Free chapter · Read without an account
22
*22*
Maijidda ce ta wuce da ledar kayan, Fullo na faɗa mata kar ta soma ta ambaci sunanta idan Kaka ta nemi ba'asin karɓan kayan Dr Yusuf. Ai ta san an hana su shine yana miƙowa ta amshe.
Maijidda na ɗan jin tsoro tabce,"To ni ai nayi zaton da gaske alluran ne shiyasa na karɓa".
Fullo na dariya ta ce,"Kinga ke dai ki je ki sha faɗanki ke ɗaya, ni na tafi aiki. Da in sha faɗan Kaka gwara na sha na Hajiya Madina".
Tana faɗa ta ƙara saurin tafiyarta tana ta yiwa Maijidda dariya, ita kuma na jin shakkar shiga da kayan, ji take kamar ta koma ta ga idan Dr Yusuf bai tafi ba ta basa kayansa, to amma ta san zuwa yanzu ya tafi kam, dan ko ɓata lokacin da suka yi a wurin duba kayan ta san ya je inda zai je.
Tun shigowarsu gate Fullo ta dage sai sun wuce inda ake zubar da bolar gidan sun zubar da maganun, wanda a zaton su abin da ya faɗa hakan yake. kuma sai da suka je za su zubar ne suka tsaya suna kallon uban kayan da mamaki.
Leda ɗaya tulin kayan ƙwalama ne kamar hauka, madara, snacks da choculates da lemukan kwali, tarkace dai iri-iri. Sai ɗayan ledan kuma kayan makeup ne a ciki, shower gel manyan roba guda biyu wanda mutum sai yafi wata yana wanka da roba, sai lotions da su powder, duka dai dangin kayan kwalliya, kuma da gani kuɗi ne ba na wasa ba aka kashe wajen sayayyar.
Fullo ta shiga parlon da sallama tana tafiya a hankali, kanta a ƙasa sai jan yatsun hannunta take yi, Hajiya Madina na zaune akan kujera, ƙafafunta duka biyu akan tum-tum, Sameer na zaune a gaban ƙafafun nata ya tankwashe ƙafa yana yanke mata farcen ƙafarta. Sai Nihal da ke ɗaya kujeran a zaune tana duba wata handout, daga dining area kuma Zaytuna ce a zaune tana danna waya.
Fullo ta ƙarasa ta durƙusa a gefen kujera tana gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ɗauke idonta daga karanta story book ɗin da take yi ta kalleta tana amsa gaisuwar tata.
"Halimatu an ji sauƙi kenan".
Ta ce,"Ehh Maama na wartsake gaba ɗaya".
"To ma sha Allahu, Allah ƙara miki lafiya. kina da ƙwarin dai da zaki iya aiki ko? Idan ba zaki iya ba ki bari ki ƙara hutawa".
Fullo ta ce,"ehh Maama zan iya".
Hajiya Madina ta gyaɗa kanta, tayi shiru for some seconds sannan ta ce.
"To jiya an kawo miki ƴar'uwa da zaku ke aikin tare, ta kammala komai tun ɗazu, yanzu sai ki tashi ki je lesson teacher ɗin ku ya zo, idan ku ka kammala ke sai ki yi aikin rana".
Wani daɗi ya mamaye Fullo, ko babu komai burinta na yin karatun boko zai cika, abin da mahaifinsu ya kasa yi musu yau wasu bayin Allah za su mata shi. Tunaninta ya tafi can wani lokaci baya, tana wannan tunanin ta ji Hajiya Madina na ƙara cewa,"Dan Allah ku mayar da hankali kun ji ko, abin da za'a muku a makaranta shi zai yi muku, kuɗi masu yawa aka biyasa, so idan kun mayar da hankali akan karatun kanku ku ka taimaka, idan kuma kun ƙi kun yiwa kanku asara babba".
Fullo ta ce,"In sha Allahu Maama zamu mayar da hankali, ba zan baku kunya ba zan yi abin da ku ke so nayi".
Hajiya Madina ta jinjina kanta. A lokacin sabuwar ƴar aikin da aka kawo ta iso wurin ta tsuguna kusa da inda Fullo take.
Ta ce,"Hajiya ga ni".
Maama ta ce,"Ga ƴar'uwar aikin naki nan. Ki bata na ta reading materials ɗin da Zaytuna ta baki ɗazu, sai ku yi maza ku wuce Malamin na can na jiranku, awa biyu zaku dinƙa yi, da zarar kun kammala ku yo cikin gida, a kama kai bana son shashashancin banza idan ba haka ba zan sallami yarinya".
Duk su biyun suka amsa da,"To". Sannan Fullo ta ce,"A ina zamu sami Malamin?".
Nihal ta ce,"Ku tashi mu je let me escort you". Ta faɗa tana gyara zaman glasses ɗin idonta, da gyara dogon wandon dake jikinta.
"Je ki ɗauko littafan naku". Ta faɗa tana nuna Ɗausiyya ɗaya ƴar aikin. Da ganinta tana da hanzari akan yin abu, dan cikin sauri ta ɗauko ta dawo, kuma kallo ɗaya zaka mata zaka san she is typical ƴar ƙauye, balle kuma ka kai ka ga kallon the way take abubuwanta, maganarta duka hi da ha ne, jiya ana kawota Hajiya Madina tasa Baba Jummai dake kawo mata ƴan aiki ta kai ta saloon aka wanko dattin kanta, kuma suna dawowa tasa ta yi wanka mai kyau da dettol da turaren ƙamshi. Haka Hajiya Madina take, bata nuna ƙyama ko ƙyanƙyami ga duk yaran da ake kawo mata, karɓarsu take ta nuna musu hanyar gyara kawai.
Nihal na gaba suna biye da ita a baya, za su fita daga falon Zaytuna ta kira sunan Fullo, ta waigo tana kallonta bayan ta amsa kiran. Ta mayar wa da Zaytuna murmushin da take yi mata.
"I wish you all the best in your studies dear".
Abin da Zaytuna ta ce mata kenan, kuma kamar yadda bata fahimci mai ta ce ba haka itama Zaytunan ta fahimci bata san abin da ta ce mata ba.
Zaytuna ta ƙara mata wani murmushin ta ce,"Ina yi miki fatan alkhairi a karatunki, Allah ya bada sa'a".
Kan Fillo na ƙasa ta ce,"Amin ya Allah, na gode Adda".
Da haka tabi bayan su Nihal da suka riga suka fice.
Awa biyu suka ɗauka suna karatun kafin su gama, sosai Fullo ta gane duk abin da aka koya musu ɗin, karatun ya mata daɗi fiye da yadda ta tsammata, ashe shima karatun boko haka yake da daɗi? Shi kansa teacher ɗin na su sai da ya mata kyautar biro, har yana tambayarta ko ba yanzu ta fara ɗaukar darasi ba ne.
Da ya ba su class work guda biyu ta faɗi a examples ɗin da ya ce su bayar, rubutun ta kuwa baka ce wacce ke koyo ba, Ɗausiyya ce yayi ta fama da ita, to ita ma kuma da yake tana da kishi sai da tayi ƙoƙarin iyawar.
Teacher ɗin na su ba bahaushe bane, amma yana jin hausa sai dai bata kama bakinsa sosai ba. Yayi da hausa ya haɗe da turanci, su gane hausar da yake yi su bagarar da turancin nasa, idan ya faɗi wani abin da hausa Fullo har gimtse dariyar dake taho mata take yi. Dan da ace ita da Maijidda ne ma sai sun saki kayarsu.
Suna komawa sallah kawai su ka yi sannan suka fito suka shiga kitchen, suna aikin Fullo na bitar karatunta, ɗan gutun turancin da brain ɗinta ta haddace sai maimaita shi take a zuciyarta, idan ta faɗesa a fili kuma sai ta ji maganarta wani banbarakwai sai tayi dariya, haka kawai Amir ya faɗo mata a lokacin, idan yayi mata turanci sai ya ce ta faɗi abin da ya ce sai ta kasa, ya ce zata iya ta ce ita kunya take ji ta san ba zai yi daɗi a bakinta ba irin yadda yake daɗi a nasa bakin, sai kuma ta tuna abin da ya faru tsakaninsu a ɗazu, tayi saurin watsi da tunaninsa tana jin zuciyarta na zafi.
Zaytuna ce ta taya su Fried rice ɗin da ba su iya ba, sun maida hankali sosai wajen ganin yadda ake yi, duk abin da ta ɗauko na vegetable zata faɗa musu sunansa da amfaninsa da kuma yacca ake sawa, babu jimawa suka kammala Fried rice ɗin.
Suna aikin Ɗausiyya ke tambayarta,"Anty kuma sai ku iya cin abin da muka saka hannu?".
Zaytuna ta yi murmushi ta ce,"Hammah ne kawai ba ya cin abin da ƴan aiki suka dafa, amma mu kam muna cin duk abin da ƴar aiki ta dafa muddin ta kula da irin tsaftar da muke so, kema baki ga yau fes dake kika fito ba, kuma ina kallonki duk abin da kike yi cikin tsabta kike yinsa. Yanzu ma kalle ki tsab, to tsabta ita ke sawa aci girkin mutum, duk daɗin girkin mutum idan bai da tsabta nisantarsa ake yi. Saboda haka ku kula da tsabta sosai ƙanne na".
Zaytuna da Ɗausiyya suka ɗauka tray suka fita da shi, suka bar Fullo da ƙarasa haɗa kunun shinkafar da Samha ta ce tana so tasha. Ta fasa madarar gwangwani ta ruwa kenan sai ta ji kamar mutum a bayanta, ta waigo ta ga Turaki ne tsaye hannayensa a aljihu yana kallon abin da take haɗawar, da alama ma ba shigowarsa kenan ba.
Lokaci ɗaya ta nemi ta dirirce, ta durƙusa a gabansa da sauri tana gaishe shi, ita bata san mai yasa ba amma duk sanda ta gansa sai ta tsorata. Bai amsa mata ba ya wuce ya ɗauki cup ya dawo, tana nan durƙushen har lokacin, da wani irin tone a voice ɗin ta ta ce da shi.
"Kana buƙatar wani abu ne?".
Ya kalleta amma ba ita yake kallo ba hannayenta yake kallo, ya ce. "Tashi".
Ta miƙe tana ɗan matsawa daga kusa da shi. Fuskarsa a ɗaure ya ce,"What are you making?"
Ta so fahimtar abin da ya ce, amma hakan bai samu ba, jin ta yi shiru ya wai go ya dubeta, tana tsaye kamar gunki duk ta cika da tsoronsa, hannun nan sai karkarwa yake, shi kuma abin na basa takaici, ya lura kaf gidan shi ɗaya take yiwa wannan walaƙancin, da ta gansa sai ta kama rawar jiki.
Ya ja guntun tsaki ya ƙara cewa,"I’m asking you, what is this you’re making?”
Yanda yayi maganar murya a sama yasa ta fara ƙoƙarin hargitsewa, ta ƙanƙame hannayenta a jikinta tare da kulle idonta, shin har sai yaushe zai fara fahimtar wannan yaren ita kam bata jinsa, ita kuwa ko ba dan komai ba ai dole ta tsaya ta mayar da hankali akan wannan gatan da Hajiya Madina tayi musu ta koyi turanci. Ji take kamar tayi kuka, bata ko ƙaunar tana aiki a kitchen ya shigo, ko ba'a kitchen ba bata so tana aiki ta ga giftawarsa, ita haɗuwa ma da shi totally bata so.
Turaki ya tsaya yana kallon ikon Allah, shi kam ba dan ba dan ba, da sai ya ce yarinyar nan bata sahun mutane sai dai wata halittar. Karkawarwa take kamar wadda ruwan sanyi ya yiwa mugun duka, ko kuma wacce iskar fanka ke kaɗawa. Sai ya ajiye cup ɗin hannunsa kawai ya rungume hannunsa a ƙirji, ya jingina da jikin drower ɗin yana ta kallon sarautar Allah, ba zai ƙara magana ba balle motsi har sai ta gaji dan kanta ta dawo cikin hayyacinta, sannan zai buɗi baki ya faɗa mata karta ƙara ganinsa ta tsorata tun da shi ba abun tsoro ba ne.
Lokacin da ya tsareta da tambaya a asibiti ya haska a cikin kansa da cikin idonsa, wannan lokacin da ya riƙe hannayenta dan hana su rawar da suke yi, amma still ba su daina ɗin ba sai ma rawar hannun nata ya haɗe har da nasa, tambayarta yayi kawai mai ya kaita wannan wajen, amma yanda tabi ta ruɗe ta nemi ta firgice har sai da yasa ɗaya hannunsa ya riƙeta da kyau, dan kamar zata faɗo daga kan gadon.
_"Me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?"_
Tambayar da yayi mata kenan amma kamar ya tuhumeta ne akan me yasa ta yi kisan kai. Sai da ya matse hannunta da ƙarfi sannan ta buɗe ido ta kalle shi hawaye na sakko mata ta ce masa,_"Ina?"_
Harara kawai ya galla mata a lokacin, kafin ya ce,_"Wurin da kika je za ki kashe kanki"._
Sai kawai ta shiga girgiza masa kai, cikin rawar murya ta ce,_"Allah ba kashe kaina na je yi ba, ai babu kyau mutum ya kashe kansa"._
Ta ji yayi shiru bai yi magana ba, sai ta buɗe idonta dake rufe ta sauke a kansa, ƙwayar idonta ta shiga nasa, ta ji wani abu da bata taɓa jinsa ba, ta ga ya ɗaga mata gira duka biyun yana cewa,_"Uhmmm ina jinki, to wa kika je kashewa?"._
Saura kaɗan yayi dariya saboda yacca ta ƙara ruɗewa da tambayar tasa, har tana ja da baya wanda inda ba'a kan gadon take ba tsab zata arta da gudu.
Ƙoƙari take ta zare hannunta a cikin nasa tana girgiza kanta cikin tashin hankalin da ya rufeta farat ɗaya. Hawaye ne sosai yake sakko mata tana ce masa,_"Allah babu wanda na je kashewa, me yasa zan kashe wani, akan me? Ko cinnaka bana iya kashewa ka tambayi Kaka, dan Allah kayi haƙuri kar ƴan sanda su ji su kama ni"._
Tayi shiru tana fashewa da kuka, har sannan bai ɗauke idonsa daga kanta ba, ganin kallon da yake mata yasa ta ce,_"Na rantse da Allah babu wanda na je kashewa, nima ganina kawai nayi a wajen, ban san ya aka yi na je ba, kuma ina ta neman hanyar gida na rasa"._
Ya ƙara damƙe hannunta sannan ya ce,_"Har lokacin da ya kaɗe ki baki sani ba?"._
Ba tare da ta kalle sa ba ta ce,_"Na sani, ina ta ɗaga masa hannu bai ganni ba kawai sai ya bige ni"._
Numfashi ya sauke ya ce,_"To kin yafe masa ko kin barsa da Allah?"._
Sai da ta ɗago ta ɗan kallesa tukunna ta ce,_"Na yafe masa"._
Ya ƙara sauke numfashi sannan ya ce,_"To aljanun naki da suka kai ki su nawa ne? Dama suna yawo dake ko ranar su ka fara?"_
A wannan lokacin kawai tsayar da idonta tayi akan kafaɗunsa, ta girgiza masa kai ta ce,_"Banda aljanu ai, ni banda aljanu, ko Malami za'a kira a tambaya zai faɗa mu ku gaskiya"._
Ya ce,_"Wanne Malamin?"._ Ta ce,_"Malamin Ruƙiyya"_.
Yana kallon yadda take kallon ƙirjinsa kamar mai karantar wani abu a wajen, sai da ya kalli wajen ya ga babu komai kawai dai ba zata iya kallonsa ba shine take kallon wajen. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saki hannayenta ya miƙe ya fita daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba.
A yanzu da yake kallonta sai yake ganin kamar a wancan lokacin, har yanzu yana mamakin me ya kaita wajen, Me ta je yi? Abu ɗaya kawai zai yarda da shi tana da aljanu kuma su suka kai ta, abin da kowa ya faɗa kenan.
Ya yarda da wannan, amma wannan tsoron nata fa? Shi jininsa babu tsoro a cikinsa, saboda haka ya kamata wannan tsoron nata ya ragu tun da har jininsa na yawo a jikinta yanzu. Ya rumtse ido yana tuna the first abin da likitoci suka faɗa lokacin da suka isa hospital, _"Ta zubar da jini da yawa, jini take buƙata a halin yanzu, cikin gaggawa ba da ƙurewar lokaci ba"._
Haka suka faɗa a sannan, kuma ba zai iya cewa ga wanda ya nuna masa hanyar laboratory ba, tsintar kansa kawai yayi a wurin, ba tare da kowa ya sani ba. Abin da ya tsana a rayuwarsa shine ɓata lokaci da kuma dogon bayani.
Abin da ya sani jininsa O-negative ne, to don me kuma sai an tsaya wani ɓata lokacin gwadawa? Saboda haka dawowa kawai yayi ya kama hannun Zaytuna suka faɗa room ɗin da aka kwantar da Fullo.
_"Ki saka mata jinina, ko leda nawa ake buƙata, ko da za'a kwashe nawa ɗin ne duka"._
Tana kallonsa ido warwaje ta ce,"To ai Hammah duk da haka akwai buƙatar wasu tests ɗin da dole ake yi kafin bayarwar."
A tsawace ya ce mata,"Wanne test ne akwa buƙaga Zaytuna, kina daga cikin masu bayar da shaida akan cikakkiyar lafiyata. Ki ɗebi jinina ki zuba mata na ce miki."
Kayan aiki a ajiye suke to jiran me za tayi? Dan haka kwanciya kawai yayi akan gado tayi jone-jonen da zata yi, nan take jininsa ya fara shiga jikin Fullo. Daga fara shigar jinin bai kuma sanin me ya faru ba, farkawa kawai yayi yaga wani yayi replacing nasa akan gadon, wani ne aka samu da duk sanda buƙatar hakan ta taso a asibitin yake bayar da kyautar nasa jinin. A lokacin ya ji haushi, babu wani yawun baki da zai iya faɗar baƙin ciki da takaicin da ya ji, wanda bai san dalili ba.
Sai daga baya Zaytuna ke masa bayanin ai an ce shima yana buƙatar ya huta ne dalilin da yasa aka cire nasa kenan, dama leda ɗaya da rabi ake buƙata, kuma ɗaya mutumin shi ya bayar da rabin.
Turaki ya numfasa yayi tattaki ya ƙarasa gaban Fullo da ke tsaye har yanzu bata buɗe idonta ba, wataƙila tana jira ne taji ya fita daga kitchen ɗin sannan sai ta buɗe idon, ko kuma tana jira ne ya bata umarnin buɗewar, tun da ita bata da umarnin kanta sai na wani, ya lura da hakan tun farkon zuwanta.
Yana zuwa dab da ita ta ji gabanta yayi mugun faɗuwa, allon ƙirjinta ya girgiza, ta ji kamar ta arta a guje. So take tasa hannu ta toshe hancinta saboda ƙamshin turarensa da ke shiga hancinta, ba saboda rashin daɗinsa ba, idan ta ce ƙamshinsa babu daɗi tayi ƙarya, wannan ƙamshin yana ɗaya daga cikin ƙamshin da zata iya cewa da wuya a samu ƙamshi mai daɗi irinsa.
Sai dai da ace tana da iko, da ace tana da iko da Turaki da ta haramta masa sanya wannan turaren, da tasa ya bar ƙasar nan ya je wata ƙasar sun wanke duk wani sauran ƙamshi na irin turaren nan da ke jikinsa, ba ta son ƙamshin ta tsane shi, ba don komai ba sai don an haɗa asiri da shi, wannan asirin da yayi sanadin zuwanta cikin dajin da ta kusa mutuwa.
Ranar da Turaki ya tsareta da tambayar me ya kaita wancan wurin yana kama hannunta ta ji ƙamshin, ƙamshi ne da ba zata manta da shi ba, ta jima tana zuƙar ƙamshin a lokacin don tabbatar daga inda yake fitowa, tunaninta ko asirin ne ya kuma biyota, da ga baya ta ankara da cewa ba ƙamshin kowa ba ne sai nasa, that means ya tabbata kenan asirin nan nasan ne, kuma an haɗa asirin ne da turaren da yake sawa.
Saboda haka yanzu fatanta guda ɗaya ne, Allah ya bata wata dama da zata hana Turaki saka wannan turaren, ko kuma Allah ya ɓatar da turaren daga duniya gaba ɗaya.
Jin takalmin Turaki gaba ɗaya akan kafaɗunta tayi firgit ta buɗe ido ta sauke kallonta akan ƙafafunsa dake cikin takalmin shigowa kitchen. Ta haɗiye wani busashshen yawu sannan ta iya buɗe baki ta ce,"Kayi haƙuri ban san me kake cewa ba".
Ya fito da hannayensa daga aljihu ya tamke fuska ya ce,"Na miki kama da Eodo?".
Da sauri ta girgiza kanta alamar a'a.
Ya ce,"To me yasa duk ranar da kika ganni kike rikicewa ki bi ki firgice, ko ina kama da aljaninki?".
Nan ma ta girgiza kai cikin sauri ta ce,"A'a".
Ya ce,"To ina jinki tsoron na mene?".
A hankali tana shirin yin kuka ta ce,"Bana so a ɗaga min murya ko kuma a min tsawa".
Ya ce,"Ni kuma haka nake miki ko?".
Bata ce komai ba tayi shiru. Sai taji yayi ƙasa da muryarsa ya ce,"Mene wancan abun da kike haɗawa?".
Ta ɗaga ido ta kalli robar da take dama kunun ta ce,"kunun shinkafa ne, Adda Samha tance na dama mata".
Ya matsa daga gabanta ya ƙarasa wurin yana faɗin,"An gama?".
Ta ce,"A'a zan zuba madara ne".
Ya ce,"Zo ki ƙarasa".
Ta yi ɗan jim bata motsa ba, ya juyo ya wurga mata wani kallo da niyyar ya doka mata tsawa sai kuma ya taushi zuciyarsa ya sauke murya ƙasa ya ce,"Na ce ki zo ki ƙarasa ko".
Ta taho kamar mai ciwon ƙafa, ta fasa madarar ta ɗaga gwangwanin tana zubawa hannunta na ta rawa, madarar rabi ce ta shiga rabi duk ta zube a ƙasa, haka har ta juye gwangwani ɗaya sannan ta ƙara fasa wani, zata zuba sai ji tayi ya kama hannunta ya karɓi madarar ya zuba da kansa ya jujjuya.
Yana gama juyawa ya tura mata cup ɗin da ya ɗauko gabanta, bai magana ba amma ta fahimci me yake nufi.
A hankali ta ce,"Zan zuba siga".
Ta faɗa tana nufar durowa dake sama, ya bita da kallo yana tunanin ta inda wannan ƴar a bar da ke iyakar cikinsa zata iya ɗauko abu a wancan durowan da ke luluƙin sama. Ya lissafa ya ga ko da abu zata taka sai ta ɗora mai tsayi tukunna tsayinta zai kai, lissafin nasa ya ƙare a kallon siraran ƙafafunta da ke yawo a cikin zani, babu makawa ta taka wani abun ta faɗo sai ƙashinta ya ragargaje.
Ta ɗauko doguwan kujera zata taka ta hau, sai ganinsa tayi ya ɗauko roban ya miƙo mata, tana so ta kalle shi amma tana tsoron idonsa, tasa hannu biyu ta karɓa ya wuce ya bar mata wajen.
Zata zuba sugar ɗin ta ji Ya ce,"A little bit".
Ta dakata da zubawan. Yana ganin hakan sai ya ce,"Ɗan kaɗan".
Kaɗan ɗin ta zuba, kuma da ta zuba sai da ta ɗago ta kalle shi, ba tayi magana ba amma kallon na ta ya bayyana masa abin da take nufi, itama kuma shirun nasa ta gane cewar yayi.
Ta zuba kunun a cup ɗin da ya ijje mata sannan ta ɗauko ƙaramin plate ta ɗora cup ɗin akai ta ɗora spoon, ta ɗauka zata fitar masa da shi taji ya ce,"Bani".
Da sauri ta miƙa masa ya karɓa. Yana karɓa ya fice ya bar kitchen ɗin, da fitarsa ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, ta ɗauki tea flask ta juye kunun aciki ta ɗauka ta fita da shi, tana fatan Allah yasa Turaki ba ya falon a lokacin.
Samunsu tayi duk suna dining suna lunch, ta ce da Samha.
"Adda Samha nan zan ajiye ko ɗakinki zan kai miki?".
Samha bata kalleta ba tana wani shan ƙamshi ta ce,"Ajiye anan".
Ta zagaya ta gefen da Nihal ke zaune ta aje, sannan tayi tsaye ƙeƙam a wurin. Tana jin idon Hajiya Madina akanta, duk sai take jin wani iri da kallon, ta ƙara yin ƙasa da kai.
"Idan kin kawo abu kike tafiya bayan kin ajiye ba sai kin jira an miki izinin tafiya ba, kin ji ko?".
Ta ce,"Tom Maama".
Hajiya Madina ta ce,"Da sauran abincin a kitchen ko zaku ɗiba anan, ko kuma wani abun zaku dafa?".
Ta ce,"Akwai saura Maama".
Ta ce mata,"To ki je ku ci".
Har zata tafi Zaytuna ta kalli cup ɗin dake gaban Turaki, ya shanye rabin kunun ya bar saura. Ta ga idan an barsa asararsa za ayi, kuma wannan na flask ɗin yanda suke da son kunun shinkafa ba zasu bar ko kaɗan ba, kuma ta san Fullon da ta haɗa bata rage ko kaɗan da zata sha ba, ta san abin da zata iya aikatawa.
Saboda haka ta ce mata,"Zo ki ɗauki wannan".
Fullo ta zagayo gefen da take, ta ɗau cup ta riƙe.
"Ki shanye shi karki zubar".
Ta wuce ta koma kitchen ɗin, ta tarar Ɗausiyya ta zuba musu abincinsu a wani ƙaton roba, da dukkan alama Ɗausiyyan na da shegen ci, kuma bata saba cin abinci a ƙaramin kwano ba. Ta ɗauki wani cup ɗin separately ta juye kunun da Turaki ya rage, bayan ta wanke cup ɗin ta maida shi ma'ajiyarsa tabi bayan Ɗausiyya suka fita.
****
Boɗejo na zaune a tamfatsetsen falon na gidan Hakimi, wata ƴar nayi mata tausa. Da sallama aka shigo falon, Boɗejo ta ɗauke kanta ga barin kallon tv ta koma kallon ƙofa. Ganin masu shigowa ta buɗe baki cike da jin daɗi ta ce,"Ilham". Ta faɗi sunan tana mai cike da mamakin ganinta.
Ilham da ƙawarta suka ƙaraso ciki, ita ta ƙarasa inda Boɗejo take ƙawartata kuma ta zauna akan kujera. "Bari in samu ladan nima".
Ilham ta faɗa tana zaunawa a ƙasa tana cewa da ƴar aikin ta tashi ta tafi zata ƙarasa ma Boɗejo tausar.
"Rai kan ga rai, ashe da rabon ƴar nan zan ƙara ganinki kamin na mutu".
Ilham ta ce,"Bar zancen mutuwa my Only Granny, yanzu ai zaki ke ganina akai-akai tun da dai Allah ya yarda an kammala karatun".
Boɗejo da har yanzu daɗi bai saketa ba ta ce,"Ai kuwa dai na ji daɗin kammala karatun nan, haka kawai Hashimu ya wani kwasheki ya kai ki wata uwa can duniya ki yi karatu ke ɗaya, ranar nan sai da na masa tatas na ce idan baya ƙaunarki ne ya faɗa mana sai mu je mu ɗauko ki mu dawo dake, wannan wane irin karatu ne ace shekara biyar anata faman yinsa babu ƙarewa".
Ilham tayi murmushi ta ce,"To Boɗejo ba ga shi har mun kammala ba".
"Haka ne dama komai lokaci ne, yanzu ai ba tausa zaki ba Ilham jikina zaki taho".
Ilham ta bar matsa ƙafar da ta fara tayi jikinta suka rungume juna. Duk su biyun suna masu jin daɗi. Ilham ƴar gidan Hashim ce mai martaba na yanzu ɗan Boɗejo, ita ce ƴarsa mace ta biyu wacce ta ci sunan Boɗejo Rumana, ta tafi america karatu inda ta karanci business administration, kuma tun da ta tafi bata dawo ba sai yanzu, shekara biyar cif.
Ba don babu halin dawowar ba sai dan kawai mahaifinta yafi so ta nutsu tayi karatunta, ya kan je ya dubata akai-akai shi da mahaifiyarta wacce ita ce mata ta biyu a wurinsa. Boɗejo ko da yaushe acikin mitar karatun Ilham ɗin take yi duk sanda ta je wajen mai martaba.
Har ta kan ce ko dai dan yaga an saka mata sunanta ne shiyasa baya ƙaunarta, da ƙyar yake samu ya lallasheta, idan ya ce ta shirya a kaita ta je ta ganota sai ta ce ita ba zata je ƙasar arna ba, dama dai saudiya ne to anan tafi kauri amma ita kam ba dai ta hau jirgi ta je ƙasar arna ta kwasowa kanta zunubi ba.
Aisha na gefe tana kallonsu da burgewa, ita bata ta so ta sami kakanninta ko ɗaya ba duk sun mutu. shiyasa idan taga tsofaffi sai ta ji suna burgeta, dalilin da ya sa ta biyo Ilham kenan suka taho tare, amma yau tayi niyyar komawa kano saboda kar mahaifinta meaimartaba sarkin kano ya dawo bata nan, yana dira wanda zai so ya fara ganawa da shi ita ce, kasancewarta Auta.
Hajiya Atika matar Hakimi ta shigo ɗakin, itama tayi mamakin ganin Ihlam ta ce,"Yaushe kika dawo?".
Ta ce,"Jiya da yamma, tun jiyan ma na so na zo na ga Boɗejo, Mami ta ce na bari dai zuwa yau".
Hajiya Atika na murmushi ta ce,"lallai ne to sannun da zuwa, fatan an kammala karatu lafiya?".
Ta ce,"Lafiya lau Hajiya, ban ma taho ba sai da na jira result ya fita. Jiya ina dawowa Mai Martaba yayi min kyautar wannan gidajen guda biyu na estate ɗinsa".
Hajiya Atika ta ce,"Ma sha Allahu, Allah yasa a amfana da karatun da aka yi, ita kuma ƙawar taki fa?".
Ilham ta kalli Aisha sannan ta ce,"Ba tare mu kai karatu ba, ta zo min sannu da zuwa ne, itama ta kusa kammalawa tana karantar AEE ne a Germany".
Aisha ta gaida Hajiya da Boɗejo, suka amsa suna sanya musu albarka. Ilham ta ce,"Hajiya ita ɗin fa ƴar sarkin kano ce".
Boɗejo ta ce,"Ni fa in ce, shiyasa da ta shigo taƙi gaishe ni ta hakimce mana akan kujera, ashe izzar masu sarautan ce, to ni nan da kike gani na haka kamar ba kowa ba to sarauniya ce ada, kuma ni na haifi Baban wannan yarinyar, kinga na zama matar sarki uwar sarki, nan gaba kaɗan ma zan zama Kakar Sarki, dan sai an sami wani jikan nawa ya hau kujerar sarautar nan, ki sadda kanki ƙasa ki min biyayya ki kwashi albarka, ko mai gidan nan Hakimi da kike ganinsa ɗana ne shine na fari, kinga kuwa indai girman izzar sarauta ne aini ke da ita bake ba yarinya".
Dukansu suka yi dariya. Sai yanzu Hajiya Atika ta samu damar isar da saƙon Hakimi.
"Dama Hakimi ne ya ce na faɗa miki ko kema zaki je wajen taron nan na buɗe company ɗin su Turaki".
Boɗejo ta ce,"Shi Turakin ne zai buɗe kamfani ko kuma ɗana Dikko ya buɗe masa?".
Hajiya Atika ta ce,"Ehhh Alƙalin ne ya gina ya kuma mallaka masa shi da Khalil, kamfanin haɗa lemuka ne".
Boɗejo ta ce,"Ni dai in ce, amma ina Turaki ya ga kuɗin buɗe wani kamfani ai sai dai ɗan nawa. Kuma tun da dai ya riga ya mallaka masa ba zani ba, babu wani taro da zanje ni kam, gwara na ja mutuncina".
Aisha da Ilham na kallonta, Hajiya ta ce,"To akwai wata matsala ne Boɗejo?".
Ta ce,"Matsaltsalu ma kuwa, wa ya aike ni zuwa gurin da yake mallakin Turaki! Tun fa ranar da aka yi wannan zaman akan batun aurensa na ce ko aikin asiri ke cinsa shikenan fa ya daina kula ni, idan ya ganni ma ɗauke kai ya ke, jiya ma da suka zo gidan nan shi da ubansa kallon arziƙi bai min ba, ya na ji Dikko na gaishe ni amma balagaggen yaron nan sai yasha mur ya kauda fuska gefe, to yanda ya ƙullace ni ɗin nan na sake na je kamfanin nasa ai sakawa zai yi a kore ni, kaɗan daga aikinsa, dama ya taɓa korata daga ɗakinsa daga zuwa in dubasa, kinga kuwa me zai kai ni kamfani kuma, a'a ku ɗin dai ku je sai kun dawo, wannan ɗan ai halin wan Kakansa ya yo, Sarki Adam ba, ba su da kyau sam".
Hajiya ta ce,"To Allah ya kyauta, bari na sanar ma Hakimin".
Boɗejo tayi shiru bata ce komai ba tana ta shafa kan Ilham, har Hajiya ta fita sai ta dawo ta ce,"Ilham ku ba zaku je ba? Su Hanifa tun ɗazu suka tafi. Shi ma Mai Martaban yanzu na ji sunyi waya yana batun za su tafi".
Kafin Ilham ta ce komai Boɗejo ta ce,"Kin ga Atika du Allah tafiyarki, yaushe yarinyar ta dawo ko hutawa bata yi ba ace ta wani kama shiga cikin hayaniya, ƙila ma ta je taron buɗewar kuma a fara haɗa lemon aƙi sammata, tun da mai kamfanin ba mutumci garesa ba, gwara ta ja mutumcinta da ajinta".
Ilham ta ce,"Boɗejo ina son zuwa fa, dama haka na ce ma Mami zan bi ku mu tafi, kuma fa idan ban je ba Hammah Turaki ba zai ji daɗi ba tun da ya san na dawo, ya ga duk ƴan'uwa sun je ni ban je ba, sai yayi zaton wani abu".
Tana rufe baki Boɗejo ta ce,"Allah ba zaki ba, babu wani taron buɗe kamfanin lemu da zaki je, ki zauna ki huta abinki. Mene wani wani Hammah Turaki balle rashin jin daɗinsa, ya daɗe bai ji rashin jin daɗin ba".
Tun da Ilham ta ji ta rantse kawai sai ta haƙura, ita da Aisha suka durfafi dubulan da alkaki da aka kawo musu. Suna ci Boɗejo na ba su labarin sarautarsu ta da.
©Halima.hz✍🏻
***