Free chapter · Read without an account

86

by ZAHRA B MRS · Bayan Murmushi

Ko da yake Farhana ba ta ɓoye wa Farooq komai ba, amma Farooq ya kasa daina kishin Zayd. Idan ya ga hotunan da Farhana take ɗauka tare da Zayd a filin jirgi ko kishin yadda Zayd yake kula da yaranta, sai ya ji ransa yana ɓaci, duk da ya san Farhana shi take so.

"baby girl , ban ce kada ku yi abota ba," Farooq ya faɗa mata wata rana sanda suke hira a cikin motarsa. "Amma wannan Balaraben ya cika nacin kula da ke da yaranki. Kina ganin ba wata manufar yake da ita ba?"

Farhana ta yi dariya, ta kamo hannun Farooq. "soulmate  Zayd aboki ne na gaskiya. Shi ya maida ni yadda nake yanzu a fannin aiki. Karka damu, zuciyata tana wurin mutum ɗaya tak—shi ne kake rike da hannuna yanzu."

Farooq ya yi ajiyar zuciya, ya matse hannunta. "Ina so na kammala wannan aikin na Boston , akwai babban mataki da nake so mu ɗauka, baby girl."


An shirya wani babban taron masu zuba jari a birnin Washington D.C., inda aka yi hayar wani kebantaccen jirgi (Chartered Flight) domin kwashe wasu hamshakan 'yan kasuwa daga Boston. Farhana ce aka zaba a matsayin Pilot-in-Command na wannan tafiyar saboda kwarewarta da aka fara yabo.


Abdulkadir (AK) yana daya daga cikin wanda zai  halartar taron. Ya shigo jirgin sanye da suit yana takun isa.

Farhana tana zaune a cockpit sanye da kakin matukan jirgi, ta sanya bakar hula da gilashin gani na zamani. Ta ganshi ta madubin dake nuna kofar shiga jirgi sanda yake shigowa. Zuciyarta ta buga, amma sai ta tuna kalaman Farooq: "Ke jaruma ce." Ta ja gilashinta ta rage hasken fuskar ta, ba tare da ya gane ko wacece ba.


Bayan jirgin ya fara shawagi a sararin samaniya cikin natsuwa, lokaci ya yi da matukin jirgi zai gaishe da fasinjoji. Farhana ta dauki lasifikar jirgin (PA system).

"Good afternoon, ladies and gentlemen. This is your Captain speaking. Muna tashi a tsayin kafa dubu talatin da biyu, kuma yanayin garin Washington yana da kyau. Sunana Captain Maryam Ibrahim Matazu, kuma ina muku maraba da shigowa jirginmu."

A can cikin dakin fasinjoji, AK ya daskare. Kofi shayin dake hannunsa ya kusa faduwa. Maryam Ibrahim Matazu? Wannan sunan mutum daya ya sani da shi  Ya girgiza kansa, "Ba zai taba yiwuwa ba. Maryam tana can tana wanke kwanuka a italian restaurant ,wannan kuma Maryam din Captain ce." Amma muryar ay baza ta masa karya ba tabbas tsohuwar matarsa ce .


Suna sauka a Washington, manyan baki suka fara fitowa. Farhana ta fito daga cockpit ta tsaya a kofar jirgi don yi wa baki bankwana, yadda dokar kamfaninsu take. Ta cire hular kanta, gashinta ya zubo kadan, fuskarta tana sheki da kwarjini.

AK yana fitowa ya zura mata ido. Numfashinsa ya dauke. "Ma... Maryam?" ya fada a hankali, yana neman ya suma.

A daidai nan, wani babban attajiri Bahaushe, Alhaji Dan-Azumi, wanda shahararren dan kasuwa ne a Najeriya, ya karaso wurin Farhana. Ya ji sunanta a sanarwar jirgi kuma hakan ya burge shi sosae.

"Masha Allah! Captain Maryam Ibrahim Matazu," Alhaji Dan-Azumi ya fada yana girgiza hannu cikin girmamawa a gaban AK. "Ke ce kika tuka mu haka cikin natsuwa? Gaskiya kin ba wa mata da kuma 'yan asalin jihar Katsina da Najeriya kunya ta gari. Ina alfahari da ke yar nan."

AK ya tsaya kamar gunki, kansa yana juyawa. Ganin yadda babban attajiri irin Dan-Azumi yake girmama Maryam dinsa ya sa ya ji wani irin daci.

Alhaji Dan-Azumi ya ci gaba, "Yar nan, muna bukatar kwararru irinki a Najeriya. Ga katin na (Business Card), ina so ki kira ni, akwai wasu kwangiloli na tashi da sauka da nake so ki kula min da su a kamfanina na jirage."


AK ya yi karfin halin takowa kusa, muryarsa tana rawa. "Maryam... kece kuwa? "

Farhana ta kalli AK da wani irin kallo na ko-o-ho, kallon da ya nuna masa cewa yanzu ya zama kankanin mutum a idonta. Ba ta amsa masa ba, sai ta juya ga Alhaji Dan-Azumi da murmushi.

"Na gode sosae Alhaji. Zan kira ku insha Allah."

"Ina son lambar wayarki yanzu don in sanya sakatarena ya sanya ki a lissafi," Alhaji ya fada.

Farhana ta ciro lambar wayarta ta bashi, amma tana gama bashi, ta ga AK yana kokarin kara mata magana  Farhana ta yi sauri ta sanya hular ta, ta juya da sauri ta koma cikin jirgi, ta bar AK a tsaye yana bin ta da kallo, cike da nadama da kuma mamakin yadda Maryam ta zama tauraruwa mai wuyar kamawa.


Farhana tana shiga gidan Isabella, ta iske su duka a falo. Ta ajiye hular Pilot dinta ta zauna a kasa tana dariya. "Ba za ku yarda da abinda ya faru yau ba!"


Zayd ne ya fara zuwa kusa da ita.bai dade da shigowa ba inda ya dawo da twins daga bostan comman park  Sanda ta ba shi labarin yadda AK ya daskare, da kuma yadda Alhaji Dan-Azumi ya karrama ta a gabansa, Zayd ya bushe da dariya har sai da idanunsa suka yi hawaye.

"Maryam, wannan shi ne abinda nake kira da Sweet Revenge!" Zayd ya fada yana tafa hannu. "AK ya zaci kudin karatun zai gajiyar da ke, ya manta cewa akwai Allah. Mutumin nan ya dade yana raina miki hankali saboda yana tunanin ba zaki iya komai ba tare da shi ba. Yanzu gashi, yana kasa kina sama. Please, ki cigaba da wannan takun, kar ki sake nuna masa rauni."

"The Warrior Queen"

Isabella kuwa ta dauki hular Farhana ta dora a kanta tana tsalle. "I knew it! Na san ranar nan zata zo. Maryam, kin ga yadda AK yake kallon kudin karatun Boston a matsayin dutse, ashe ke kuwa kin mayar da shi matakala. Yau ya san cewa ke ba 'tsohuwar matar Abdulkadir' bace, ke Captain Maryam ce wadda manyan attajirai suke neman lambarta."


Farhana tana zaune, sai kiran Farooq ya shigo. Ta ba shi labarin komai dalla-dalla, har yadda ta nuna wa AK halin ko-o-ho ta gudu cikin jirgi.

Muryar Farooq ta fito cike da wani irin natsuwa da sanyin dake nuna tsantsar alfahari. "Good girl, Maryam. Am so proud of you. Wannan kadan ne daga cikin daukakar da kike jiran samu. Na san AK yana zaton tunda ya raba ki da kudi, ya raba ki da rayuwa. Bai sani ba ashe ya raba ki da duhu ne don ki ga haske."

Farooq ya yi ajiyar zuciya, "Karka damu da shi. Yanzu hankalinsa zai tashi sosae, zai mulmula kansa yana neman yadda zai sake dawo da ke. Amma kin riga kin wuce nan, baby girl. Focus on your Instrument Rating, nan gaba kadan zaki tuka babban jirgin 

da zai kai mu mataki na gaba."

text din abbi tagani

maryam indai ni na haife ki ki tattara na baki wata daya jal ki dawa abuja ,gaban farhana ne ya fadi ras….







Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.