kuskuren ne ya ke girma ya zama babba" Ya yi cikin ɗan tsawa. Ya cigaba da faɗin "Irin wannan karamin kuskuren Arwa ta aikata, ta faɗa soyayya da Lateef bayan ya na da aure.
Hakan ya sa na ce wa Lateef ya zaɓa ko ya cigaba da rayuwa da Leen cikin halin ƙunci na rayuwa ko kuma ya aure Arwa ya rabu da Leen gaba ɗaya, ya yi rayuwa cikin yelwa da arziƙi sannan ga tagomashin hannu jari a cikin kamfaninmu. Ya zaɓi Arwa ya rabu da Leen ni kuma na cika alƙawari na ta hanyar cika mishi burin shi.
Na ƙawata shi da duk wani jin daɗi na rayuwa da ya ke burin samu sannan na saka shi ya mini alƙawarin ba zai sake waiwayar Leen da ƴaƴanta ba. Amma yanzu bayan shekaru ashirin ya ƙarya alƙawarin shi"
*****************
"Jaddah idan manya sun riƙe girmansu a matsayinsu na manya babu mai raina su, shi waye da zai dinga min irin wannan tambayoyin? Ta ya wasu za su dinga tsara min ko ya kamata na ga yayana ko bai kamata ba?Jaddah Ɗan uwana fa! Yayana farin ciki na, wanda duk duniya ba ni da kamar shi, shine har wani ya ke da ikon yi mini iyaka da shi. To wallahi ba zai yiwu ba. Na sani duk Abie ne ya jawo mana wannan abin.
Allah ya azurta shi da komai sai dai bai san mutuncin kanshi ba. Wani irin ubana wannan wanda wani zai dinga mishi shamaki da zuwa wajen ɗanshi har ya din ga tuhumar shi saboda ya je ya ganshi a asibiti bai da lafiya kuma har ya jure, sai ya dinga abu kamar bawan Uncle ne shi. Wallahi na ji kunyar kiran shi a matsayin mahaifina"
Tasss ka ke ji Jaddah ta ɗauke shi da mari. Jaddah ta ce "Shin kasan kana rayuwa ne a duniya ta sanadiyar Lateef ne kuwa? Ya watsar da Asad kai ya nuna maka gatan mahaifi, abin da Asad bai samu ba kenan kai ka samu shine za ka nema ka wulakanta ubanka?"
*******************
"Aunt kin san ba zan taɓa iya komawa Paris ba ba tare da na samu amsoshin tambayoyina ba, saboda shine abin da ya kawo ni cairo"
"Hayat will you please stop arguing with me! Abin da kuma ba ki isa yi ba kenan dole sai kin koma Paris tare da mu duk rintsi"
"Aunt ba zan koma ba and that is my final decision i'm locking in final decision" Aunt ta ce "Za mu ga mai zai faru idan lokacin yayi" Hayat ta ce "Yes lets see what will by then ba za ki tilasta min dole ba ai"
Aunt ta ce "Jan ki zan yi a ƙasa Hayat kin ji ni ko!"
"Tom zamu gani idan lokacin yayi da rabon police ne za su raba mu".
Zama Aunt ta yi kan sofa cikin kuka ta na kallon sama ta ce "Tante ki na ganin abin da ƴarki ta ke yi min ko, ba ta jin maganata na rasa ya zan yi da ita" Dariya Hayat ta shiga yi ƙasa ƙasa ta na ɗaɗɗaga kai itama ta ga mai Aunt ɗin ke kallo.........
******************
Wani irin uba ne kai Abie? Karka manta fa haƙƙin Asad ya na rataye a wuyarka. Ta ya za ka saka ƙafa ka shure wannan haƙƙunan da su ke kanka? Me ya saka ba ka son Asad? Me ya saka kake bawa Abbu damar juya maka iyalinka wanda kai kake da haƙƙin yin hakan? Tell me Abie why are you so helpless and irresponsible? Ka bani amsa Abie!" Tasss Tasss.............
*****************
A fusace ta miƙe tsaye tana faɗin "Au haushi ka ji?" Shima miƙewa tsayen ya yi ya ce "Na mene?" Hayat ta ce "Eh mana ka so kashe ni Allah bai yi ba" Asad ya ce "Kamar ya ban fahimce ki ba" Ta ce "Idan kasan ba ka iya tuƙi ba me ya sa za ka yi?"
A fusace Asad shima ya ce "Idan ba za ki iya tafiya da kyau ba me ya sa ba za ki zauna a gida ba?" Hayat ta ce "Idan ba ka san yanda ake magana mai kyau ba me ya sa ba za ka yi shiru ba?" A fusace ya nuna ta da yatsa ya ce "Hey ki iya bakinki ba wanda taɓa min magana cikin irin wannan sigar" Hayat ta ce "Oh! No wonder i see shiyasa ba ka iya magana ba"
"Inda matan za su dinga saukar da kansu ƙasa ba su buƙatar wani kariya, idan ki ka fito cikin shigar mutunci babu mai kallonki" ya juya ya nufa motar shi. Da sauri Hayat ta miƙe tsaye ta ce "Excuse me! Me ya sa duk wani ƙuntatawa ake ɗaura mace ne ita kaɗai? Me ya kuke jin cewa a koda yaushe mace da laifi ta fannin kare kanta? Me ya sa kuke ɗaura laifi gaba ɗaya a kan mace idan wani abu ya tafi ba daidai ba? Don me yasa a ƙasar za'a ce dole sai mace ta zauna cikin ƙuntatawa?
"Abin da kike ɗauka ƙuntatawa shi ake kira da Etiquette wato ladabi, ladabin sanin ya kamata, ladabin iya magana cikin mutunci, ladabin girmama mutane, ladabin sanin yanda ake zama a wurare daban-daban, ladabin cin abinci cikin nustuwa ba tare da hayaniya ba, ladabin bin ka'idojin zamantakewa, ladabin shiga ta mutunci!
***************
"Ummie gaskiya ɗaci gareta wanda ba za ki iya jure mata ba. Ya kamata ki fuskanci gaskiyar sannan ki amince da gaskiyar na cewa Lateef Shareek Khan makashi n"... Kasa ƙarasa maganar ya yi sakamakon Afeef da ya yi tozali da shi ya na tsaye a wajen cikin hawaye....
"Asad ko da kana tunanin Abie ya yi kuskure amma ai har yanzu mahaifinmu ne shi" Asad ya ce "No Afeef he is just your not mine" Afeef ya ce "But Please Asad...
Asad ya yi saurin dakatar da shi ba tare da ya tsaya jin abin da zai ce ba ta hanyar faɗin "Idan ka ce na baka rayuwata zan baka shi cikin farin ciki da annushuwa, amma a yanzu ba zan iya baka abin da kake tambaya na ba a kai. Na riga na yi alƙawari a kan ba zan taɓa yafe wa wanda ya yi ƙoƙarin kashe min mahaifiya ba"
Afeef ya ce "Nima na yi wa mahaifiyata alƙawari kan cewa duk rintsi zan yi iya yi na domin na dawo da mahaifina gida Asad. Saboda idan wani abu ya same shi mahaifiyta ba za ta iya jurewa ba, mutuwa za ta yi idan bai fito ba Asad don Allah ka taimaka mini"
Asad ya ce "Ni kuma idan ya fito my own mother will not be safe"................
**********************
SHIN ME KU KA FAHIMTA GAME DA WANNAN TAFIYAR?
SKELETON ƊIN WATA MATA CE AKE MAGANA A KAI? SANNAN WANI HUJJA WANNAN ƳAR TSANAR KE ƊAUKE DA ITA?WA ZAI NASSARA SAMUN ƳAR TSANAR A TSAKANINSU?
SHIN HAYAT TA NA CIKA BURINTA WAJEN SANIN ASALINTA? SANNAN DA WANI FUSKA ASALIN NA TA ZAI BAYYANA?
TSAKANIN ASAD DA AFEEF WA ZAI NASSARA KAN ƘUDURIN SHI GAME DA MAHAIFINSU ABIE? SANNAN MENE DALILIN WANZUWAR TSANANIN ƘIYAYYAR DA ASAD YA KE YI WA MAHAIFIN NA SHI?
MEYE DALILIN GABAR DA KE TSAKANIN ASAD DA ABIE?
Duka waɗannan amsar tambayoyin mai ɗauke sarƙaƙiya na nan ƙunshe a cikin littafin TURƁAYA wanda zai zo muku a matsayin barka da sallah in sha Allah......
TURƁAYA Coming soon..........
Save d date: 01-June-2026
Zeeyluv (Autar Yota).........✍🏻
***