Free chapter · Read without an account
90
Diddi tana tsaye, idanunta suna yawo a kofar da fasinjoji suke fitowa, zuciyarta tana dukan sauri. Abbi da Hamma Fahad da sauran ’yan uwa duk suna wurin, kowa ya sanya mafi kyawun kayansa. A gefe guda kuma, AK da Hanadi suna tsaye, su ma suna zare ido, AK yana kokarin ganin ta ina Farhana za ta fito.
Ba zato ba tsammani, sai ga su Sultana da Lamido sun fito hannunsu rike da na ma'aikatan jirgin. , fuskarsu tana sheki da kyan hutu.
"Diddi! Abbi!" Sultana ta kwace hannunta ta ruga da gudu ta fada jikin Diddi.yaran Sun San kakaninsu dan farhana kullum cikin nuna masu vidoes da hoton yan gidansu take,a times ba diddi takan kira su dadi suna vidoe call
Diddi ta dauki Sultana tana kuka, "Ina maman taku? Ina Maryam din take?"
Can sai aka ga wasu mutane hudu sun fito daga wata kofa ta daban (Crew Exit), inda matukan jirgi suke fitowa. A tsakiya, akwai wata mace wadda takun tafiyarta kadai ya isa ya gaya maka cewa ita din ba talaka bace.
Tana sanye da bakar riga ta matukan jirgi (Pilot Blazer) mai ratsin zinare hudu a kafada, hular Pilot dinta a kanta, sannan gilashin Ray-Ban a idonta. Ta rataya jakar tashi a kafada, tana tafiya cikin natsuwa da isa.
Abbi ya gyara gilashinsa, "Fahad, wacece wannan matukiyar jirgin dake tahowa wurinmu?"
Hamma Fahad ya zura ido, "Abbi... kamar... kamar Maryam ce."
Diddi ta saki Sultana, ta matso gaba tana rarraba ido. Farhana ta iso daidai gabansu, ta tsaya cak, sannan ta cire gilashin idonta ta sakar musu wani lallausar murmushi.
"Diddi... Na dawo," Farhana ta fada cikin muryar da ta dashe saboda shauki• Diddi Ta saki wani irin kuka na murna, ta rungume Farhana tana sumbatar kumatunta. "Maryam! Kece kika tuka wannan katon jirgin? Kece kika dawo mana a matsayin Pilot? Allahu Akbar!Abbi Ya kasa magana, sai Kawai ya sanya hannu ya dafa kafadar Farhana, hawayen alfahari suna zuba a kumatunsa. Shi da ya taba tunanin rayuwar Maryam ta kare a matsayin matar gida, yau gata tana jan ragamar samaniya.
A gefe guda kuma, AK ya daskare. Ganin yadda dangi suka kewaye Farhana tana walkiya a cikin kakin Pilot dinta, ya ji kansa ya yi masa nauyi. Hanadi kuwa, ji take kamar kasa ta tsage ta shiye ta saboda kunya da kishi. Wadanda take kira "talakawa " yanzu sune taurarin da kowa yake kallo an airport din.
Farhana ta kalli inda hanadi take , ta sakar mata wani kallo daya mai cike da ko-o-ho, sannan ta juya ga danginta.
"Abbi, wannan jirgin da kuka gani a waje, ni da tawagar mu muka dauko shi daga usa Kuma wannan surprise din nawa ne gare ku duka—don ku sani cewa Maryam Ibrahim Matazu ta zama zakara.
Diddi ta kalli kakin jikin Farhana, ta taba ratsin zinaren dake kafadarta kamar tana tsoron kar ace mafarki take yi.
"Ya Allah! Maryam, ashe dama abinda kike kikeyi kenan? Kullum idan muka yi waya sai kice min kina karatu, ashe karatun sararin samaniya ne wannan? Na gode wa Allah da ya nuna min wannan ranar. Yau duk wanda ya taba kiran ki da gazawa, Allah ya nuna masa ke jaruma ce!"
Abbi ya kasa daina murmushi, idanunsa har yanzu akwai kwalla, amma a wannan karon ta dadi ce. Ya gyara tsayuwar sa, ya kalli jama'ar dake wurin cikin alfahari.
"Maryam, kin wanke mini dukkan kunyar da na ji a baya. Ranar da kika bar gidan nan cikin kuka, ban taba tunanin zan gan ki a haka ba. Kin nuna mini cewa ilimi da jajircewa su ne makamin mace. Ina alfahari da ke, 'yata. Yau ko yanzu Allah ya dauki raina, na san na bar zakara a duniya."
"Adda farhana Na shiga uku! Gaskiya kinsan yadda ake suprise. Kinga yadda kowa yake kallonmu kuwa? Yau zan iya cewa yayata ita ce tuka wanan Katon jirgi mun I love you Adda !
Yayin da dangi suke ta murna, AK yana tsaye kamar gunki. Ya ji kalaman Abbi sun soke shi har cikin zuciya. Hanadi kuwa, ta kasa cewa uffan, domin duk kudin da take takama da su, ba su kai darajar wannan kakin dake jikin Farhana ba.
A filin jirgin, yayin da aka fara nufi wurin motoci, Hamma Fahad ya tsaya cak, ya kasa motsawa. Ya tuna yadda shekaru da dama da suka wuce, duk lokacin da Farhana tace tana son zama Pilot, sai ya yi dariya yace: "Mace da tuki? Maryam ki duba wani aikin mana, ko dai ki zauna ki koyi girki, ko kuma ki zama malamar makaranta. In ba haka ba, sauka zaki yi kiyi ta kukan rashin miji."
Adda Sabrina kuma, wadda take tsaye kusa da shi, fuskarta ta kasa nuna komai sai al'ajabi. Ta tuna lokacin da Farhana take gidan AK, tace mata: "Ki daina wannan mafarkin Maryam, AK ba zai taba bari ki yi karatun da zai sa ki dinga shawagi a sama ba. Matar gida ce ke."
Adda Sabrina ta matso kusa da Farhana, muryarta tana rawa. "Maryam... lallai Allah Mai iko ne. Na taba cewa wannan aikin ba naki ba ne, na zaci wasan yara kike yi. Amma yau, kin nuna min cewa ke din tafi karfin tunaninmu. I'm... I'm so sorry, kuma ina alfahari da ke."
Hamma Fahad ya sosa keya, yana dariyar jin kunya. "Gaskiya ne Maryam. Na sha gaya miki ba zaki iya ba, ashe ni ne nake gani da idon makiya. Yau gashi kin tuka jirgi kuma Nasan kowa an Abuja yana maganar Captain din da ta sauko da babban jirgi."
Farhana ta yi musu murmushi mai cike da darasi. "Ba komai Hamma, dama can nasara ita ce kadai hanyar da zaka yi magana kowa ya ji ka."
Hotona suka fara da farhana Kala Kala
Suka jera zuwa motoci, inda aka nufi Lugbe cikin jerin gwano, dangi suna ta sowa.
A cikin motar AK, shiru ne ya gauraye ko'ina. Hanadi tana zaune a bayaa, tana huci tamkar macijiyar da aka taka wa jela. Shi kuwa AK, tunanin Maryam kadai yake yi—yadda ta koma kyakkyawa, kwarjinin da ta samu, da kuma yadda kowa yake girmamata.
Suna isa gidan su dake Asokoro, yaran duk Sun shige gida AK ya dade bai fito ba. Hanadi ta fusata, "AK! Me kake tunani ne haka? Tunda muka fito daga airport din nan kake wani shiru-shiru."
AK ya buga jikin kujera , ya juyo ya kalli Hanadi da idanunsa da suka rine. "Hanadi, kin ga Maryam kuwa? Kin ga yadda ta koma? Kin ga yadda danginta suka kalle ni kamar wani bako? Wannan macen tawa ce, ni na fara mallakarta kafin wani Farooq ko wani Balarabe ya ganta."
Hanadi ta kwala ihu , "Maryam! Maryam! Ita din mecece? Pilot ce fa kawai!"
"Ba kawai ba ne Hanadi!" AK ya daka mata tsawa. "Muna maganar mace ce da tafi kowace mace daukaka a northern Nigeria . In gaya miki gaskiya, ba zan iya zama a Najeriya in bar Maryam tana yawo a matsayin matar wani ba. Dole ne Maryam ta dawo gidan nan. ! Ko ta wace hanya, dole ne in mayar da ita matata."
Hanadi ta daskare. Ta san idan AK ya ce zai yi abu, to zai iya komai. Ta fara jin tsoron cewa matsayinta na sarauniyar gidan Asokoro yana girgiza.
Suna isa ƙofar gidan su dake Lugbe, Farhana ta ji gabanta ya fadi, amma ba na tsoro ba ne; na tsantsar mamaki ne. Gidan da ta bari a dā, wanda yake talaka-talaka, yau ya koma tamkar wani ƙasaitaccen gida. 'Yan uwanta maza, waɗanda kowannensu yanzu Allah ya buɗe masa ta fannoni daban-daban, sun haɗa ƙarfi sun mayar da gidan mazaunin masu hannu da shuni.
Farhana ta shiga falon, ƙafarta tana takawa a kan lafiyayyen kafet. Ta kalli rufin dakin, ta ga aikin POP mai kyau da fitilu dake bayar da haske mai sanyaya rai. Ga sanyin AC dake ratsa ko'ina.
"Diddi, wannan gidan namu ne?" Farhana ta tambaya tana murmushi.
Diddi ta gyaɗa kai, idanunta cike da hawaun murna. "Alhamdu lillahi Maryam. 'Yan uwanki ne suka ce ba za su bar ni a cikin tsohon yanayi ba. Kema kuma kudin da kike aikowa sun taimaka Allah ya maku Albarka ,Komai kin ganshi ya sauya."
Farhana ta nufi ɗakin Diddi, nan ma ta tarar da shi yasha gyara na musamman. Gadon dake dakin mai laushi ne, ga kamshin turaren wuta na alfarma yana tashi. Ta ji wani irin farin ciki ya ziyarce ta, ganin cewa mahaifiyarta tana cikin jin daɗi.
Su Sultana da Lamido kuwa tuni sun zama taurari a wurin kakanni da uncles. An raba su kashi-kashi; wasu suna can wurin Grandma, wasu wurin Grandpa.
"Look, Sultana! Grandma has cookies!" Lamido ya fada yana murna.
Suna ta wasa da uncles dinsu wadanda suke ta faman daukar su hoto suna cewa "Ga yaran Captain dinmu."
Bayan hayaniya ta dan lafa, Farhana ta ji wani irin jiri yana kwasarta. Tuki daga Turai zuwa Najeriya ba karamin aiki ba ne, ga kuma nauyin nauyin kaddamar da babban jirgi a karon farko.
Ta nufi dakin da aka ware mata, ta cire kakin Pilot dinta cikin natsuwa. Ta shiga wanka, ruwan dumi ya rinka ratsa jikinta yana wanke mata gajiyar sararin samaniya. Tana fitowa, ta sanya wasu riga da wando na bacci masu laushi, ta sanya su Sultana ma wanka, sannan suka baje a kan gado.
Kafin ma kanta ya taba matashin kai, bacci ya kwashe ta. Wani baccin dadi da nutsuwa, baccin da mutum yake yi a gida, karkashin inuwar iyayensa.
Diddi ta tura kofar dakin a hankali, ta shigo rike da bargo. Ta iske Farhana a kwance, fuskarta tana sheki kamar wata. Ta kalli fuskar 'yarta, ta ga yadda lokaci ya goge mata dukkan sauran wahalar da AK ya sanya ta a ciki. Yanzu Farhana ta zama cikakkiyar mace, mai kwarjini da matsayi.
Diddi ta ja bargon ta rufe musu kafa, ta zauna a gefen gadon tana kallon Farhana. Ta sanya hannu ta shafa kanta a hankali.
"Allah Ya yi miki albarka Maryam," Diddi ta rada a hankali. "Kin nuna wa duniya cewa addu'ar uwa ba ta fadi kasa banza. Kin dawo mini da kima ta a idon mutane. Allah Ya kara daukaka ki."
Ta dade tana kallon su, kafin ta tashi ta kashe fitilar dakin, ta fita tana godiya ga Allah da ya raya ta har ta ga wannan ranar.