Free chapter · Read without an account
CHAPTER 13 ( Becoming Mrs BAY
by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
CHAPTER 13 ( Becoming Mrs BAY)
Shirye-shirye aka cigaba kamar ma ba a yi wata magana ba ko da yake ba wanda ya ji ko ya gani balle maganar ta isa ga masu shirin, a hankali har aka shiga satin biki. A lokacin ba k'aramin had'uwa amare sukayi ba ko makaho ya shiga inda suke ya san akwai amaren gata a wurin balle masu idanu da ba wanda yake iya ganinsu bai tanka ba, su Aunty Fadwaah kam har da cewa an nuna musu wariya ai ba irin haka akai musu da biki ba ita dai Hajjah sai dariya tayi ta musu bata ko tanka ba don ta san tayi musu gyaran da ya kamata kawai hange ne yake damun su Najmahn ba komai ba.
Monday
A yau aka fara gabatar da event na biki inda aka fara da bridal shower isu-isu y'an matan da friends d'insu sun ci kyau ainun amma basu yi makeup ba sun ci sunsha sun kuma yi raha a tsakaninsu da friends akayi video aka watse.
Tuesday kuma family hangout/get-together aka yi a Yerwa Gardens. inda kowa ya ajiye aikin gabanshi suka had'u aka yi raha da nishad'i k'aida ne duk biki sai anyi irin wannan had'uwar ba kakanni ba jikoki babu tattab'a kunne kowa sai yazo picnic d'in ba biki kad'ai ba every year sukan yi irin zaman musamman in ba su da shaani. Zama akayi na yini d'aya akayi lunch da dinner tare sai ten suka koma gida, irin zaman ba k'aramin bond yake k'arawa a tsakanin juna ba ko zaman shiru akayi yana sa sabo balle anyi fira an dara sun yi sallahr Zuhr, Asr, Magrib da ishai tare. Anci abinci a circles dukan su an tsokani juna ta hanyar wannan ya d'auke naman gaban wancan wancan ya kwashe abincin wancan abun dai sai san barka babu abinda ya kai zumunci dad'i shiyasa duk da cewa they are quite diverse amma kuma kan su a had'e yake akwai kuma shak'uwa da respect mai yawa tsakanin juna.
Wednesday da safe akayi gyaran kai da jiki wa ƴan matan amarya a Yerwa's touch, inda aka gyara kan kowa for free harda amaren da kayan gyara masu tsada sannan suka dawo gida.
4;pm akayi friendly match a Yerwa Court inda aka yi k'wallo tsakanin team Brides da aka bawa sunan Team(SNZ) wato first alphabet na sunan su. Against team grooms Team( BSF) suma haka. Seven aside akayi Mazan family suka shigan ma amare su kuma friends suka shigar ma grooms. Brides maids suna ta cheering Team SNZ inda suka cinye Team BSF 5-3 aka basu kofi aka watse.
Thursday akayi sa lalle wato Nalle inda duka aka taru a gidan Hajjah, Mommy ce ta kawo kayan lallen dukansu. Nan aka shafawa amaren kamar yadda al'ada ta tanadar. Taron yayi armashi sosai saboda isu-isu ne y'anuwa ga amare sun sha kyau cikin atamfarsu mai matuk'ar tsada sai k'amshi yake tashi ta kowani sashe yadda kasan anyi b'arin turare.
Amaren an sanya sun tuk'a tuwon biski aka sanya man shanu, kowa dake wurin sai da yaci aka sha kunun gyad'a mai kyau da gard'i sai sauran kayan alada dai.
Washe gari friday aka yi wushe-wushe inda zamu iya fassara shi da kamu a hausance but su suna fassara shi da " barka" ( barkanku da samun juna a matsayin ma'aurata, barkanku da barin gwauranci da kuma sanya albarka ga maauratan da fatan Allah ya sa mutuwa ce zata raba tsakani). A nan Yerwa hall suka yi amma a outdoor d'in inda akayi decorating d'inshi sosai.
A ranar kam amare sun yi kyau cikin kyakkyawan Gambarar su inda shahararriyar makeup artist da suka d'auko ta tsantsara musu kwalliya, dama ga jiki ya samu gyara komai ya fito.
Gambarar da suka sanya mai fari da adon red, buba ce doguwa har idon sawu sai zani shi kuma navy blue shima akwai adon ja akai basu d'aura d'ankwali ba sai mandil da suka nad'a akai sai lafaya da aka d'aura musu shi ma ja ne dukan su iri d'aya suka sa bambancin flowers ne kawai, a wuya kunne hanci da hannuwa adon zinarai sukayi sai beads ja da suka sanya ta al'ada. A kujerar alfarma aka sanya su gefen angwayen da suka sha wagambari dakakka sak'ar Dakar bugun Yerwa blue mai bak'i an musu babbar riga da wando.
A saman 'yar ciki suka sanya k'aramar himar ja mai adon golden sai hula Dara mai tsada da takalmansu covered shoe. Ta a gefe take ta kallonshi tunda suka rabu ranar da su Baba Tijjani suka zaunar dasu sai yau suka had'u, yayi mugun mata kyau a idanunta ainun. Takalminshi na Berluti Alessandro Demessure studded leather sun mugun hawa da kayan da ya sanya haka wristwatch d'in shi na Graff ya samu waje a golden skin d'in shi ya zauna daram.
Lumshe idanu tayi tana murmushi jin shi kusa da ita kad'ai yana saukar mata da natsuwa, balle kuma turarenshi na boadecia the victorious da Roja dove Auod yau kuma ya had'a da Yves saint Laurent black opium da ya sake taimakawa wurin ruguza duk wani kuzarinta ya kuma had'e da khumran da tayi using da turaren Amarige na givenchy ya had'u yana bada wani soft ƙamshi mai tsayawa a zuciya.
Tsaki yayi yana mai jin haushin kallon da take masa, in bata sani ba zamansu waje d'aya takura ne gareshi ga shi tana k'ara ma takurarshi girma da munafikin murmushinta. Ta d'ayan gefen kuma ganin Suleim da babu abinda ya rage a soyayyarta sai ma dad'uwa da yake yi with each passing day, ganinta a wurin kuma ya sake taso mikin da ya kwanta kamar wasa macen da yake so fiye da komai zata auri wanin shi. Miyan takaici ya sake had'iyewa yana kallon jama'ar wajen da suma sukai shiga cikin kamfala da mandil sai masu lafaya suma dake rausaya ga sautin ganga kura da ake kad'awa cikeda nishad'i.
Suma sauran angwayen sunyi kyau abinsu musamman da ya kasance su sai murmushi sukeyi wa amarensu har d'a rad'a-rad'a wanda bai wuce yanda sukayi missing d'insu suke gaya musu ba da abinda ba a rasa ba. Kallo d'aya zakai musu ka san suna matuk'ar son juna, kuma sun dace da juna ainun.
Abincin gargajiya aka gabatar su Sinasir da margi special da taji kifi, Biski da miyar yauk'i, tea Alkhindir da kunun gyad'ar da sauransu. Anci an sha anyi b'arin kud'i musamman sanda angwayen suka shiga fili duk yanda Burhaan yak'i sai da yayi rawa ga sautin gangaa kuraa kuma sai da sukayi kusan dance steps guda biyar tundaga na fifita, sa hula, juyi da sauransu. Abun yayi armashi sosai yanda kasan a can Yerwan ake bikin aka bar 'yan Morocco da hotuna don an tashi kan su, photographers sai aikinsu sukeyi sai Magrib aka tashi kowa ya wuce gidanshi inda su ElSadeeq sai da suka maida amaren gidan Hajjah shi ko Burhaan ana fitowa dama yayi wucewarshi bata damu ba tabi su twins suka sauketa.
After ishai akayi Arabian night still a cikin halls d'in nan kuma filin y'an morocco ne sosai suka nuna tasu aladun, suma anci traditional foods d'insu a wurin and as usual tea. Amare kayan amaren can s
suka sanya da crown na golds ga k'amshi yana tashi. Traditional dancers da suka zo dasu suma sun yi rawar bajinta, shi ma an yi b'arin kud'i. Islaam da dan dole yazo yana ta yatsina amma ba wanda ya kula shi haka sukayi layin gaisuwa ga dattijan wurin duk inda suka je sai an musu lik'i an kuma sa musu albarka, sai da suka zagaye kaf kafin suka koma wajen zaman su 10 aka tashi kowa ya watse.
Saturday wato ( Nyiya) ranar d'aurin aure aka maida amaren gidan Ya Madari inda akai wankin kai, Ammi matar Baba Tijjani itace ta wanke wa amare kai a babban Bath kowa da nashi, YaMara ita ta fanshi wankin da turamen zani da kud'i mai kauri harda zinarai aka bawa Ya Madarin. Su kuma friends d'in amarya suka d'auki baths d'in kowa ta fita da ruwan zuwa wurin angwaye da abokansu kowa ya biya kud'in fansa kafin aka zubar, daga haka amare suka shirya cikin bridal gowns d'insu farare suka had'a da costumes na gold ( kun san mutanen da zinare). Suka d'aura alkyabba a kai aka maidasu gidan Hajjah.
Yerwa central mosque.
11am dubban alumma suka shaida d'aurin auren Muhammad Burhaan Abdallah Yerwa da Nadeefah Yusuf Yerwa, Abubakar Sadeeq Yusuf Yerwa da Ummu Suleim Aliyu Yerwa sai kuma Muhammad Farhaan Yerwa da Zulfahat Adam Yerwa akan sisin gold 100-100. Auren da ya tara manyan y'an kasuwa, sarakuna, maaikata, y'an siyasa da ma Academia na Nigeria bakid'aya kai ba ma Nigeria zallah ba har ma Africa da duniya musamman masu sauratar daular labarawar Africa kasancewar Ummu y'ar gidan sarautar Morocco ce. Bikin gidan Yerwa bikine da yake amsa suna a k'asar nan kasancewar babu wata field da babu su kuma Aji Garwa Zannah Yerwa da 'yan uwanshi sun bada gudunmawa sosai a k'asar kuma har yanzu y'ay'ansu basu fasa ba amma wannan karon bikin ya tara mutane sosai Kaduna ta cika ta batse sai fatan alkhairi sukeyi.
Ana gama d'aurin auren aka had'u a Yerwa hall inda aka gabatar da lafiyayyar luncheon ga manyan bak'i sai kusan laasar aka watse.
A can gidan Hajjah kuma 2pm akayi kususurum inda sai lokacin aka kawo lefen amare, kowacce nata Masha Allah tun ana counting har aka b'ace da irga kuma kun san bikin gidan Yerwa ai akwai aji balle na masu ji da zamani da gayu. Lefen ya'kunshi akwatunan amare kowacce set biyar masu 6 each, akwatin maman amarya (su Mommy, Ummu da kuma Ummi suma su Mommy haka suka bayan na Suleim), akwatin 'kannen maman amarya(innaso), akwatin 'yan uwan baban amarya (bawaso), sai sisters (su cousins) sai na 'kawayen iyayen amare su Mommy, Ummi da Ummu (ya samma soye) sai na matan waliyinsa (Matar Baba Tijjani), sai matan kawunnanta (kamu rawaye). sai na 'yan bayarwa (na rabo) sune a jakankuna, sai na wadda tayi mata wankin kai (Ya Madari) an bata atampopi da kudi ban da wacce YaMara ta bayar. Aka ce wani kaya sai amale kuma in baka yi bani wuri wato alaji ana biki a k'asar nan har gobe kuma kanuri suna yin wainnan kayan al'adar amma kuma dai-dai ruwa dai-dai tsaki kowa yana yin iya k'arfinshi ne in an kai akwatina a wasu gidan gidaje da yawa sai dai akai guda d'aya a ciccire kowa ya samu.
Kaya suka chanja zuwa Almond milk, angwaye suka shigo aka din ga hotuna da y'anuwa da abokan arziki suma su Baba daga wurin walima suka dawo gidan aka d'ad'd'auka da su.
Da yamma 5 aka fara shirin kai amare gidajensu ( Lorusa) wanka akayi musu aka shirya su cikin lafaya masu taushi da tsada yanzu ma farare suka sa, aka kaisu gidan Baba tijjani inda a nan akayi zaman musu nasiha. A tsakiyar iyaye aka ajiye su. Daga nan kuma aka bar su sukayi sallama kowa da iyayenta. Lele haka ta k'ank'ame Ummu jikinta yayi mugun yin sanyi har ji take kamar kar su rabu.
Ummu ko albarka ta dinga sanya mata don duk wani sallama sun yi shi tunda a satin bikin duka a gidan su tayi shi, not only her dukansu ma 1 week to biki kowa ya koma gidansu sai dai kullum suje gidan Hajjah.
Daga haka Baba prof ya rik'e hannun Zulfaa zuwa mota kasancewar shi zai kai ta, Suleim kuma Baba Adam while Lele Baba Tijjani da kanshi ya sata a mota ita dashi zuwa gidajensu dake Yerwa New Extension inda a nan yaran familyn suke da zama, har parlour ya shigar da ita sannan sauran mutane suka shigo daga baya kowa da nashi, fad'in tsari da had'uwar gidan b'ata baki ne ku dai yi imagining yanda gidan y'ay'an gata yake toh ya zarce nan.
A nan living room ya zaunar da ita ya sake mata nasiha kafin yayi gaba inda ya bar mutane suna ta touring gidan.
Ta jikin carved wood d'in ne akayi ƙofofi biyu masu kallon juna amma da tazara sosai k'ofar dama a nan parlorn Burhaan yake babban parlorn na su komai na ciki ash ne da black. Kama daga curtains da furniture sai TV a ɗayan side ɗin akwai dining a parlorn da wata k'ofa da zai kai ka harshe sai ɗakuna biyu d'aya master bedroom sai mini home office.
Bedroom d'in shi kuma komai White ne ( da alamu masu gidan suna son white) Kama daga Round bed d'in har zuwa kan zanin gado da kuma sofa k'walli d'aya a room d'in sai closet d'in shi shima da ke gefe gabad'aya room d'in a zagaye yake da labule wanda ya ƙara masa kyau da ƙawa.
Part d'inta kuma komai na parlorn light blue/ sky blue da gold ne wasu Italian cushions ne masu matuk'ar kyau da tsada, 3 bedrooms ne a ciki kowanne da kalar tsarin shi da haɗuwar shi sai art room d'in ta daga gefe. Itama akwai dining a parlorn nata sai TV set komai dai tsaf.
Ɗakin farko ta shiga ciki komai emerald green da gold aka shimfid'a zanin gado gold masu taushi d'akin yayi kyau sosai, zama tayi a kan gado tana kallon d'akin. Sai da sukayi ishai mutane suka rage aka barta da friends da zasu tayata kwana, suna ta shakiyancinsu ita dai ko uffan bata ce ba sai murmushi kawai takeyi.
A time d'in ta samu damar kiransu Zulfaa da Suleim sun dad'e suna hira da Suleim sai around 10 suka rabu, ta kira Ummu tayi mata shagwab'a kamar ba da Magrib suka rabu ba. Sanda ta gama wayar har y'anmatan sun fara bacci, ita kam tsallake su tayi ta shiga toilet wanka ta sallo da alwala doguwar riga ta sanya cikin kayan da ta d'auko da hijabi ta hau kan dadduma. Nafilu ta dinga jerowa a kowacce addua tana mai doguwar addua akan Allah ya daidaita zamantakewarsu ya kawo alkhairi madauwami a tsakaninsu ko da ta idar ma adduar da tai-tayi kenan har sai da taji idanunta na zafi around 3 kafin ta kwanta.
Washegari after subh baccinta ta sake komawa ba ita ta tashi ba sai 11 wanka tayi ta zura riga da skirt na lace sea green ta fito parlor bayan ta kintsa room d'in ta yi shara da injin shara tana fita aka din ga mata tsiya ita dai ba baki sai wayarta ta d'auko a time d'in ne ta kunna data nan taga yanda pics d'in bikinsu yayi yawo a social media tundaga IG, twitter da tiktok captions kala-kala kake gani daga wannan blog d'in zuwa wannan kowa dai yana ta tofa albarkacin bakinsa, kusan jama'a da yawa sun yaba da had'in nasu musamman masoya auren zumunci murmushi kawai tayi ta kashe datar.
4pm gidan ya fara cika saboda wuskuru wato walima inda kowa da yazo bikin zai taru gidan amarya da ango aci abinci sannan ayi bud'an kai, su da yake su uku ne sai aka rarrabu hatta iyayen ma kowa da inda yaje. Taron yayi armashi kuma as usual anyi b'arin kud'i ga kyaututtuka da aka ba wa ma'auratan.
Tayi kyau cikin shigar atamfa aura da akayi wa d'inkin riga da skirt sai lafaya black da ya hau da atamfar, shi ko Burhaan all white ya sanya Riga da wando ba babbar riga da yake rigar har k'asa ta kai masa ( Bornu style) kallonshi ta din ga yi shi ko ko gefen da take bai kalla ba. Magrib kowa ya watse aka bar amarya, ango da iyaye nan fa sukayi sallah tare after Magrib suka tasa su gaba da nasiha mai had'e da fad'a akan kar suji ko suga abinda ba shikenan ba. Musamman ma Burhaan tunda ance shi ne mai matsalar Abba wanke shi yayi tas har da cewa idan yayi mata wani abu ta kirashi, ita dai tace toh amma ai ko giyar wake ta sha ba zata tab'a kai k'arar shi ba.
Shima Burhaan dake duk'e gabansu kai kawai yake gyad'awa amma hakan ba shi ke nuna yana jin abinda ake fad'i ba aballe ayi tunanin zamansu.
Baba Adam ne ya rufe taron da addua ya rik'e hannayensu guri d'aya yace " Allah ya albarkci rayuwarku tare, yardarsa ta game koina na cikin gidanku, ya baku yara masu biyayya gareku kamar yacce kukai mana,,,,,,,wa'tasimu bi hablin minallahi wala tafarraqu, wala tafarraqu, wala tafarraqu". Ita dai ta amsa har cikin ranta shi ko Burhaan ya amsa a fatar baki amma zuciyar mutum,,,,,birninsa. Sai bayan ishai aka tafi aka barsu, tashi yayi zai musu rakiya Daddy yace " koma abinka mun hutasshe ka" ai ko komawar yayi ya zauna cikeda takaicin bud'e mai aiki da sukayi a gabanta, tsaki yayi ya ciro wayarshi yana aikin latsawa kamar ya manta da kasancewar wata Nadeefah a wajen.
Sai da ya mula ya mulmule kafin yayi gyaran murya doguwa, a tsorace ta d'ago tana kallonshi. Shi ma zuba mata idanu yayi idan yace bata yi masa kyau ba toh yayi k'arya kuma ya san ko aina ya nunata as wife bai da kaico kawai abu d'aya ne cikas bai sonta, bai tab'a sonta ba kuma itace ta zama shamaki ga samun muradin ranshi a take ya saki wata zazzafar tsaki yana cewa " ai sai dai ki kalla mayya, amma ba zaki taɓa samu na ba".
"Ouch my bad Nadeefah Yerwa na san kina nan kina godiya ga Allah akan kin zama matata ko? Well, congratulations oand you're welcome zuwa ga nadamar rayuwar ki bake kika ce ni zaki aura ba? Hum toh gani nan kin aura amma ki sani sai kin gwammaci zama a gidan yari da zaman gidana!!"
"Ina ce burinki kenan zama matata toh gashi nan ya cika amma ina son inyi warning d'inki a kai na dukda na lura baki san warning ba kin fi son ki gani a zahiri well zan miki kashedin so that in wani abun ya faru ba zaki ce ban gaya miki ba".
Miyau ta had'iye tana kallon yadda yake motsa bakin shi cikeda masifa, harara ya jefa mata da sauri ta maida idanuwanta ta rintse tana mai jin sabon tsoro amma sai ta dake tana mai cewa " la takhaf innallaha ma'a naaaa".
"First of all a suna ne kike matata don haka banson ji ko ganin kin alak'anta kanki dani but hakan ba shi ke nufi zaki dinga yin abubuwa sakaka kina muamala da maza yanda kika saba ba, zaki yi mamaki na in kika kuskura secondly ban son ganin tarkacen k'awayenki a gidana duk randa na ga k'afar wata shegiya sai na b'alla shi, kar ki sake ki shiga part d'ina ko a mafarki kika ga kin shiga in kika farka kiyi sadaka don mummunan k'addara ce take biye dake".
Dakatawa yayi yana mai ajiyar numfashi sai da ya natsa kafin ya d'aura da fad'in " ba wata y'ar aiki da za a kawo miki gidan nan I can see an ajiye miki injinan aiki saboda an san lalacinki well ba damuwata bane tunda ke zaki rayu cikin gidan naki ba wata ba, kar ki sake ki yi girkin ki da ni don bana cin jagwalgwalo na san banda fentin fuska baki iya komai ba, ki koma bakin business d'inki but ba zan d'auki shigar banzar da kika iya ba and lastly I'll repeat babu ruwanki da ni da harkata!!!".
Daga haka ya tashi ya wuce part d'in shi tana zaune kamar ruwa ya cinyeta, buga k'ofarshi ya dawo da ita hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke bata zata ma zai yi sauk'i haka ba, murmushi ta sake cikin son k'arfafawa kanta gwuiwa ta mik'e ta shige part d'inta.
Bata shiga room d'in jiya ba na tsakiyar ta shiga, tsayawa tayi tana kallon ɗakin don komai ya haɗu ya kuma ƙawatu kana gani ka san d'akin mace ce y'ar gayu y'ar zamani " well this is my room" ta furta tana hawa gadon ta rungumi teddyn dake kai, tuni ta nemi damuwar da maganganunsa suka sanyata ta rasa wanka tayi ta sa nighties tana rungume teddy d'inta tana ta tunanin dubarun da aka koya mata da kuma perfect time da ya kamata ta fara acting...... Wahalurrrr!.
Shiko yana shiga ciki a kan gado ya kwanta yana mai kallon room d'in, yanzu fa da wacce yake so ya aura da yanzu yana tareda ita suna raya soyayya ko. A take ya fara tunanin maybe yanzu tana can rungume da ElSadeeq, tunanin kawai ya sanya mai jin zafi a ran shi tareda mugun kishin Sadeeq d'in sai kawai ga hawaye suna zubo masa kamar ba Burhaan ba yau dai ya bawa zuciyarshi damar sakin abinda takeso ko ya samu salama. Before you know it kukanshi ya canja tsari daga hawaye zuwa shesshek'a, yana yi yana sumbatu da zantukan bege akan Suleim ko baka da tausayi kaga yanda yake kukan sai ka tausaya masa don shi ba gwanin kuka bane ya iya shanye abu sosai abu d'aya ne ya kasa shanye shi wato tsanar Nadeefah but har son Suleim ba wanda ya sani sai Adnan.
A daren ranar yayi kuka har sai da kan shi ya fara ciwo kafin ya tashi yaje yayi wanka ya d'auro alwala, nafilfili ya jero tareda adduar Allah ya yaye masa mugun son Suleim a ranshi ko ya samu sukuni. Ya dad'e kafin ya idar a kan daddumar ya kwanta yana kissima yanda zai ci uban Nadeefah ko dan katsalandan da ta mai kadhedin da yayi mata a baya ba wai yana nufin wai haka zai k'yaleta yana da plans da zai ci ubanta la'ada ciki ba waje ba murmushin mugunta ya saki yana mai cewa " welcome to the hell baby......."
Burhaan oooo you guy no wan peace at all 😂
Deejasmah