Free chapter · Read without an account

89

by ZAHRA B MRS · Bayan Murmushi

Ana saura 'yan kwanaki su Farhana su bar Amurka, sai kaddara ta sake hada ta da Abdulkadir (AK). Sultana da Lamido sun tafi hutun karshen mako (weekend) gidan mahaifinsu, kwatsam sai kiran AK ya shigo wayar Farhana.

"Maryam, muna asibiti. Sultana ce take zazzabi mai zafi," muryar AK ta fito cike da fargaba.

A lokacin Farhana tana tare da Zayd Al-Mansur, suna tattaunawa akan takardun tafiyarta. Farhana ta rude, Zayd bai tsaya wata-wata ba ya kwashe ta a motarsa ta alfarma suka nufi asibitin.


Suna isa, Farhana ta tarar da AK yana ta zagaye a corridor din asibitin. Ganin Farhana sanye da riga ta alfarma da kwarjini ya sa AK tsayawa cak, amma abinda ya fi soka masa zuciya shi ne ganin katafaren Balaraben nan (Zayd) a gefenta, yana tafiya tamkar wani babban jami'in tsaro (Bodyguard) dake kare gimbiyarsa.

Farhana ta shiga dakin Sultana tana duba jikin ta ,Wanda Alhamduillah Zazzabin ya sauka , bayan ta tabbatar jikinta ya yi sauki, sai ta kalli AK cikin sanyi.

"Zamu tafi Najeriya da yaran nan a wannan hutun na makaranta nanda 5 days inshaAllah Muna hanya .Rabonsu da gida tun suna shekara daya da rabi, lokaci ya yi da zasu san asalinsu."

AK ya zura mata ido, kishin dake cin sa ya sa ya juya harshensa zuwa Turanci .

"And this one... where did you find him?" AK ya tambaya yana hararar Zayd.

Farhana ta masa wani kallo na raini. "Ba matsalar ka ba ne AK. Stay out my life 

AK ya yi murmushi mai ciki da daci, "To gara ma ki aure shi (Zayd) akan Farooq. . Amma ki sani Maryam, nima na san zaki dawo mini ne. Zamanmu bai kare ba, wuyar ta mu koma Najeriya."

Ya fada cikin harshen hausa 

Zayd, wanda bai jin Hausa kuma bai san me ake tattaunawa ba, ya lura da yadda AK yake bin sa da harara da kuma yadda yake magana da sauri-sauri cikin bacin rai. Ya matso kusa da Farhana

"Maryam, what is going on? Is this man bothering you?" Zayd ya tambaya cikin natsuwa amma muryarsa tana nuna zai iya yin komai don kare ta. "What is he saying? Why is he looking at me like he wants to fight?"

Farhana ta kalli Zayd, sannan ta kalli AK wanda kishi ya sa ya fara zufa. Ta san cewa idan ta gaya wa Zayd gaskiyar abinda AK ya fada (na cewa tana nan zata dawo gare shi), Zayd zai iya daka wa AK rashin mutunci a asibitin nan.

"He's just being difficult, Zayd," Farhana ta amsa cikin Turanci don AK ya ji. "He’s finding it hard to accept that I am no longer under his control. Let's take the kids and go. I have no words for him."

AK ya tsaya yana kallon yadda Zayd ya kwashe yaran cikin mota, ya bude wa Farhana kofa cikin girmamawa suka bar shi a tsaye. Ya ji tamkar an watsa masa garwashin wuta a rai. Ganin Farhana da wani babban Balarabe ya fi kona masa rai fiye da ganinta da Farooq.yayi nadamar kawo farhana Boston sau ba adadi


Garin Boston ya yi sanyi, amma zuciyoyin su Isabella sun yi nauyi fiye da sanyin garin. Kowa ya hallara a filin jirgi don yi wa su Farhana bankwana.

Isabella ta kankame Farhana tana kuka. "Maryam, don Allah kar ki manta da mu. Ina jin tsoron idan kika tafi Najeriya, dangi da abokan arziki za su sa ki ki ki dawowa."

Farhana ta goge mata hawaye, "Isabella, Boston ita ce kasar da ta ba ni mafarki na. Ke ce kika zama uwata da yar uwata. Zan dawo, wannan tafiyar ta aiki ce da kuma bikin Fateeha. Ba zan taba mance ku ba."Hailey da Kevin suna gefe suna kukan rabuwa da twins ,inda sultana ta fara buga kafar Akan a tafi da Kevin 

Zayd Al-Mansur kuwa ya kasa boye damuwarsa. Ya dauki Lamido da Sultana yana sumbatar su, idanunsa sun yi jawur. "My little pilots," ya fada cikin muryar radadi. "Zan yi kewarku sosae. Maryam, ki kula min da su. Idan wani ya taba su a Najeriya, ki kira ni zan sauka da jirgina na kaina a Lagos cikin sa'o'i kadan."ba Aa Lagos muke ba zayd a abuja muke farhana ta fada cikin murmushin yake 

Farooq kuma ya ja Farhana gefe, ya kamo hannunta ya sumbata. "Baby girl, kiyi tuki lafiya. Ki nuna musu ke wacece. Nan da mako guda zan zo Najeriya in same ki kafin ki gama aikinki ki dawo. Zuciyata tana tare da ke."

A

Farhana tana sanye da kakinta na International Co-Pilot mai ratsin zinare a kafada. Tana zaune a bangaren dama na Cockpit din babban jirgin Boeing 737.

A daya bangaren kuma, Abdulkadir (AK) da Hanadi suna zaune a sashen first Class. Hanadi tana ta faman korafi akan yadda jirgin ya cika, ga Afifa sai rigima take mata yayin da AK yake lallashinta, yana tunanin yadda zai sake ganin Farhana idan sun sauka.sultana da Lamido suna gefen sit din su Ak 

Ba zato ba tsammani, sai muryar matukin jirgin ta gauraye ko'ina.

Farhana ta gyara mic dinta, ta dauki numfashi mai zurfi, sannan ta fara magana cikin sanyin murya da turanci mai natsuwa, sannan ta koma Hausa:


"Good afternoon, ladies and gentlemen. This is your Co-Pilot, Maryam Ibrahim Matazu, speaking from the flight deck. On behalf of Captain Richards and the entire crew, I welcome you aboard this special ferry flight Abuja Nigeria.


Zamu tashi a tsayin kafa dubu talatin da shida (36,000ft), kuma yanayin garin Abuja yana da kyau. Muna godiya da kuka zabi tafiya tare da mu. To our passengers, especially those returning home for special occasions, we wish you a pleasant journey.


Suna jin sunan "Maryam Ibrahim Matazu", Hanadi ta kusa sakin afifa dake hannunta, Idanunta sun fito waje tamkar zasu fadi.

"Darling Kaji abinda na ji?" Hanadi ta fada cikin rarraba murya. "Maryam? Wace Maryam din? Ba dai waccan kucakar  matar taka bace take jan wannan katon jirgin?"

AK ya lumshe ido, wani irin daci da alfahari suka ziyarce shi a lokaci guda. "Ita ce, Hanadi. Na gaya miki Maryam ta zama Captain a Boston, amma baki yarda ba. Yanzu gashi, ita ce take tuka mu zuwa gida."

Hanadi ta fara gumi, zuciyarta tana bugawa. Tunanin yadda zasu hadu da Farhana a filin jirgi na Abuja ya fara sanya ta jin kishirwa. Ta kalli AK, ta ga yadda yake kallon kofar cockpit din cikin wani irin shauki, sai ta ji tamkar ta kurma ihu.

Tafiya ta kankama, Farhana tana sama tana tashi cikin gajimare, yayin da wadanda suka wulakanta ta suke kasa, suna jiran jin kalma daya daga bakinta.


Duk da cewa Farhana tana cikin Cockpit, Sultana da Lamido suna zaune a sashen First Class, inda kamfanin jirgin ya tanadar musu wurin zama na musamman don karrama mahaifiyarsu. 


Suna jin muryar Farhana tana yin announcement, Sultana ta mike tsaye tana tsalle a kan kujerarta.

"Lamido! Listen! It's Ammi! Ammi  is the Pilot!" ta fada cikin sanyin muryarta ta yara tana nuna lasifikar jirgin.

Lamido, w, ya gyara zaman hularsa ta p cap da yake mugun so ya yi murmushi. "I told you Sultana, Ammi  is the best Pilot in the world."

Fasinjojin dake kusa da su duk suka juyo suna kallon wadannan kyawawan yaran. Wata mata baturiya dake zaune a kusa da su ta tambaya, "Is your mom really the pilot of this big plane?"

"Yes!" Sultana ta amsa cikin. "And she's taking us home to Nigeria."

Hawayen takaici suka shake hanadi ,


Ta tsaya cak, zuciyarta ta buga. Wadannan yaran sune dai wadanda ta kalla a matsayin "yaran kucakar  mace" a gidan AK, amma yanzu gashi sun zama tamkar yaran sarki. Kyawunsu, natsuwarsu, da kuma yadda a shekaran su 4 har Sun San alfahari da naman su yasa Hanadi jin wani irin bakin ciki.

Sultana ta kalli Hanadi, ta gane fuskarta Ta daka mata wani kallo na rashin sani, sannan ta juya kanta ta cigaba da wasa da iPad dinta.

Hanadi ta juyo Wajan AK tana huci. "AK, kaga yaran can? Har sultana tayi girman da zata Harare ni ?"kausar da take yar 13 years yanzu tayi mamakin yadda anty farhana ta zama pilot ,intisar kam baki yaki rufewa Sabida murna 

AK ya yi shiru, idonsa a lumshe. A ransa yana hango ranar da zai dawo da Maryam gidansa , yana fatan ko da wasa ne ta kalle shi yadda take kallonsa a da. Bai san cewa yanzu Maryam ta wuce tunaninsa ba.


Farhana tana rike da ragamar jirgin, tana kallon na'urorin dake gabanta. Tana jin dadi a ranta cewa yaranta suna bayanta, suna takun alfahari da ita. Wannan tafiyar ba kawai ta aiki bace; tafiya ce ta nuna wa duniya cewa jarumta da juriya suna kai mutum ga gaci.

"Captain Richards," Farhana ta kira babban Pilot din dake kusa da ita.

"Yes, Maryam?"

"I'm so happy to be flying my kids home. It feels like a dream."

Richards ya yi murmushi, "You earned it, Maryam. You are a great pilot and a great mom."

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.