Free chapter · Read without an account

CHAPTER 25 ( Setting the grounds)

by Khadeejah Bint Ismail · NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 25 ( Setting the grounds)




Ba ta wani yi bacci ba sai juyi take yi hakan ya sa ta mik'e kawai ta fita living room, gyaran gidan ta fara kamar yadda ta saba. Ta na kammalawa ta wuci kitchen simple breakfast ta fara haɗa loaded fries ta had'a da ta ji kaza da sausage ba ta cika mozerella ba haka shi ma cream d'in da tayi spicing da kyau da ketchup,sauce da paprika ta zuba a saman lettuce da cabbage  sai k'amshi ke tashi. Shayin zobo ta dafa da ya ji mint, cumin, cinnamon d'an daidai sai niƙaƙƙen apple, lemon da kuma kanunfari kad'an ba mai yawa ba.



Na shi ta jera masa akan dining shi kuma na ta ba ta had'a ba ta dai soya chips d'in ta ajiye don ba ta son ya huce, gyara kitchen d'in tayi ta goge koina shi ma ta ba shi tsarabar turarenshi kafin ta fito. Nan ta had'u da Burhaan ya na fitowa daga part d'in shi, d'an dakatawa tayi har ya k'araso dining d'in ba ta ko sassauta fuskar ta ba tace " Nda watu".



"Wadu klewa?" Ya tambaya da d'an kulawa tunda ya lura yau faru ake ji, cuna baki tayi tana cewa " klewa slai" nuna masa dining tayi tana mai nufin wucewa ciki, hannu ya sa ya rik'o na ta hakan ne ya tilasta mata tsayawa amma ba ta waigo ba yanyota yayi dukanta gabanshi yana cewa " ki daina fushi wife, bai yi kama da ke ba". Taune lips d'inta tayi ta ciki tana sake turo bakinta cewa yayi " yeah, kin fi kyau in kina murmushi ko baki sani ba ne?".



Yanzu kam ta kasa danne murmushin da take yi, ta d'an yi k'arami sai kuma ta so maida fuskarta da sauri ya rik'e fuskar a hannunshi yana cewa " yawwa ga Nadeefahr da na sani nan, ki daina tunani da yawa kina sawa ranki damuwa ok? Ki kuma daina tunanin ban sonki, a je ma hakan ne amma ina so ki san kina da muhimmanci a rayuwata. So ki ajiye soyayya a gefe don ba shi ne ginshiƙi na zaman aure ba, girmama juna da muke ya ishemu a rayuwarmu, zancen soyayyar da kike kawowa zai dinga ɓata miki rai ne a banza a wofi kuma shi ne abinda na fi tsana".



"But.......!"


"No Buts Nadeefah, kina haƙuri da ni toh ki ƙara. Ban iya yaudara ba ban kuma son in fara balle har ta shiga tsakanin mu na kuma gode da kyautar ki Allah ya k'ara bud'i Aunty CEO" ya k'arashe yana janyota jikinshi wanda ya d'aukesu kusan minti biyar kafin ya janyeta. Zama yayi a dining itama ta zauna a kujerar dake opposite d'in shi ta tafi duniyar li'irabin kalamanshi a iya falsafar da k'walwarta za ta iya d'auka, hakan ya sa har ya kammala ba ta sani ba sai da yayi kissing d'in ta kafin ta d'ago ta kalleshi " sai na dawo" ya furta yana fita, ita ko ta bishi da idanu ko adduar da ta saba masa yau ba tayi ba.



"Ohhh wow yanzu ya gama shaida min bai sona amma kuma jikin shi na so na kenan ina da dama kan ka, ka cigaba da b'oyewa Yaa Islaam amma ba zaka iya ɓoyewa ba har abada". Ta furta a fili tana sakin wani munafikin murmushi da ya sake k'awata fuskarta, kwashe kayan ta yi zuwa kitchen tana cigaba da murmushinta.



Ba ta dad'e a gidan ba ta tattara komatsanta zuwa office, ayyuka ta tarar ba laifi da yawa don har an fara gyaran azumi na 'yan gayu. Sorting turaren wuta na special Ramadhan package kawai suka yi da staffs d'in ta, sai lissafin da ya d'aukesu time musamman ita da ta yi zaman ware riba da kuma uwar kud'in. A lokacin ta sanya ordern kayan da hemani suke had'a mata, da na Sudan shi ma saboda kar sallah ya zo ba su da isassun kayan gyaran. Bayan zuhr ta samu aka mata gyaran kai suka mata kitson kalba 'yan manya mai matuk'ar kyau, ya kuma fito mata da fatar kanta dake fari tas. Ko 4 ba ta kai ba ta kama hanyar gida su ma ta shaida musu kar su kai 6 daga gobe ma da za a fara azumi 10-2 kawai za su na yi babu zancen kai yamma.




Maimakon ta wuce gida kai tsaye sai kawai ta zarce gidan Hajjah ita da ta gama cika baki ba ta zuwa gidan, tunda ko ta shiga kwanciyarta tayi a kafad'arta tana mata shagwab'a ita ko tana tureta wai ta girma. Cewa tayi " ni fa ban wani girma ba, Hajjahta ko min girman da zanyi ko ina da jikoki nima ai sai nayi miki shagwab'a saboda dai nice jikar ki da kika fi so".


"Ai ko da kinji haushi Lele a ce kina da jikoki kina sangarta ke da ya kamata su jikokin su yi miki, da yake kuma zama zan tayi har lokacin ko?". 



"Toh in ba ki zauna ba kwanciya za ki yi a lokacin".


"Eh mana kwanta dama zan yi kafin lokacin".

"Kwanta dama kuma, what's that?".


"Mutuwa kenan Lele".


Turb'une fuska tayi tana cewa " kuma ke ce wai zaki mutun? Wa ye ma yace miki zaki mutu kafin lokacin?".


"Haaa in ban mutu ba tsayawa zan yi gadin duniya ko me? In ma har na kai lokacin ai na zamar muku kaya ba k'arami ba sai dai in ta damunku da wahala".



"Ba wani wahala mu mun fi son ki a ko yaya kike Hajjah, in kika mutu ya kike son na yi ai ni ma mutuwan zan yi, so ki daina maganarta please".



"Ban da ke da abinki Lele ai mutuwa dole ce ko mun so ko mun k'i, yau ina Aji Garwa, ina Bunami ina Mai Yerwa? Duk ba sun rasu ba? Ai Allah bai barin wani don wani ya ji dad'i. In kwanana ya k'are dole in tafi kuma babu wani mutuwar da ke ma zaki yi haka nan zaki hak'ura ki fawwalawa Allah. In kika mutu ki bar Burhaan da yaran da zaki haifa da wa?".



"Ni dai Hajjah please...! Ki daina wannan maganar, Allah in kina yi hankalina tashi yake yi. In shaa Allah ba zaki mutu ba" ta k'arashe da kuka, dariya Hajjahn ta yi tana cewa " ikon Allah, wannan kuka kamar an ce miki na mutun ne? Ai kya tara hawayen zuwa san da zan mutun sai ki samu damar sharce kayanki".



Jakarta ta figa ta nufi k'ofa har lokacin kukan take yi ba kuma na shagwab'a ba, Aa na gaske fa kamar an ce ta mutun ne da gaske. Kawai ta na imagining rayuwarta babu Hajjah ai gwara ta mutu da ta ga wannan ranar, Umma da ke k'ok'arin shigowa ne ta ganta a rikice da sauri ta sa hannu ta janyota zuwa jikinta don ta tsorata a tunaninta ko wani abu ne ya faru da ita ko a cikin gidan.
 

Ba tareda ta lura da wanda ya rungumeta ba sai ta sake shigewa jikinta tana sake sakin kukan da k'arfinta, jan ta tayi zuwa cikin gidan nan ta tarda Hajjahn zaune tana murmushi da girmama rigimar Lele wai daga magana sai kuka. 




Sallama ta yi tana mai bin Hajjajr da idanu, sai dai ba tayi magana ba illa zama da sukayi a kujera mafi kusa da su. Ko gaisawa ba ta tsaya yi ba ta fara aikin lallashi duk da ba ta san abinda aka yi mata ba, sai da ta samu ta tsagaita kafin ta dubi Hajjahn tana mai cewa " nda dubdo Hajjah ".


"Klewa Sato, klewa slai ya gidan daga zuwa kin ci karo da rigimar d'iyarku da bai k'arewa kamar ta d'iyar goye". Ta furta cike da shaawar yadda ta rungumeta a jiki, alamun soyayya mai k'arfi tsakaninsu ko yanzun ma da suke maganar a lafe take a jikinta sai sauke ajiyar zuciya takeyi.



"Wallahi fa Hajjah, ai farko hankalina tashi yayi na yi zaton abun dake ya faru ashe da ita ne yau an samu sab'ani da sahibar taki kenan na ga zata yi yaji a fusace".


"Ina fa aka samu sab'ani rigimar Lele ce fa da ba ta k'arewa, wai dan na ce mata zan mutu....." Nan ta kwashe labarin abinda ya faru tsakaninsu, wata muguwar dariya ce ta kusa sark'e Umman sai dai Allah ya taimake ta danne musamman ma yanda ta ga Lelen tana shirin fashe musu da sabon kuka.



Cewa tayi " Aa Hajjah ina fa magana kina zancen mutuwa kusa ai sai mu ma mu rikice mu fita hayyacinmu kar ki damu Lele Hajjahnmu ba yanzu za ta mutu ba " cikin muryar kuka tace " amma fa Umma kina jin fa abinda take sake maimaitawa ".



Hajjah tace " ai gwara ku zauna cikin shiri, ke kuma Sato ki daina d'aurata kan keken b'era ita mutuwa ko ana so ko ba a so sai na tafi".



"Hajjah kiyi ta tafiya, Allah ya tsare hanya gwara in tafi in bar miki gidanki don kin ga nazo ne da har kike maganar wata tafiya " ta furta tana sake jan jakarta hawayenta suna dawowa kamar ma jira take yi, sake kamota Umma tayi don fishinta yafi kama da na mai juna biyu duk da dai tun kusan wata biyu baya suke wannan hasashen amma har yanzu ba amo ba labari. So yanzu tana sa ran hakan don ta san masu ciki da ɓacin rai, so duk abinda zai iya jawo matsala ga cikin ba zata tab'a so ba. Ta gefe guda kuma tana jinjina girman shak'uwar dake tsakanin Lele da Hajjah, yanda take kukan nan yau in aka ce mutuwa ta yi ai k'ila sai dai a dinga shek'a mata ruwa ga kuma dariyar reaction d'in nata.


Cewa tayi " don Allah Hajjah ki yi hak'uri a bar maganar kin ga yanda hankalinta ya tashi kar wani abu ya sameta". Tace " ki daina biyewa 'yarki wurin son zuciya fa ahh toh, ai ba don in zauna da ita aka halliceni ba ibada nazo yi kuma ita barin duniyar ce cikon ibaduna ".


"Mun san haka Hajjah amma kin san irin wannan gaskiyar ba abu ne mai dad'i ba, so tunda dai tana kan kowa sai a bar maganar iya haka don Allah".


"Ni Umma kawai ki bar ni in tafi gida don Allah".



"Za ki tafi gida amma ba a haka ba Sweetheart, sai kin natsu tukunna ". Zama tayi kawai tana sauke ajiyar zuciya ta san mutuwa dole ne amma na Hajjah ina! Ai gwara ita ta mutu da tayi witnessing wannan ranar, Umman ce cikin sigar lallashi tace " ki kwantar da hankalinki, Hajjah wasa take miki ba wani abu ba in shaa Allah za ta rayu taga 'ya'yanki".



"Wai a na wasa da mutuwa ne Sato? Ai ita d'in ba abar wasa ba ce sai dai muyi ta adduar Allah ya ba mu sa'ar tafiya kawai ita ma ta sani son zuciya ne kawai irin nata ".



"Ni dai Hajjah na rok'e ki please ki bar maganar nan, Allah zuciyata za ta iya bugawa". Ta fad'i da iyakar gaskiyarta hakan ne ya sa Umma jin tsoron kar wani abu ya samu tayin cikin da take hangowa a jikinta tace " an bar ta, kin ji kar ki saka ka kanki damuwa ".


Hummm kawai tace sai yanzu Hajjah tace " Bibtie wannan kuka haka? Ai sai kan ki yayi ciwo, kar ki damu ba inda zan je ina nan tare da ke". Ta k'arashe tana janyota jikinta cikeda tsokana amma ko gezau ba tayi ba, hasalima shiru tayi ba tareda ta tanka ba don har yanzu ba dai-dai take jin kanta ba.


Umma tace " kin ji ko?" Baki ta bud'e da niyyar amsawa sai wayarta yayi k'ara, d'agawa tayi tana duba mai kiran "infinite love" ne ke yawo akan screen d'in, da sauri ta tashi ta nufi ciki cikeda kunya don har Umma ta ga sunan ita dai ko a jikinta sai ma wani fara'a da tayi na musamman.



Tana shiga ta d'aga lokacin wayar na gab da tsinkewa " Hello" ya furta cikin muryarshi da alamun gajiya, a hankali cikin k'ok'ari ln daidaita maganarta tace " Hello Yaa, barka da yammaci ya aikin?".


"Are you okay? Ko ba ki da lafiya ne?" Ya tambaya da d'an damuwa a harshenshi, amsawa tayi da " i'm fine....."


"But muryar ki ta nuna akasin haka, ko dai har yanzu maganar jiya ce?".


"Aa wallahi Yaa, maganar da ta riga da ta wuce?".


"Toh me yake damunki? Tukunna ma where are you?".



"Ina Yerwa, gida Hajjah".


"Ok" kawai yace yana katse wayar, kan shi tsaye number Hajjah ya kira. Tana ganin kiran sai da ta sanya dariya ta nunawa Umma tana cewa " an kai k'arana da alamu". D'agawa tayi cikin saita murya alamun ba wasa ta tayi sallama, amsawa yayi ko gaisawa ba suyi ya jeho mata tambayar " Hajjah wani abu ya samu Nadeefah ne yau?".



"Wata Nadeefah kuma?".


Rintse idanu yayi yana cewa " kash Hajjah, yanzu fa na kirata na jita wani iri kuma tace min tana gidanki shi yasa na kira don in ji ko lafiya".



"Ita ba ka kirata ba sai ni marainiyar wayarka ka turke ni da magana ko gaisuwa babu tunda ga warinka ko?".



"Haba Hajjah ni fa ba abinda ya sa na kira ba? Ki yi hak'uri toh Nda dubdo?".


"Ban sani ba" tas fad'i daidai lokacin Nadeefah na shigowa parlorn, hararar wasa ta jefa mata tana sauraronshi yana cewa " Allah ya huci zuciyarki". Ameen ta furta cikin son gimtse dariyar da ke k'ok'arin turketa, katse wayar tayi ba ta ko jira cewarshi ba ta dubi Lelen tana cewa " sannu masu miji, har da kai k'arata ko".



"Ni fa ban kai k'ararki ba, meye ma abun kai k'ara a ciki? Na lura yau dai ban zo da sa'a ba, gwara in san inda dare yayi min in kin sauka na dawo dama barka da azumi na zo miki tunda kuma baki so ni kinga tafiyata". Ta k'arashe tana mik'ewa tsaye jakarta da ke watse gaban Umma tana cewa " Umma mu zamu tafi, Allah ya sa a d'auka a sa'a ya kuma ba mu ikon yin ibada karb'ab'biya, Hajjah na wuce ".


Dariyar da take dannewa ne ta kufce mata tana cewa " zo Leleta, zo Bibtie". A shagwab'e ta shige jikinta tana shesshek'a kamar wacce za tayi sabon kuka "shhhhh, kar ki yi kuka kin ji masoyiyata?".


"Ba zan yi ba, ki yi hak'uri kin ji?".


"Nayi to Lele ai baki min komai ba, wasa ne nima nake miki kar ki sake d'aga hankalinki ina nan tare da har sai ran da kwanana zai k'are kin ji ".


"Tohm Hajjah ina son ki da yawa ne shiyasa na shiga damuwa, na san babu wanda zai dawwama har abada amma wallahi ban shirya wa rabuwa da ke ba".



"Cikar imani shi ne ki zama cikin shiri da wannan ranar, don daga ni har ke ba wanda ya zo don ya zauna har abada ina sonki nima abar sona".



Ajiyar zuciya kawai ta sauke tana kwantar da kanta a kafad'arta tana lumshe idanu, Umma tana zaune tana kallonsu cike da sha'awa tabbas ana fad'in shak'uwar Hajjah da Lele ba ta tab'a sanin abun ya kai haka ba sai yanzu. Ai ko uwa da 'ya sai haka, Allah dai ya sake had'a kan su ya kuma bar soyayyar dake tsakaninsu.



Daga wannan maganar ta gyare tana zabga hira da su Hajjahn, ba ita ta baro gidan ba sai after 5 har tuwo da sukayi da miyar gyad'a( kase in ji fulani wacce ake yinta da gyad'ar k'uli da kuma d'an yakuwa da alaiyaho sai man shanu da suka zabga sai k'amshi yake yi) ta d'auka ta wuce da shi gidanta tana jin ta sakayau. A harabar gidan ta iske Burhaan shi da Hamza dake ta shiga da kaya ciki, tana fitowa daga motar ya bita da idanu basket d'inta ta d'auko ta nufi in da yake.



"Sannunku da aiki" ta fad'i a sanda ta k'arasa gabanshi, da kai ya amsa yana mai zura mata idanu studying her face da kyau. "Me ya samu idanun ki?".


"Nothing Yaa" kai ya gyad'a yana nufar hanyar parlorn bin shi tayi a baya, a dining ta ajiye basket d'in ta fara tayashi shigar da kayan cikin kitchen. Kamar yanda ta saba shirya kayan ta yi kowanne ta ajiye shi a inda ta saba, siyayya ce mai yawa sosai na kayan cefane har da fruits da kayan miya har da nama da kifi. Kusan a tare suka kammala tana wanke hannu ya shigo kitchen d'in yana kallonta yace " Ban san me kike son b'oye min ba Nadeefah, fuskar ki ta kumbura idonki yayi ja sosai ga muryarki kamar ta masu mura wanda ke nuna kin yi kuka sosai ba zaki iya gaya min ba ne saboda ban kai ba ne ko me?" Ba sauk'i a harshenshi yayi maganar alamun ran shi ya ɓaci.



Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa " ko d'aya Yaa, kawai dai ba wata matsala ba ce mai girma shiyasa....."



"Shi ne har ta saki kuka?" Ya katseta.


"Hajjah ce fa take ta maganar mutuwa.....wai mutuwa za tayi ta bar ni......." Ta ba shi labarin abinda ya faru sababbin hawaye na taruwa a idanunta, cewa yayi " shi ne wani abun kuka saboda ke dai hawayen ya miki yawa right? Samun wuri ne da sangarta ce ke damunki ba komai ba,,,,,,,,ki duba kayan nan abinda babu sai ki rubuta da ma abinda na kira in tambayeki kenan d'azu na ji kina kuka ".




Tura baki tayi kawai ba ta yi magana ba tana bud'e ledar da ya ajiye ta k'arshe mai d'auke da Maggi da spices su cumin, star anise,cinnamon, parsely, bay leaf, thyme leaf, corriander, garlic, nutmeg da duk wasu kayan gyaran girki dai na 'yan gayu. Sai d'ayar kuma salad cream ne, ketchup, su cheese, ham, icing sugar, whipping cream da sauransu. Cewa tayi " komai sun yi wainda ba a siyo ba kuma duk muna da ragowarsu masu yawa ma, Allah ya k'ara bud'i Yaa".



"Ameen ya rabb". Yana gama fad'in haka ya fita, da murmushi ta rakashi ta ciro containers d'in da take sanya spices d'in ta wanda suke nan counter guda akwai na powder da raw duka daban an rubuta sunan kowanne ta zuba a ciki. Sauran kuma na cikin fridge ta maida su ciki sake wanke hannunta tayi ta fito ba ya parlorn da alamu ya tafi shirin masallaci don an kusa shiga jakarta da mayafi dake kan d'ining ta d'auka ta wice ciki don yin wanka kafin lokacin sallah yayi.





Washegari d'aukacin alummar musulmai suka tashi da azumi ta Ramadana mai girma, daraja da kuma falala mai yawa. Kusan a tare suka ta shi ita da Burhaan alwala sukayi shi ya jasu sallahr cikeda kushu'i da tawaliu sai 3:30 suka idar. K'urani ya janyo ya bud'e dubanshi tayi cikin sanyin murya tace '' me kake so na sahur?".


"Dafaffiyar madara da apple". Gyad'a kai tayi tana sauke ajiyar zuciya 'shi ma ba ya suhr da abu mai nauyi kenan' ta furta a k'asan ran ta, tashi tayi ta bar shi a zaune yana karatunsa. Kitchen ta nufa madarar tayi warming ita kuma ta had'a oat wa kanta ta yanka strawberry, apple da dabino ta sanya a cikin madarar da oat ɗin ta sai ruwa. A tray ta d'aura ta shiga da shi zuwa d'akinshi da a can suka kwana yau, a kan side table irin na gefen sofan nan wanda yawanci fitila ake d'aurawa akai da sauran abubuwa ta ajiye masa ita kuma ta zauna tana shan na ta. Tasowa yayi ya zauna a sofan ta gefenta, madarar ya shanye duka sannan ya d'an tattab'a fruits d'in da ta ajiye masa ba laifi shima ruwan ya sha ya koma bakin karatunshi har lokacin ba ta gama shanye oat d'in ba.



Strawberryn ta sha ita don ya cinye apple d'in duka sai dabino, ruwa itama ta sha ta koma kan daddumar da yake a zaune. Kanta ta d'aura kan kafad'arshi tana mai sauraron karatun da yake yi cikin harshen warshu don shi da mafi akasarin 'yan familyn haddar warsh sukeyi sai in sauka na biyu za suyi suke yin hafs, ko su da ba su tashi a k'asar ba sun yi warsh amma hafs ta fi iyawa don ma makarantar su da ke atlanta suna yin warsh duk da ba a matakin farko ba amma tana son ruwayar sosai musamman in tana jin karatun cikin cikakken k'iraar wanda ya k'ware a tajwidinta imaala tana fita sosai irin yanda Burhaan yake yi lumshe idanu tayi tana bin karatun a zuciyarta.




Sai da aka kira sallah lokacin yayi tak'arar kusan izu hud'u masu kyau, kafin ya tashi raka'atainil fijr sukayi tare kana ya wuce masallaci ita kuma tayi na ta a gida. Tana idarwa ko gado ta haye tana lumshe idanu alamun bacci, ba ta dad'e ba baccin ya d'auketa shi ma yana dawowa AC ya k'ara ya shige gefenta. Sosai suka yi bacci shi ya fara tashi kusan 8 da 'yan mintuna, gyara mata rufa yayi ya wuce toilet. Wanka yayo ya fito shiryawa yayi cikin shirinshi na kullum, har ya kammala ba ta sani ba kissing d'in ta yayi a goshi yayi wucewarshi.




Ba ita ta tashi ba sai 10 hamma tayi tana mik'a, bin d'akin tayi da idanu babu kowa sai ita kad'ai sauka tayi daga gadon tana gyarawa. Ba ita ta bar gidan ba sai 12:17 har ji tayi ma kaman ta fasa fitan don hakanan azumin yake bugunta, ko a office d'in ma kwanciya ta dinga yi tana bin wuri 2 nayi suka tashi kowa ya kama hanyar gida.



Ko da ta koma gidan nan ma sake kwanciyar tayi tana karatun Quran sai after 3 da ta d'an ji dama-dama ne ta fito, shirin abincin bud'e baki ta fara. Flat bread tayi da chicken curry, sai buttered yam da vegetable egg rice sai ta had'a salad. Tea ta dafa sai kunun aya da ta yi wanda yaji kwakwa da d'an dabino mara yawa , saboda sonta da kifi tayi grilling ta d'an yi sauce mai d'an yawa ana yi ana video abinka da 'yan #first_Ramadhan_with_Habibie. Sabbin kuloli da kwanuka ta bud'e ta sanya a ciki tana cikin jerawa a dining Burhaan ya fito ashe ya dawo tun kusan four kwanciyarshi yayi duk da k'amshin abincin da take yi yana ta kai masa ziyara sai yanzu 6 ya fito. 



Sannu da aiki yayi mata yana zama a cikin kujerun parlorn, waigowa tayi ta kalleshi da murmushi tana amsawa shi ma duk yayi laushi alamun yana jin azumin ba ta k'araso inda yake ba don tayi aiki sosai har k'arnin kifi take ji a jikinta, yayinda shi ya bazo k'amshi mai sanyi fuskar nan wasai gashin nan ya sha gyara sosai. Komawa tayi kitchen ta ciro fruit ta wanke da dabino again, ruwa ta sake d'aukowa da drinks ta ajiye a kan dining d'in duk yana ta kallonta cikeda yabawa tana kammalawa d'aki ta gudu wanka ta je ta yi ta shirya cikin top da skirt bak'ak'e na Balenciaga inner cap fara ta sanya ba ta sa turare ba khumrah ce kawai ta shafa da spray sai lipgloss turarenta na Ramadhan special ta sanya a burner ta kunna humidifier slippers masu taushi bak'ake suma ta sanya ta d'auko wayarta ta fito parlorn.





Yana zaune yana kallon news a tashar France24, ba ta zauna ba sai da ta kunna turaren wuta da humidifier a kusurwowin parlorn sannan ta sake zama a gefenshi tana mai sauke ajiyar zuciyar gajiya da tayi. Dubanta yayi ya sake furta " ushe " fari tayi da idanunta tana cewa " thanks" daga haka ta d'an maida kan ta ga TVn da yake kallo itama don in yamma tayi da azumi ba ta cika son magana ba. Ko 10mins ba tayi da zama ba aka kira sallah tashi tayi da niyyar d'auko ruwa da dabino sai dai ya hanata damar hakan ta hanyar janta cikin jikinshi idanunshi ya lumshe yana had'e bakinsu wuri d'aya sai da ya d'auki mintoci kafin ya janye yana mai sauke ajiyar zuciya, ita ma idanun ta lumshe tana mai mamakin halayyar wannan bawan Allah.




Sakinta ya d'anyi ta samu ta tashi shi ma mik'ewar yayi suka nufi dining, ruwan d'umi ta tsiyaya daga dispenser ta zuba zuma a ciki ta juya ta sha. Shi ko apple ya d'auka yana ci sai da ya cinye guda d'aya kafin ya d'auki dabinon suma ya ci, ita ma dabinon ta ci da d'an raspberry. Kana ta dubeshi tana cewa " barka da shan ruwa". 


"Bari in je masjid in dawo". 



" A dawo lafiya " ta fad'i tana murmushi da kai kawai ya amsa mata instead ya wuce masallacin kai tsaye sai da ya fara shigewa toilet d'in parlorn ya kama ruwa ya sake d'aura alwala kafin ya wuce itama ta wuce ciki yin sallahr tata.



Tana idarwa ta dawo parlorn ta zauna, ba ta dad'e da zama ba ya shigo shi ma bai zauna a kan kujera ba sai a kan rug yana sauke numfashi. Saukowa tayi gabanshi tana cewa " a kawo nan ne?" Kai ya gyad'a mata tashi ta yi ta fara d'auko kayan tana jerawa a gabanshi, tea ta zuba masa a teacup ta sanya 2 cubes na sugar tana juyawa mik'a masa amsa yayi ya kai baki da bismillah. Flat bread ta sanya masa da buttered yam d'in sai ta zuba chicken curry d'in a bowl k'arama shi ma ta ajiye a gabanshi, thanks ya furta a k'asan mak'ogwaro kawai ya sa hannu ya fara ci. Ita ma nata ta zuba suka ci abincin ita dai ba da yawa sosai ta ci ba, tean ma ba ta sha ba sai shi ne yayi ta zubawa yana k'erawa kununta ta sha ta sha ruwa ta koma gefe.



Sai da ya ji ya kai geji kafin ya cire hannunshi yana hamdala, dubanta yayi da kyau yana sakin fuska yace " sannu da k'ok'ari Allah yayi miki albarka ". Murmushi ta saki har hakan ya sake fito da dimples d'in ta sosai tace " Ameen Yaa" a d'an bazata yace " yanzu an daina Aortan ne wai?" Rufe idanunta tayi tana sake fad'ad'a murmushinta tace " ai ba ka son sunan ne shiyasa na daina ". Kai ya gyad'a yana cewa " ohhh, hakan ma yayi kyau". Daga haka bai sake magana ba, ita ma haka sai ma kwashe kayan da ta yi zuwa kitchen wainda suka b'ata while sauran abincin da suka rage kuma ta ajiyesu a kan dining dawowa tayi parlorn ta zauna wayarta ta janyo ta fara kiran numbern Ummu. Barka da shan ruwa tayi mata sukayi waya har da su Ɗayyib da Ɗalhat har da Abbu don lokacin duk suna tare dukansu, sun dad'e sosai suna hirar yana ta kallonta. Suna katse wayar ta kira Hajjah nan ma sun dad'e sosai suna hira kamar ba zasu rabu ba, YaMara ta kira da su Ya Madari duk ta musu barka da shan ruwa sai Umma da Abba duk suma. Wani mugun kunya ne ya kamashi don shi bai ma yi hakan ba, amma ita ji ba ta bar kowa ba sai da ta kira duk kusan manyan familyn kafin ta ajiye wayar.



Shi dai yana zaune har aka kira ishai bai fita masallaci ba shi ya ja su ishai da taraweeh wanda ana idarwa nan ta kwanta kan daddumar ba ta ko dad'e ba bacci ya kwashe ta a wurin, da idanu ya bita cikeda tausayi don ya san ba ta saba wannan wahalar ba amma yau d'aya tayi abun a yaba. Maida ta yayi kan gado shi ko ya fita waje, pool ya nufa ya shige ciki ya dad'e yana swimming sai kusan to 10 kafin ya fito towel ya d'aura a kan boxers d'in jikinshi ya koma ciki time d'in har ta farka daga baccin da tayi har ta wuce d'akinta


Armless shirt ya sanya ya fito parlor, bai jira fitowarta ba ya zauna a dining ya zuba shinkafar da ta dafa 'yar dai-dai da salad sai lokacin ya sha kunun ayar da ta yi. Yana cikin cin abincin ta fito sanye da nighties marasa nauyi amma ba irin shara-sharar nan ba sai dai sun kwanta mata a jiki zama tayi itama ta d'an sa abincin ta ci ta sha kunun sosai tattara kayan ta yi ragowar abincin ta had'a da na iftar d'in su flat bread d'in kawai ta ajiye don tana son ci da asuba. 


"Ko za a mik'awa securities abincin nan kar a bar shi ya lalace?". Ta furta cikin muryar gajiya cewa yayi " kin yi tunani mai kyau bari in kai musu ". Had'asu yayi tsaf ya fita ya mik'a musu duk da yana ba su kud'in abinci ne amma ta kan ba su duk da ba kullum ba time to time dai haka. Ko da ya kai musu sa wa yayi suka juye abincin kafin ya shigo mata da warmers d'in lokacin har ta fara wanke-wanke ajiyewa yayi ya fita, wanke su ta yi tsaf ta tsane ta jera su kafin ta fita itama zama tayi ta kwantar da kanta kan cinyarshi ta kunna data WhatsApp ta shiga tana kallon story murmushi take tayi tana kallon wulak'ancin da a ke ta yiwa 'yan first_Ramadan_with_Habibie. Ba ta wani dad'e ba ta rufe datar tana kallon news d'in da bai gajiya da kallonsu, sai 11:30 suka wuce d'aki ba su wani dad'e ba suka shige ciki suka kwanta.



Haka ranaku suka cigaba da shud'ewa azumi yana ta game jikin mutane, koina ka bi kowa zaka gan shi da hula da casbaha ko counter da asuwaki. Ta gefen Nadeefah dai tana ji a jikinta da ayyukan azumin da ta kasa sabawa da su, sai dai juriya da aro ta yafa har yau ba ta tab'a nuna gazawarta ba har yau da aka d'auki na goma kuma yau ne take shirya iftar ga duk familynsu dake cikin Kaduna da kewaye wanda ba ta sha wani wahala da Burhaan ba tana gaya masa cewa yayi Allah ya kai mu kawai.



Tun da azahar ita da su Suleim dake fama da tula-tulan cikinsu da ya turo gaba sosai da 'yan aikinsu suka fara aikin abincin, da yake hannu da yawa wai maganin k'azamin miya ya sanya aikin na su yake sauri sosai. Sun yi abinci nau'ika tundaga kan gudun gyad'a mai dalayi a ciki da k'osai, har da masa, sinasir da miya sai a kayi alkhindir da alkubus, jollof rice, har da pizza da sukayi kusan guda 5 sai peppersoup na kan sa da na kaza sai yam pritata da sukayi shi ma da egg sauce, sannan potato cake sai tea da yaji kayan k'amshi zob'o suka had'a mai dad'i sai aka yayyanka fruit suma.  A bakin swimming pool aka shirya abincin a kan manyan carpets masu taushi ga k'amshin turaren rushi ya na tashi ga haske mai k'ayatarwa.




10 minutes kafin kiran sallah gidan ya cika da 'yan family kowa ka gani sanye cikin kayan alfarma, sai hira ake yi cikin nishad'i da raha don wurin tun daga kan su Hajjah har zuwa kan 'ya'yayen su Yaa Budu da Aunty Najwah duk sun zo har da Aunty Ainah mutanen duniya. Ana kiran sallah kowa ya ci dabino da ruwa, sannan Ya Kyari ya ja su sallah gabad'aya sukayi jam'i. Da aka idar da sallahn ne aka fara iftar d'in cikin natsuwa, maids d'in da suke wurin ne sukayi serving d'in su suma suka saka na su suka koma gefe. Sai da aka kammala ne aka ne aka fara hirar yaushe gamo don tabbas rabon da ayi had'uwa irin wannan tun na meeting, har taraweeh duk a nan suka yi ana idarwa aka fara haramar tafiya. Yayinda maids d'in suka kwashe kayan wurin tsaf sai da suka wankesu suka kimtsa mata gidan tukunna suka wuce, su ma ko ten ba su kai ba kowa ya watse zuwa gidanshi ai ko ranar ba k'aramin baccin gajiya ta yi ba sai da ta kusa makara da asuba Burhaan ne ma ya had'a musu abin suhr.



Washe gari ko da ta tashi gyara tayi kawai ta wuce office, in da aka kunce mata gashinta aka wanke mata shi tsaf ba ta ko jima ba ta wuce gida kayanta ta had'a tsaf ta sake dubawa don tabbatar da ta d'auki duk abun buk'ata. Washe gari da misalin k'arfe 2:15pm jirginsu ya tashi zuwa Abuja ita da Burhaan, Hajjah, Yamara da Ya Madari har da Yana a tafiyar don ta can za su bi jirgin tafiya umrahnsu.



Tun da jirgin ya tashi take faman duba agogon hannunta, burinta kawai bai wuce ta ganta gidan Ummu ba. Sosai take kewar garin don rabonta da shi tun dawowarta da Burhaan da ta sha gwagwarmaya ba k'arami ba, duk Burhaan yana hankalce da ita amma kamar yadda ya saba yin shiru bai ko tanka ba a haka har suka sauka.




Tayyib da Dalhat ne suka zo d'aukarsu wanda suna fitowa daga arrivals ta k'ank'amesu kamar wata yarinyar goye, kau da idanu Burhaan yayi cikeda jin mugun kishi bai ko sake duban inda suke ba har Dalhat da ta fara hayewa ya sauketa yana dubansu Hajjah yana musu barka da zuwa da ma Burhaan d'in a d'an dak'ile ya amsa masa babu faraa jakukunansu suka taya su kwashewa zuwa boot. Ita dai motar Dalhat ta shige duk da yanda Tayyib ya gama mata nacin na shi za ta shiga, ita kuma ta san halinshi in dai ta shiga sai sunyi fad'a shi kuma yana gudun k'aidojin Burhaan ne shiyasa yake son ya jona shi da Dalhat tunda ko ba komai suna da d'an fahimta sosai. Burhaan ne ya shige gaban motar su ya YaMara suka shiga baya, ita kuma ta Dalhat Nadeefah a gaba sai Hajjah da yana a baya a haka suka ja zuwa gidan Ummu dake Embassy.



Suna shiga ko jakarta ba ta d'aga ba ta fara k'walla kiran Ummu kamar wacce ta warke makanta, kusan karo Ummu dake shirin bud'e k'ofa ta fito don tarbarsu sai dai ko kulawa da hakan ba tayi ba ta d'afe ta tana sakin kuka. Rungumeta tayi kawai tana lallashinta da buga bayanta, su Hajjah suka k'araso inda suke Tayyib da ke rik'e da backpack d'in Burhaan ne yace " ai dama nace ba ranar da Nadeefah za tayi hankali ta daina sargarta ji be fa kamar wata jaririya kina wani b'are k'aton baki kina wani ihu ".




Janyewa tayi daga jikin Ummu hakan ne ya ba ta damar fitowa da kyau tana wa su Hajjah barka da zuwa ita ko murgud'a baki tayi wa Tayyib d'in tana cewa " ai ko ashe zan rigaka yin hankali tunda kai ma har gobe baka daina sangartar ba shiyasa ma ba ka iya zuwa koina kullum kana gefen Umma ". Tasowa yayi zai hayayyak'o mata Dalhat yace " ai ba k'arya tayi ba Tata ". Umma ce tace " kuna ganin mutane ku ba su hanya su wuce kun tsaya kuna yin halinku da kuka saba ko?".




"Sorry Ummulkhair" suka fad'i cikin haɗa baki ba ta tanka ba ta jagoranci su Hajjah zuwa cikin gidan, zama suka aka sake sabon gaisuwa Nadeefah dai na mak'ale a gefenta kamar za ta koma ciki. Shi dai Burhaan bai tanka ba fuskar nan a tsuke kamar an masa dole, Hajjah ce ta dubi Ummu tana cewa ''Yanzu ai ba lokacin hirar nan bane Sameeha bari mu fara natsawa kafin a kira sallah''. Murmushi tayi tana cewa " toh Hajjah ku mu shiga ciki, kai kuma Dalhat ka raka yayanku d'akinshi" tana fad'in haka ta taya Yana kwasar jukunkunansu zuwa ciki in da a nan k'asan aka ware part guda don zuwan Hajjah ita d'aya inda aka tanada komai na buk'ata aka ajiye duk da ko in ba a yanayi irin wannan ba ba zuwa gidan take yi ba.




A parlor kuwa suna wucewa Burhaan ya mik'e tsaye bai ko dubi inda take ba ya nufi k'ofa, Dalhat yana tafe a bayanshi da kayakinshi sai da ya kai k'ofar ne ya waigo ya kalleta yana cewa " ke ba zaki tashi kiyi sallah ba ne?".



Lumshe idanu tayi ta bud'e tace " yanzu zan tashi Yaa" uhmm kawai ya furta ya k'arasa ficewa, Tayyib yace " ai ke dama sai irinsu Yaa Islaam, shi ma na lura fama yake da rigimarki " murgud'a masa baki ta sake yi tana cewa " yana fama d'in, ko famanka ne ?" tana fad'in haka ta ruga zuwa sama d'akinta ta shige yana nan a gyare tsaf kamar tana ciki, gadon ta haye cikeda wani annashuwa na musamman tana cewa " kai nayi missing ɗakin nan" ta k'arashe tana janyo lilly teddynta da ta dinga naci a kawo mata abinta aka k'i har ta gidan Hajjah ma fitar da shi tayi ta kyautar ta kuma kashe mata kashedi akan ko da wasa ta ji ta sai wata toh har gida za ta biyota ta cicci mata. Murmushi ta sake tana cewa "ohhh my lilly, I missed you" kamar tana magana da mutum.



Haka ma a wurin wanka ta d'inga yi komai na toilet sai da aka gaya musu an yi missing d'in su, tana shiga closet d'in ta ko zama tayi dirshan tana kallon kayanta na gida tace "ai ko kwashe kayana zan yi, jifa yanda duk na bar kaya a nan ina can ina nemansu tabd'in kuma masu kyan ne fa ma,,,,,,,na san kuma kuna missing mai ku toh gani nan nazo". Da k'yar ta iya zab'an kayan da zata saka don duk wanda ta d'auko sai ta yi magana da shi kafin ta ajiye a d'auko wani tana tuna siyan kayan in kuma Ummu ko Abbu suka siya shi ma sai an tuno har da date d'in da aka siya..................



Ahhhh lallai da gaskiyar Tayyib yin hankalin nan na Nadeefah da d'an saura maybe kuma lokacin ya kusa.

Deejasmah 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.