Free chapter · Read without an account
KUSKURE 14
*KUSKURE* 🙆🏼♀_🤱🏼
BY maman shaheed
shafi na shahuɗu
Haka zama yaci gaba da gudana tsakanin momyn su Noor d Indo , aikin ta dai Yana Nan kamar yadda yake na hidiman gidan ta hak'ura tabar maganar badan Tana so ba .
Su twins Kuma Nawal Tana Nan ta hak'esu aranta ,wato d t hanasu siyama Indo Kaya saida suka siya Mata ,har d dinka Mata harda Mata kwaliya Dan kuturun wulakanci suna had'a level d'in ta da Mai Aikin ta ,zata had'u dasu ne zata yanka musu warning Mai yaji Kuwa.
Indon ma badan tasan in ta rasa ta ,zata Jima kafin ta Sami kamarta ba ai d ta k'ara Mata wuta .
Ango d Amarya anacan anata gurzar amarci ,Yaya Ahmad suna waya d k'anin shi SAFWAN yanata cewa yaushe zasu Zo ,shiko safwan kunya yakeji Yana cewa" zamu Zo ne yaya kar ka damu"
Har ya sanar da shi "su twins fa sunzo har su huzna"
,safwan yace" dama Wa'yan Nan ai 'yan tamore ne 'yan sai gara takare zamu rabu kenan" ,suka dinga dariya , har suka gama wayar.
Su huzna Ana gari ,anata faman zirga zirga Ana zazu a cikin garin, ta rasa yadda zata ɓuloma Safwan.
, har takardun NAWAL sun fito na kammala karatun ta ,ta dukufa neman Aiki haik'an dama can Tana nema .
Yau Bata Nan ,gobe Bata can , shima safwan yanzu y zage Yana neman Mata aikin a wajen d hankalin shi zai kwanta , Dan da aikin ne bayaso yasa ya k'i dagewa ya Nemo Mata aikin , Amman gani tak'i Nutsuwa yasa y fara nema Mata shima a inda ya dace dan su sami dedeto ko zata nutsu.
Cikin ikon Allah ta Sami , Aiki a wani private hospital ,tayi murna kuwa , safwan nema y samo Mata ba lefi hankalin sa ya d'an kwanta d hospital d'in ,saidai yanayin aikin kamar tafiso a government hospital kawai dai ta Raina sallary d za 'a Bata, kuma da yawa.
Bayan wani lokaci ta Fara fita Aiki ,hidiman gidan y sake samun matsuguni da kyau a hannun Indo ,hatta breakfast d hidiman safwan Indo Ce Mai Yi ,saidai in ya shirya da wuri sai su fita tare dashi Dan ita Tana rigashi fita MA wani lokaci.
Huzna kuwa ta Sami Kiran gagawa daga gdn su haka ta tatara ta koma batare da ta gama cika burin ta ba ,amman ta k'udiri aniyar dawowa Nan Kusa da niyar ayi mai yiwuwa tsakanin ta da Safwan.
Su Noor ko dama sun Kara zama yaran Indo , tun tashin su d safe ita take zama dasu har sai momyn su ta dawo ko ta dawo ma Indo Ce koman su, sun sake mugun sabawa da ita.
Indo hak'uri kawai takeyi ,Dan ma Inna na rarashin ta ,sanan hadiya ma n Bata hak'uri Kan ta cigaba da hak'uri wata Rana sai labari har ta samu ta cika burikan ta guda biyu.
************
*WACE CE INDO*❓
"Aishatu wacce aka fi sani da Indo 'ya ce ga Hafiz mamman ,ita kad'ai Allah yaba su shida matar shi Umaima
K'auna ce mai tsafta da inganci tsakanin sa da umaima , suna nunama junan su kulawa sosai Hafiz beyi nisa a karatun shi n Boko ba daga sakandiri be Kara ko Ina ba shima d kyar y samu y Kamala ,saka makon tasowa da yayi a hannun kishiya maman shi, Amman ya Sami na addini har matakin sauke Al'Qur'ani da wasu litattafan, ya azabtu a wajen ta iya azabtuwa gashi baban shi bashi d kata bus sai Abin da tace Mai, dan ba haka ta barshi ba.
A haka da Dadi ba Dadi har ya samu y auri umaima har Allah y azurtasu da samun Aishatu , mahaifin sa na son sa Amman baya nunawa agaban kishiyar uwar sa saidai abayan idon ta ..
Haka rayuwa Tayi ta tafiyar musu a tsanani dama b wata sana'ace dashi ba jiran shago na provision yake, gashi ba wani sallamar kirki ake Mai ba ,hakuri kawai yakeyi Dan ma aihuwa t tsaya musu tun haihuwar Aishatu ...
bame temaka Masa a garin ,Inna mahaifiyar umaima itace kawai take temakon su dama Tana saida kayan ƙule ƙule irin na Mata acikin gida .
Shekarar Aishatu biyar aduniya ,umaima ko Bari Bata sakeyi ba ,
A cikin shekarar ne , Allah y Aiko ma da umaima jinya wacce aka rasa kanta ,Dan daga baya ma tun Ana zuwa asibiti har hakura akayi aka dawo da ita gidan Inna ta Dan jinya ,hankalin Hafiz mamman in yayi dubu ya tashi , magani yakeyi daidai karfin sa Amman Ina Saida cutar Nan takai umaima kushewar ta Allah y karbi Rayuwar ta .
tashin hankali da kid'ima d shiga rud'u Inna da Hafiz mamman sun shiga Dan su akama mutuwa , yaci kuka kamar ransa ze fita .
Inama taci kuka kamar me Dan itama ita kad'ai Allah y Bata sai Aishatu da Allah y Bata a matsayin jika ..
Ana cikin wanan tashin hankalin Bayan sati biyu da rasuwar umaima ,barayi Wanda ake tunanin turo su akayi suka fasa shagon da Hafiz yake jira sukayi sata .
Da gari ya waye kuwa gari ya d'auka ,wai talauci yasa Hafiz ya fasa shagon Dan Maliki ya kwashe Mai kaya , wasu d dama sun San k'age akemai wasu ko sun yadda ..
Da safe Dan Maliki yazo y dinga surfama Hafiz masifa wai ko y fitomai da kayan shagon sa ko yayi prison ,Kuma ansan shi fagen rashin MUTUNCI tas zai aikata ..
Ganin y tafi ,yasa Hafiz yaje gdn Inna yanata Bata hak'uri Kan ta rike Aisha ya barmata har abada shi tashi t kare baida kudin biyan kayan ,Kuma duk garin Bamai biya Mai kud'in ,ko yayi zaman gidan yarin ko ya gudu ya bar garin ,acikin biyu dai za'ayi d'aya .....cikin kuka suka rabu shida Inna d 'yar shi tilo Aishatu, duk yadda inna taso hana shi ko shiga maganar yaƙi amincewa sai da yabar gari ya sami nutsuwa.
Ana haka ,mahaifin hafiz hawan jinin shi y tashi sakamakon sharin da akama d'ansa Hafiz ,Aiko tuni shima Rai yayi halin sa ,sanadin sharin.
Hafiz Yama rasa yadda zeyi Banda kuka ba Abin da yakeyi ..
Anata zaman makoki , ranar sadakan uku Dan Maliki ya kwaso tawagar 'yan sanda har su 5 anzo tafiya da Hafiz .
Aiko abokin Hafiz nuhu ya Zo y Gaya Mai a kunne batare d kowa yaji ko ya gani ba ..
Atake aka nemi Hafiz aka rasa ya gudu guduwar da shima besan inda zashi ba gudun ceton Rai .
Ko da sukazo ,haka aka dinga neman shi babu shi babu lbr Hafiz ,har gdn Inna sukaje suka d'aga Mata hankali ta dinga kuka ,manyan garine suka ba Dan Maliki hakuri da kyar y hakura Amman yace idon shi idon Hafiz wlh sai ya ziyarci gdn maza (prison)
Haka Inna tashiga tashin hankali ,itako Aishatu nada shekara 5 Bata ma San rayuwa ba, Amman ta San baban ta Dan ko lokacin d mahaifiyar ta ta rasu taci kuka Amman daga baya ta ma manta tun Tana tambayar ina take har t daina ..
Yanzuma haka kulin cikin tmby Inna Ina baban ta yake ,Inna na cemata yayi tafia ,haka dai kulin sukeyi har ta Fara mantawa d shi ..
Wasa_wasa har shekaru suka shud'e ba Hafiz mamman ba lbr sa har Aishatu t Dena tambayar Inna shi,Dan Maliki ya baza mutanen na neman Hafiz a duk inda aka ganshi Dan be hak'ura ba ..
Ayanzu b Wanda indo ta sani sama da Inna , Bayan wasu shekaru ma akazo aka sanar ma d Inna wai anganshi mota ta kad'e shi , taci kukan ta ta k'oshi tabisu da addu'a har umaima da mahaifin Hafiz din mamman Dan mutumin kwarai ne se mata da Allah ya jarabe shi d ita ba ta kirki ,yanzu ko ai tafara Raina kanta .
Bayan wasu shekaru Aisha nata girma inda Inna take kiran da indo a tsokane shine Indo y bita daga wasa .
Inna tayi ƙoƙari wajen temakama Indo wajen karatun ta adadafe ta gama makarantar firamari,tanayi Tana had'awa da islamiya da makarantar dare har ta wuce karamar sakandiri inda tayi aji uku da kyar a makarantar gwamnati ...
Daga hakane Bata ci gaba ba ga Inna karfi na karewa shine fa , akazo akace ta bada Indo tayi aikatau lokacin indon na tausayama Inna ganin yadda take hidima da ita shine taci buri biyu a Rayuwar ta ..
Na farko taci burin neman nakanta Dan ta taimaki kanta ta taimaki Inna ta .
Na biyu sai tayi karatu insha Allah arayuwar ta na Arabic d boko dan ta zama wani abu.
Wanan sune burikan Indo,arayuwar t ayanzu.
Ba lefi Indo tayi karatun addini ta ,tare take hadawa d bokon ta har t gama.
Wanan shine labarin Aisha Indo.
Har ta Fara Aiki a gidan su NAWAL ta hanyar wata mak'ociyar su Inna .