Free chapter · Read without an account

CHAPTER 23 ( DAY AFTER, WELL HIM)

by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)


A haka dai yana tunani har barci ya kwashe shi a wurin, sai kusan asuba ta farka. A kan fuskarshi ta sauke idanu yanda yake bacci kamar ba Islaam ba, akwai wata muguwar kamala da annuri na musamman a tattare da shi. Janye jikinta tayi da k'yar tana son tafiya toilet don fitsari yayi mugun matsanta, k'afarta ta sauke k'asa sai dai ya k'i sauka yayinda wani zafi ya ziyarci k'wak'walwarta.



Mai da k'afarta tayi tana hawaye ga fitsari ga kuma azaba, k'ara saukewa tayi shima same zafi taji amma ta daure don ya matse ta. D'ayan ta k'ara saukewa itama tana rintse idanu, barinsu tayi a haka na minutes sannan ta ja jikinta daga gadon. Ta sauka k'asa sai dai fa k'afafu sun ce ba zasu iya tafiya ta dad'i ba hakan ya sanya ta duk'awa kawai, ta fara rarrafe kamar wata yarinya shi ma tana yi tana hawaye.




A haka har ta iso gaban toilet d'in dafa bango tayi ta samu ta bud'e k'ofar, da rarrafenta ta shige ciki. Zama tayi a kan toilet seat tana k'ok'arin sakin fitsarin da ya tokare mata mara. Sai dai ya k'i fitowa nishi ta dinga yi sannan ta samu ya fito sai dai fitar shi wani mugun azaba ne da shi kamar irin mutum ya ji ciwon nan a saka masa ruwan gishiri akan ciwon.




Haka dai ta daure har ya gama fita tana kuka, tsarki tayi da ruwan d'umi da sai ta sake gane kurenta. Tashi tayi ta je gaban bathtub ruwan zafi ta tara tana durk'ushe a wurin, hannu ta saka taji ruwan ya mata yanda take so. Rigar jikinta ta zare ta yar a wurin ta shige ciki, zafi taji musamman a mazaunanta haka ya sa ta mik'e sirkashi tayi zuwa d'an dai-dai sannan ta sake shiga ta zauna tana maida numfashi.



Yana hucewa ta sake tara wani mai irin zafinshi ta sake zama a ciki, nan kam ta dad'e don har an fara shiga masallacin sallahr asuba kafin ta fito. Tana d'an jin dama-dama riga ta zara yau ko ta su kayan gyaran jikin nata ba ta bi ba, riga kawai ta zura ta koma kan dadduma sallahr ta gabatar ta taso zuwa gado sai lokacin ne ta lura da ba ya kai alamun da tana toilet ne ya fice.


Kwashe zanin gadon tayi duka ta kai su toilet, a washing machine ta saka su sannan ta fito. Wasu brown ta ciro ta shimfid'a kawai ko gyarawa ba tayi ba ta ja blanket ta shige, idanu ta lumshe tana jin cikinta na kukan yunwa dama tun tashinta taji kamar an mata yasa a ciki.




Wutan ta sake kunnawa ta zauna akan gado tana tunanin abinda za ta samu ta ci, don ta san a halinda take ciki ai ba iya girki za tayi ba. Nan idanunta ya fad'a kan trayn da ya bari kan centre table, ajiyar zuciya ta sauke ta tashi ta nufi wurin zama tayi a k'asa ta janyo trayn.



Da sanyi da komai ta sak'umi tsiren ta kora da exotic don tana son d'an d'and'ano a kan harshenta saboda ba ta da wani appetite a bakinta, kamar wacce tayi ciwo sosai d'in nan. Tana samu cikinta ya d'auka ta d'auki ruwan, a side drawernta ta samu diclofenac ta sha ta koma ta kwanta. Babu dad'ewa bacci mai nauyi ya sake kwasarta.


9 dai-dai ya fito cikin shirinshi na kullum, yayi kyau sosai ga wani haske na musamman kan fuskar shi sai k'amshi yake bazawa. Tsayawa yayi a parlor komai yana nan yanda ya bar shi alamun ba ta fito parlorn ba kenan, sai ya doshi d'akinta a kwance ya tardata cikin bargo amma ta canja zanin gado tana sauke numfashi alamun bacci. Matsawa yayi gaban gadon ya zira mata idanu, fuskarta ta nuna rashin jin daɗi a tattare da ita ga bakin nan a tab'e alamun shagwab'a.


Hannu ya kai ya d'aura a goshinta dake tsattsafo zufa alamun zafi yayi mata yawa, nan yaji shi sanyi k'alau babu zafi. Ajiyar zuciya ya sauke a k'asan ranshi hankalinshi ya kwanta ganin ba ta wani hali don ya zata za ta girgiza ko ta kwanta ciwo sosai, amma ga mamakin shi ta kula da kan ta da kyau ga shi nan har ta samu bacci. Wani girmanta ne ya k'aru a idanunshi yana son juriya bai son raki da sakalta a gefe guda kuma yana jinjina k'arfin halinta kamar ba Lelen Hajjah mai komai sai an mata ba, bin d'akin yayi da idanu nan ya ga alamun har naman da ya bari ta ci kayanta. Murmushi ya saki ya k'ara mata AC, hannunta ya sunkuya yai kissing kafin ya fita motarshi ya ja zuwa office yana jin shi wasai babu damuwa ko d'aya a ranshi.




Ba ita ta farka ba sai to 10 bin d'akin da kallo, babu alamun ya sake shigowa cikinsa sai dai k'amshinsa da take ji wanda ba ta raba d'ayan biyu kwanan da yayi ne don har jikinta ya kama irin k'amshinshi takeyi. Yunk'urawa tayi da k'arfinta za ta tashi nan taji sabon azaba yana ziyartarta kamar ma ya so ya fi na d'azu, cije baki tayi tana shishita kamar wacce taci yaji.




Bud'e k'afafun tayi taji sun sandare, gefe da gefen tsakiyar cinyoyinta sun wani rik'e kamar wacce aka yanka namar wurin. 'Yau ake yinta' ta furta tana mai yarfa hannu hawaye yana zubo mata, jin har da bayanta da k'afafunta a ciwon shi ko can ai ba a magana. 




"Ba na gasa jikina ba da asuba?" Ta tambaya kan ta a fili tana cuna baki, 'yoh dama gasa jiki tayi ko tsaka tsami? Ana gasa jiki da ruwan zafi ta sirke ruwa tana cewa ta gasa jiki lallai ma Lele shugabar masu gashi ta k'asa?'. Ba ta da mai ba ta amsa amma ita fa a nata tunanin tayi abinda ya kamata tayiwa jikinta ne, amma yanzu ga shi nan kamar ba ta yi ba sai azaba ne ya taso mata fiyeda d'azu d'in ma. Shiru tayi tana tunanin yanda za tayi, don ba zai yiwu ta yini kwance ba ga kuma tsamin jiki yana tasowa kamar wacce aka yanka. 



Jarumta ta sake ara ta sauka daga gadon, yanzu kam ta d'an dad'e a tsayen da kuma bin bango ta kai kanta bayin tana tafiya tana jan hanci. Shiga ciki tayi ta sake had'a wani ruwan mai zafi ta had'a tana tuna maganar Hajjah a ran da za a kawota gidan miji, "ban da sake da ruwan zafi " kuma fa tana son ruwa mai d'an zafi ba sosai ba a kuma fashion school an gaya musu illar ruwan zafi sosai ga jiki musamman can wajen.  Sai dai a yau ta san ba ta da mai taimakonta face shi ruwan zafin tunda dai a wannan yanayin ta tabbatar su kansu sinadaran wajen  sun yi balaguro saboda azaba, tuno maganar Hajjah ya sanya ta tuna wani gari da mai da ta ba su tace su na sawa a ruwa in zasu shiga duk da ba ta gaya musu na menene ba ita dai ba ta tab'a amfani da nata ba saboda tsab'ar tsarinta.



A kit ɗin wankan ta ta ciro powdern a wata roba mai murfi shi ma man haka, a gaban bathtub d'in ta tsaya zubawa tayi d'an dai-dai sannan ta shige ciki. Zafin ruwan ya ratsa har kwanyarta bombom d'inta ya sake d'auka, "Hajjahnah!" da bata samu daman kira a daren jiya ba ne yau ta kwad'awa kiran tana fitowa daga ruwan. 



Hannu ta sake yarfewa ta daure ta sake komawa ciki, fitowa tayi d'an sama kad'an yanda ruwan yake d'an shiga jikinta ba sosai ba. Nishi tayi mai k'arfi tana sake shigewa completely, hannu ta kai ta dafe bakinta tana sakin ihu a hankali. K'afafunta ta bud'e da kyau tana kukanta ita d'aya, tana ciki har ruwan ya huce juyeshi tayi ta sake tara wani. A yanzu kam ba ta ji zafi kamar d'azu ba don ruwan yana gama ratsa jikinta har wani rahama taji kamar an zare mata k'aya, wanna tayi da kyau ta fito man ta shafa a wurin da wata abun shafawa da yake cikin rubbern kafin ta d'aura towel ta fito.




Ta d'an samu sauk'in jikinta sai dai kuma jin ta da take fayau, ga yunwa tana ji ga rashin taste. Zama tayi ta shirya cikin kaya marasa nauyi short skirt pwanda da kad'an ya wuce guiwarta, sai crop top mahad'in skirt d'in ba ta sa hula a kan ba sai ma tufka biyu da tayi masa bayan ta busar da shi. Turare ta feshe jikinta ta d'auko trayn jiya da wayarta ta fito, ajiyewa tayi tana tunanin me zata yi sai ta zauna a wata doguwar kujera a kitchen d'in tea ta fara had'awa ta sha sannan ta fara k'ok'arin dahuwar peppered soup had'in amaren gata tunda ita dai Umma ta kawo mata nata tun washe garin aure so na yau dai sai dai tayi abinta da kanta.




Yau a zaune tayi aikin don ba ta iya duk'awa, ga shi ba zata iya barin gidan babu shara ba. Dabara ce ta fad'o mata da sauri ta d'aga wayarta ta kirayi Suliem, bugu biyu ta d'aga tana cewa " yau dai ba inda zan zo Allah Lele, bacci zan rama yaron nan naki bai barina inyi bacci".




Cikin disasshiyar muryarta tace " nima ba inda zan iya zuwa ai ". Da sauri tace " ya naji muryarki kamar mara lafiya me ya faru?". D'an tab'e baki tayi ta kasa magana sai shesshek'a takeyi, d'an dariya tayi mai sauti tana cewa " aiki fa ya kama gwari kadara sai kallo, dama ke ya lafiyar giwa ciwo kin masa kuka balle kuma an tab'a ki".



"Ai duk ke kika ja min, na gaya miki ban shirya ba yanzu ga shi nan kin sa an kusa kasheni ".




"Aiyyiriri, ba ki shirya ba keh? Dama sai kin shirya kafin ki sauke hak'kin da ubangiji ya rataya a wuyanki? Ai party ma ya kamata mu yi, Lele an zama mace". Ta furta kamar ba ita ta marairaice voice ba d'azu.



"Ba wata sweetheart a nan tunda celebrating kike yi na kusa mutuwa, sai anjima".



"Ke d'iyar k'warai yi hak'uri kar ki kaini inda Allah bai kaini ba, ai dole in damu in kika ji ciwo abinda kawai nake murna shine kin ba wa Ya Islaam mafi darajar kyauta kuma shi ne sahun farko na mallakarshi yanzu yana ina?".





Tura baki tayi tace " uhmmm, na ko ji jiki. Ya fita office ni d'aya ce a gida". 



Rik'e baki tayi tana mai mamakin taurin zuciyar Burhaan, ka sille yarinyar mutane amma ka tsallake ka bar ta? Sai kuma wata zuciyar tace " likita ne fa kar ki manta fa, wa ya sani ko ya riga ya bata kulawa kafin ya fita rashin kirkin na shi bai kai na barin matarahi a gida a halin ciwo kuma tana da buƙatar shi ba". Tab'e baki tayi tana cewa " atleast da ya zauna da ita dai, ko da na yau kawai ne ",a k'asan ran ta a fili kuma tace.


"Allah sarki, sannu da k'ok'ari Allah ya k'ara sauk'i, ki tabbatar kin huta ko na kwana uku ne haka".




"Ai dole na, ki d'an ara min ƴar aikin ki mana ta d'an min shara ban iya duk'awa wallah".



" Baraka? Bari in turo miki ita amma kin samu kin shiga ruwan zafi ko? Ban da dai raki na san halinki ".



"Na shiga ai, ba zanyi wasa da lafiyata ba kin sani ".



Ok tace suka kashe wayar.



Ba suyi ko 15 minutes ba yarinyar ta iso, ba ta fi 16 ba yarinyar akwai dai tsafta ga ta shiru-shiru ba irin masu rawan kan nan ba ne. Gaisheta tayi ta amsa da kulawa, sa wa tayi ta d'auko kayan sharar daga toilet d'in parlorn ta nunnuna mata amfanin komai daga parlornta ta fara gyaran sai living room, kitchen da waiting room. Aiki ta kama ita kuma ta wuce ciki, lallab'awa tayi ta gyara gadon da kyau ta wanke toilet tayi shara da mopping ta sa turare ta fito lokacin har ta gama da parlorn.



Ba ta wani d'auki time ba ta gyara koina, godiya tayi mata ta kawo kud'i ta dank'a mata a hannu. K'in karb'a ta so yi sai da Lelen ta dage kafin ta amsa tana ta godiya, ta kuma zuba mata peppered soup d'in da tayi ta wuce da shi.



Zama tayi bayan fitarta ta saka peppered soup d'in ta na shan kayanta, sai shishitan yaji take yi don ta cika yaji ba laifi sosai ta sha ta kora da abu mai sanyi ta koma ta sake kwanciya. Bacci ya fara d'ibanta kira ya shigo wayarta, d'agawa tayi ganin sunan Hajjah na yawo akan screen d'inta.



Karawa tayi a kunne cikeda shagwab'a ta amsa sallamar Hajjahn, cewa tayi " su Lele har an fara mantawa da Meram ko?". Lumshe idanu tayi ta bud'e tana cewa " ni ai ban isa in manta da ke ba, ai in ba Merama babu ni ". Murmushi ta saki tana cewa " gashi nan kuwa, yau har rana ta b'ullo tana shirin takewa babu kiranki a wayata".




Sake shagwab'e murya tayi " haba Hajjahta ban mance ki ba, yau na bari sai bayan zuhr ne sai in kiraki yakike? Ya gidan?".



"Ina lafiya, gida ma haka ke fa? Babu wata matsala dai ko?".



"Babu wata matsala Alhamdulillah, kin ganni nan ma bacci nake son yi kafin Zuhr ".



"Bacci kuma Lele? Baki fita ba ne halan?".


"Uhmm na gaji ne Hajjah shi ne nake so in d'an huta ". Ta furta tana tura baki, cewa tayi " sai kace wani aikin a zo a gani kike yi a office d'in, d'iyar nan rakinki fa yayi yawa haihuwa zaki yi ".



"Ku wai Hajjah da anyi magana sai ku kawo haihuwa ku yita tsorata mutum haka kawai, Álà nàngàrò ( saboda Allah fa) ".



Dariya ta sanya jin yanda tayi maganar tace " ai ko kin k'i sai kin haihun nan sai dai Allah na tuba in baki da rabonta ba ma fata nuri( my child)".




"Toh a bari lokacin yayi dai (Zau yaye) Please".



"Allah ya kaimu lokacin, Naran Burhaan? (Ina Burhaan fa?) Klewa nju? ( ya na lafiya?)".


"Aaà kl3wanju ( eh yana lafiya)".


"Álà kámbò ( Masha Allah), Allah kad'ai ya san dad'in da nakeji yanzu da na ga hankalinki ya kwanta a gidan mijinki Lele ban da wani burin da yafi haka. Allah ya sake shiga lamarinku ya daidaita ku ya kuma yi muku albarka".



"Ameen Hajjahta" ta furta da murmushi mai fad'i, d'an hira suka sake yi akan maganar rabonda za tayi d'in don an fara siyo kayan hatsin kuma gidan Hajjah aka ajiye.


Lissafin kasafin ta fara mata ta d'aura da cewa " zan ma zo gidan ai may be weekend in shaa Allah".




"Álà kə̀léwà Lele ( Allah ya kaimu) bari in barki kiyi barcin ko?".



"Toh Hajjah dubdunowan klewan ( ki huta lafiya)".



"Ayiye Say tusha ( tohm,sai anjima)".


"Yo" ta furta suna katse wayar, komawa tayi ta kwanta kawai ba ta wani jima ba baccin ya sake kwasheta.


Haka ta yini ba aikin fari babu na bak'i, sai bin wuri take yi kamar ruwa sallah yake tadata. Ta gasa jikinta sosai har ji tayi ta d'an samu dama zafin wurin ya rage ba laifi, ko girki ba tayi ba sai indomie da ta dafa ma kanta wurin la'asar. 



Lokaci-lokaci ta kan amsa kira daga mutane, har da Ummu ma da kusan k'orafin Hajjah tayi mata ita kuma tana avoiding ta kirasu ne su b'aro halinda take ciki. A kuma kaf kiran da akayi mata babu na Burhaan ko misscall balle ya nuna ya damu ya san halinda take ciki, har ta so saka damuwa a ranta sai kuma ta cire ma kanta tunda ta san zai iya yin abinda ya fi haka gwara ta daina sa abun a ranta ya dameta da yawa.


Ta gefenshi kuwa yinin ranar tana ran shi, har waya ya d'aga da niyyar kiranta sai kuma rashin abun cewa ya hanashi. Kun san mutumin da pride kamar yahudawan da, duk da ya san kyautuwar kiran nata amma kuma in ya kirata gani yake kamar girmanshi ya zube ne a idanunta. Zubewar girma na nawa kuma Malam, bayan ta riga ta san kalar girman? Uhmm zaka yi bayani ne mu je dai zuwa.




5 dai-dai ya dawo gidan jaka kawai ya ajiye yayi wa parlorn tsinke, a kwance akan kujera ya tarda ta sai k'amshi ke tashi. Tsayawa yayi yana kallonta ta canja kaya zuwa wata spaghetti hand 3quater gown, sai ta d'aura vintage scarp fari a kanta fuskarta ba ko makeup tayi fayau da ita.




Waigowa tayi ta kalleshi hakan ya sa shi saita kanshi ya shigo cikin parlorn da kyau, zama yayi a gefenta yana d'an sake fuska. D'an yatsina fuska tayi tana cewa " sannu da dawowa " ta kawar da fuska alamun tana jin haushinshi, ko ya kula da hakan yace "yawwa, ya jikinki?".




"Alhamdulillah" kawai ta furta ba tareda ta dubeshi ba, ganin yanda tayi d'in ne ya sashi kallonta yana nazari. Sai yayi tunanin akwai inda yake mata ciwo ne hakan ya sa yace " ba dai inda yake miki ciwo dai ko?".


Ajiyar zuciya ta sauke cikeda shagwab'a tace" duka jikina, ko ina duka ciwo yake min ". Cewa yayi " so sorry, kina buƙatar massage zan kula da hakan zuwa anjima hope kin ci abinci ?". Kumbura baki tayi a k'asan ranta tana cewa " Massage! Massage! Dama massage abinda ya kamaci matar da ta baka kanta ta raya daren farkonku? Bai ko kula da ita ba haka ya barta ita kaɗai daga safe zuwa yamma ba kira a waya ba ko kalmar yabo da godiya balle kuma wasu kalamai masu daɗi har a gangara ga kyaututtuka da amaren novels kan samu daga mazajensu? Sai ma tambayar ta yake ko ta ci abinci, ba sai da cikakkiyar lafiya ake cin abincin ba? ( ke ma dai kin san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ki ma godewa Allah da massage d'in Madam).




Sake maimaita tambayar yayi, a hankali ta rufe idanu tana cewa " ban da appetite, ko ma ina da shi ban da k'arfin yin girki ".



"Ba kuma zaki iya yin order ba ko? Yanzu kina nufin yau gabad'aya baki ci wani abu ba?". Da d'an fad'a ya tambaya, k'in amsa shi tayi tana kawar da kanta. Ji k'arfin hali waj b'arawo da sallama " kina ji na fa, Nadeefah!!".


A d'an tsorace tace " na dafa indomie na ci". Tsaki ya saki yana cewa " indomie abinci ne? Ya miki kyau ai " daga haka ya tashi ya nufi d'akinshi a ranshi yana mai mitar ' samun wuri ne ma irin na yaran nan, in ba samun wuri ba amare nawa ne ke girki a washe garin tarewarsu gidan mijinsu. Kuma ba wai ba su kwanta da su bane infact duk wani abu da masu aure ke yi a daren farkon su sun yi har fiye kuma matan basu bar su da yunwa ba amma ita sai wani yauk'i take masa da iyayi don ya kwanta da ita kawai ko an gaya mata don yana sakin mata fuska ya canja daga Burhaan d'in da yake ne?'. ( Sannu Malam Zalimu da k'ok'ari, dole ai a gaisheka Mr Burhaan ga mari ga tsinka jaka).




Da idanu ta rakashi tana kuma tab'e baki "wannan binbinin da yake ai ba na Allah da annabi ba ne, so yake da dare ya sake zuwa ya taushe ni ban ko yarda wallahi sai na warke haka kawai in bari ya kashe ni shi sa ba zafina ya sani ba. Harda wani tambayar na ci abinci, ban ci d'in ba cikina ne ai " ta furta har da murgud'a baki ( Nadeefah case ashe ba su Tayyib kawai ake wa tsiwar ba).





Wanka yayi yana ta kumbure-kumbure yayinda soft zuciyarshi take sake bijiro masa da Nadeefah da kuma kamata da yayi ya nemo musu abinci musamman ma shi da tun safe tea ne kawai a cikinshi. Fitowa yayi ya shirya cikin casual wears, car keys ya d'auka ya fita daga gidan. Eatery ya samu yayi musu order har da pepper soup na kifi dan ya lura tana son kifi, sannan ya juyo zuwa gida. A inda ya barta a nan ya tarda ta ajiyewa yayi ba tareda yayi mata magana ba yayi wucewarshi, lumshe idanu tayi tana murmushi ashe ya san abinda ya kamata.



Ko motsawa ba tayi daga inda take ba tunda ba ta da yunwa, sai da aka kira sallah kafin ta kwashi ledan ta wuce ciki. Sai da tayi sallah kafin ta bud'e abincin fried rice ce da chicken, tab'e baki tayi ta rufe tana matsarwa gefe. D'ayan ta bud'e ita kuma semo ce da miya guda biyu ta yauk'i da kuma vegetable kowanne da nama a ciki, sai peppered soup na kifi.



Semon ta ci abinta da vegetable soup d'in don dama shi take marmari, bakinta ba taste in ba tuwo ba ba zata ji dad'in komai ba. Ba taci da wani yawa ba ta ajiye ta ja kifinta gabanta, tas ta cinye ta sha soup d'in don yayi mata dad'i kuma anyi spicing d'in shi da kyau.



Toilet ta shiga ta sake shiga cikin ruwa na kusan 15 minutes tayi brush da alwala ta fito, lokacin an shiga masallacin sallahr ishai. Pj yau ta saka mai gajeren wando, ta sanya hijab ta gabatar da sallahr tana idarwa ta yi azkar da lazumin da ta saba kafin ta nufi gado ta kwanta. 




Kusan 30 minutes da Kwanciyarta ta ji an bud'e d'akin an shigo, switch ya kunna haske ya gauraye d'akin gabad'aya. Kallonshi tayi yana sanye da PJ hannunshi d'auke da wani kit mai d'an girma da kuma towel a kafad'arshi. Cewa yayi " zaki kwanta kin manta da massage d'in kenan?".



Tunzura baki tayi sama tana cewa " ni fa na ma ji sauk'i yanzu, ba ma sai anyi masssage ba ".


"Wasa ma kenan yarinya, gwara ma ki taso ko a gadon da za ayi ne?".


"Yaa ai anayi a bed d'in".



"Ba massage za'ayi ba kenan? Get up my friend".


Ji tayi kamar ta d'aura hannu aka ta fashe da kuka, don tana tsoron wannan massage da ya nace mawa haka kawai a b'ige da massage a kasheta. Ganin yanda yake yi da baki alamun 'yan masifa na cinshi ya sa ta tashi daga gadon, hanyar toilet ya nufa ta bishi a baya. Towel ya mik'o mata ta d'aura wai, shi kuma ya fita ya bata wuri.



D'aurawan tayi tana kallon ikon Allah, ba ta cire wandonta ba amma knocking yayi ya shigo wata hula ya bata ta rufe gashinta ta sai ya ciro wata lanƙwasassiyar katako a cikin kit d'in shi. Bud'eta yayi abun mamaki sai ta ga ta koma ƙaramar kujera mara k'arfi, ta san kayan massage da yawa a spa tunda suna yin shi musamman ma kafaɗa da na gadon baya amma ba ta san miye haɗin wannan da ciwon jikin da take fama da shi? Na ta ido.



Kwanciya tayi kamar yadda yayi mata nuni akan cikinta, shi kuma ya fara aikinshi cikeda k'warewa. Daga kafad'unta ya fara yana massaging na su ta sigar lallashi yana kuma shafe su da mai, kowace gab'a idan yaje sai ya bata kulawa yanda ya dace kafin ya matsa gaba.

Tun ba ayi nisa ba ta fara jin jikinta yana sakewa, har wani bacci-bacci take ji sai lumshe idanu take yi tunda take a spa ba a tab'a mata massage irin wannan ba. Da farko kamar abun arzik'i sai dai kuma da tafiya tayi tafiya sai massage ya canja alƙibla daga hagu aka koma dama, don juyo da ita yayi kawai ya rungumeta ya had'e bakinta. Ba ta ko turje ba don itama tun farawar take jin yanda taɓawar shi suke saka ta jin wani iri kafin kace me ta biye masa ita ma tana nuna mai colorn Lelen da bai tab'a sani ba, sai ji sukayi kujerar ta b'alle don dama ba wata shahararriyar k'wari ke gareta ba akan bayanta ta fad'a ga shi a samanta "ouch" ta furta tana zare bakinta daga nasa. Shi kam bai ko kula ba don yayi nisa sai ma kinkimar kayanshi da yayi zuwa bedroom cikin rufewar ido............




One word for Burhaan pilis

Ban da zagi fa guys🥺

Deejasmah ✍🏼

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.