Free chapter · Read without an account
The Safest Option
by NorthernAngel · His Rose
Ganin Zara tsaye ya sa Zafar buɗe mata hannu kafin ya fara takawa inda take, his eyes locked onto her with pure admiration. Yana isa ya yi hugging ɗinta yana kissing chubby cheek ɗinta ya raɗa mata, “Kin yi kyau.” Murmushi kawai ta sakar masa ba tare da ta ce komai ba, her playful mood from earlier still lingering. Zafar ya ja hannunta ya nufi sofa, yayin da Khairy dake kallon su tana washe baki ta ce, “Amarya, sannu da fitowa.. Allah ya sa dai kar in sha zagi yau.” Ta ƙarasa maganar tana yiwa kanta da kanta dariya, trying to break the ice. Zafar ma dariyar da bai yi niyya ba ce ta so kwace masa, amma ya danne instantly saboda bai son yinta gaban Khairy. Zama ya yi kan sofa yana kallon Zara da ta ƙi sakin fuska keenly. Zama ta yi ita ma a sofa ɗin da yake amma nesa da shi, tana ɗan shan kunu. Zafar dake kallon ta sarai ya sa hannu ya fara janyo ta yana cewa, “Near me jhoor, no dulling.” Daga haka ya sata a jikinsa wanda Zara ba ta ba shi musu ba, sai ma kwanciya da ta yi, her back pressed against his chest, tana miƙar da ƙafarta kan sofa. Zafar ya kai bakinsa daidai kunnentai cikin raɗa ya ce mata, “Behave,” daga haka ya yi kissing earlobe ɗinta. Turo baki ta yi kafin ta kalli inda Khairy take zaune tana pressing wayarta, ga coconut water ɗinnan a hannunta tana sha. Calmly Zara ta ce, “Welcome, Doctor. I hope this wasn’t an inconvenience.” Da mamaki Khairy ta kalli Zara kafin ta saki wani sassanyan murmushi, tana sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya ta ce, “Ah, haba, it’s nothing. This is my job. Besides, my boss sent me, shi yayi nisa.” Zafar cike da jin daɗin yadda matarsa ta yi ɗin ya duƙar da kansa yana kissing hancinta sannan ya yi kissing bakinta. Ai kuwa cikin sauri Zara ta goge bakin tana ba shi pointed look. Shammatar ta ya sake yi, ya ƙara kissing lips ɗin nata. Ai kuwa da sauri ta tura kansa da ƙarfi tana ƙoƙarin miƙewa. Danneta ya yi yana dariya yayin da ita kuma ta sa kukan shagwaɓa a hankali—sun ma mance da baƙuwa a ɗakin, **lost in their own little world.** Ganin Zara za ta fara kukan gaske ya sa ya ɗago ta ya rungume cikin lallashi yana cewa, “Sorry, sorry, na daina.” Shiru ta fara yi kafin cike da shagwaɓa ta ce, “I’m only letting this slide because you’re rich rich.” Dariya Zafar ya fashe da ita mai ƙarfi da ya sa Khairy ɗagowa tana kallon sa da mamaki, unused to seeing him this carefree. Yana kallon Zara ya ce, “So my money outranks me in your heart now, princess? I’m wounded.” Ya faɗa yana dafa ƙirjinsa, feigning a heartbreak. Zara ta sake kwantowa jikinsa tana kallon sa, ta sa hannunta cikin ɗan gemunsa nasa tana wasa da shi ta ce, “Not you obviously. I love you more of course, but your money kisses harder.” Nan ma dariyar ya sake yi, yana ƙoƙarin kissing bakinta again. Da wani irin sauri ta sake matsawa, cike da shagwaɓar mai cin rai take cewa, “Eww, get awayyy! You seriously want to put the Salima-19 variant on my lips! You need to go get fully decontaminated first!” Zaro ido Zafar ya yi jin abun da ta faɗa, wata dariya mai ƙarfi na kwace masa. Cikin mamaki da dariya ya girgiza kai, “Zaraa, you’re too spoiled for your own good.” Ita ma Khairy dake jin Zara dariya take yi ƙasa-ƙasa, highly amused and slightly shocked, tana mamakin daman akwai macen da Zafar ya sakewa haka a duniya. Zafar ya sa hannu ya kama bakinta har lokacin yana dariya, ya sake cewa, “Sai na yanka bakin nan since baya shuru.” Zara ta cire hannunsa tana murguɗa masa bakin, her dynamic expressions changing in a split second. Kansa ya nuna alamar shi? Zara ta gyaɗa kai tana turo masa baki. Gyaɗa kansa ya yi yana ɗagowa ya kalli Khairy yana cewa, “Khairy, come over and give her that injection you mentioned.” Zara ta ɗago kai tana kallon sa hankali kwance. Cikin calm voice ta ce, ”Waye za a yi injecting?” Zafar na kallon ta ya nuna ta, “Zara za a yi wa allura.” Kai ta girgiza tana dariya ta ce, “Sai dai a yi wa Zafar in place of Zara!” Daga haka ta kalle sa tana washe baki ta ce, “Thank you so much for volunteering, Obim!” Khairy dake faman dube-dube a medical bag ɗinta ta miƙe tana ’yar dariya ta ce, “Ba allura, but I have to draw your blood for a test.” Zafar ya kalli Zara da ta zaro ido, ya kalle ta smugly ya ce, “Kin gani? Allura kenan! You're still getting poked anyway.” Shiru Zara ta yi tana lafewa jikinsa, ba ta sake cewa komai ba. Ta fara bin Khairy da kallo yayin da ta doso ta da medical bag ɗin a hannunta. Ottoman ɗin gefen sofa ɗin da suke ta janyo ta zauna gabansu tana murmushi calmly, dan ta san Zara jin allura ne ya sa take binta kallo keenly, tana jiran ta ga ta ina zai fito. Duba ta Khairy ta fara yi, gently take komai cikin lallashi kamar dai yadda ta yi mata few years back a Toronto. Ta fara da duba vitals ɗinta, from her pulse to her BP, da kuma weight ɗinta, sannan ta hau yi mata tambayoyi akan LMP ɗinta, yadda take jin jikinta da kuma abun da ya faru da ita a bathroom da safen—wanda mostly Zafar ke amsawa, his tone clipped and precise. Ita dai ta koma kwance a jikinsa tana bin Khairyn da kallo, sai in Zafar ko Khairy sun tambaye ta ko daidai ya faɗa sai ta gyaɗa kai. Shi dai Zafar yana lura da ita akan yadda ta yi sanyi daga maganar allura. Bayan Khairy ta gama duba ta, ta ɗauko wasu specimen containers daga cikin medical kit ɗin, ta kalli Zara tana murmushi ta ce, "Next up are the blood and urine samples. Which one feels easier for you to start with right now?" Cikin sauri Zara ta miƙa hannu tana faɗin, “I’ll go with the urine sample first. I actually really need to pee anyway.” Daga haka ta fara ƙoƙarin miƙewa daga jikin Zafar. Cikin sauri ya riƙe ta yana cewa, “Muje in raka ki.” Shiru ta yi tana kallon sa at first, dan ta ga rashin yarda da ita ƙarara a fuskarsa, knowing he suspected she’d try to delay things. Sai kuma ta gyaɗa kai ba tare da ta ce komai ba ta miƙe. Ƙaramar container ɗin Zafar ya karɓa a hannun Khairy kafin ya miƙe shi ma yana kama hannun matarsa suka nufi ciki. Bathroom suka shiga, Zara ta ɗan dakata tana kallon Zafar ta ce, “Obim, kasan me?” Zafar ya ja hannunta zuwa gaban vanity drawers yana cewa, “Menene?” Drawers ɗin ya fara buɗewa yana dube-dube, wanda duk hygiene products ɗinta ne a ciki sai wata locker dake da first aid a ciki. A cikin locker ɗin ya ga medical gloves ɗinda yake nema. Miƙa mata guda biyu ya yi, shi ma ya ɗauki guda biyu ya miƙe. Sakawa suka yi, daga haka ya ja hannunta zuwa inda za ta yi fitsarin. Zara dake faman ɓata rai ta ce, “In fa na yi fitsarin shikenan, ba sai an ɗauki blood sample ɗina ba.” Zafar ya kalle ta, kafin ya juya yana girgiza kansa ya ce, “Nice try, Doctor Zara.” Daga haka bai sake ce mata komai ba. Ita kuma ta zauna ta fara fitsarin, and in less than two minutes, she was done. Zafar ya karɓi robar ya yi amfani da paper towel ya goge tass, Zara kuma ta cire gloves ɗin ta yi disposing ɗinsu sannan ta wanke hannunta suka fito, to face the dreaded blood test. Suna fitowa bedroom, Zara ta sake tsayawa tana kallon sa kamar za ta yi kuka, ta ce, “Obim…” Zafar ya yi sighing yana cewa, “Princess, you’re not escaping that needle today.” Daga haka ya fara yin gaba, har ya kai bakin ƙofa ya lura ba ta biyo shi ba. Ya juyo yana kallon ta a tsaye inda ya barta, “Zara?” Shiru ta yi ba ta amsa shi ba, sai ma juyawa da ta yi nufar gado. Ganin za ta hau gado ta kwanta ya sa da sauri ya ce, “Zo muje toh, zan ce mata kar ta yi miki.” The desperation to avoid her tears completely overriding his initial firmness. Turo baki ta yi kafin ta isa inda yake, ta yi gaba yana binta a baya. Suna isa parlour, suka tarar da Khairy a zaune inda suka bar ta tana waya, ga gloves a hannunta tana sakawa. Sai da suka ƙaraso suka zauna sannan ta kashe wayar, ta ɗago tana kallon su. Karɓar container ɗin hannun Zafar ta yi, ta saka ta cikin biohazard specimen bag, sannan ta fito da wani sterile, sealed packet daga cikin jakar ta. Wani pink butterfly needle set ne a ciki, Khairy ta fara buɗewa tana cewa, "Omar ne ya sa aka buɗe min office ɗinsa, he told me right where your infusion set is kept.” Zara da ba ta ma lura da abun da Khairy ta fito da shi ba sai da ta ji abun da ta ce. Da sauri ta kalli Zafar, her eyes searching his face, waiting for him to step in and defend her. Zafar dake kallon ta ya sauke ajiyar zuciya kafin ya maida kallon sa kan Khairy yana cewa, “Khairy, I thought only one was required between the urine and blood tests.” Khairy ta girgiza kai cikin mamakin yadda Zafar ya zama wani mijin tace—a completely domesticated version of the fiercely private man he usually was. Wannan shi ne abun da ba ta taɓa tunanin za ta yi witnessing a rayuwar ta ba. Girgiza kai ta yi tana ’yar dariya, ta maida kallon ta kan Zara, tana tuna sanda ta je wurinta Toronto ma haka suka sha drama, daga ƙarshe ba a yi mata allurar nan ba. Cikin ɗan lallashi Khairy ta farawa Zara magana, “I wish it was that easy, my dear, but at just four to five weeks, it's way too early. The pregnancy hormones hit your bloodstream first before they ever show up in your urine. If we only do the urine test, it might give us a false negative. Kiyi haƙuri, ba za kiji wani zafi ba. A hankali zan miki, before you even know it, na gama.“ Shiru Zara ta yi ba ta ce komai ba. Zafar kuwa rubbing hands ɗinta yake cikin nasa in a comforting way, sending steady warmth through her trembling fingers. A hankali Zara ta gyara kwanciyar ta a jikin Zafar, kanta ta tusa a ƙirjinsa tana rufe fuskar, sannan ta miƙa wa Khairy hannunta, completely surrendering to the moment. Zafar ne ya riƙe hannun yana kaiwa lips ɗinsa ya yi kissing cike da so. Khairy kuma da abubuwan, ta fito da tiny needle ɗin mai two pink wings, a plastic tube holder, two glass vacutainer tubes masu pink stoppers, sai kuma lastly, a pink tourniquet. Ta karɓi hannun Zara daga na Zafar, wanda Zara na jin Khairy ta fara ƙoƙarin ɗaura mata tourniquet ɗin, ta fashe da kuka a hankali—a soft, muffled whimper against his chest wanda Zafar ne kawai ya ji sound ɗin. Zafar ya ɗago ya kalli Khairy, yana girgiza kai ya ce, “Khairy, kawai—” Khairy ta sa hannu a lips ɗinta tana girgiza masa kai alamar ya yi shuru. A hankali ta ce, “Yanzu zan gama mata, calm down.” Daga haka ta ɗaga murya kaɗan cikin lallashi ta ce, "Keep your hand in a fist for me, kin ji Rose? I need to find the right spot quickly. Kiyi haƙuri, ai na ce miki ba za kiji zafi ba." Ita dai Zara ba ta ce komai ba, ta ƙara ƙanƙame Zafar da ƙarfi, yana jin hawayenta na sauka akan ƙirjinsa, soaking through his black shadda. Ai kuwa, tana suka needle ɗin, ta fashe da kuka sosai, completely losing her composure. Zafar sai shafa bayanta yake yana kissing ɗin kanta, har da yi wa Khairy masifar cewa jinin ya isa haka, his protective instincts flaring up aggressively at her distress. Ita dai Khairy murmushi kawai take yi expertly filling the tubes, tana ganin irin tabarar da Zarar ke yi. Bayan ta gama cirewa, ta sa cotton ball a gurin da sauri ta kalli Zafar dake faman lallashin Zara ta ce, "Hold this down for a few seconds, Zafar." Hannu ya sa ya danne audugar, applying steady pressure, daga haka ita kuma ta fara tattara kayan tana cewa, “Honestly, Zafar, kasan that coconut water da kace min tana sha is the only thing keeping her standing right now. It’s packed with natural electrolytes, which is why her body is craving it to fight the nausea. But coconut water alone can't replace solid food. Her blood pressure is going to drop like a stone, which is exactly why she fainted—ai nace maka suma ta yi, and I think she’s stressed.” Zafar dai cikin damuwa yake kallon ta, jin ta ce she’s stressed ya sa ya kalli Zara da har lokacin tana kuka, her silent tears breaking his heart. Cikin soft voice ya ce, “Zara, menene? What’s stressing you?” Kamar jira take ta ɗago. Tana kallon sa da idanunta dake jike da hawaye, ta ƙi cewa komai. Fuskarsa ya kai daf da ita, ya sa hannu yana goge mata hawaye, da wata low voice ya ce, “Nine?” Gyaɗa kai ta yi kafin ta lafe a jikinsa, cikin muryar kuka ta ce, “Ba kai bane kake son kaje Dubai…” Ɗan zaro ido ya yi da mamaki—Dubai ɗinda ya dinga roƙon ta ta bishi ɗazu! Ajiyar zuciya ya sauke, struggling to suppress a smile at her adorable logic. Cikin lallashi ya ce, “Toh za ki bini?” Maƙe kafaɗa ta yi, sabbin hawaye na sake zuwa idonta. Ita dai Khairy ta koma ta zauna kan sofa, idonta na kan TV, giving them a bit of privacy. Zara ta sake maƙe kafaɗa ba tare da ta ce masa komai ba. Khairy ta kalle su ta ce, “Yanzu dole zan ɗaura ta on a regular fluid drip to balance her system out. I'll be injecting an anti-nausea medication directly acikin tube ɗin. It carries a heavy drowsiness effect, which is going to cure her nausea and make her incredibly sleepy. She’ll get all the rest she needs.” Zafar ya gyaɗa kai yana sauke ajiyar zuciya, relieved that she would finally get some comfort. Zara dai ƙara ɓata rai ta yi jin za’a sa mata ruwa, the thought of another needle annoying her. Zafar ya ce, “In that case, let’s move into the bedroom then.” Zara ta miƙe tana cewa, “I need to pray first.” Khairy ta gyaɗa kai, “Eh fa, ni ma zan yi sallah. And I’m hungry, Zafar, a ba ni abinci please.” Gyaɗa kai ya yi yana miƙewa ya kama hannun Zara, ya kalli Khairy yana cewa, “Muje.” Khairy ta miƙe tana bin bayan su. Suna isa hallway ɗin, Zafar ya nuna wa Khairy jerin four bedrooms ɗin da ke kallon juna, “Enter one of the rooms, in kin idar sai ki shigo,” ya ƙarasa maganar yana nuna mata parlour ɗin Zara. Daga haka suka wuce shi da Zara ciki. Alwala Zara ta yi yana tsaye watching over her protective layout. Bayan ta gama kuma, ya kama hannunta suka wuce zuwa praying corner ɗin dake ɗakinta, ko da suka shiga, wani ƙamshi na musamman ne ke tashi a gurin. Wardrobe ɗinta ke wurin ya buɗe; cike take da bubu gowns ɗin sallarta da hijabs. Zafar ya juyo ya kalle ta yana cewa, “In baki hijab kawai?” Gyaɗa masa kai ta yi. Ya ciro wani ƙaton soft cotton pink hijab da bai da nauyi ya miƙa mata, sannan ya kunna mata AC ɗinda ke gurin. Ita kuma Zara ta saka hijab ɗin, ta ɗauki ɗaya daga cikin ouds ɗinta dake jere cikin niches ɗin da littattafan addini ke jere, ta fesa turaren kaɗan. Zafar kuma ya nufi inda dadduma take, ya ɗauko ta ya shimfiɗa mata akan lallausan carpet ɗinda ke shimfiɗe a filin gurin. Sai da ya ga ta tada sallah sannan shi ma ya juya ya fice zuwa masallaci. Bayan Zara ta idar da sallah, ta ji sallamar Khairy a cikin ɗakin tana tashi. Shafa addu'a ta yi ta miƙe tare da naɗe sallayar, sannan ta cire hijab ɗin ta da ya jiƙe da gumin ta, ta ajiye a fili don ya sha iska sannan ta fito. Khairy ta gani a tsakar ɗakin a tsaye, tana ganin ta ta ce, “Kin gama? A maid directed me here, ta ce Zafar yace in na idar ta kawo ni nan,” ta ƙarasa maganar tana cire mayafin abayar ta, ta nufi sofa ta zauna. Zara ta gyaɗa kai tana cewa, “I need to rinse off quickly, zafi nake ji.” Daga haka ta nufi bathroom, Khairy kuma ta yi kwanciyar ta kan sofa, drifting into her own zone. Kusan five minutes, Zafar ya shigo da ’yar sallama a bakinsa. Khairy ta amsa tana ɗaura mayafinta a kai. Ya ƙaraso ciki yana kallon ɗakin kafin ya kalli Khairy, “Ina take?” Khairy ta nuna masa bathroom, “Ta ce za ta watsa ruwa ne.” Gyaɗa kai ya yi kafin ya nufi closet ɗinta. Wurin sleepwears ɗinta ya je ya ɗauko mata wani Ivory cami and shorts set, ya fito ya shiga bathroom ɗinta. Ita dai Khairy ta bi sa da kallo ganin ya nufi bathroom ɗin da kayan baccin Zara. Cikin mamaki ta girgiza kai tana dariya ta ce, “Namiji kenan.” Zafar na shiga bathroom, ya tarar da Zara ta ɗaura towel, looking fresh but still thoroughly exhausted. Pajamas ɗinta ya miƙa mata yana cewa, “Wear this, princess. Kiga bacci zaki yi, you’ll feel much more comfortable in it.” Karɓa ta yi, ta fara sakawa. Cikin shagwaɓa ta ce, “Obim, ni ba na so ta sa min wani cannula, zan ji zafi.” Zafar ya sauke ajiyar zuciya, ya janyo ta jikinsa ya fara taya ta saka kayan yana cewa, “I’m sorry, but it’s for your own good. Kina ji fa, she said you fainted because you need nutrients in your body.” Shiru ta yi ba ta ce komai ba. Sai da ya gama saka mata kayan, ya rungume ta a jikinsa yana jin tsananin damuwa a ransa. Abun da ya fi ba shi tsoro shi ne wai Zara ta suma, kuma ba ya kusa da ita har ta tashi da kanta! Kwanan ta ɗaya kacal a gidansa, a ce ya yi wannan sakacin? Anya ya riƙe amanar da Allah ya ba shi kuwa? Kansa ya girgiza yana bawa kansa amsa cikin ransa, the guilt gnawing at him deeply. Kallon ta ya yi tana ta lafe a jikinsa, tana turo baki gami da shafa gurin da Khairy ta ɗibi jininta. Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa, “Zara..” Ɗagowa ta yi tana kallon sa. Babu abun da take gani cikin idonsa sai tsananin sonta da tausayin ta; gaba ɗaya hankalinsa in ya yi dubu ya tashi jin wai ta suma. Ya sake sauke ajiyar zuciya kafin ya sa thumb ɗinsa yana rubbing cheeks ɗinta, ya ce, “Tell me, what’s stressing my princess?” Lafewa ta yi a jikinsa, tana juya maganar dake ranta. Tana tunanin yadda zai ɗauki maganar, fassarar da zai mata, da kuma abun da zai ce—musamman da ya ce cika umarnin Yemma ne tafiya da Salma. So, she chose the safest option. Idan tace masa kar ya tafi da Salma, kamar ta hana shi bin umarnin Yemma ne, but idan tace kar ya tafi gaba ɗaya fa? Ganin ta yi shiru ya sa Zafar cewa, “Zara, please—” “Ba na so ka yi tafiya,” ta katse masa magana da faɗan safe option ɗin da ta zaɓa, her voice barely a whisper. Frowning, Zafar ya yi kafin ya ɗago ta yana kallon ta. Cikin mamaki ya ce, “Shikenan?” Gyaɗa masa kai ta yi tana sunkuyar da kanta, feeling a bit vulnerable. Ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya sa hannu ya ɗago kanta yana kallon cikin idonta ya ce, “I’ll see if I can send Tijjani. Otherwise, sai dai na yi postponing. Once you leave for Saudi, sai na tafi.” Wani satisfied murmushi Zara ta saki, ta sake lafewa jikin sa cike da so, feeling completely secure in his love…