Free chapter · Read without an account

25

by Halima Zakariyya Haruna · LULLUƁIN BIRI

*25*
Da wani irin amon sauti da yayi daban da na muryar Turaki, ya ƙara maimaita mata cewa,"Help me pleasssss". 

Ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta sosai. Ta haɗiye yawun bakinta da ƙyar, yadda ya wuce sai ta ji kamar ta jima tana ciwon maƙogoro kuma bai samu waraka ba har yanzu. 
Bata taɓa jinta a jikin Ɗa namiji ba ko da Yayanta Abdulhamid. Amma yau ita ce gaɓa ɗaya cikin jikin wani ƙaton ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da tasa ta jin jikinta kamar yana neman macewa, ga shi sai ƙoƙarin ta fita a jikin nasa take ta kasa.

Ta yi shiru kawai tana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa, beat ɗin na fita da ƙarfin gaske, yadda ka san zata faso ƙirjin ta fito, sai ta ji tsoro ya kamata sosai.

Muryarta a hankali kamar zata yi kuka ta ce,"Taimakon me zan yi maka?". 

Ta faɗa tana so ta raba jikin nata da na shi, lokaci ɗaya sai tsoronta ya ƙaru jin yadda jikinsa ya saki gaba ɗaya, hannayensa suka faɗi daga jikinta, tamkar dai haka ta ga Adda ta yi a wancan ranar da ta suma a jikin Ummin su.

Zamewa ta yi daga jikin nasa, ya tafi luu ya faɗi ƙasa, bata san lokacin da ta kurma uban ihu tana tallafo kansa da sauri ba. Ta shiga girgiza shi tana cewa,"Ka faɗa min taimakon me zan maka? Me kake so na maka?bTuraki ka tashi don Allah".

Kuka sosai ya ƙwace mata a lokaci ɗaya babu shiri, maimaitawa take tana cewa ya tashi. Da ta tabbatar cewa ya suma sai ta miƙe a ruɗe ta fice daga ɗakin, har ta kai step na ƙarshe zata sauka daga stairs sai kuma ta fara tunanin idan ta tafi ta barsa shi ɗaya cikin wannan halin me zai iya faruwa da shi?. 

Da sauri ta ƙara komawa har tana kusa zamewa, Allah ya taƙaita tsautsayi bata faɗo daga benen ba. 
Yana nan a sumen har yanzu, ta yi kansa cikin kiɗima tana ƙara jijjiga shi tana cewa,"Ka tashi don Allah, ka tashi ka faɗa min duk abin da kake so zanyi, zan taimaka da ko menene, ko da ace zan rasa raina ta sanadin hakan, ni dai fatana kawai ka tashi, ka tashi ka ci gaba da rayuwa Turaki don Allah".

Duk wata dabara na ta da tunaninta ya gushe a ƙwaƙwalwarta, ta yi dirshen a wajen tana ta kuka abinta, tsoronta Allah tsoronta ace mutuwa yayi, wa ya kashe shi?. Sai kawai ta ƙara fashewa da kuka tana tallafo kansa zuwa kan cinyarta, tasa hannu ta share hawayenta tana ta maganganu ita ɗaya.

"Kar ka yi min haka dan Allah, kar ka mutu a sanda yake daga ni sai kai a wajen, za a ce ni na kashe ka, wallahi haka za su ce. Kuma ni ban san komai ba, ban san me ya sameka ba, don Allah don Annabi ka farka kar ka mutu yanzu, ka farka ka faɗa min duk abin da kake so, ka faɗan duk kalan taimakon da zanyi maka, ni kuma nayi alƙawarin zan maka shi".

Ta ƙarasa maganar tana kifa goshinta akan nasa, sam sam bata san me ya kamata tayi a yanzu ba, abu ɗaya ta sani, shine ba zata taɓa fita ta barsa shi ɗaya a cikin wannan halin ba. Can kawai sai ta ji zuciyarta na faɗa mata cewar ta kira waya, ta kira Maama ta sanar mata komai, to amma da wacce wayar?.

Ɗago da kanta tayi ta fara laluben aljihunsa zata ɗauki wayarsa, ta gama lalubenta bata ji komai ba sai wallet ɗinsa. Tunaninta wayar ko tana cikin wallet ɗin ne, hakan yasa ta buɗe wallet ɗin da niyyar ɗaukowa, amma da mamakinta tana buɗewa ta ci karo da hoton mutum biyu, na Zaytuna da kuma Dattijuwar matar da ta gani a jikin wancan hoton.

Kanta ya ƙara ƙullewa ta rasa wanne irin tunani za tayi akan lamarin da ke yawo cikin ranta, yanzu ba lokacin buƙatar lallai sai ta san komai ba ne, yanzu lokaci ne na ta kuɓutar da Turaki da take ganin kamar rayuwarsa tana jingine da ita ne, warwarewar abin da bata sani ba shi yafi komai sauƙi a wajenta, idan ya farka zata zauna ta zana komai da ke ƙulle cikin kanta a tsakiyar tafin hannunta, tukunna ta karance shi da zurfin tunaninta, idan lissafin na ta ya yi dai-dai, to ta tabbata daga nan zata warware komai a cikin sauƙi. 

Cikin azama ta miƙe ta nufi hanyar fita sai Allah ya nufeta da ganin wayarsa akan locker, ta isa wajen ta ɗau wayar hannunta sai karkarwa yake yi.
Ba security a wayar, tana buɗewa kai tsaye lambar Maama ta laluba, bata ma san ta yadda aka yi ta iya wayar ba tun da ba taɓa riƙe babbar waya tayi ba a rayuwarta, ko ƙaramar wayar Yami ma tsakaninta da ita in Amir ya kira Maijidda ta kawo mata tasa mata a kunne.

Bata san ta ya aka yi ta fara scrolling a ɓangaren misscalls ba, ta rasa lambar da ta da ce ta kira, bata san wani Bello Ƙaraye ba, haka bata san lambobin biyun da babu suna a jiki na waye ba, fita tai daga ɓangaren call ta shiga contact, take ta ci karo da sunan My world, cikin sauri ta danna kiran ya tafi. Daga can ɓangaren Hajiya Madina da ke zaune akan kujerar da ke cikin ɗakinta.

Ƙafafunta a harɗe tana jin yadda zuciyarta ke matsewa, tana jin yadda zuciyarta ke faɗa mata kamar ba zata iya komai ba, tana jin yadda idanuwanta ke faɗa mata kamar ba ita ta haifi ƴaƴan da ke zaune a gabanta ba, tana jin yadda ƙwaƙwalwarta ke faɗa mata rayuwar Turaki ita tafi cancanta da ta ingata sama da ta sauran. Cikin kanta na lissafa mata kamar yadda take jin bata da kowa a duniyarta sai Turaki, haka shima Turaki ke jin ba shi da kowa a duniyarsa sai ita, ita ɗaya jallin jal.

Ƙwayar idonta ta wulƙita ta kalli Zaytuna, sannan ta kalli Nihal, tukunna ta sauka akan Samha, duka Yaran suna daga kan gadonta ne suna hira cike da soyayyar junansu. Samha kawai take iya gani a lokacin, kallon yarinyar take da irin kallon da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta kuma san manufarsa, ta kuma san lissafin da ƙwayar idonta ke yi akan yarinyar, ta kuma san ciwon da kallon na ta ke hifarwa da ƙwayar idanuwanta.
Da ace zata iya, tabbas da ta ce komai ɗin da take ji take gani ƙarya ne, to amma bata isa ba, bata isa ta kira abubuwan da ta san suna tafiya ba a matsayin ƙarya, ita gaskiya take bi, kuma gaskiyar ta sani, kuma gaskiyar zata bi.

Ta rufe idonta tana sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ne wayarta da ke kan cinyarta ta yi ƙara, ta ɗaga tana kallon screen ɗin da sunan THE BEST na yawo a jiki. Lokaci ɗaya ta ji duk wani ɗaci da ɓacin ranta ya gushe, tana jin wani ɓari na damuwar da take ciki ya yaye, fuskarta ta bayyana jin daɗin ganin kiran nasa, sai ta ɗaga tana faɗin.

"Mai Babban suna kana ina? Ina ta kiran wayanka baka ɗauka ba, na kira Bello ya ce ba kwa tare, ina ka tafi? Khalil ya ce baka je office ba yau, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, duk inda ka ke ka dawo gida yanzu ka ji, ina nan na kasa samun nutsuwa tun kiran farko da nayi maka ban samu ba, yau na kiraka ya fi sau goma baka picking, tukunna dai ka ci abinci?".

Maganar take muryarta na bayyana tsananin damuwar dake ƙunshe a cikin ranta, ba don komai sai don rashin sanin halin da yake ciki tun safe da ya bar gida. Haka take ita, indai ya fita a gida basa cikakken awa guda ba su yi waya ba ta ji ya lafiyarsa, idan kuma yana gida to jiddan walahairan yana part ɗinta, suna tare ko a parlo ko kuma a bedroom ɗinta, sai dai idan ranar yana jin miskilancinsa har da ita, to sai dai ita ta bisa part ɗinsu.

Ta kan tsokane shi da cewa,"Hamman su kana juya ni kamar waina a tanda". 

Fullo da ke tsaye tana sauraren maganar Hajiya Madina, tausayin matar yayi bala'in kamata, sai ta kasa yin ko da motsi, tayi shiru ta kasa yin magana, ta bi inda Turaki yake yashe kawai tana kallonsa, me yake faruwa da rayuwarsa ne? Me zata faɗawa Hajiya Madina yanzu? Ya zata yi idan ta ji a halin da ɗanta yake ciki?.

Ta tuno yadda Hajiya Madina ta shiga tsananin tashin hankali a wata rana da ya yanke da wuƙa yana yanka lemu, ta dinga kuka akan ɗan jinin da ya zuba daga yatsan sa, ta tuna yadda Hajiya Madina ta koma bata iya nutsuwar minti ɗaya babu Turaki a kusa da ita a lokacin, ta tuna yadda duk bugawar sakan, duk wani motsi na sa sai ta ce masa,"Menene Mai Babban suna? Me kake so? Me zan maka? Ciwon yana zafi? Sannu kaji, Allah ya baka lafiya". 

Haka ta dinƙa ririta shi kamar jariri sabuwar haihuwa a lokacin. Sai Fullo ta ji inaa ba zata taɓa iya kasassaɓar sanarwa da Hajiya Madina halin da Turaki yake ciki ba a yanzu, ba zata iya ba har ga Allah, bata son ta ga uwa ta shiga tashin hankali, balle kuma Uwa irin wannan da lokaci ɗaya take fita daga hayyacinta akan ɗan da ta ƙwallafa rai akansa duk kuwa da tana da wasu Ƴaƴan da Allah ya bata.

Hajiya Madina ta rufe ido ta buɗe tana kallon agogo, ƙarfe biyar na yamma, yau wata rana ce da ta kafa tarihi a tsakaninta da Turaki, rana ta farko da Turaki ya saɓa umarninta a iyaka tsayin rayuwarsa, amma me yasa?. Kawai ta rufe ido ta ƙara buɗewa ta na sauke ganinta a daidai lokacin da agogo ya nuna biyar har da minti ɗaya, sai ta ji ranta ya ɓaci.

Cikin nuna ɓacin rai ta ce,"Ba ka taɓa zama stubborn ba, kuma a cikin ku shida da Allah ya ba ni kai ne na fi ƙoƙarin karewa daga duk abin da zai sa ka zama haka. Amma me ya sa sai yanzu da ka girma? Kana so ka zama stubborn kamar Khalil ne? Saboda na ce duk inda za ka fita, ya zama kana tare da shi ko Bello, ba wai ina nufin ka zama mara ji ba kamar Khalil.
Na san yana da takura ace duk inda za ka je sai da wani, alhalin ka mallaki hankalinka. Amma ka sani, ni uwa ce; ba zan so wani abu ya cutar da ɗana ba. Ya kamata ka tuna akwai masu farautar rayuwarka a kullum. Shi ya sa na ce duk inda za ka fita, ka kasance tare da Khalil ko Bello. Duk da na san dabarata ba za ta hana abin da Allah Ya ƙaddara ba, amma aƙalla kasancewarka tare da wani zai sa su ji tsoron tunkararka.
Kuma ka yi min alƙawarin ba za ka saɓa umarnina a kan hakan ba. Mai Babban suna, me ya sa yau, rana ta farko ka saɓa umarnina? Khalil ya ce ko minti biyu ba ka yi a office ba ka fita. Bello ya ce ka ɗauko shi a airport, amma ku ka rabu babu daɗi. Ina ka tafi tun bayan rabuwarku? Me ya sa ba ka dawo gida ka ci abincin rana ba? Me ya sa ka ƙi ɗaga wayata? Me ya sa kake son haddasa ciwona ya tashi? Me ya sa tun ɗazu ina maka magana ka yi min shiru? Wannan shiru naka na menene? Are you really okay?”

Tunani da lissafi da ke a cikin kan Fillo ya tarwatse, gabanta yayi dukan tara-tara, kallon Turaki take yi tana tuna irin tarin ta sa soyayyar wa mahaifiyarsa, zuciyarta na faɗa mata ta je ta same shi ta faɗa masa Maama ce, Maama na son yin magana da shi, zai farka idan ya ji hakan, tabbas zai farka.
Ta isa gabansa tana jijjiga shi a hankali, dai-dai kunnensa tana faɗin,"Ka tashi ga Maama". 

A zatonta ko jin hakan zai sa ya farka daga dogon suman da yayi, amma inaa kamar ma da gawa take magana.
Sai kawai wani kuka ya kubce mata. Cikin kiɗima Hajiya Madina ta ce,"Innalillaihi wa'inna ilaihi raji'un...". 

Ko salatin bata ƙarasa ba Fullo ta ce,"Maama ki zo". 

Ta faɗa tana kuka sosai. Daga ɓangaren Hajiya Madina ta zabura ta miƙe daga kan kujera, cikin gigita da tsananin tashin hankali na farat ɗaya. Me kunnenta yake ji ne? Kamar kukan wani take ji kuma kamar ana so ace mata ta zo ga Turaki babu lafiya.

"Waye ke magana? Ina Muhammad ɗin? Ke wacece?".

Kukan Fullo ya ƙaru ta ce,"Maama ni ce, Hammah ɗin ya faɗi ya suma Maama ki zo da sauri". 

Wayar da ke hannun Hajiya Madina ta nemi ta faɗi a ƙasa, Samha da idonta ya kai wurin tayi saurin taro wayar, tana sauka daga saman gadon. Ta taro wayar a lokacin da itama Hajiya Madina ke neman faɗuwa, Nihal ta yi saurin riƙota.

Samha ta ce,"Lafiya Maama, menene?". 

Hajiya Madina ta kalleta ido a waje, a hankali ta kalli Nihal, sannan ta kai idonta ga Zaytuna wacce ta yi tsaye ƙeƙam. Sai kuma ta dawo da idonta ta sauke akan wayar tana kallon call ɗin da ke tafiya, Hammah aka ce mata alhalin ga ƙannensa anan tare da ita. 

Cikin neman fitar hayyaci ta ce,"To wace me magana a wayar? Wai Hammanku ya suma, to ai na? Garin ya?". Ta jefa tambayoyin ga Samha.

Duk su ukun suka maimaita a tare,
"Hammah ya suma?". 

Hajiya Madina ta ɗaga musu kai kawai hawaye na sintiri a saman fuskarta. 
"Hello, don Allah wake magana, ina me wayar yake don Allah?". 

Nihal ta faɗa  bayan ta amshi wayar daga hannun Samha. Babu amsa sai kuka da ke tashi kawai, Zaytuna ta silale a wajen, Nihal ta yi kanta da sauri. Samha ta ɗau wayar ta kai kunne, tuni Hajiya Madina ta yi mutuwar zaune, ta koma kamar mai paralize idonta a wuri ɗaya kawai yake, jinta take kamar rayuwarta ta ƙare, kamar shikenan ta gama aiki.

Da ga ɓangaren Fillo ta ce,"Hammah ne ya suma". 

Samha ta waiga ta ga sauran sisters ɗinta suna nan, ɗaya ta suma ɗaya na ƙoƙarin ganin ta sumen ta farfaɗo. To wace ke faɗin Hammah ya suma?. 

Ta dakewa faɗuwar gaban da take ji ta ce,"To waye yake magana, kuma wanne Hammah ɗin?".

Fullo na ƙara jijjiga Turaki ta ce,"Ni ce Fullo mai aiki, Hammah Turaki ne ya suma Maama, tun ɗazu yaƙi yayi motsi kamar ya mutu".

A matuƙar razane Samha ta miƙe tsaye tana faɗin,"What! Mutuwa?, dan uwarki ke kina ina? Ta ya kika san abin da ya faru da Hamman mu?".

Jin furucin Samha ya sa jikin Fillo yin rawa a lokacin zuciyarta na faɗa mata shikenan tata kuma ta ƙare, ita dama ta sani ita za'a ɗorawa alhakin faruwar komai. 

"Fullo a ina? A ina ya suma?".

Hajiya Madina da ta karɓi wayar take tambaya kuka na ƙwace mata. 

"Maama ɓangaren su Adda Zay...". 

Bata ƙarasa ba ta ji alamun faɗuwar waya a ƙasa. Kuma zata iya cewa rabin second ne ya kawo su, don ganin su kawai tayi tsaye a kanta.

Hajiya Madina ta fizgo Fullo ta miƙe tsaye, ta zabga mata mari a fuska, marin da yasa jinta da ganinta suka ɗauke na wucin gadi. Kamin ta dawo dai-dai ta ƙara ɗauketa da wasu marikan har uku. 

"Uban wa ya buɗe room ɗin nan?". Babu abin da Fillo ke ji a lokacin balle ta iya bada amsa.

"Ba magana nake miki ba, ban yi muku iyaka da wannan room ɗin ba? Ban ce duk lokacin da zaku yi aiki babu ruwanku da taɓa wannan ɗakin ba? Wa ya baki key ɗinsa? Me yasa baki hana shi shigowa ba? Kin buɗe baki kin yi min magana ko sai nasa ƴan sanda sun kamaki kin ƙare rayuwarki a gidan yari".

Fullo na kuka ta ce,"Wallahi Maama ba ni na buɗe ba, na zo wucewa ne...". 

Bata barta ta ƙarasa maganar ba tasa bayan hannunta ta kifar da ita a ƙasa, Fullo ta zube a ƙasan tiles kanta na dukan bango, lokaci ɗaya ta ga giftawar wasu taurari a cikin idanuwanta. 

Abin da kawai zata ce ta ƙara ji shine Hajiya Madina ta mata gargaɗin cewa,"Duk abin da ya sami ɗana, duk abin da ya sami lafiyar ɗana sai na ga bayanki Fullo, tabbas sai kin ƙwammace ina ma baki zo duniyar nan ba".

Daga nan bata ƙara jin komai ba kamar yadda bata ƙara ganin komai ba na tsawon wucewar minti goma sha biyar.
Kuma da ta dawo hayyacinta da ga buguwar kan da tayi, sai ta ga babu kowa a ɗakin sai ita ɗaya.

Tsawon minti biyar tana kuka, a hankali ta dinƙa kewaye ɗakin da kallo, babu komai a cikinsa face shirgin takardu dake cikin locker, sai kuma gadon jarirai irin wanda ta taɓa gani a ɗakin Fulani, sanda Kaka ta zauna yiwa Gimbiya Zahra wankan jego.

Wanne abu ne a cikin ɗakin da ya haddasa shigar Turaki situation ɗin da ta zo ta same shi a ciki? Ina abin da yasa ba'a so a buɗe ɗakin?. Ta kalli komai kuma bata ga komai ɗin da zai zama dalili ba.

Taimakonsa ta yi, kuma taimakon take da niyyar yi masa, amma ga abin da aka saka mata da shi, ya za ayi ta manta? Waye zai taushi zuciyarta akan abin da ta ƙudurce na ramuwa?.
Amir ne kawai, kuma yanzu babu Amir a cikin rayuwarta, tsawon watanni huɗu sai ta ji tana kewar Amir a yau kawai.

Ta runtse ido tana jin zafi a zuciyarta, ta miƙe tsaye da ƙyar tana dafa bango saboda jirin da ke neman rinjayarta ya kayar da ita. Ko ina na ɗakin take bi da kallo, so take taga illarsa, ba zata taɓa barin ɗakin nan ba sai ta ga dalili, wannan dalilin da ya haifar da komai.

 ƙafarta da ke yi mata zugi har ta ƙarasa gaban ƙaton hoton da ke manne a jikin bango. Kallon matar take yi da kyau cike da nazari da son gano wani abu amma ta kasa, abu ɗaya ta fahimta matar nan na da alaƙa mai ƙarfin gaske da Turaki, saboda tsananin kama, kamannin da suka zama kamar an tsaga kara.

Sai dai irin alaƙar da take tunani zuciyarta na faɗa mata cewa ba ita ba ce, wannan matar bata yi kama da wacce ta ajiye ɗa kamar Turaki ba, shekarunta kaɗan ne, kuma ko da auren ƙauye aka yi mata bai ci ace ta haifi ɗa kamarsa ba balle har ta haife shi, ta kuma haifi Zaytuna.
Ba ma wannan ba, idan ma tayi tunanin ita mahaifiyarsu ce to Hajiya Madina fa?.

Ta dafe kanta da take jin kamar zai fashe tana saurin dafa gadon jariran, bata buɗe idonta ba har sai da ta daina jin juwar, idonta ya sauka a cikin gadon jariran, kan award frame da ke kan bargon jariri, tasa hannu ta ɗauko tana kallon award frame ɗin, ta tattara dukkan hankalinta da natsuwarta akan hoton jiki da sunan jiki. *Her Excellency RAMLA MUHAMMAD TURAKI* sunan da yake rubuce a jiki kenan.

Wai wace wannan matar? Mene alaƙarta da sunan Turaki?
*MATARSA!* Haka zuciyarta ta faɗa mata, kuma tabbas hakan yake, amma ina take? Mutuwa ta yi? Rabuwa suka yi? Take anan zuciyarta ta warware mata dalilin da ya sa ba'a son buɗe ɗakin, da kuma dalilin da yasa Turaki shiga critical condition, ba don komai ba sai saboda wannan ɗakin na da alaƙa da ita shiyasa ba a so a buɗesa, sannan ganin hotonta na fama ciwon da ta jiwa Turaki a zuciyarsa, wannan ciwon da tabonsa ya kasa goguwa daga garesa. Wanne irin ciwo ne? Me tayi masa wanda ya kasa mantawa?.

Ta ƙara ƙulle idonta na tsawon minti ɗaya sannan ta buɗe tana ƙarewa gadon jariran kallo, ta tabbata wannan ɗakin shine silar komai, kamar yadda gadon jariran nan ke da alaƙar komai, tana da tabbacin hakan, don komai ya fara haska mata tamkar a yanzu komai ɗin ke wanzuwa a gaban idonta.

Kenan idan tunaninta ya ba ta dai-dai *ƊA* ne silar komai, jaririnsu! To ina jaririn? Kuma itama uwar tana ina? Ta mutu ne? Ita da Babyn suka mutu? Kenan wannan shine ciwon dake manne a zuciyar Turaki?.

Kawai Fullo ta sauke numfashi tana hurar da iska a bakinta, ta koma ta isa gaban hoton ta ciro shi, sannan ta dawo ta ɗauko award frame ɗin ta fice da su daga ɗakin.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.