Free chapter · Read without an account

PAGE 52

by Aminatu Ibrahim · DUHUN DARE

D U H U N D A R E

A 2026 N O V E L

BOOK ONE

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHEEM

OUM-AMEER

Arewapen: @Oumameer2671

Wattpad: @Ummu-Amir

BOOK ONE

PAGE 52

"Subhanallah!"

Hajiya Salamatu ta furta cikin tsananin mamaki da firici sannan ta sake cewa.

"Amma dai ko Alhaji baka da ɗabi'a ta ƙwarai domin wannan magana da ka faɗa ba ƙarama bace… ya kamata ka tsaya ka saurari kanka fa tun kafin mafita ta kuɓuce maka.."

Wani kallon uku saura kwata ya yi mata sannan yace.

"Ke har kina da bakin magana? Duk abunda ya faru ai kece sila domin kece kike hure masa kunne domin kun jima kuna goyon bayan Alhaji Mas'ood tun ba yau ba. Kuma wallahy Allah ya isa tsakanina dake tunda har kike goyawa Faris baya don kawai ya bijire min... "

Wani irin numfashi ne mai nauyi Alhaji Ridwan ya sauke yana girgiza kai cike da takaici ya ce.

" Alhaji Gimba… ka daina ɗaukar awa kanka wahala, Wannan ba abun faɗa bane aure ne wanda yaro da yarinya suna son juna..."

" SO?"

Alhajin Gimban ya katseshi da wata irin dariya mai cike izgili sannan ya ci gaba da cewa.

"Wane irin so? Wai har akwai Son da Faris zai iya yiwa wata Mace wanda zai sa ya raina ni ya nuna ban isa ba? Ni ne nan wanda ya raine sa, ya bashi abinci da tarbiyya, sutura, wurin kwana, makaranta, kuɗin magana! Ni da na yi masa duk wannan idan shi ɗan kirki ne har akwai wata Macen da ta isa ta sa ya bijirewa Umarnina?"

" Ba raini bane Alhaji Gimba. "

Baba Sa'idu yace yana mai gyara zamansa cikin nutsuwa yaci gaba da cewa.

" Faris yaron ne kirki ne mai biyayya wanda yasan abin da yake. Kawai dai kasan yaran nan zamanin nan idan suna son Mace rufe musu ido yake, sannan kada ka manta kai ma fa ka yi naka lokacin Kamar shi"

Saurin girgiza kansa ya yi ya ce.

"Ni ban taɓa saɓawa mahaifina ba! Na san cewa ina da rashin ji amma kuma ina da gudun zuciya wani lokacin..."

Girgiza kai Hajiya Hadiza ta yi tana kallon shi ta ce.

"Uhm! Gimba kenan! Ka dai manta ne amma abin da kayi ai ba ƙarami ba ne,Ya kamata ka tuno halayenka lokacin da ka ke saurayi wanda kai kanka na san idan ka tuna wani abun sai dai ya baka mamaki..."

A zabure ya miƙe tsaye cike da bala'i ya ce.

"To me kike nufi Hadiza? Wasu shekaru kika bani masu yawa da har kike tunanin kema bansan irin ƙurciyar da kika yi ba da ni kike so ki kwayemin baya?"

Kwantar da murya ta yi tana mai girgiza kanta ta ce.

"A a! Ni fa ba wani abu nake nufi ba, nidai ina nufin ka tausayawa ɗanka tilo ƙwallin ƙwal da kake da shi a duniya, tunda yarinyar nan ba wani halin banza ke gare ta ba don Allah na roƙeka ka bari ayi auren ka daina duk wannan abun,farin cikin ɗanka ai shi ne naka ko ba haka ba?"

Hajiya Salamatu ta amsa da cewa.

"Wallahi wannan gaskiya ne Yaya Hadiza. Ni ma ina goyon bayan tunda har abubuwan sun kasance haka, Faris ya kafe ya ƙi ya saurari kowa to ya kamata ka hak'ura ka barwa Allah.... Yarinyar nan dai ba laifin ta yi maka…"

"Ku Daina!!!"

Ya wani daki table ɗinda ke gaban sa da ƙarfi har sai da suka tsorata sannan ya miƙe tsaye.

"Dukkanku ku fita daga maganar nan! Ni dai na haifi ɗana kuma na gama yanke hukunci! Wannan aure ba zai taɓa faruwa ba. Na rantse da Allah da ya aure ta gwanda ya mutu a yanda yake bai yi auren ba. Sannan kai Baba Sa'idu da kake ta wani kare Alhaji Mas'ood dake Hadiza...ku faɗamin miye ya taɓa tsinana muku a rayuwa? Babu! Amma ni na kai ku Makka, na baku jari, hidima da ta ku da ta yaranku babu wacce ban yi ba, saboda haka dole dai nine naku kuma ni za ku marawa baya. Wannan maganar auren babu ita har abada! Idan kuma wani yace zai yi gigin shiga gaba wallahy tallahy kotu ce za ta rabamu da shi ko waye ko!"

Daga haka ya saka hannunsa ya ɗauki hularsa ya fice daga falon fuuu kamar zai tashi sama.

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu tamkar ɗakin mutuwa tsabar mamaki da baƙin cikin Alhaji Gimba da ya gama cika musu zuciya.

Jiki sanyaye Baba Sa'idu ya ce.

" Uh uhm! Gimba har abada ba zai daina tijara ba. Ni har yau ban taɓa ganin mutum irin sa ba. Bawan Allahn nan ya jaka a jiki ya tsaya maka ya nuna maka hanyar samun arziki wanda Allah ne sanadi shi ne sanadi amma kuma kace babu wanda ka tsana kake takun saƙa da shi sai wannan ɗin! Ina amfanin wannan rayuwa wacce babu amana a cikin ta. Kun taso ku huɗu kun bunƙasa a tare, ɗaya yazo ya rasu, maimakon ku haɗe kanku ku uku domin ku ci gaba da tafiyar da kasuwancinku shi ne kai ka farraƙe kana rashin mutunci..."

Ajiyar zuciya Alhaji Ridwan ya sauke a hankali sannan ya ce.

" Tau! Allah ubangiji ya kyauta mana yasa mu fi ƙarfin zukatanmu amin...magana ta gaba kuma ba za mu tsaya haka ba, ba zamu zauna muyi shiru kuna kallon sa ba, wannan aure dole sai ya faru in sha Allahu. Ku manta da shi, indai yaga an yi auren ai dole ya shafawa kan sa ruwa ya sauko. "

" Allah yasa. "

Cewar Hajiya Salamatu sannan suka amsa da amin suka tashi suka wuce tare da ci gaba da jinjina maganar.

*******

Tun daga ranar ta dawo girka masa abinci kamar can farko da ta fara, sannan za ta yi wanka ta shirya kaman yanda ta saba su zauna da dare yana aikinsa ita kuma tana kallo ko kuma tana chart. Tun da ya fahimci cewa tana son kayan Ice cream da snacks da su chocolate tun daga ranar kullum baya dawo mata empty handed, dole sai ya samu wani abinda ya riƙo mata. Idan  kuma za su kai ƙarfe nawa a zaune wuri ɗaya to shiru shi ne abinda yafi yawa a tsakanin su. Lokacin tashinsa daga aiki na yi zai kakkaɓo ya dawo cikin lokaci wanda yanzu har ta rage fargabar cewa zai iya sake yin tafiyarsa ya barta. Bacci ma a ɗakin ta suke yi but saidai tana kan gado yana kan kujera har gari ya waye.

Yau ma yana fita ba jimawa Na'ima Hassan ta kira ta take sanar mata cewa sun koma second semester tun kwana biyu da suka wuce har an fara lectures. Bayan sun sha firarsu sun gama tace mata daga zaran ya dawo daga aiki za ta tuna masa.

Da wannan ta wuni a ranta wanda bayan ya dawo yaci abinci har ya yi wanka ta same shi har cikin ɗakin sa abinda ta jima ba ta aikata ba.

Tsaye ta ganshi da frame ɗinda ke ɗauke da hoton wannan mutumin da ruwan hawaye a idon sa.

Da sauri ya ajiye tare da goge hawayen nasa cikin zafin nama gudun kada ta ganshi but ya riga da ya makara domin ta ganshi kuma ta gane kuka yake yi.

Wani murmushi ya ƙirƙiro yana mai kallonta da mamakin abinda ya shigo da ita ya ce.

"Maryam..."

Daga inda take tsaye kawai ta ce.

"Daman ina so ne zamu yi magana."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Okay...Just 2mnt."

Parlour ta dawo ta zauna tare da ɗaukan remote control ta canja tasha Zuwa Zee world amma kuma gabaɗaya hankalinta baya wurin. Tunani kawai na neman dalilin da yasa yake kallon wannan hoton yana kuka. Wait...ko dai shi ne Abiyh ɗin da ta ji wacce ya rubutawa Maami ta ambata? He's condition is getting worst this time around.

Wannan ita ce maganar da ta tuna wacce ta sanya a ranta cewa wata ƙila kukan rashin lafiyar mutumin ce yake, to amma miyasa wannan wurin aikin nasu suke da tsauri haka? Miyasa ba za su bashi dama yaje ya dubo mahaifinsa ba nan da Zaria?

A hankali ta hango shi yana zuwa wanda shi ne abinda ya katse mata tunanin ta. Kallon shi take har ya ƙara so ya zauna ɗan nesa da ita ya ce.

"Barka da hutawa..."

Wani guntun murmushin ta saki domin maganar ta ɗan bata dariya daban, sai kace wata gimbiya.

"Daman ina so in tuna maka cewa mun koma lectures..."

Jinjina kansa ya yi yana Kallonta ya ce.

"Ba mantawa na yi ba, alƙawarin one week muka yi dake saboda haka sai jibi in sha Allahu zamu koma..."

Wani irin farin ciki ta ce.

"Thank you so much..."

Kallonta yake da mamaki ya ce.

"Ohh! Wato murna ma kike yi ko? Kan ki kawai kika sani.."

Girgixa kanta tayi tana murmushi alamar a'a sannan ya sake cewa.

"zan yi kewanki sosai...zan yi kewan wannan girkin naki mai daɗi plus kyakkyawan murmushin ki da kuma dressing ɗinki..."

"Uhm.."

Abinda kawai ta ce kenan ba tare da ta sake kallon inda yake ba. A ranta ji take duk abinda take ji dole ta yi masa uzuri tunda a gabanta ma kullum cikin aiki yake ba dare ba rana and ga shi har yana da marar lafiya amma kuma sun kasa masa uzuri.

******

Rabi'a kuwa, tana nan tana ta shagalinta tana abinda ranta yake so a gidan Abbah musamman da Yaa Muhammad ya iso suka tattauna kuma suka amince.

Duk da cewa tana gidan, kullum cikin waya take da Umma suna ta shirye-shirye da tsare-tsaren buki wanda sun lissafa event da za su yi yafi guda goma wanda tace a ajiye sauran maganan anko a bari sai Faris ya zo idan suka tattauna za ta yi musu bayani kafin ta koma gida idan buki ya rage saura kwana uku.

Yau tunda ta wayi gari taje ta samu Nene a kitchen ta sanar mata cewa Mijinta yana kan hanya tana so a haɗa mishi kalolin girki kamar guda biyar da drinks da snacks na tarbon babban baƙo.

Yanda ta bada order haka Nene ta zaɓi mutum biyu daga cikin masu aikin kitchen ɗin tace su yi mata duk abinda tace.

Zuwa ta yi tasha wankan ta ta fito ta zauna ta tsara wa kanta kwalliya ta ji da gani sannan ta samu wuri a ɗakin na ta ta zauna zaman jiran shi domin ta yi alƙawarin babu wani ƙaton da zai ga wannan kwalliyar sai Farrab ɗinta habibiyn zuciyar ta.

Tana nan tana chart tana kuma yi tana duba time har sai da taji ya kira ta da cewa ya iso.

Cike da wani irin jiji da kai take tafiya tana wani rangwaɗa tana ƙallewa tana tashi tamkar wata taliya har ta isa bakin motarsa tana masa murmushi.

"Beeyh.."

Ya ambata yana mai fitowa daga motar ya tsaya a gefenta.

Fitowan shi a mota kenan suka yi Ido biyu shi da Yaa Mukkaram wanda in banda mugun kallo da harara babu abinda Mukarram ɗin ke jefa musu

        ✍️ *OUM AMEER✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.