Free chapter · Read without an account
49
Fullo idanunta a rufe suke har yanzu, tsawon mintoci masu yawan da suke zaune a wajen har yanzu. Bata da lafiya, magani take buƙata domin ta ji sauƙin tarin ciwukan da take ji a ilahirin jikinta da ma zuciyarta.
A gefe guda kuma murmushin ƙarfin hali ne yake fita a saman fuskarta da har zuwa yanzu tashin hankali ya gaza ɓoyuwa. Ita fa tata matsalar kamar ta manta da ita, jin tausayin kanta take ya na bin iska yana tafiya, yayin da na Hajiya Ramla ke biyo iskar ya na lulluɓeta.
"Ba zan cutar da ke ba Mum, addu'a nake so ki yi mu fita daga wurin nan lafiya".
Ba wai don ta sake yi mata tambayar ba ne ta faɗi hakan. Kawai ta samu kanta da faɗin hakan ne.
Hajiya Ramla ta ɗago daga jikin Fullo, sai dai tsam Fullo na riƙe da hannayenta. Ita kuma ta dinƙa kallon Fullo tana jin kamar wani ya taɓa kiranta da wannan sunan Mum, tun a ɗazun take ta so ta tantance hakan da take jin yarinyar na faɗa.
Gaba ɗaya Fullo ta manta da wata waya da aka bata. Sai yanzu da tasirin ambaton Allah da take ta yi ya fara wanzar mata da natsuwa, ta tuna akwai waya maƙale a jikinta.
Tasa hannu a rigarta ta ɗauko wayar ɗazu, ta kunna sannan ta kalli Hajiya Ramla ta ce,"Mum za ki iya faɗin lambar Baffa ko ta Maama? Sai mu kira azo a tafi damu".
Mum ta ce,"Su waye hakan?".
Fullo tana ta kallonta da jin tasirin wani abu na tsarga mata, sannan ta ce,"Lambar mijinki Alƙali Dikko ko ta abokiyar zamanki Hajiya Madina".
Mum ta girgiza kanta ta ce,"Ni ban san su ba ai, ban taɓa jin sunansu ba".
Sai kuma ta haɗe hannayenta ta ce,"Idan kin san sune mutanen da suka saka ni a ɗakin duhu don Allah karki kira su".
Fullo tasa hannu ta goge hawayenta, babu makawa ƙwaƙwalwarta ta yi formating abubuwa da yawa, kuma ba lallai ta tuna komai ba a yanzu ƙila sai ta gani da idonta. Kuma hakan take a ɓangaren tunanin Hajiya Ramla, abu ɗaya kawai ta sani tana so ta isa ga iyalinta, amma bata san su waye ba.
A lokacin suka ƙara jin harbin bindiga, cikin azama Fullo ta miƙe ta kamo hannunta a rikice tana cewa,"Mum zo mu gudu kar su kama mu".
Hajiya Ramla ta miƙe da ƙyar suka nausa inda ba su san ina za su ɓulle ba, suna ta zabga gudu, da sun gaji sai su tsaya su huta, sannan su ci gaba da gudun, gaba ɗayansu a galabaice suke. Kowa so yake ya samu a taimaka masa, dukkan su ruwan sha suke buƙata ya shiga maƙoshinsu ya ratsa fatar jikinsu.
*A dai-dai wannan lokacin.*
Fulani Azima zaune a gaban boka dunƙus, idanuwanta na manne a cikin ruwan ƙwaryar da ke gabansa yana mata bayani, tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda baƙin ciki.
"To ban san dai abin da hakan ke nufi ba, amma kwata-kwata ko aljani ɗaya ya kasa nuna mana fuskar yarinyar, amma tabbas dai aljanu sun shaida ita ke lalata miki aiki".
Maganar ta ƙara ƙona ran Fulani Azima, ta ɗaga murya tana saka hannu ta toshe kunnenta ta ce,"Wacece wannan? Wacece ita da har aljanu suka kasa gano min fuskarta?".
Sai kuma ta yi ƙasa da murya tana kallon Boka ta ce,"Ni dai na roƙe ka da Aljani Jambus ka nuna min fuskar yarinyar nan ko kuma sunanta, na yi maka alƙawarin ko menene zan bayar ko da kuwa kaina ne".
Boka yay dariya ya ce,"Haba Azima, yanda muke da ke, ai kin fi ƙarfin haka a wajena. Abin da nake so ki fahimta shine yarinyar nan tafi ƙarfinmu saboda tana tare da tsari a jikinta".
Sai yasa wani mifici ya rufe ƙwaryar sannan ya buɗe yace,"Leƙo ki gani".
Ta leƙa kanta ta hango wata mace a tsaye, doguwa siririya kamar kara, amma baka ganin komai nata sai ɗan banzan duhu.
Ya ce,"To kinga ni babu ta yanda zamu ga fuskarta haka kuma sunanta ɓacewa yake akan aljanunmu".
Fuskar Fulani Azima na shaida mamaki matuƙa ta ce,"To wai saboda me boka?".
Yasa hannunsa a cikin ruwan ya zuƙo hoton, daidai inda hannun Fullo yake ya ce,"Ba lallai ke ki gani ba amma ni ina iya gani, wannan azurfar ta yatsanta, azurfa ce ta tsari wadda ba zata taɓa barin wani aljani ya ganta ba balle har ya sami damar shigarta, bayan haka kuma ɗan autan aljanu ya faɗa min cewa yarinyar na kasancewa kullum cikin yin addu'oin tsari, bata minti ɗaya bata ambaci sunan Allah ba, haka kuma bata minti ɗaya bata ambaci addu'ar neman tsari ba. Saboda haka babu yanda zamu yi da ita gaskiya, kuma shugaban Aljanu ya shaida mana muddin yarinyar na tare da Turaki, babu abin da asirinmu ya isa ya yi masa, domin ita ɗin kamar sila ce ta kariya a tare da shi, kamar an halicceta ne domin shi".
Kan Fulani Azima yay matuƙar ɗaurewa, ta dinƙa hasaso tsayin yarinyar tana so ta kwatanta shi da na Ilham amma sam babu haɗi, tsayin Ilham bai ko kusan nata ba. To wacece wannan ɗin? Tabbas ya zamar mata dole ta je gidan Alƙali Dikko da ƙafafunta, idan aljanu sun kasa ita ba zata gaza ba, domin ba ta taɓa barin wani ya shiga gaban al'amarinta, dole sai taga bayanta ko wace.
Ta numfasa ta ce,"Shikenan mai girma boka, yanzu ya batun mu na janyo hankalin Alƙali Dikko gare ni? Na rantse da Allah na kasa haƙura da Dikko a duniyata".
Bokan ya bushe da dariya yace,"Kin ga uwar bari kenan, ai na yi zaton har yanzu kina kan bakanki na cewar son gaskiya kike so Dikko ya yi miki, ba sai anyi amfani da asiri ba".
Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba sai ta ce,"Mu bar tuna baya. Yanzu dai a san abinyi akan Mai martaba, a kashe shi kawai na huta da aurensa da ke kaina. Shi kuma Alƙali ayi aikin da za'a gama da rayuwarsa kawai, ina nufin ya saki kowa ya kamani ni ɗaya hatta kuwa da mahaifiyarsa. Tashin farko abin da nake so shine Alƙali ya fita daga hayyacinsa yay wa Madina saki uku sannan duk ya kori ƴaƴansa, daga baya kuma sai ya dawo kaina ya mallaken ta yanda zamu yi rayuwa da shi har a bada. Da wannan buƙatar ta biya sai a raba auren Ilham da Turaki, kuma ta yanda nake so mutuwar auren ta kasance Dikko ya je gidan da kansa ya umarci Turaki ya saki Ilham".
Boka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana ɗaga hannu sama ya ce,"Buƙata taki ta biya Azima, duk yanda kika nema haka za'ai, kuma komai da kika nema zai faru tabbas, angama da wannan buƙata taki".
Fulani Azima ta saki wani murmushi na jin daɗi da kuma nasara, sannan ta miƙawa Jakadiya hannu. Cikin rawar jiki Jakadiya tasa hannu cikin jaka ta ɗauko yari da sarƙa da zobe ta saka a tafin hannun Fulani Azima.
Har yanzu murmushi bai ɗauke a fuskar Fulani Azima ba ta ajiye sarƙar a gefen boka ta ce,"Wannan kyauta ce na baka. Kuɗinta kimanin miliyan goma ne, kyauta ce kawai ba kuɗin aikinka ba".
Boka na murmushi ya ce,"Kin yi farin kai".
Ta ce,"Sai mu je ga lissafin abin da zan bayar akan aikin".
Ya ɗaga kansa sama yana kallon reshen bishiyoyi na tsawon daƙiƙa kafin ya sauke ya ce,"Da farko za ki bayar da miliyan goma, sannan za ki kawowa jikokin Aljanu baƙin jaki guda biyar, sannan za ki haƙa ƙabari ki yanko mana zuciyar jariri fari wanda ana haihuwarsa ya mutu, sannan kuma muna buƙatar yatsa ɗaya na ita mahaifiyar Dikko".
Rufe bakinsa kenan sai suka ga jan ƙyalle ya faɗo gabansu ɗaure da wani dunƙulen abu.
Da tsananin mamaki yake kallon abin na tsawon daƙiƙa biyu kafin ya kai hannu ya ɗauko ƙyallen, ya ɗauko zaren da aka ƙulle shi yana warwarewa.
Mamakin dake tare da shi bai gama sakinsa ba yaga baƙar kurciya ta faɗo kan hannunsa a mace, sabon mamaki tsantsa ya kama shi.
Ya ɗau kurciyar ya haɗe da wannan ƙyallan sannan ya juyo yana kallon Fulani Azima wadda idanuwanta ke a warwaje tana binsa da kallo.
Ta ji ya ce,"Ya aka yi haka?".
Ta ce,"Me ya faru?".
Ya ce,"Me na faɗa miki shekaru ashirin da biyar da suka wuce kafin na yi miki aiki akan Ramla?".
Cikin saurin baki da rawar murya ta ce,"Ka ce kar na kuskura inyi sakacin da asirin nan zai karye, domin duk ranar da ya karye ba zan ji da daɗi ba".
Tana yin shiru yay wani guntun murmushi na tayata jimami sannan ya ce,"Ban labarin yanda aka yi bayan barinta gida".
Jikinta na rawa ta ce,"Lokacin da ta bar gida can ƙasar china ta nufa kamar yanda ka faɗa, bayan wata uku na bi sahunta zuwa dajin da ka ce anan aka jefa kurciyar domin na tabbatar da ta je can ɗin. Kuma ko da na je na ganta ɗin a gefen wata bishiya tana cin ganye, itama kuma ta ganni dan har ta dinƙa roƙona akan in taimaka mata bata san ta yanda aka yi ta zo wurin ba, ta bar Muhammad da Zaytun a cikin ɗaki wuta tana ci bata san ba ko Madina ta kula. Sai na yi mata dariya na ke faɗa mata cewar ni ce silar zuwanta wurin kuma ita da ƙara komawa wajen ƴaƴanta har abada. To muna cikin haka da ita ne sai ga wasu turawa sun zo, suna zuwa suke tambayata cewar na san wannan mahaukaciyar ne? Da farko har zan ce musu a'a sai kuma na ce ehh, sai ɗaya daga cikinsu ya ce min to suna da buƙatar siyanta idan zan siyar musu za su yi tsafi da jininta, ni kuma jin hakan yasa ba tare da wani tunani ba na amince musu, har inda suke da zama muka je tare, suka min bayanin cewar za su ajiyeta a ɗakin tsafi tsawon shekara ashirin kafin nan sai su zuƙe jinin jikinta su yi tsafin da za su yi da shi, kuma tare da ni suka sakata a ɗakin duhu, babu komai a cikinsa sai kayan tsafi. suka kulle suka ce za'a ke bata abinci ne kawai tana ci, don har sarƙoƙi suka saka suka ɗaureta saboda kar ɓacin rana yasa ta gudu, ka ji abin da ya faru Boka, ko ɗaya ban saɓa ƙa'idar aikinka ba wallahi".
Boka ya ƙara murmushi sannan ya ce,"Azima aikinki ya lalace, domin kuwa maganar da nake miki yanzu asirin da yake kan Ramla ya barta kuma ba da jimawa ba za ki karɓi sakamakonki, saboda aljanin da yay wannan aikin ba mai yafiya ba ne".
Fulani Azima ta dafe ƙirji cikin bayyanuwar tashin hankali a tare da ita ta ce,"Kamar ya Boka ban gane ba, me kake so kace min? Ta ya hakan zata faru? Shekara ashirin da biyar fa suka ce za su yi asirin da ita, yanzu ga shi muna cikin shekara ta ashirin da shida ne fa".
Yana ɗago matacciyar kurciyar da jan ƙyallen ya ce,"Waɗannan sune asirin da ke kan Ramla, wannan kurciyar da kike ganinta tun ranar da ta ɗauki Ramla bata ƙara zuwa nan ba sai yanzu, wanda ke tabbatar da cewa Ramla ta baro inda ta ke ta dawo cikin garin nan, kuma mutuwar kurciyar nan shine zahirin cewa babu wani abu da ya sami Ramla".
Sai ya jefar da kurciyar sannan ya ɗauko ƙyallen ya ci gaba da cewa,"Wannan kuma shine ƙyallen da muka ƙulle ƙwaƙwalwar kifaye a cikinsa saboda Ramla ta manta komai, dan haka faɗowar wannan da kuma warwarewarsa ya shaida mana Ramla ta dawo cikin tunaninta".
Ya jefar da ƙyallen sannan ya juya bayansa yana kallon akuyar da ke tahowa tana kuka ya ce,"Idan za ki iya tunawa wannan ita ce akuyar da kika kawo muka ɗaurewa baki saboda rufe bakin Ramla, tsawon wannan shekarun tana nan tare da ni bata taɓa kuka ba sai yau kuma a yanzu, hakan ke tabbatar da cewa bakin Ramla ya buɗe duk inda take, yanzu tana can tana magana".
Fulani Azima ta ɗora hannu akanta tare da kurma ihu ta ce,"Na shiga ukuna".
Boka ya ce,"Ba ki shiga uku ba tukunna, sai kinga yadda reshe zai juye da mujiya".
Ya faɗa yana sa hannu ya daki ƙasar da ke gabansa sannan ya ce,"Kar hankalinki ya tashi sosai, ke ko garin da kike ba za ki bari ba, amma sai dai za ki kwanta baƙar jinyar da za ki ji gwara ace mutuwa kika yi. Domin za'a zo har kan gaɓar da hatta ƴarki ba zata iya zuwa kusa da ke ba".
Fulani Azima ta fashe da kuka sosai tana cewa da boka yay mata rai. Cikin wata razananniyar tsawa ya ce da ita,"Azima ta shi ki bar mana wuri. Bama ƙaunar mai yi mana wasa da aiki". Ya faɗa yana nuna mata hanya.
Suka miƙe tare ita da Jakadiya jikinsu sai rawa yake suka fita daga wajen tana ta uban kuka. Suna fitowa ta yi wani kukan kura ta shaƙi wuyan Jakadiya tana girgizata tana faɗin,"Wallahi ba ki isa kin tona min asiri ba, ba zan kwanta cuta ba ki bi ta bayan fage ki je ki fallasa ni, zan kasheki sannan zan je in kashe Ramlar ma, Ramla gonata ta shiga, wanda na ke so ta aura, kuma har yanzu ina kan dakon son sa, ba zan iya haƙura da Alƙali ba, ina so na rayu da shi ko ba da aure ba".
Haka ta dinƙa sambatun magana bata saki wuyan jakadiya ba har sai da ta tabbatar ta mutu tukunna ta jefar da ita a wajen, ta bar wurin kamar ana tankaɗata har ta fito daga cikin jejin, tana zuwa ta buɗe mota ta shiga Driver yaja su, sai da suka shigo cikin gari sannan tasa ɗankwalinta ta shaƙo wuyan driver shima tana faɗar,"Ba zan barka a raye ba kai ma ka tona min asiri, ba zan barka ka ga ciwona ba ka tona min asiri".
Bata sake shi ba sai da ta tabbatar ya mutu, kuma kamin Fulani Azima ta yi wani ƙoƙari na karɓar kan motar, motar ta gangara ta faɗa gefe, nan take glass ɗin motar ya tarwatse da yawa suka soki cikin kanta, ta kurma ihu tana neman ɗauki tana ƙoƙarin fitowa a motar, bata ankara ba ta kai fuskarta saitin wani glass da yay kamar kibiya, ƙwayar idonta ɗaya ta soki glass ɗin, nan take ruwan idon ya shiga tsiyayewa.
*A dai-dai wannan lokacin.*
*Yanda Abin ya kasance da kuma yanda abin ke faruwa.*
Lokacin da Turaki ya ƙaraso wurin da kidnappers suka buƙaci ya ajiye kuɗin, yay parking motarsa ya fito ɗauke da dumin jakar kuɗin.
Ya tsallako side ɗin da suka ce yay tafiya mai nisa sannan ya ajiye jakar a wajen, ya ɗauko wayar Maama da ke aljihunsa ya ɗaga kiransu da ke shigowa.
Daga can ɓangaren ya ji an ce,"Kai ne kasa coffee yadi?".
Ya ce,"Ehh ni ne".
Ya faɗa yana duddubawa ko zai ga ta inda mutumin yake. Sai ya ji mutumin na dariya ya ce,"Ai ba zaka taɓa ganinmu ba, ka bar wahalar da kanka da waige-waige, ka juya ka bar wajen ka koma bakin motarka, ka jira yaronka zai zo ya sameka".
Jin haka yasa Turaki saurin juyawa ya bar wajen, wucewar minti biyar sai ga mutumin ya zo ya ɗauki jakar shi kaɗai, cikin sauri yake tafiya don barin wajen, a lokacin Turaki ya fito daga jikin wata bishiya da ya laɓe.
Yasa hannu a bayan wandonsa ya zaro bindigar da bai taɓa riƙeta ba sai a yau, ya saita ƙafafun mutumin ƙwayar idonsa na hasko masa yadda ake harbi a cikin film, bai taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai a yau da ya shiga office ɗin DSP ya ɗauko ba tare da sanin kowa ba, kazalika bai taɓa riƙe bindiga ba balle har yay attempt na harbi, but today bindiga ta zo hannunsa, and zai gwada amfani da ita ko da ace wannan ita ce dama ta ƙarshe da yake da ita a duniya. Fulani suka kama, ba zai barsu da rai ba.
Ya saita ƙafar mutumin ba don yana tunanin dai-dai ya saita ba, kuma babu ɓata lokaci kai tsaye ya saki bullet, kuma cikin sa'a bullet ɗin ya shige ƙafar mutumin, hakan bai sa Turaki ya haƙura ba, ya ƙara sakin bullet ɗin wanda a yanzu kai tsaye ya wuce zuwa kaɗar mutumin daidai sanda ƙafafunsa ke durƙushewa a ƙasa yana sakin jakar kuɗin ya riƙe ƙafarsa da ke zubar da jini.
Abinka da wanda bai san kan lamarin ba, kawai sai ya jefar da bindigar a wajen ya kwasa a guje ya ƙarasa gaban mutumin, ta baya ya damƙi kwalar rigarsa ya ɗago da kansa, ya zagayo ta gabansa yasa gwiwar ƙafarsa ya daki haɓarsa, take jini da ƙwaƙwalwarsa suka haɗu waje ɗaya, ƙwayar idonsa ta firfito waje yana buɗe su da ƙyar saboda azabar harbin da ya shige shi, ya kalli Turaki, cikin zafin nama Turaki yasa hannu ya fizge facemask ɗin da ke fuskarsa.
Yana faman huci kamar mayunwaci za ki ya ce,"Ina yarinyar take?". Ya faɗa cikin ɗaga murya sosai.
Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce,"Zaka tsira da ranka, kuma zan kai ka asibiti sannan zan barka da wannan jakar kuɗin ka tafi safely, but at first tell me ina Matata?".
Shirunsa ya haɗe da ƙarasowar ƴan sanda wajen, suna zuwa ɗaya daga cikin ƴan sanda yasa ƙafa ya daki gabansa, a take ya ƙwalla wata razananniyar ƙara saboda yadda ya ji kamar za'a zare masa rai, babu shiri ya ɗaga hannu yana yi musu nuni da katangar gidan dake can gabansu.
Ashe ma ƙananan ƴan iska ne, yanzu ne suka shiga harkar kidnapping ɗin. Ai dama tun yadda suka zo ɗaukar kuɗin ya raina su, in ya san haka ne ai ko shi kaɗai zai iya zuwa ya gama da dukkan su.
Turaki is the first one da ya bar wajen a cikin gudu, wasu cikin ƴan sanda suka mara masa baya, yayin da wasu mutum biyu suka ɗauke wannan wanda Turaki ya harba su ka yi mota da shi.
Harbin farko da Turaki ya yi su Amir sun ji a lokacin suna laluben Fullo a cikin gidan, kuma rashin tabbatar da cewar harbin bindigar suka ji da gaske yasa basu bi ta kai ba sai a harbi na biyu, anan hankalinsu ya tattaru wuri ɗaya saboda haka duk sai suka dakata da batun nemanta, suka koma ta yanda za su tsira.
Amir ya ce,"Duk yanda aka yi shegun mutanen nan da police suka zo".
Wani mai kama da shi ya ce,"Tabbas kuwa, but har ta ya mu ka yi sakacin hakan ya faru?".
Sai ya juya yana kallon mutumin da ya taimakawa Fullo ya ce,"Hau katanga ka duba mana".
Yana hawa katangar yaga ƴan sanda birjiki daga can nesa kamar cinnaku sun baibaye faɗin wajen, hakan yasa da ƙarfi ya ce musu,"Police ne mota har guda biyar".
Yana faɗar hakan ya dirge ta baya dan ba ya tunanin zai iya bari a rutsa har da shi.
Su kuma nan suka fara neman hanyar guduwa ta ƙofar baya da Fullo ta bi, sai dai cikin rashin sa'a suna buɗewar su ka ga police tsaitsaye a wajen riƙe da bindigu, kuma babu wata-wata suka shiga sakar musu harbi ratata, harbin ya sami kusan mutum huɗu, su kuma sauran suka koma ciki da gudu don tsira da ransu, sai dai ko a lokacin tuni wasu ƴan sandan ma sun cika gidan.
"Raise your hands up".
Su shidan da suka rage ba'a harba ba suka ɗaga hannayensu sama, time ɗin da Dsp yay arresting ɗinsu.
Turaki kuwa tun shigowarsu babu ta kan wanda yabi sai laluben inda zai ga Fullo, haka ya koma kamar wani zautacce ya shiga can ya fito, ya faɗa can ya leƙa can, kaf babu inda bai duba a cikin gidan nan bai ganta ba, sai ga shi ya faɗo parlon kamar an jefo shi yana zazzare ido, wai ko zai ganta a nan duk da cewa ta falon ya fara dubawa.
Jiri ya ɗebe shi ya tafi ya faɗa kan wata kujera da ke wurin, yasa hannu ya dafe kansa da yake jin yana barazanar tsage masa, ya rumtse idonsa sosai yana rasa me ke masa daɗi a duniyarsa, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗago kai ya buɗe idonsa wadda ƙwayar ta kaɗa ta yi jawurr, ya sauke kallonsa akan Dsp ya ce,"Yallaɓai ban fa ganta ba, bata cikin gidan nan Yallaɓai".
Muryarsa ta fito cikin bala'in rauni kamar zai yi kuka.
Dsp na tsaye daga gefe yana kallonsa bai ce masa komai ba, har sai lokacin da wasu ƴan sanda guda uku suka zo, waɗanda sune aka saka su nemo Fullo da suka shigo gidan.
"Yallaɓai babu wurin da bamu duba ba a cikin gidan nan kaf babu yarinyar".
Dsp ya kalli tawagar su Amir da suke tsaye hannaye a sama, idanu duk sun raina fata, ya sakar musu wata uwar tsawa ya ce,"Ku faɗa min ina ku ka ɓoye yarinyar?".
Da farko duk shiru suka yi, sai da ya ƙara doka musu tsawar da tafi ta farko.
Tukunna ɗaya a cikinsu yana karkarwa ya ce,"Mu ma bamu san inda take ba".
Yana rufe baki yana jin saukar harbi a gwiwarsa, ba shiri ya saki ƙara ta azaba yana duƙewa a wajen, tuni zufa ta shiga haɗo masa yana faɗin,"Wallahi bamu san inda ta yi ba, ta gudu tun ɗazu, muna cikin nemanta ne ma ku ka zo".
Furucin nasa yasa Turaki miƙewa daga kan kujerar da yake a kiɗime yana faɗin,"What! Ta gudu? Baku san ina tayi ba?".
Ya furta yana jin kamar zuciyarsa zata buga. Dsp ya ƙara harbin ƙafar wanda yay maganar, azaba ta ƙara ratsa shi ya kuma ihu wajen faɗin,"Assshhhh".
Dsp ya ƙara sakar masa wani a hannu, a wannan karon ko motsawa bai yi ba don tsabar azaba, maganarsa ta fito a hankali yana cewa,"Na rantse da Allah ta gudu tun ɗazu".
Turaki yana shirin sauke ƙwayar idonsa kan mutumin, kawai sai Allah ya kai idonsa kan Amir, yay saurin maida kallonsa kan Amir gaba ɗaya yana ƙare masa kallo, da son tabbatar da abin da ƙwayar idonsa ke gani.
Cikin kansa ya haska da hoton lokacin da yake tsaye gaban Fullo, har yana riƙe mata hannu, har zuwa lokacin da ya juya ya bar wajen.
"You!". Turaki ya faɗa in shock. Sai kuma ya nufi wurin Amir gadan gadan kamar zakin dake cikin yunwa ya ga abinci.
Yana zuwa yasa hannu ya shaƙi wuyan Amir, ya dinga tura shi da baya har sai da ya kaisa bango ya gwara kansa a jiki.
"Waye kai?". Turaki ya tambaya. Tun Amir bai basa amsa ba ya dunƙule hannunsa ya bawa fuskarsa wani mahaukacin naushi, wanda yay sanadiyar ɗaukewar ji da ganin Amir na wucin gadin, hakama haƙorinsa ɗaya ya tsinke ya fara lilo.
Amir ya ɗago kansa a galabaice sai dai tun bai gama buɗe idonsa ba Turaki ya ƙara sakar ma fuskarsa mugun naushin da yafi na farko, kan Amir ya yi ƙasa jini na zuba ta hancinsa. Turaki ya ƙara yin kukan kura ya ɗago da fuskar tasa ya kuma naushin fuskarsa a gefen ido, take jini ya taru cikin idon Amir, haka ma jini ya shiga fita ta hanci ta baki.
Amir yay yunƙurin ƙwatar kansa, amma inaa lokaci ɗaya Turaki ya damƙi hannusa, da wani irin ƙarfin da bai san yana da shi ba, ya barƙala hannun har sai da hannun Amir ya ɓalle.
A taƙaice dai Turaki sai ya koma kamar mahaukacin zaki wajen dukan Amir, ya koma tamkar zakin da ya shekara ba abinci ya kuma samu abinci a daidai lokacin da yake so, naushi yake ta kaiwa fuskar Amir hagu da dama cikin ƙaraji yana tambayarsa,"Who are you? Ina ka kai ta?".
Sai da fuskar Amir ta kumbura ta yi suntum babu kyan gani, ko'ina ya farfashe banda uban jini dake zuba ta gefen idonsa.
Turaki ya bar fuskar tasa ya kai shi ƙasa yana tattaka ruwan cikinsa, yasa ƙafa ya dako shi ta can, ya doko shi ta nan, yay fatali da shi ta can, ya jefa shi ta can ya gwaru da bango, haka Turaki yay ta ball da shi kamar wanda ya samu ball ɗin gaske.
Tun Amir na iya ihu har ya zo ya daina, tun yana buɗe baki yana uban nishi da son yin magana har ya kasa, shi kansa so yake ya ce da Turaki who is he, dan wannan dukan da yake masa ko uwarsa ya kashe sai haka.