Free chapter · Read without an account

CHAPTER 14 (DAY ONE......)

by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 14 ( Day one)

Baccin da bai yi da wuri ba ya sanya shi makara sosai, don bai iya tashi ba sai after 6. Time d'in gari yayi haske tarwai a d'aki yayi, yana idarwa da k'yar ya iya azkar ya koma ya kwanta yana mai dafe kanshi da har yanzu bai daina ciwo ba.

Baccinsa ya sake komawa sab'anin dare yanzu kam bacci mai dad'i yayi, kuma da d'an natsuwa. Kiran da ya shigo wayarshi ce ta sanya shi bud'e idanu cikeda kasala, hannu ya kai ya janyo wayar tsaki ya sanya ganin videocall ne.

Picking yayi ya zura musu idanu ba tareda yace uffan ba, Farhaan ne ya kwashe da wata muguwar dariya yana cewa " da alamu guy d'in nan k'aramin kai ne dashi, jibi yanda yayi wani laushi". Sadeeq ya kwashe da dariyar shima yana mai cewa " kamar ba sir BAY the great ba".

"Maza sun faɗi!!'' Cewar Farhaan.

Dak'uwa yayi musu yana cewa " ku dai an yi lalatattu, gwara da akayi muku aure da wuri gudun yin abun kunya".

Farhaan da ya ajiye wayar a gabanshi ne ya fara tafa hannaye har da rik'e hab'a wurin cewa " ai kaine shugaban lalatattu, wa yayi maganar wani abu yanzu har ka fassara mutane? kace ba k'aramin rigakafi akayi ba da yanzu ka bi kwalta".

" Banzan yaro" ya furta yana gyara zama.  "Wai Islaam me kakeyi ne har yanzu a kan gado.....?". Hararar shi yayi kana yace " abinda aka min auren domin shi..." Ya k'arashe har da masa gwalo, ai ba Farhaan ba har Sadeeq sai da suka sanya salati don ya musu bazata shi kam ko a jikinshi doguwar mik'a ma ya sanya yana cewa " wannan fa shiga hak'k'i ne, ya kamata ku san time d'in kiran mijin aure".


Yanzu kam Sadeeq ne yace " Burhaan kar ka manta fa I'm your in-law". Ware idanu yayi cike da shak'iyanci yace " kai ma ai in-lawn Farhaan ne amma a gabanshi kake min zancen banza ". Harararshi Farhaan d'in yayi yana cewa " har ya wuce wanda kake yi? Toh ka dai bi Lelen Hajjah a hankali don wallahi kayi rawan kai zata gyara maka zama ne ahh toh ".

"Ai matata ce ba na wani ba and ba wanda ya isa ya min doka da gidana ehh he". Ya furta har da murgud'a baki, mik'a ya sake yana tashi daga gadon slippers masu taushi dake zube a gaban gadon na Nike farare tas ya zura yana nufar parlorn ba tareda ya sa riga ba.


Main parlor ya shiga da wayar yana mai basu amsa, fuskar a d'an sake. Turus ya tsaya da maganar da yakeyi " ku dai kun shiga uku fallasa sirrin gidan aurenku a duniya......". Sakamakon kyakkyawan ganin da yayi da Nadeefah sanye cikin d'anyen Voile anyi mata surfani mai stoneworks a hannu da wuya, rigar ba fitted bace but straight ce ba shape ba komai amma yayi mugun yi mata kyau ga mugun k'amshin turarenta ga na wanda take sawa a burners a kusurwan parlorn mai sanya natsuwa a zuciyar mai shak'arshi banda humidifiern da ta kame d'akin gwanin sanyi.


Mantawa da yana kan waya yayi yabita da idanu, in yace ba tayi kyau ba yayi k'atuwar k'arya amma yana ganinta sai ya ganta a Suleim ba Lele ba sai da ya zura ido ne ya dawo kan saiti. Tsaki ya ja yana zama a kan couch, a firgice ta waigo don bata san da fitowasrsa ba sai tsaki taji. Ganinshi da tayi ba riga sai shorts sake firgitata yayi, ai ko da sauri ta maida kanta inda yake amma jikinta yana shirin ba da ita saboda muggan jarababbun idanun shi da ya zuba mata su cikin wani k'ask'antaccen kallo yana ciccije baki.


Farhan ne yace " da alamu wani yana buk'atar privacy, go ahead zaka iya tafiya an ɗaga maka ƙafa" lumshe idanu yayi yana mai cewa " ai ba sai an ce min ba, kuma dai ku tafi wurin matayenku ba ku tsaya k'ananun iskanci ba". Daga haka ya katse yana mai jin yanayin jiya na dawo masa, runtse idanu yayi ya na kwantar da kanshi a jikin couch d'in da yake zaune.

"Nda watu" ta furta a d'an tsorace bayan ta ajiye turaren hannunta, a harzuk'e ya taso yana kallonta. Sai kuma ya yafito ta kamar abun arziki, tahowa tayi cikin sanyin jiki. A kujerar gefenshi ta zauna kan ta a k'asa, shi ko har time d'in idonshi na kanta.

K'wafa yayi yana cewa " you!! Ban ce kar ki min magana ba? Ehhh?". Kasa magana tayi sai kawai ta girgiza kan ta, ya cigaba da cewa " ohh saboda kin raina ni shi ne kika yi ko? I've told you ba ruwanki dani ki yi rayuwar ki tunda haka kika zaɓarwa kan ki, kamar kina zaman kanki ba kowa cikin gidan nan sai ke shi ne kwanciyar hankalin ki".

"I'm sorry Yaa Islaam" ta furta hawaye yana taruwa a idanunta, tsaki yaja yana cewa " ba ki ga sorry ba ai tukuna yarinya zaki gani. Ki sake zuwa inda nake you'll see, za ki bar nan wurin ko sai na tattaka ki mayya!!!". A guje ta ruga izuwa room d'in ta a parlor ta kwanta kan rug ta sa kuka, duk yadda ta so daure maganganunshi ta kasa yanzu kam ta yards da cewa ba k'aramin aiki ba ne a gabanta a ce mijinka bai son ko ganinka? Ya rabb!!.


Kukanta tayi ma'ishi ta godewa Allah, ita da kanta ta bawa kanta hak'uri ta share hawayenta. Kana ta lallab'a zuwa bedroom d'inta ta kwanta, tana mai jin nauyi a zuciyarta a haka wani wahalallen bacci ya d'auketa.


A parlorn tana wucewa shi ma ya tashi, part d'in shi ya koma. Gyaran d'akin yayi ya sa turaren wuta shi ma, kafin yayi wanka. Tsayawa yayi a gaban mirror yana mai kallon kanshi a zahirance, but a bad'ini tunani ya tafi. Girgiza kai yayi kawai yana mai lissafin inda ya kamata yaje, ba zai iya zama a gidan nan ba gwara kawai yaje clinic dukda an bashi 2 weeks amma shi dai bai amsa ba don bai ga amfaninsu ba.

Shiryawa yayi tsaf cikina suit da wando sai white shirt da tie s, briefcase d'in shi ya rik'e bayan ya sa bak'ak'en single monk straps k'irar milano. Kan nan yana ta shek'in hair cream ga k'amshinshi na dindindin da ya game room d'in, ta k'ofar baya ya fita hakan ya sanya bata san da fitar ta shi ba ga shi dama bacci takeyi.

Ita ko baccinta takeyi hanian ko san da Safwaan ya kawo musu breakfast a waiting room ya ajiye don k'ofar living room a rufe yake, ya kuma kira ta bata d'aga ba gudun kar ya takura musu ya sa shi k'in knocking sai ma komawar da yayi gida yana jin zuciyar shi kamar zata tsage. Don tunanikan da k'wak'walshi ta bashi sun fi ƙarfin kan shi a wahalce ya koma gida cikeda alhini a yau kam ya hak'ura da Nadeefah har abada don ya tabbatar da ba zata tab'a zama tashi ba.


Yana shiga clinic d'in haka aka bishi da idanu, don kowa ya san da labarin d'aurin aurenshi shekaran jiya amma sai ga shi yau a office. Sai dai ba wanda ya tanka saboda kowa ya san halinshi na rashin wasa da mutane, and bai son shisshigi shiyasa kowa yake d'ari-d'ari da shi tun daga kan Soldiers, Doctors, Nurses, Lab workers, Radiographers har zuwa department d'in su wato physiotherapy.

Ba wai tsoronshi suke ji ba aa kwarjini yake dashi kuma yana cikin wainda ake ji dasu a asibitin. Kai baa ma asibitin ba a Kaduna baki d'aya, last year har award aka bashi as NO.1 practicing physiotherapist a Nigeria a NPS banda sauran awards da yake samu. Ya na da nashi clinic d'in mai suna BAY physio clinic amma yafi zuwa asibitin sojoji na 44, na shin kuma sai time-time yake zuwa. Suma 44 d'in ba k'aramin ji dashi sukeyi ba, ko dan baiwar da Allah ya zuba na ilhama da ilimi a k'walwarshi ga iya aiki kamar machine. Wasu da yawa ma gani sukeyi abunda ya sa yake girman kai kenan, abinda basu sani ba shi ne haka halittarshi take ko san da yana d'alibi har kuma a gida.

Direct office d'in shi ya wuce, zama yayi bayan ya rataye suit d'in na shi a hanger. Wayarshi ya d'auko yana placing order na breakfast a eateryn da ya saba breakfast. Yana ajiye wayar Adnan yana fad'owa cikin office d'in , tsayawa yayi yana kallonshi cikeda mamaki.

Shiko ko kallonshi bai yi ba sai k'ok'arin kunna system d'in shi da yake yi, ganin rainin hankalin na shi yayi yawa ya sanya shi cewa " Malam meye haka?". Ware manyan idanunshi yayi yana cewa " me kenan kuma?".


"Me kake yi yau a clinic d'in nan? Ba an baka hutu ba?". Ya furta yana mai hararar sa, tab'e baki yayi yana cewa " me zan huta ma wa?". 

"Wai ya kake amsa min tambaya Da tambaya ne? You know quite what I'm talking of, hutu aka baka na 2 weeks amma saboda son nunawa duniya cewa baka maraba da matar shi ne har ka fito this is but a disrespect to your wife!!" A d'an tsawace ya k'arashe maganar, shiru yayi masa kamar ba zai tanka ba sai kuma yace " Toh ban amshi hutun ba don ba na buk'ata, in ina buk'ata ai zan zauna ko? Maganar mata kuma ka bari time d'in da na shirya ajiye mai irin wannan sunan zan nemi hutun not now".



"Are you in your right senses Burhaan Yerwa? naji baka amshi hutun ba, but baka iya zuwa ko wani wuri ne ka yini a can. Ko da baka shirya ajiye mata ba can't you show a lil respect to that girl, me kake so mutane su ce a kanta? Haba man this ain't no like you".

"I'm in my right sense man, but ba zan iya zaman ko yini d'aya a gida d'aya da yarinyar nan ba. Seeing her suffocate me, in kuma na dage zan iya yin abinda ba shi ne ba this is my decision I've resume ".

"Burhaan.....!"


"Please Dr. Adnan, wannan sabgar da ta shafi gidana ne. Please maintain your lane". Ya k'arashe babu ko d'igo na sense of humiliation, gyad'a kai yayi yana mai furta "ok" ya nufi k'ofar fita. Shi ko rakashi yayi da idanu, he sees nothing wrong with abinda ya fad'a mai don bai ga dalilin da zai wani sa shi a gaba akan wata Nadeefah ba. Kamar yadda ya fad'i she's his wife, so ya k'yaleshi mana tun da shi ma bai tab'a masa shisshigi a lamarin na shi gidan ba. Tsaki ya ja ya na mai cigaba da aikin gabanshi, sawa yayi aka kawo masa files ya fara ganin patients.


San da ta farka 12 tayi har da minutes, sabon wanka ta sake don kayanta sun yamutse ainun. Sai kawai ta zura Abaya burnt coffee color, mai kawai ta shafa sai kwalli da ta zirara ma idanunta da sukayi luhu-luhu alamun taci kuka sai kuma wet lips da ta goga.


Tayi kyau skin d'in ta yana ta glowing, kama gashinta tayi ta d'aura veil d'in abayar a kanta. Wayarta ta d'auko tana nufar parlor cikeda tunanin abinda zata karya da shi, miss calls d'in Safwaan ta tarda da sauri ta fara kiranshi tana mai mamakin kiran.


"Assalamu alaikum fav". Ta furtaaa hankali, cije baki yayi yana mai cewa " fav a ina? Ai yanzu Yaya Islaam ne ya cancanci wannan sunan not me ". Da d'an kishi a harshenshi, murmushi tayi tana mai cewa " matsayinku ai ba d'aya ba ne, no matter what you'll forever be my favorite cousin". Tab'e baki yayi amma har ranshi yaji dad'i ko da tayi masa nisa, but at least yana da matsayi ko kad'an ne a wajenta.

Hakan yasa shi cewa " a cousin d'in ma nagode since I'm your favorite among them, so how far? Ya sabon wuri". Murmushi ta sake mai sauti tana cewa " Alhamdulillahi, ya gidan ya gajiyarku kuma?". 

"Well, gajiya ta bi lafiya d'azu nazo gidanku na gama zamana a waiting room ina ta kira ba a d'aga ba sai kawai nayi tafiyata".

"Allah sarki, wallahi wayar na silent ne shiyasa but we are sorry. Yaushe zaka dawo tohm?". Ta tambaya cikeda sanyin murya, shi ko cewa yayi " dama breakfast na kawo muku, na ajiye a nan waiting parlor d'in zuwana kuma ba rana but sha zaki ganni".

"Toh Yaa ina zuba idanu sai na ganka d'in".

"Alright, ki gaida Yaa Islaam see ya".

"Bye" ta furta tana datse kiran, waiting parlor ta nufa ta d'auko basket d'in. Breakfast ne mai rai da lafiya har da peppered soup, zama tayi taci abunta ita d'aya a dining. Tana gamawa ta kwashe kayan da ta b'ata ta kai kitchen, wanke su tayi kafin ta fito, sauran ta danna intercom ta shaidawa security su zo su d'auka a waiting room.

Zama tayi ta fara waya da y'an gidansu, kusan sai da ta kira kowa a manyan familyn. Sun ji dad'in kiran ainun kuma kowa sai ya mata nasiha akan tayi hak'uri, Hajjah ce last da ta kira sun dad'e suna wayar da ita sosai ta bata tips na zaman gidan sosai taji dad'insu ainun har damuwarta ta washe.

Ba ita ta katse kiran ba sai da tayi bak'i, friends d'in ta ne ( tarkacen da Burhaan yake kira). Sune suka zo kusan so 7, mantawa da kashedinshi tayi ta karb'e su hannu bibbiyu. Nan suka tasa ta a gaba da tsokana, wai idanunta sunji ja alamun anji maza.  

Sophia ( bestie) har da kwaikwayar muryarta da ta dishe, Ayush Maleek na tayata. Sai Radeeyah ( Deeyah Habeeb) ce take shigar mata, su Heedaya, Jam-jam, Seemah da Chu-chu suna aikin dariya. 
Ita dai bata biye musu ba sai murmushi takeyi, Kazan amarcin da ta gani a dining da tana gyara da safe shi tayi microwaving ta kawo musu da drinks.

Ita Heedayar har da cewa wai Zulfaa ta mata overtaking ai Farhan crush d'in ta ne, Seemah wai kuma Sadeeq. Nan aka fara tsokanarsu suma, Bestie tace " toh shi Islaam d'in fa?" Dariya suka kece dashi Ayush tace " wooo wannan ai sai dai K'amshi, kullum fuska a d'aure ". Dariya suka kwashe da shi Deeyah tace " ai ni haka nake son namiji, no nonsense wanda zai tsaya min a komai ba sai inda nayi dashi yayi ba Allah na tuba mai akeyi da namiji mara aji".

Dariya suka kwashe da shi Ayush tace " ai d'aure fuska bashi ke nuna namiji mai aji ba ne, most of miskilayen nan are a wurin matayen su ba su da maraba da jarirai". Sophia tace " d'an yi hak'uri dai madam, miskilanci and sakin kai basu tab'a had'uwa za dai a iya kiransu as tsaka-tsaki. Like suna so da kula da duk abinda ya zama mallakin su and hakan bashi zai sa su bar matan su kauce hanya ko su raina su ba, sun isa da gidansu su ake kira da Alfawan ainihi ba 'yan wahalan nan masu da'awar alphanci ba".

Dariya suka sanya mai k'arfi Lele tace " Sosai ta waje na".

Hira suka dinga yi cikin nishad'i, 2 aka kawo lunch daga gidan Umma. Tare suka ci abincin, bak'i ne suka dinga sintiri y'an ganin amarya da masu sallama mutanen morocco. Su suka tayata serving d'insu basu suka bar gidan ba sai after 5, har harabar gidan ta rako su tana mai jin kamar kar su tafi don ta ji daɗin zuwan su sosai.

Tana tsaye a parking lot suna sallama, abunka da mata kasan sai za a rabu ake dasa wata sabuwar hira. Toh suma haka sukayi don wata sabuwar hira ce ta b'arke a tsakaninsu, ko motocinsu ma ba su bud'e ba suna ta dariyarsu.

Bud'e gate da security sukayi ne ya maida hankalinsu ga gate d'in gabad'aya, a take k'irjinta ya buga ganin wanda ya shigo gidan. Sai dai ta basar ta cigaba da murmushin yak'e. A garage yayi parking a da ta inda ya fita yaso shiga sai dai ganinta da wainda ya gama mata kashedi akansu ne ya sa ya fasa ya fito kawai.



Gaishe da shi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa, yana mai wucewarshi ciki. Deeyah tace " sojoji ba sauk'i hala basu ba shi hutu bane ?". Girgiza kai tayi tana mai cewa " emergency ne aka kirashi wai akwai wanda zai d'aure, amma hutu yake ai". (Lai Lawal, Nadeefah a ji tsoron Allah dai ). 

Seemah cewa tayi " dama irin aikinsu ai sai da hak'uri, suna ƙoƙari sosai ga abu da gidan soja. Kuzo mu taf guys don da alamu a gajiye yake ". Sophia tace " gaskiya kam, Babe mun wuce fa ".  Murmushi tayi tana mai cewa " thanks for coming guys, Allah ya bar zumunci ya tsare hanya". Ameen suka amsa kusan a tare kafin kowa ta shige motarta suka bar gidan.

Shiga ciki tayi cikeda sanyin jiki da fargaba, a k'ofar shigowa parlorn ta tsaya turus tana kallonshi yana zaune a couch hannunshi bottle water ne mai sanyi. Yafito ta yayi da hannunshi yana kai gorar bakinshi, daga inda take tace " I'm sorry ba da son raina suka zo ba kayi hak'uri".

"Na tambaye ki ne? Zo nan!!" Ya k'arashe yana mai cire ruwan daga bakinshi, yawu ta had'iye a tsorace ta k'arasa gabanshi durk'usawa tayi jikinta yana kakkarwa. Ruwan da ya gumtsa ya fesa mata a fuska yana cewa " me na gaya miki jiya?".

Kawar da fuska tayi cikeda tsoro fuskarta na d'igar ruwan da ya watsa mata " I'm sorry " ta sake furtawa hawaye na forming a idanunta. Hannunta ya kama ya murd'a cikeda mugunta " just answer me! Ki adana ban haƙurin ki zata miki amfani anjima, now tell me ya muka yi dake jiya ?".

"Kace kar su zo maka gida" ta amsa masa hawayen da suka taru suna zuba a kuncinta " and today....?".

"They came today, but bani na kirasu ba wallahi. Basu ma kirani ba kawai zuwa sukayi kurum". Gyad'a kai yayi yana mai cewa " and saboda kin rainani shi ne baki kore su ba? Ni sa'anki ne?". 

"Ka yi hak'uri ba zasu sake zuwa ba ". 

"And in su ka kuma fa?".

"Ka yi min duk hukuncin da ya dace dani."

"In haka ne kira su yanzu ki gaya musu kar su kuma zuwa mana...?".



"Na maka alƙawarin ba zasu sake zuwa ba, but kiransu bai kamata ba Dan Allah ". Ta fad'a cikin sauri, harararta yayi yana cewa " saboda ban isa dake ba ko?" Girgiza kai tayi tana mai cewa " ka isa har kayi yawa Yaa..."

"To kira su maza" ya fad'a cikeda umarni, cikin kwantar da murya har lokacin hawayenta yana gudana tace " But yaa Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam ya mana gargad'i da yanke zumunci har ma yace ba ya tare da duk mai yankeshi kuma bana so ka zama cikin wainda basu tare dashi kiransu in musu kashedi akan zuwa gidan nan tamkar sa almakashi ne a datse igiyar zumuncin dake tsakaninmu in aikata hakan?".

Jikinshi ne yayi mugun sanyi yayinda kalamanta suka fara tasirantuwa akanshi, lumshe idanu yayi ya rufe yana mai sakin hannayenta. A hankali ya fara magana " uwar 'yan fassara ba abinda na sa ki ba kenan,  kar kuma a kai ni gaba. But kar ki sake in k'ara ganin k'afufunsu a gidana, nan gidan aurenki ne ba gidan taron biki da tarkacenki zasu dinga min sintiri ba. Ni ne sama dake dole abinda nake so shi za ayi, saɓawa umarni na zai janyo hukuncin da ba zamu so ba. Now, bar nan wurin!!".

Da sauri ta tashi tana mai wucewa ciki jikinta na rawa, kukan da take son yi ta zauna tana kayanta kashirb'an. Kwanan ta guda a gidanshi amma tayi kuka tashi biyu kenan, anya zata iya? Anya ba dambun magaji da nishi ta kinkimo ba? Anya kafin ta gama zuciyarta ba zata buga ba?.

Tambayoyine masu nauyi da suka taru suka cunkushe a rai da zuciyarta, yayinda gwuiwarta yayi mugun sanyi tana mai jin kamar tayi gangancin zab'an zama da shi. Shin da gaske ba mugun wauta tayi ba kuwa........?

Ni ma dai gani nake kamar fa har da wautar, don't mind me sha mai hak'uri ai yana tare da Allah. Meye ma na saurin sarewa Hajiya Nadeefah bayan yanzu ma aka fara, ai Burhaan bai ma yi komai ba ko kuwa ?..........

Deejasmah✍
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.