Free chapter · Read without an account
CHAPTER 19 ( Sick...)
by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
CHAPTER 19 ( Sick...)
Tsawa ya daka wa Safwaan dake k'ok'arin kiran sunanta bakinshi a bud'e, rufe bakin yayi ruf jin yana cewa " kar ka sake kayi wata magana a nan, koma motarka ka wuce gida ".
"And you, me kika fito yi a nan? Wa ya kira ki?" Ya juya kan ta kamar wani namijin zaki, duk gajiyar da ya kwaso ma nemanta yayi ya rasa saboda tsabar tsiyar da take cin shi. Da mabanbantan yanayi suka bi shi da idanu, shi Safwaan bai wuce na yanda ya ga yana hak'ilo gira na hayak'i ido na ci da wuta akan abinda bai raba d'ayan biyu kishi ne. Toh abin tambayar a nan shi ne yaushe har ya fara son ta har haka ne da yake mugun kishinta.
Ita kuwa rauni ne ya lullub'eta ganin yadda yake shirin tijarata a gaban k'aninshi, wai me yasa Yaa Islaam yake son nuna wa duniya kalar tsanar da yake mata ne? Me tayi masa da zafi har haka ne?......
Katse musu tunaninsu yayi ta hanyar sakin wata tsawar yana mai cewa " wai ba daku nake magana ba ne kuka tsaya kallon-kallo? You!! Bar gidan nan!! ". Tura baki yayi yana cewa " haba Yaa korata fa kake daga gidanka?".
"Tambayata ma ka tsaya yi kenan?" Ya tambaya a hasale, cewa yayi " well zan tafi, Allah ya baka hak'uri sak'o zan amsa yanzu zan wuce ". Kallon Lele da ta juya baya da niyyar komawa ciki yayi yana k'wafa da sakin ajiyar zuciya yace " ka jira a motar yanzu zan kawo maka sak'on, fito min da kayana ".
Tunzura baki yayi a ran shi yana had'iye muguwar dariyar da take taso masa na kishin da ya ga yana yi akan Nadeefah bayan darun da ya gama yi akan aurenta, kayan ya fito masa da su ya ko ja akwatinshi zuwa ciki. A parlor ya ajiye jakar yana kallonta tsaye a dining tana zare idanu, a zafafe ya isa gabanta cikin muguwar masifar dake cin shi yace " ke baki jin magana ko? Me kika fita yi a wajen?".
"I'm sorry....'' Ya katseta da cewa " ki amsa min tambaya ta Malama, ne kika fita yi?!". Cikin b'arin murya da na jiki tace " na je maka barka da dawowa ne".
"Tun da nace miki ina buk'ata ne ko?, ban ce ki tsaya a matsayin ki ba?" Ya k'arashe yana tsaye a gabanta jikinshi har yana tsuma kamar zai d'auketa da mari, rasa abin cewa tayi hakan ko ba ƙaramin ɓata masa rai ya kuma yi ba. Allah da ikon shi sai Safwaan ya saki doguwar honk alamun jira.
Tsaki ya saki yana cewa " ki kiyaye ni,,,,,now ki fito da abinda zaki ba shi ya tafi ". Da sauri ko ta shige kitchen, buffet d'in da ta had'a abinci ta fito da shi guda biyu ta ajiye. D'auka yayi ba tareda ya tanka ba, ajiyar zuciya ta sauke tana bin bayanshi da kallo.
Har mota ya kai masa ya juya ciki yana cewa ya gaida su Umma, da dariyar da ya danne fitowarshi ya raka shi kana ya ja motarshi a ran shi yana ayyana yau Umma za ta sha labari. Sanda ya shigo ba ta parlorn bai bi ta kan ta ba ya ciro key a gefen trollynsa yana mai bud'e part d'in na shi.
Da sallama ya shiga ciki bayan ya kunna hasken parlorn, d'an ajiyar zuciya ya sauke ganin parlorn ba datti don kafin ya tafi sai da yayi gyaran shi tsaf sai dai k'urar da ya bayyana ba laifi don ma wai ko ina a rufe yake har ma furnitures d'in dake lullub'e da ledoji. Bai ajiye jakar a nan ba ya nufi bedroom, shi ma dai yayi k'ura in ka d'auke gadon da ya rufe da leda. Duk da ya gaji amma haka ya ajiye kayanshi cikin closet sannan ya fara k'ok'arin gyaran bedroom d'in don yana son ko wurin rab'a kataren shi ne, tas ya share da kayan sharan dake toilet d'in shi yayi mopping har da shimfid'a bedsheets masu taushi farare da duvet.
Kayanshi ya cire ya nufi bathroom wanke nan d'in ma yayi sannan ya tara ruwa mai d'umi a bathtub, shiga ciki yayi yana mai lumshe idanu. Wankan ya d'auke shi lokaci mai tsayi alwala ya d'aura ya fito, kasancewar ba a bin shi sallah sai kawai ya shirya cikin k'ananun kaya marasa nauyi. Armless d'in Louis Vuitton fara da wandonta three quater shi ma fari, bud'e fridge d'in shi yayi da niyyar d'aukar ruwa babu komai a ciki sai ma d'an karan zafin da yai masa sallama kasancewar ya kwana biyu a kashe. Tsaki ya ja ya a ran shi yana mitan in da wacce yake so ne da yanzu ya samu tarba amma ji daga dawowarshi ya fara ayyukan da bai saba ba. Don ko a gidan Umma yayi tafiya ko ta kwana uku ce ba k'aramar tarba ake masa ba, amma ji nan sai ma fashewar zuciyar da aka kusa saka masa ba don Allah ya kare ba.
Turus ya tsaya a k'ofar bedroom d'in sakamakon k'amshi da kuma ni'imar da ya gauraye parlorn akasin yanda ya bar shi, duk wani k'ura babu an cire har ledojin da aka rufe kujerun da shi. Lumshe idanu yayi ya bud'e akan parlorn yana mai jin nishad'i yana cika zuciyarshi, Allah ya sani yana k'aunar k'amshi da tsafta kuma yana matuk'ar girmama ma'abocinsu. Ganin parlorn a haka ya fiye masa komai na haushinta da yake ji, k'arasowa cikin parlorn yayi ƙarin mamaki sai ganin abinci cikin wasu tsadaddun warmers masu ruwan zaiba na glass mai kauri k'irar Beirut da aka sanya cikin trayn da ba haufi mahad'in su ne.
Sai jug na transparent glass mai d'auke da lemonade a ciki, sai plate, bowl da spoon akai har da tissue. Sai kuma exotic drink da ruwa da ta d'aura akan wani trayn shi na da cup, yanda ta shirya table d'in kad'ai ya isa ya sa mutum ci ko bai yi niyya ba. Balle ma da yunwarshi. A take cikinshi ya zab'i kunyata shi ta hanyar yin doguwar kuka, dafe cikin yayi yana tsuke baki kana ba ko kunya ya samu wuri gaban table ya zauna.
Bud'e warmern yayi bayan ya wanke hannu a ruwan da ta ajiye mai na wanke hannu nan yayi ido hudu da sinasir, tab'e baki yayi don bai wani cika son sinasir ba hakan ya sa ya zuba biyu kawai da miya kad'an a gefe ya jibga nama. Bismillah yayi yana kai wa bakinshi, lumshe idanu yayi yana gyad'a kan shi.
Kafin ka ce me ya cinye wanda ya zuba ya kuma dad'a wani ci kawai yake yana korawa da lemonade, sai da yaji cikinshi ya cika ba kuma don bakinshi ya gaji da ci ba. Bud'e d'ayan yayi ya ga kaza a ciki, d'aya kuma fruit salad ne da yaji madara daga gani. "Uhmm " ya furta yana mai cewa " so kike ki fasa min ciki yarinyar nan " ya k'are da murmushi. Jingina yayi da kujera yana mai da numfashi don yayi mugun ci, bini-bini ya saki murmushi yana mai tuna d'and'anon abincin a harshenshi.
Kiran sallahr magriba ne ya tada shi a wurin, bowl d'in fruit salad d'in ya kai kitchen da jug d'in lemonade ya sa a fridge. Ya dawo parlor tattara mata kayanta yayi wuri d'aya shi ma nan ban da chicken d'in, alwala ya je ya d'aure ya kwashi kayan zuwa living room.
Fitowarta kenan daga kitchen tana shirin shiga ciki jin an kira sallah, sai ganinshi tayi da tray rigi-rigi. Da sauri ta k'araso gabanshi ta amshe shi, kusan numfashinsu ne ya kusa d'aukewa a time d'in da hannayensu suka had'u da na juna. Saurin janye hannunta tayi daga kan na shi, shi ko duk da yaji abun har cikin zuciyarshi sai bai nuna ba illa ajiye mata da yayi a kan dining.
Kamar a bazata taji muryarshi yana cewa " Nagode, duk da dai da baki wahalar da kan ki ba" daga haka ya juya, sandarewa tayi a tsaye tana bin shi da idanu cikeda mamakin godiyar da yayi mata. Sai kuma ta saki murmushi tace '' ba wahalar da kai, aikina nake yi". Cak ya tsaya sai kuma ya juyo ya kalleta, gyad'a masa kai tayi ta d'auki trayn da ya ajiye ta shige kitchen tana sake fad'ad'a murmushinta. Tab'e baki yayi alamun " damuwar ki " shi ma ya fice daga parlorn zuwa masjid, ita ko ajiyewa tayi kawai ba ta wanke ba don an fara shiga masallaci don haka ta shige nata sashen don son gabatar da farali.
Ranar bai shigo da wuri ba saboda had'uwar da sukayi da su ElSadeeq suna gaisawa har da sauran yayyinsu, sanda ya shigo har ta kwanta shi ma sashensa ya shige zama yayi ya nad'i kazar da ya ajiye iya son ran shi ya d'aura da fruit d'in kafin ya tashi. Wanka yayi ya kwanta a gadon yana jin ran shi fes a rana d'aya na rayuwarshi fiye da baya, a haka bacci ya sace shi.
Washe gari da ta tashi bata bi ta kan shi ba, duk da kuwa a mak'ale a ranta ta kwana da shi. Gyaran gida tayi tai wanka ta bar gidan zuwa office.
Shi ko bacci yayi mai ma'ana bayan dawowarshi daga sallahr asuba, ba shi ya tashi ba sai kusan 10:30. Wanka ya zubo ko kaya bai saka ba ya fito da niyyar ganin abinci, sai dai table d'in da ta ajiye masa na jiya wayam ya tarda shi ba ma alamun an shigo d'akin balle a ajiye. Sai ya nufi living room da tunanin may be a nan ta ajiye, shi ma dai zancen d'aya ne don ko abinci yace masa d'aukeni inda ka ajiye ni.
Tsaki yayi yana cewa " me yarinyar nan take nufi da ni ne? Ba tayi breakfast ba ne take son cewa or what?". Kitchen ya shiga komai tsaf babu ko cokali a waje balle yace an tanadi wani abu da sunanshi, yanzu kam ranshi ya kai k'ololuwar b'aci sai huci yake saukewa kamar na mijin da ya sa matarshi abu ta k'iyi ( k'arfin hali b'arawo da sallama, hala ya manta shi yace kar tayi abinci da shi. Ba ta ji ba tayi ya kuma nuna mata kar ta koma shi ne don tabi umarninshi har da jin haushi eh lallai ma ).
Tea pot ya d'aura akan kuka ya sa teabag da wasu kayan tean dake kan counter a ajiye, jingina bayanshi yayi a jikin fridge har sai da ya tafasa ya kashe. Juyewa yayi a wani mug kana ya soya k'wai biyu kawai ya koma dining, tea ya had'a da uban madara ya zauna ya cusa da bread da soyayyan k'wanshi. Sai da yaci yayi nak sannan ya kwashe kayan ya ajiye mata a sink ya koma d'akinshi, shiryawa yayi cikin wani cashmere brown color d'inkin fitted na maza bai ko sa hula ba sai bak'ak'en takalma da ya sanya ya rufe gidan ta side d'in shi don dama ta riga ta rufe na shiga gidan.
Gidan Umma ya nufa don bai ga amfanin zamanshi a gidan ba, a nan ya kusa wuni. Shi ne har da zazzaga wasu a cikin family har gidan Hajjah ya je, sai after la'asar ya tafi BAY physio clinics nan ya kai dare yana ayyukan dake kan shi. A hanyar komawarshi ne ya siya abinci don bai da tabbacin an dafa da shi a gidan.
Kwananshi uku da dawowa ya koma bakin aikinshi, a tsukin ya azabtu iyaka da rashin abinci. Duk da kullum sai ya siyo a waje amma kusan haka yake bayar da shi saboda saboda rashin appetite, lafiyarshi lau ba wai bai da lafiya ba amma dai bakinshi da yaudara bai jin dad'in kowani abinci. Ran shi ko sai aikin k'awata masa abincinta da yake yi, hatta tean da yake had'awa bai jin dad'insa haka za tarin drinks d'in da yake sha.
Amma da yake kan na shi ya fi dutse tauri bai nuna ba duk kuwa da azabtuwar da yake yi akan rashin abincin, ko gidan Umma ya je ta ba shi abinci bai iya ci da yawa in ma an samu ya ci cokali uku a gode Allah. Ranar da Umman tayi sakwara ta ba shi saboda k'aunarshi da yake yi, kasa ci yayi sai barin mata kayanta da yayi a wajen. Ranar shi da kan shi sai da yayi tunanin ko dai Nadeefahn wani abu ta sa masa a abinci ko makamancin haka, sai dai bai da mai bashi amsa haka ya lallab'o tsufanshi ya dawo gida yana mai tunanin na kwana biyu ne zai daina sha'awar abincin nata.
Sai dai me? Kamar wasa kwanaki na shurewa k'aunar abincin na dad'a k'aruwa a ranshi, yanzu ma ya daina wahal da kan shi wurin siye don ba zai iya ciwuwa ba. Kafin kace me ulcer ta samu waje ta shige abinta, blood sugar d'in shi ya sauka sosai. Bai tab'a lura ko maida hankali akan haka ba, sai da ya fara rama ga uban kasala da yake samu a gab'bansa bai iya zirga-zirga kamar da.
Adnan ne ya fara ankara da yadda ya rame ko da ya tambayeshi tab'e baki yayi yana cewa " ni babu abinda yake damuna" cewa yayi "kana kallon kanka kuwa?". Yatsina ya sake yi yana kawar da kanshi gefe, sake cewa yayi " Guy, ka gaya min mana".
"Na gaya maka ba abinda yake damuna, i'm ok" ya furta a hankali yace " you are not, kawai dai baka son fad'i ne. Ko fa abinci baka ci ko an ce maka ban lura da kai ne? well, damuwarka ce san da ka ga dama zaka fad'i". Da idanuwa ya rakas shi kawai a ranshi yana ayyana ai ko giyar wake ya sha bai isa ya fara labarta masa abinda yake damunshi ba, tunda shi ma ba wai ya gama sanin takamaiman damuwarta ta shi ba ne.
Da ya je gidan Umma ma haka ta sashi gaba da tambaya, itama amsa d'aya ya bata amma kuma bata gamsu ba. Ya za a ce lafiya mutum yana tsotsewa? Haka nan jikinta ya bata akwai matsala da har ta kasa jurewa sai da ta kira Ya Budu.
Ringing biyu ta d'aga da sallama " Ummanmu barka da rana". Tace " yawwa Mamana ya gidan da yaran?".
"Alhamdulillah, ya naji muryanki da damuwa lafiya kuwa?" Ta tambaya da kulawa cewa tayi " lafiya wallahi, d'anuwanki ne naga kamar bai cikin lafiya duk ya fige ya lalace na kuma tambayeshi ya kuma shaida min wai babu abinda ke damunshi".
Tace " toh fa? Da ma ana rama haka nan ne? Kin kira ita Lelen?". Girgiza kai tayi kamar tana gabanta tace '' ban kirata ba, ni so nake ke ki kirashi k'ila zai fad'a miki damuwarshi ". Cewa tayi " toh a fara kiranta a ji ko ita tana lafiya and in akwai wani abun da zata iya bamu akan matsalar ta shi kin ga ba wanda ya fita kusanci da shi yanzu ".
"Ita fa lafiya take sai ma murjewa kullum take tana k'ara yin kyau" Umman ta bata amsa cikin sanyin murya, shiru Budun tayi alamun nazari sai can ta nisa tana cewa " Umma ko dai rabo aka samu ne?". Cikin rashin fahimta tace " wani irin rabo kuma? Ana maganar Burhaan kina maganar rabo, in ciki ne a jikin shi za a samu ko na matarshi? ".
Dariya ta saki tana cewa " eh mana, ana samun irin haka sosai sai kiga mace da ciki amma mijinta shi ke mata laulayi ba kuma za a samu sauk'in ciwon ba sai in cikin yayi k'wari".
"Sai kuma aka ce miki Lelen ciki ne da ita?" Ta tambaya a d'okance, cewa tayi " zai iya yiwuwa tana da cikin, tunda ke da kanki kin shaida irin kyan da take k'arawa a kullum yayinda shi mijin yake tsotsewa kamar kud'in guzuri ".
Gud'a ta saki tana cewa " in ciki ne kuwa wannan ba k'aramar abin farinciki ba ne ba ". Tace " tabbas ko,amma mu jira jin ta bakinsu tukunna kar muyi gaggawa". Cewa tayi " in shaa Allah, Allah dai ya sa cikin ne ya rabasu lafiya shi kuma ya bashi rangwame". Ameen suka amsa a tare, kana suka yi sallama bakinta ya k'i rufuwa a wurin har da lissafi ta dinga yi sai kace wannan ne karon farko da zata rik'e jika. ( Hmmm...... Wannan ne fa ake kira dambun magaji da nishi,a gaida Hajjah Sato da Hajjah Budu da hasashe).
Duk wannan gid'imin ramar Burhaan ita matar gidan ma ba sani tayi ba, don tun dawowarshi sau biyu suka had'u shi ma kuma ba wani sakewa tayi ba. Duka a kitchen ne ma d'aya yana dafa ruwan zafinshi na fama ta so taimaka masa ya gwasaleta, ba ma ta samu kallon fuskarshi ba. Na biyu kuma ya zata shiga parlornta ya shigo gidan ko gaisuwarta ma bai amsa ba yayi wucewarshi ciki, hakan ya sa ta cigaba da hidimarta ba tareda ta sake bi ta kan shi ba. Duk da ta rage ganin takeout packs da yake siyowa, sai k'arin kofunan tea da take yawan gani dalilin da ya sa ta sake fito da tea spices ke nan suma ba da yawa yake d'auka ba daga cinnamon, lemon grass, mint, clove sai citta da yake d'auka a ciki alamun su yake so kenan a nata tunanin yayinda shi a na shi bai san kan sauran kayan dake wurin ba ne shiyasa.
Yau kusan a tare suka shigo gidan, don tana saka hancin motar ta a gidan yana isowa gate d'in shi ma. Shigewa tayi yana mara mata baya a nata parking lot d'in ta ajiye motarta haka shima ya yi a nasa, har yayi niyyar shigewa ta k'ofar baya sai kuma ya fasa don haka nan zuciyarsa ta raya masa son ganin kayan da ta saka da ta fita. Sanda ya iso har ta bud'e k'ofar shiga waiting room sai taji zuwanshi a jikinta, sanye take da Boubou gown black mai pattern wanda yake zuwa da mayafinshi mai girma kanta da hula bak'a.
Waigowa tayi tana kallonshi k'irjinta ne yayi wani mugun buguwa ganin yadda ys sirance a k'ank'anin lokaci har haka, fitinannun idanuwanshi masu tsorata ta duk sun yi mugun laushi ga kuma idanun da ya yi masa rakwa-rakwa. Za tayi magana ya jefa mata mugun kallo da su, saurin kawar da kanta tayi ta tura k'ofar ta shiga yana mai bin ta a baya. Sai da suka isa living room ne ta sake dubanshi da kyau, ganin yana k'ok'arin bud'e k'ofar side d'in shi ya shige tayi saurin cewa.
"Yaa Islaam ba ka da lafiya ne?" Waigowa yayi yana kallonta da yanayin da ya saba yace " ba matsalarki ba ce, lafiyata ko akasinta ". Matsowa gsbanshi tayi cikeda k'arfin hali tana cewa " matsalata ce mai girma kuwa, Yaa Islaam Ni matar ka ce dole in damu da lafiya da ciwon ka".
Cikin cusassiyar muryar shi da duk da ta yi k'asa saboda ciwon dake cin shi amma sai da ya shigeta har b'argo yace " ban son shisshigi, ban saki a cikin lamarina ba kar ki shiga. Ina taya ki murnan zama matata ". Daga haka yayi shigewarshi ya barta nan sororo, yawun da ya tokareta a mak'ogwaro ta had'iye girgiza kai tayi tana murmushi don halayyarshi sun daina bata mamaki da tsoro. Lallab'a 'yan matan k'afanta tayi ta shige nata sasan, mik'e k'afafu tayi akan sofa tana cewa " wash bayana" don ta gaji yau ba laifi.
Tun shigarshi yake sake jin wani kala don kuwa k'irjinshi zafi ya d'auka sosai yana kuma wani irin bugawa da k'arfi, kwantawa yayi kawai dafe da shi yayinda azaba yake sake nuk'urkusanshi. Ko da aka kira Magrib kasa fita yayi a nan yayi sallah, haka ishai wanda tsabar galabaita ma a zaune yayi ta. Yana kwance amma jiri yake gani ko wanka ya gaza yi, yana nan har kusan 9pm ganin yunwa na shirin nakasta shi ya sa ya lallab'a da bin bango ya k'arasa parlorn.
Kitchen ya nufa da niyyar samun wani abu ya ci, a tsaye ya tarda ta sanye da kayan bacci kalar light purple sai flowers manya a ciki riga da wando masu taushi. Girki take yi cikin rashin karsashi, don tun ganinta dashi hankalinta ba a kwance yake ba. Jikinta yana bata bai da lafiya sosai basarwa yake yi hakan ne ma ya sa ta gaza samawa kanta abinci sai yanzu da ita ma taji yunwa na shirin gamawa da ita kafin ta taso tana dafa noodles amma da yake yunwar ta 'yan gayu ne sai da aka gama mata iyayi wajen girkin har da su sausage da peas da carrot ƙwai ɗaya ta dafa ta d'aura akai.
Juyewa tayi a bowl tana mai juyowa da niyyar fita, tayi tozali da shi dafe da bango da kan shi. Ajiye bowl d'in tayi da sauri akan kitchen island, ta matso gabanshi tana tare shi ganin kamar zai fad'i. Hannu ta sanya a wuyanshi zafi taji zau alamun zazzab'i mai tsanani, fisgewa yake son yi don jin shi a jikinta ya jefashi cikin wani hali amma kasancewar bai da k'arfi sai ya kasa hakan sai ma saki da jikinshi ya sake yi.
Lallab'awa tayi suka fita parlor tana mai masa sannu, akan sofa ta taimaka masa ya zauna yana jingina kanshi dake sara masa akan majinginar kujerar. Rankwafowa tayi a hankali tana cewa " me zaka d'auka a kitchen d'in''. Cikin dusasshiyar murya yace " tea zan had'a".
"Bari in kawo maka " ta furta tana wucewa kitchen d'in, ruwan zafi ta d'aura ta sanya komai na kayan k'amshi a ciki sa'annan ta d'auko bowl d'in indomien fahimtar har da yunwa a lamarin. Yana a yanda ta bar shi sai dai yanzu ya sanya hannayenshi ya dafe kanshi dake sara mai dasu, zama tayi a gefenshi tana masa sannu ta d'aura da fad'in " Yaa, ga indomie kafin ruwan yayi zafi". Bud'e idanuwanshi da sukayi mugun ja yayi a kanta, har zai kauda kai sai kuma k'amshin abincin ya kai wa hancinshi ziyara. A take kuwa sabon yunwa ya sake taso masa da sai da ya sa cikinshi k'aramin kuka, Allah ne ya taimake shi ba mai k'ara ba ne da an ji kunya kam.
Gyara zamanta tayi ta sanya hannu ta d'ibo indomien zuwa bakinshi, kamar ba zai bud'e bakin ba sai kuma ganin yadda ta marairaice sai ya bud'e a yangance. Sanya masa tayi a hankali cike da rarrashi, Amsa yayi yana taunawa a hankali. Ai da sauri ya matsar da kan shi don bai ko kai da had'iyewa ba wani mugun amai ya taso mai, tashi yayi niyyar yi sai kawai abun ya taho babu control ai ko ya hau wanketa da wani kalan amai wanda kana gani kasan ba na komai ba ne face na yunwa don zallar ruwa ne a ciki.
Dafe shi tayi ba k'yamata ba komai cikeda damuwa take masa sannu, ba shi ya sarara ba sai da ya juye mata aman cikinshi tsaf sannan ya koma lak'was zai kwanta. Da sauri ta hanashi ta hanyar janyeshi ganin da tayi zai kwanta kan k'azanta, kasancewar ba a ƙarshe suke ba sai ta ja shi zuwa k'arshe ta kwantar. Tashi tayi tsamo-tsamo don rabi da kwata a jikinta ne sai sauran a kan kujera, har cikin indomien da take basa kuwa.
Tattare jikinta tayi ta juye shi a wurin kafin ta nufi toilet d'in dake parlorn, cire kayan tayi tsaf ta sakin ma kanta ruwa. Sai da ta wanke jikinta tsaf har kanta kuwa kafin ta ja towel d'in da ke ajiye ta nad'e jikinta, fitowa tayi yana a yanda ta bar shi. Da sauri ta nufi part d'in ta ko ta kan ta dake tsiyaya ba tayi ba ta bud'e wardrobe, wata free gown dai-dai guiwa ta nemo ta zura a jikinta kafin ta fito bayan ta kwaso kayan shara.
Gyara wurin da ya b'ata tayi kafin ta taimaka masa ya mik'e har d'akinshi ta kaishi cikin toilet, bakinshi ta wanke masa ta taya shi ya cire rigarshi kafin ta fito ta bar shi bayan ta d'an tara masa ruwa mai d'an d'umi ganin zazzab'inshi yana sake hauhawa.
Kitchen ta koma tana kashe gas ganin har ruwan ya k'one, tsayawa tayi tana tunanin abun yi. Rasa mafita tayi sai kawai ta koma wurinshi, ta tadda ya fito amma yana lullub'e cikin bargo yana kuma ta kakkarwa sosai. Zama tayi a side drawer cikin taushin murya tace " sannu Yaa, zaka iya mu je hospital?". Cikin rawar muryan ciwo yace " i'll be okay, ba sai mun je ba".
Girgiza kai tayi tana cewa " ba zamu iya barinka haka ba, jikin ka yayi zafi sosai kuma kana rawar sanyi dole a nemi mafita tun yanzu da yake farkon dare ba mu san yadda tsakar dare zai yi ko in kira Umma ne?". Da sauri ya rik'o hannunta yana cewa " don't, nace miki zan samu sauƙi ko?".
"Ba ka da lafiya ka daina wannan abun ba zai taimake mu ba ko in kira Safwaan kawai?" Yace " call Adnan for me" don shi ma ya san yana buk'atar likita, ok tace sannan ta d'auko wayarshi dake ajiye kan mirror ta mik'a mishi. K'in amsa yayi ya karanto mata passcode d'in shi, sawa tayi ta bud'e sannan ta shiga contact d'in. Physio Adnan yayi saving number, dialing tayi ringing biyu ya d'aga.
"Mutumin ya aka yi da wannan daren?" Shi ne abinda ya furta da tsokana a harshenshi, cewa tayi " ba shi bane Yaa Adnan bai da lafiya ne wallahi ". Innalillahi ya furta a d'an rikice, ya d'aura da cewa " me yake damunshi ne haka? And yana ina ?". Amsar wayar yayi kafin ta bashi amsa yana cewa " ni dai ba wannan ba, ka je BAY ka taho min da Dr. Adebayo yanzun nan please ". Cewa yayi " yanzun nan kuwa" don muryar da yayi masa magana ya tsorata shi, rabon da yaji yayi magana da ita tun ran da aka sanar da had'in aurensu da Nadeefah.
Mik'ewa yayi da sauri yana cewa Salmah ta mik'o mai key, da d'an tsoro ta kalleshi " lafiya kuwa?" Yace " Burhaan ne ba lafiya, yana buƙata ta a csn". Da sauri ta d'auko masa tana masa adduar neman sauk'i bai ko amsa ba ya fita da muguwar gudu, tafiyar 5 mins ya kawo shi BAY clinic d'in bai ko shiga ba ya kira Dr. Adebayo d'in akan ya iso. Fitowa yayi a rikice ya ja motar zuwa gidan, bai samu matsala da masu gadin layout d'in ba don dare bai wani yi sosai ba duka 9:42 ne.
Kafin su iso kuwa jikin ya sake rikicewa, dan hak'waransa har wani had'ewa suke da juna sosai. Zuwa lokacin hankalin Nadeefah ya kai k'ololuwar tashi, kuka take riris tana rik'e da hannunshi har da tofa masa adduoi. Duk da halin da yake ciki da ya ji motsin bud'e gate sai da ya janye daga jikinta yana cewa " ki je d'akinki kar ki fito sai sun tafi " a d'an shake yayi maganar, da sauri ko ta tashi time d'in har sun shigo cikin harabar gidan.
Gudu-gudu ta nufi part d'in ta har kuma ta shige basu shigo ba, ta k'ofar shiga part d'in shi suka shigo don waiting room a datse yake sai da Umara yayi musu jagora zuwa k'ofar kafin ya juya. Babu kowa a parlorn sai sallama suka dinga jerawa amma ba amsa, zama suka yi a kujera Adnan ya doka masa kira d'agawa yayi yana cewa " ka zo ka kamani in fito". Ok yace ya kalli Dr. Adebayo yana cewa " bari in fito da shi ". Bai jira cewarshi ba ya shiga ciki.
Yanda ya gan shin ba k'aramin tsorata yayi ba ya wani d'ashe kamar mara jini a jikinshi, kamar ba d'azun suka rabu da juna ba. Daurewa yayi ya kamo shi zuwa waje yana ta jera masa sannu, kwantar da shi yayi a 3 sitters nan fa Dr ya fara aikinshi Adnan na gefe.
Ya d'an d'auke shi lokaci mai tsayi yana duba shi, kafin ya kalli Adnan yana cewa " kamar fa ulcer ce take damun sir Burhaan ba komai ba, sai kuma damuwar da take damunshi jinin shi yayi ƙasa shi ke assasa masa jirin nan, so yanzu zan sa masa drip da allura zan kuma tafi da jininshi zuwa gobe ayi test saboda a san maganin da za a d'aura shi a kai, kafin ayi allurar a samu wani abu mai d'an ruwa like tea or yogurt ya d'an sha ".
Adnan ne yace " bari a kira Nadeefah ta kawo masa wani abun" bud'e baki yayi da sauri yana cewa " akwai milcopal a frigde a kitchen ". Mik'ewa yayi ya je kitchen d'in ya d'auko mai d'an sanyi bud'ewa yayi ya zuba masa a cup, bai wani sha da yawa ba ya ajiye sannan suka sake lallab'ashi zuwa cikin d'akin, nan ya d'aura drip d'in ya sagale a jikin hangern da yake yawan rataye suit a jiki duk da ko akwai a cikin closet d'in sa.
Yana masa allura ya fita zuwa parlor ya bar su su biyu, kallonshi Adnan yayi yana cewa " zan bar ka ne na yau, amma zuwa gobe dole ka min bayanin duk abinda ya assasa maka wannan ciwon ". Bud'e idanu yayi yana cewa " kai fa ka cika sa ido wallahi, me ye kuma yake damuna bayan abinda Ade ya gama fad'i....."
Katseshi yayi da cewa " ai ba iya abinda ya faɗi bane ko an gaya maka ban gano silar damuwar taka bane ? Kana da buƙatar iyalin ka tsabar girman kai ne ya hanaka raya sunnah wanda shi ne silar damuwarka ba komai ba, ba ma wannan ba ban san me yake hanaka cin abinci ba alhali matar ka tana ɗaya daga cikin wainda suka fi kowa iya girki ba, wai me kake so ne a duniyar nan Burhaan?". Baki ya bud'e da niyyar dakatar da shi sai yayi saurin tsayar da shi shima ta hanyar d'aga masa hannu yana cewa.
"Kurarinka ba su zasu saka ni in fasa fad'in abinda nayi niyya ba Burhaan, ban tab'a ganin mutum mai irin kafiyarka ba wai a kanka aka fara auren had'i ne or what? A kwanakin baya ina zaton ka amsheta da hannu biyu ashe nayi kuskure toh ni kam kafi k'arfina, sai dai in gaya masu Umma tunda su na san da sauran k'imarsu a idanunka idan ba za ka iya zama da ita ba ka sawwaƙe mata kawai ka daina azabtar musu da 'ya da kai kanka ba don ma ka samu mace mai hankali ko an ce maka ko wace macece za ta d'auki kalar baud'ad'dan halinka? Toh wallahi ko ka natsu ko kuma in gaya musu kowa ya san me kake ciki don ko ba zan zuba idanu akanka ka kashe kanka ba sai da safe Allah ya k'ara sauk'i".
Yana gama fad'in haka ya juya ya bar shi a wurin don da gaske ya hasala da lamarin Burhaan d'in, da idanu ya bi shi kawai bai furta ko uffan ba. Da ya fito maimakon ya fita sai kawai ya nufi parlor, a zaune a kujera ya tarda Nadeefahn da dogon hijabi ta zubawa k'ofarshi idanu alamun dai tana jiransu su tafi ne ta shiga. Ganin fitowarshi ya sa ta taso tana gaisheshi amsawa yayi a d'an sakin fuska yana cewa " ya mai jiki kuma?" Da sauk'i ta furta kawai tana kallonshi cikeda son k'arin bayani, a hankali yace '' uhmm Nadeefah wata alfarma zan nema akan Burhaan don Allah in babu damuwa".
Cewa tayi '' wani irin damuwa Yaa Adnan? Bayan nauyi ne shi da ya rataya a wuya na?" Ajiyar zuciya ya sauke ya san tana da hankali matsalar Burhaan ne don haka ya sassauta murya yana cewa " akan matsalarshi ne, na san cewa kina hak'uri da halayenshi ina son ki k'ara don tabbas ko ba dad'e ko ba jima zaki mori ribar hakan".
"In shaa Allah " ta furta a hankali, nisawa yayi yana cewa " ulcer ne ke damun Burhaan wanda ya samo asali da wasa da abinci da yake yi, sai kuma jinin shi ya sauka sosai yanzu an sa masa drip may be ma ya samu bacci ai kin iya cire ruwa in ya k'are ko?".
Kai ta gyad'a mai bata iya amsawa ba don hankalinta ya tashi, low blood pressure fa shi ne yayi sanadin Babansu Sophie. Cewa yayi " kar ki damu zai samu lafiya soon, in dai ya samu kulawar da ta dace gobe za a kawo masa magani in shaa Allah. Abincinshi kawai za a kula da shi da sauransu na tabbatar zaki iya in ruwan ya k'are zaki maida masa wani, da asuba zan zo kin ji?" Ok tace sai da ya sake kwantar mata da hankali kafin suka jero zuwa parlorn, gaisawa sukayi da Dr. Shima same bayani ya sake mata, ita dai sai gyad'a kai kawai take yi. Ba su suka bar gidan ba sai 11 saura, rufe k'ofar tayi ta zo gabanshi tana mai zura masa idanu yana ta baccin.
Janyo stool tayi ta zauna ta sanya hannunta ta rik'o wanda ke sanye da canulan, a ranta tana adduar samuwar lafiyarshi da gaggawa. A zaune a wurin tana rik'e da hannunshi bacci ya d'auketa, sai kusan 1 am ta bud'e idanu lokacin ruwan ya k'usa k'arewa shafa wuyanta tayi tana mik'ewa canjawa tayi ta sanya masa wani bayan ta k'ara masa gudu kamar yadda ya nuna mata kafin ta koma inda take zaune.
Tana nan a zaune tana kallonshi har kusan biyu da wasu mintuna, toilet d'in shi ta shiga ta d'auro alwala ta fito ta tada sallah. Ta d'an yi raka'oi masu dama a kowace addua tana mai adduar nema masa lafiya, sai after 3 ta tashi lokacin shi ma ruwan da ta sa ya k'are har jini ya fara shiga ciki.
A hankali ta zare masa ruwan ta bar canulan a wurin don an ce za ai masa allura a wurin gobe,sannan ta zauna ba ta san yadda akayi bacci ya kwasheta k'ank'ame da hannunshi ba.
Ba shi ya bud'e idanu ba sai da gari yayi tarwai da shi, shi ma nauyin da yaji a kan hannunshi ne da kuma numfashin mutum dake sauka akan fuskarshi ne ya tursasa masa bud'e idanun. A kan kyakkyawar fuskarta ya d'aura idanun tana zaune akan stool sai dai ta zamo rabin jikinta akan pillown da yake kai, sai hannunta da ta san ya ta k'ank'ame nasa kamar za a k'wace mata shi. Kasa d'auke idanunshi yayi daga kan ta don ta masa kyau sosai da yanda take baccin shi kan shi ya san ita ɗin kyakkyawa ce ta gaban kwatance ga kuma yanda lips ɗin ta da suka yi jawur suke shiga masa ido, kamar wani wanda aka ja da magnet ya samu kan shi da cike gap d'in da ke tsakaninsu yana me d'aura bakinshi kan lips d'in nata cikin ficewar hayyaci........
Majinyaci ya da haka ne? Ko dai ciwon ya tab'a k'walwa ne ka manta wacce ke gabanka? Haaa Nadeefah ce fa Malam duba gabanka da kyau ka gani🌚
Deejasmah ✍🏼