Free chapter · Read without an account
46
Ana idar da sallar Juma’ah a babban masallacin masarauta aka ɗaura auren Muhammad Habib Lateef da Rumana Hashim Lateef akan sadaki naira miliyan ɗaya.
Ɗaurin auren ya kasance irin wanda masarauta ba su cika yin irinsa ba sai a manyan lokuta. Tun safe masallacin ya cika da manyan mutane. Attajirai, gwamnoni, sanatoci, sarakuna, hafsoshin soja, manyan ƴan siyasa da masu faɗa aji daga ciki da wajen ƙasar nan. Duk wanda sunansa ke amsawa a Nigeria, Mai Martaba ya gayyace shi. Kuma abin mamaki, kusan babu wanda ya turo wakilinsa, mafi yawansu da kansu suka halarta domin girmama masarautar da alaƙar da ke tsakaninsu da sarkin.
Duk girman masallacin fada, sai da jama’a suka cika cikinsa har wajensa. Motoci na alfarma ne suka yi layi tun daga babban gate na masarautar har wajen parking. Masu tsaro na musamman suna tsaye ta ko’ina, yayin da masu aikin fada ke kai-komo cikin shiga irin ta sarauta.
Turaki yana zaune kusa da mahaifinsa cikin farar babban riga mai matuƙar kyau da alfarma, babu wani rawani a kansa sai dakakkiyar hular da ya murza, wadda a farko ma bai saka ba har sai da ya zo nan ɗin Baffa ya ɗauko tasa ya saka masa, domin ba wai a hayyacinsa yake ba, shi a halin yanzu kamar robot yake, sai yadda aka yi da shi. Duk da irin shiga da kamalarsa, fuskarsa gaba ɗaya babu walwala da annuri ko kaɗan, tamkar ma ba shi ne ake ɗaura wa aure ba.
Babu ɗaya daga cikin abokansa a kusa da shi. Bello ma da ya shirya dawowa a yau ya biyo jirgin safe, Maama ta hana shi zuwa saboda tsananin ɓacin ran da take ciki.
Gaba ɗaya hankalin Turaki ba a wajen bikin yake ba. Duk irin tarin hayaniyar jama’a da surutun farin ciki da ake ta yi, tasa zuciyarsa na can wani wuri daban.
Fillo! Ita kawai yake tunani, tunanin halin da take ciki da kuma inda take. Ta ina zai fara nemanta? Ji yake kamar komai ya tsaya masa cak.
Haka aka ɗaura auren cikin cikar al’ada da girmamawa. Aka yi addu’o’i masu yawa, mutane na ta addu'a da fatan alkhairi.
Bayan an tashi daga masallaci aka wuce reception. Reception ɗin da ya kasance irin na gidan sarauta na gaske. Wani katafaren filin taro da aka ƙawata da fararen tents masu tsada, kujeru da tebura masu walƙiya, ga flower arrangements a ko’ina. Masu hidima na ta kai-komo cikin uniform iri ɗaya.
Manyan mutane suna ta shiga suna gaisawa da Mai Martaba da Alƙali Dikko, ana ta ɗaukar hotuna, ana ta yi wa amarya da ango addu’a. Da aka dawo daga reception kuma aka koma cikin masarautar Mai Martaba.
Turaki dai tun daga lokacin yake ƙoƙarin samun hanyar zillewa ya koma gida, amma abin ya gagara. Baffa yaƙi sakin hannunsa sam. Ai ba sai wani ya faɗa masa ba, yana da tabbacin Hajiya Madina ta yi masa huɗubar da ana ɗaura auren ya nemi ya hanya ya ɓace, don sauran yaran ma ga su nan gaba ɗaya bai gansu ba. Shi kuma a yau ɗin jinsa ya ke cike da wani irin farin ciki da alfahari ga ɗansa nasa, irin farin ciki da da alfaharin da bai taɓa riskar kansa a ciki ba a tsawon rayuwarsa.
Duk inda suka tsaya gaisuwa sai ya jawo Turaki gaba ya ce da murmushi mai faɗi,"Ai Shi ne babban ɗan nawa, ku sa masa albarka."
Haka yake ta yawo da shi yana gabatar da shi ga jama’arsa da jama’ar Mai Martaba. Har Turakin da kansa sai da ya fara jin tausayin mahaifinsa, Saboda irin yadda ya ga tsantsar farin cikin da Baffa yake ciki har bakinsa ya ƙi rufuwa gaba ɗaya.
Bayan sun dawo cikin fada ne Turaki ya sami ɗan salama. A lokacin mafi yawancin waɗanda suka rage duk dangin gida ne da makusanta na musamman.
A babban falon mai martaba suka zauna. Mai Martaba na zaune akan katafaren royal chair, cikin shiga irin ta sarauta da ta cika idon mai kallo. A gefensa na dama Hakimi ne zaune cikin alkyabba mai tsada da rawani. A hagu kuma Baffa ne zaune cikin shiga ta alfarma, fuskarsa ta gaza ɓoye farin cikin da yake ciki game da wannan rana ta auren Turaki.
Falmata na zaune itama da nata bayyana farin cikin, Boɗejo kuwa ta wani hakimci ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin alkyabba mai ƙallin bala'i, sai ɗaukar idon jama'a take, bakinta yaƙi rufewa, haƙwaran makka ɗinta guda huɗu duk a waje. Duk wanda ya kalleta sai ya san yau ɗin ba ƙaramin farin ciki take ciki ba.
Mai Martaba ne ya fara doguwar nasiha ga amarya da ango akan zaman aure, bayan ya gama ya damƙa amanarta a hannun mijinta, ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba. Bayan ya gama Hajiya Boɗejo ta ɗora da nata, ta yi doguwar nasihar aure da babu wanda jikinsa bai amsa ba a wajen hatta Turaki, daga ƙarshe kuma sai ta fashe da kuka tana zuba musu adu'oi iri-iri.
Bayan ta gama Hakimi ma yay nasa, bayan ya gama Baffa yay musu tasa, sai a sanda yake yi musu nasihar ne kawai Turaki ji yay hawaye na neman ya sauko masa, daga ƙarshe Inna Falmata ma ta yi nata.
Bayan nan kuma aka rarraba ƙur'ani da littafan addu'oi. Daga nan kuma aka ɗauki amarya aka yi cikin gida da ita ana batun gobe idan Allah ya kaimu za'a shiga sauran hidiman taron biki.
Turaki na fitowa daga fada ya fice bai bari sun haɗu da Baffa ba, iyakar kyau dai ya yi kyau kowa ya gansa yaga sabon ango, amma sam babu wannan annurin na farin ciki a saman fuskarsa.
Gimbiya Ilham kam tun da ta yi ƙoƙarin kama hannun Turaki ta ji yanda ya make hannunta jikinta ya yi sanyi, musamman da ta kalla fuskarsa taga ya murtuke kamar wanda aka yowa aiken mutuwa, ka ce bai taɓa dariya ba a duniyarsa, kamar ba wannan Hammah Turakin ba da suke ɗasawa da shi.
Turaki na isa gida Hajiya Madina tasa key ta kulle side ɗinta don bata ma so wasu ƴan bani ka iya ɗin suzo mata, ko kuma Baffa ya dawo ya ce zai shigo, ganinsa ma a yau ita ba ta shiryawa ba.
Hakan ko sai da ta faru, mutane suka dinga zuwa gidan suna juyawa, Mai Gadi na faɗa musu abin da Hajiya Madina ta ce masa na cewar basa nan, a same su a can masarautar.
To haka dai ranar Hajiya Madina da yaranta suka yini cikin ɓacin rai, iyakar yin Baffa ya gana da matarsa da yaransa Hajiya Madina ta toshe duk wannan ƙofar, sai haƙura ya yi dole.
Ko a washe gari sai gidan Hakimi ya tafi yay breakfast don shima irin Turaki ne bai iya cin abincin kowanne wuri ba.
Kuma a ranar da daddare Boɗejo ta zo ta tayar da wuta a gidan, kamar zata cinye su saboda masifa akan Turaki sai ya je Dinner, har da cewa,"Ai ni Madina ban san ke fitinanniya ba ce sai yanzu, ashe kin ma fi Fulani Azima haɗari, to wallahi dai akan auren jikana da jikata zan mummunan ɓata miki rai a gidan nan".
Maama dai ɗaga kai bata yi ta kalla Boɗejo ba balle ta tanka mata, ta gama zazzaga masifarta da yaɓa magangunta.
Boɗejo ta tasa ƙeyar Turaki a gaba ta ce,"Wuce motar Nasiruddeen na waje su yi maka rakiya, in an hana abokanka zuwa ai kana da ƴan'uwa".
Sannan ta juya kan su Zaytuna ta ce,"Ku kuma ku wuce mu je, haka kawai za'a tusa muku baƙin hali a zuciyarku, tsakani da Allah mene abin baƙin ciki a wannan aure banda ma dai zuciyar mutum akwai sharri. to ku yi gaba mu je ba sai kunyi wata kwalliya ba, idan ban isa da wasu ba ku ai na isa da ku. Ƙulla auren zumunci kuma yanzu na fara, kuma inga uban da zai sa Turaki ƙaro aure, don na ji ana ƙishin ƙishin ɗin haka, shege ka fasa".
Haka ta saka su a gaba har Khalil da su Samha da suka dawo a yau suka wuce suka tafi. Wajen dinner dai iyakar haɗuwa ya haɗu, amarya da ango sun haska guri, amma ko kaɗan fuskar ango bata murmusa ba, haka dai suka bayar da kunya a wajen, suka yarfa Ilham.
Kuma fuskar ango kaɗai zaka kalla ka hasko tsantsar rashin son auren a tare da shi, Ilham da ƙyar ta iya controlling hawayenta ta dinƙa yaƙen ƙarya, saboda gaba ɗaya ta fahimci Turaki ba auren ne baya so kaɗai ba, ita kanta ba sonta yake ba.
Bata tabbatar da hakan ba sai after an tashi daga dinner sun zo shiga mota ya ce,"Ki bar cusa kanki gare ni, domin ni ba sonki nake ba, cusa min ke aka yi. Idan kuma wancan son kike tunani har kika iya amfani da shi kika sa aka ƙulla wannan auren, to kin yi babban kuskure, domin ni son ƙanwa nake miki kawai. And ki san da cewar baki da matsuguni a zuciyar Turaki har abada, domin already wata da ta fiki komai ta cike wannan gurbin".
Wannan maganganun nasa yasa tayi kuka ta gode Allah a wannan daren, kuma sai ta dasa zarginta akan ƙawarta Gimbiya Aisha.
Washe gari ma kamar ba zata je Cocktail party ba amma haka dole ta je, shima kuma ta ga abin da yafi na jiya a wurin Turaki, don ya nunawa kowa ba auren so suka yi ba.
Ranar lahadi da za'a kaita tamkar ta shiɗe haka ta ji, tunanin ta inda zata fara zama da shi kawai take yi, Mai Martaba da Fulani Azima su suka kaita gidan anan Estate ɗin su Turaki, daga gidansa zuwa na su babu nisa, gidan ya gaji da haɗuwa kamar a turai, bai san sanda Baffa ma ya gina gidan ba, ban da ɗazu da yake ce masa ga key ɗin gidanka.
Shima Turaki Baffa da Maama ne suka masa rakiya, kuma banda cewar ɗanta za'a kai, shima wanda take tausayi da tsananin so, babu abin da zai sa ta je. ko kula Baffa bata yi ba har suka je, yana ta janta da hira ta yi banza da shi sai Turaki da take kulawa, tana faɗa masa ya cire damuwa saboda yanda duk ya rame.
A can gidan Amarya da Ango ma Hajiya Madina kallon inda Mai Martaba yake bata yi ba balle wata Fulani Azima, bata san ita ma Fulanin ba so take ba. Haka suka gama yiwa ma'auratan nasiha da addu'o'i ma su tarin yawa, sannan suka tafi su bar yaran na su.
Kamar yadda sunnah ta koyar, Turaki ya yi nafila tare da matarsa. Bayan sun idar da sallar ne ya ɗora hannunsa akan kanta ya yi mata addu’a cikin nutsuwa da saukar da murya, da kansa ya ɗauko tray na banƙararriyar kazar da Boɗejo ke faɗa masa an tanadar musu tana kitchen, ya kawo wa Ilham ya ajiye mata. Ilham ɗin ce kawai ta ci, amma shi ko ƙamshin ma bai ji ya tsarga ta hancinsa ba. Cikinsa a cushe yake da tunani da damuwa fiye da yadda zai iya misaltawa.
Tana cin naman ya tashi a hankali ya fice daga ɗakin zuwa parlour, ya barta zaune ita ɗaya. Daga can babban cushion ya zauna, ko hannayensa bai iya cirewa duka daga cikin aljihu ba, kansa a sunkuye yana ta kallon ƙasan carpet, tamkar anan zai ga amsar tarin tambyoyin da ke cikin kansa.
Tunanin Fullo ne duk ya sake cika masa zuciya gaba ɗaya. Ina take yanzu? Tana cikin wane hali? Tana cin abinci? A tare da wa take? Tana Ray?
Da sauri ya damƙe kansa tare da rumtse ido sosai, don ko kusa ba ya so ma ya yi tunanin wai tana raye ko ta mutu ne.
Allah kaɗai yasan irin ciwon da yake ji a ƙirjinsa. Ya jima zaune a wajen cikin shiru, sai motsin AC da ƙamshin turaren gidan kaɗai ke busawa yana shiga ta ko ina.
Sai can dare wajen ƙarfe uku tukunna ya tuna cewa fa aure aka yi masa… kuma yarinyar na can ita ɗaya a ɗaki.
A hankali ya sake lumshe idonsa yana jin idanun na ƙara yi masa nauyi, yana buƙatar ya rufe idonsa ya rumtsa amma bai isa ba, baccin ya ƙaura ce. Tsawon wasu mintuna tukunna ya buɗe idonsa ya sauke kallonsa akan hanyar da zata sada shi da bedroom ɗin da ya fito ya barta.
Ko kaɗan baya jin yana ƙaunar ganin Ilham a kusa da shi. Baya jin zai iya haɗa jikinsa da nata su kwana akan shimfiɗa ɗaya. Amma kuma ba shi da wani zaɓi. Ba shi da wata hanya face bin abin da addini ya koyar.
Shi mutum ne mai ilimi kuma mai tsoron Allah. Duk da halin da zuciyarsa take ciki, yana sane da cewa aure ibada ne, kuma yana sane da irin haƙƙoƙin da addini ya ɗora masa akan matarsa a daren farko.
Saboda haka ya ƙudurta cewa ba zai bari ɓacin ransa ko rashin son da yake ji ya sa ya kaucewa koyarwar addini ko sunnar Ma’aiki SAW ba.
Sai da ya kai ruwa rana wajen kokawa da zuciyarsa, kafin ta tsayar masa da matsaya akan babu maganar ƙauracewa shimfiɗarta a yau.
A wannan daren… Turaki ya maida Ilham cikakkiyar mace. Ba dan ya so ba, kuma ba dan yana farin ciki ba, kuma ba dan ya yi farin ciki da samun budurcinta ba.
Haka kuma rashin sonta bai sa ya zalunceta ba wajen kusantarta, ya tafiyar da ita a hankali ta yanda yasan ba zai ƙuntata mata ba, sai dai hakan ba shi ya hana Ilham kuka sosai ba a wannan daren.
Ba wai saboda zafi kaɗai ba. Sai saboda zafin da take ji a zuciyarta. Ta kasa mantawa da kalamansa, Kalaman da suka tabbatar mata cewa tana tare da namijin da gangar jikinsa ta aura. Zuciyarsa tana wajen wata Macen daban.
Wacece ita?
A ina take?
Me tafi ta da shi da har tafi ta samun gurbin zama a zuciyar Turaki?
Ko saboda haka ne dama a ɗazu Nihal ta kalleta tace mata matar shige? Kenan nan gaba akwai matar so a tare da shi?
Ta ina zata fara? Nemanta! Dole ta nemeta ta jaddada mata cewa Turaki na ta ne, ita ɗaya ba da wata macen ba.
Saboda haka tun dare bai ƙure mata ba, tun bata sa duniyarta a cikin ƙuntata ba, ta yi nesa da mijinta, kar ta yi kuskuren raɓarsa, kar ta so zama matarsa, domin gidansa ƙabari ne a gareta. Ya zama dole ta faɗa mata hakan, don kuwa tabbas ba zata taɓa iya shairing Mijinta da wata macen ba.