Free chapter · Read without an account

92

by ZAHRA B MRS · Bayan Murmushi

Bayan Sun gama wayar falo ta fito har lokacin twins na bacci . Farhana tana zaune a kan kafet, kewaye da Diddi, Abbi, Hamma Fahad, sajid ,Muhammad harda Adda Sabrina wacce itama ta bugo sammako ga sameena auta ma a gefe . Kowa ya yi tsit, idanunsu a kanta, suna jiran jin yadda aka yi "talakar " gidan AK ta koma  pilot.

"Diddi," Farhana ta fara magana, muryarta tana rawa kaɗan. "Mutane suna ganin kakin nan na jikina, amma ba su san gumin  da ya fita daga jikina ba kafin in sa shi. Ranar da na bar chestnut hill , ban da komai sai tsoro. Mun rabu ba tare da ko sisi ba a jikina ba 

Ta kalli hannunta, ta cigaba. "Na yi aiki a matsayin waitress a gidan abinci (Restaurant). Dan kawai in sami kudin da zan biya na tuka jirgi na tsawon awa daya.nakan kwana ina kuka , amma na san idan na yi kuka, babu mai share min."


"Idan ba don Isabella ba, da ban san inda rayuwata za ta kare ba. Ita ta ba ni wurin kwana, ita ta zama yar uwa gare ni. Ita da Hailey su ne suka zama dangina a lokacin da kowa ya manta da ni. Su ne suka koya min cewa mace ba ta buƙatar namiji kafin ta yi rayuwa."nasha wahala a gidan Ak behind the scenes,kawai murmushi na kuke gani amma Baku san menene a BAYAN MURMUSHIN ba ,inda ta fara basu labarin tundaga aurenta da Ak har zuwa rabuwarsu ,(amma bata basu labarin attempt murder case din Ak ba ) 

Diddi  Ta  sauke numfashi, "To ya aka yi kika  kara haɗuwa da Farooq kuma?"

Farhana ta yi murmushi, "Farooq kaddara ce daga Allah. Ya dawo rayuwata a lokacin da ban yi tsammani ba. Shi ne ya karfafa min gwiwa, ya ce Maryam ba zata tsaya a Waitress ba. Sannan Zayd kuma, shi ne abokin da Allah ya ba ni don ya nuna mini cewa akwai maza masu mutunci. Zayd ya tsaya mini tamkar danuwa uwa daya uba daya 


Yayin da take ba su labarin yadda take tafiya a cikin dusar ƙanƙara (Snow) don zuwa makaranta saboda ba ta da kudin mota kuma bata son ta dame motar Isabella takan rage tafiyar kafa Kafin ta je boss station dan karasawa airport Diddi ta kasa daurewa. Ta fashe da kuka, ta jawo Farhana ta rungume.

"Ashe  wannan wahalar kika sha Maryam? Me yasa baki gaya mana ba?" Diddi ta fada cikin kuka.

Farhana ta goge wa mahaifiyarta hawaye. "Diddi, idan na gaya muku, zaku damu, kuma babu abinda zaku iya yi a lokacin. Na so in nuna muku nasara ne kafin in gaya muku zafi. Yau gashi, dukkan wahalar ta zama tarihi."

Hamma Fahad ya sunkuyar da kansa, . "Maryam, lallai mu ma mun yi miki rashin adalci. Mun dauka rayuwar hutu kike yi a can, ashe fadi-tashi kike yi na neman rayuwa."Meyasa tuntuni biki fada yadda Ak da danginsa suke miki ba farhana da wallahi bazaki Kai war haka a gidansa ba ,cewar Hamma Muhammad Wanda kowa ya sani da saukin kai 


Abbi ya gyara zamansa, ya dube su duka. "Kowa ya saurara ya ji. Wannan labarin na Maryam, babban darasi ne gare ku duka. Kada wani ya sake raina kananan mafarkin wani. Maryam, Allah ya miki albarka. Yau kin kara girma a idona fiye da kowane lokaci."

Wannan zama ya kara dankon soyayya a tsakanin dangi. Sun fahimci cewa nasarar Farhana ba ta zo cikin sauki ba; nasara ce da aka gina ta da hawaye, gumi ,da kuma juriya.


Farhana tana tsaka da ba su Diddi labarin wahalar da ta sha, sai aka ji tsayuwar mota a waje. Hamma Fahad ya fita don duba ko su wane ne. Cikin mintuna kalilan ya dawo fuskarsa dauke da tsantsar mamaki.

"Abbi... Nene ce! Daga Matazu!"

Kowa ya mike tsaye. Nene, tsohuwa mai ran karfe, ta shigo falon tana dingisa sanda, tana bin kowa da kallo. Diddi ta karasa ta karbi kayanta, tana mata sannu da zuwa.


"Nene, yaya aka yi kika taho haka babu sanarwa?" Abbi ya tambaya bayan an gama gaishe gaishe an kawo mata ruwa.

Nene ta gyara zamanta, tana kallon kowa daya Bayan daya "Hmm... Abdulkadir ne ya aiko aka dauko ni. Wai Maryam ta dawo, shi ne ya ce dole in zo in ga gimbiyar tashi. Jirgi ma ya sanya aka dauko ni daga matazu ya kawo ni nan habuja Yaron nan yana da kirki

Farhana dake zaune a gefe, ta ji zuciyarta ta buga. AK ya san Nene ita ce kadai ake shakka, shi ya sa ya dauko ta don ta zama katsalandan a rayuwata.


Nene ta juya, ta kalli Farhana wadda take zaune sanye da riga da wando na tracksuit masu kyau. Nene ta kankance ido, tana bin Farhana da wani irin kallo  na  raini—kallon tara saura kwata.

"Sannu maryam Haka kika zama kenan  ?Nene ta tambaya cikin muryarta ta tsoffi. "Wato ashe abinda nake ji gaskiya ne? Kece kike shawagi a sama kamar tsuntsuwa? Maryam, ni dai a sanina mace dakin miji aka san ta. Wannan shigar taki ta 'yan iskan zamani, ita kike kira nasara?"

Farhana ta sunkuyar da kanta, tana kokarin danne bacin ranta. "Nene, barka da zuwa. , shiga ya zaman gida ce Kema fa kin zauna dani a Massachusetts kin San haka muke zama a gida ,kuma daukaka Allah ne ya ba ni."

"Daukaka a sama?" Nene ta tabe baki. "Abdulkadir ya gaya min komai. Ya ce har yanzu yana son ki, kuma yana so ki dawo dakin ki ki huta wannan wahalar da kike sha a cikin gajimare. Maryam, ki sani, duk inda kika kai a sama, kasa zaki sauko. Kuma baki da kasa mafi kyau kamar gidan Abdulkadir."


Farhana ta kalli Diddi, ta ga mahaifiyarta ta yi shiru domin ba ta son fada da Nene. Ta fahimci cewa AK ya yi amfani da makami mafi hadari

"Nene," Farhana ta fara magana cikin natsuwa amma da jarumta. "Akwai abubuwa da yawa da Abdulkadir bai gaya muku ba. Amma ki sani, Maryam din da kika sani a da, ta dade da mutuwa. Wannan Captain Maryam ce, kuma ni ba zan taba komawa gidan da aka wulakanta ni ba."

Nene ta saki wani irin kallo, ta juya ga Abbi. "Ibrahim, kana jin abinda 'yarka take fada? Wato ilimin bature ya sanya tana  raina maganar manya? To zaku gani, idan har ni na haifi ubanku, sai na ga inda wannan taurin kan naki zai kai ki."


Wannan daren, Farhana ta kasa bacci mai dadi. Zuwan Nene ya bata mata lissafi. Ta san cewa Nene zata iya sanya Abbi ya canza shawara, ko kuma ta rinka matsa masa  lamba .

Ta dauki wayarta, ta ga sakon Farooq: "Goodnight my Pilot. I'm counting down to see you."

Ta yi ajiyar zuciya. Tana bukatar Farooq ya zo Najeriya da wuri, kafin AK da Nene su gama kulla makircin da zai iya sake dagula mata rayuwa.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.