Free chapter · Read without an account
The Foyer Incident
by NorthernAngel · His Rose
Bayan few minutes, Zafar ya ja hannun Zara suka fito bedroom. Gado ya nufa da ita yana cewa, “Khairy tashi.” Khairy dake kwance ta miƙe, ta ɗauki abubuwan da ta shigo da su ta nufi inda suke. Zama Zara ta yi kan gadon tana jingina bayanta jikin headboard ɗin gadon, yayin da Zafar kuma ya sa soft linens ɗinda ke kan gadon yana rufe mata fararen cinyoyinta dake bayyane, preserving her modesty. Nan ma dramar da ta fi ta ɗazu aka sha da Zara gurin fixing drip ɗinnan. Wani irin rakin bala’i gare ta, ga tijara! Kuka take yi tana tirjewa, tana buge hannun Khairy, completely terrified of the needle. Har gwara gurin ɗibar jinin ba ta yi rigima haka ba. Gaba ɗaya Zafar ya rikice; ganin yadda take kuka yana taɓa zuciyarsa, he couldn't stand seeing her in distress. Ya kalli Khairy softly yana cewa, "Khairy, barshi kawai! Just stop... I think we should try another method." Cikin sanyin murya da ƙwarewa, Khairy ta tunatar da shi mahimmancin IV fluids ɗin ga jikin Zara da kuma ƙaramin cikin jikinta. Ta ce masa dole ne ta daure saboda lafiyarsu. Da ƙyar dai Zafar ya lallashi Zara aka sa cannula ɗinnan a hannu. Har aka gama komai ba ta fasa kuka ba, sai dai tana kwance a jikinsa, sautin kukan nata na fita a hankali, her frame trembling against him. Khairy ta sauke ajiyar zuciya cike da gajiya, wiping a stray sweat from her brow. Zafar ya kalle ta yana cewa, "Please head downstairs, and the maids will serve you." Khairy ta gyaɗa kai tana cewa, “Zan wuce after eating, kafin ya ƙare na san Omar ya dawo.” Zafar ya gyaɗa kai yana cewa, "No problem. How many days is she going to be on the drip, since you mentioned it’s a regular one?" Khairy dake packing kayanta ta ce, “Three days to four, saboda ta yi regaining nutrients ɗinta, kuma ta fara cin abinci. If she still can't eat, let her try cold foods. Tunda kace she likes cold drinks, but you know liquid alone is not enough. Ta dinga shan cold smoothies, frozen yogurts, ice cream, frozen fruits, chocolate pudding... Sannan you should also stock up things like boiled eggs, boiled or fried potatoes, pasta salad, and chicken strips a fridge ko freezer ma su yi sanyi. Duk za ta iya ci InshaAllah.” Zafar ya gyaɗa kai yana cewa, “Thank you!” Khairy ta kalli Zara dake jikin Zafar ta ce, “Toh amarya, Allah ya bada lafiya ko?” Zara ba ta yi acknowledging ɗinta ba, too exhausted and sulky to respond. Haka Khairy ta juya. Sai lokacin ta samu damar bin ko ina na gidan da kallo. Da ta fito cikin filin ƙaton library ɗinnan, ta ga ba kowa, unlike sanda suka shigo da Zafar da ta ga maids su biyu a gurin zaune suna hirarsu comfortably. Staircase ɗin third floor ta kalla tana gyaɗa kai cikin mamakin irin daular dake gidan nan, and the sheer architectural brilliance blowing her away. Tana sauka ƙasa, ta tarar da wasu maids guda biyu a zaune a parlour. Jagora suka mata zuwa dining room ɗin, inda ta ga abunci kala-kala a jere, a lavish spread fit for royalty. Zama ta yi, har da cire mayafin ta ta ajiye a gefe, ta ci abincinta sai da ta ƙoshi sannan ta tashi. Har waje maid ta raka ta, inda driver ke jiran ta a compound ɗin, ready to drive her back to the hospital. Ko 15 minutes ba’a yi ba da saukar Khairy, bacci mai nauyi ya ɗauki Zara, the heavy sedative from the drip pulling her under immediately. Tana kwance kan jikin Zafar har huɗu saura aka kira Asr. Kwantar da ita ya yi a hankali, tucking her in with absolute care, sannan ya fito ya nufi masallaci. Bayan ya yi sallah, ya fito tare da Baffa. Zafar ya gaya wa Baffa cewa ya fasa tafiya saboda Zara ba ta jin daɗi. Baffa ya yi mata addu'a, sannan ya ce zai shigo ya duba ta zuwa dare. Daga haka kuma ya ce masa, tunda ya fasa tafiyar, ya shirya in 4 days ranar Saturday za su je Abuja ɗaurin auren Muazzam. Daga haka suka yi sallama, Baffa ya shige wing ɗinsa, Zafar kuma ya wuce wing ɗin Yemma. Sama ya hau, a lounge ɗinta ya tarar da ita ga Imaan a kwance kan ƙafarta suna kallon TV abunsu. Ga parental remote control a hannun Yemma tana controlling ɗin kids power wheels ɗin da Mezyan ke ciki yana wasa abunsa, the room lookin peaceful, bakajin komai sai maganar TV. Zama Zafar ya yi yana cewa, “Ina Zwar da Noori suka shiga ne yau?” Imaan ta ɗan kalle sa ta ce, “Zwar followed Ya Ahmad over to the Nexus. And Noori is sleeping, I guess.” Gyaɗa kai ya yi. Daga haka ya ce a kawo masa abunci. A nan parlour ya zauna yana ba Yemma labarin Zara ba ta jin daɗi, dan har suma ta yi kuma likita ta zo ta duba ta. Ita dai Yemma jinsa kawai take yi, ba ta ce masa komai ba, her face unreadable as usual. Bayan ya gama cin abuncin, ya gaya mata ya fasa tafiyar. Nan ma ba ta ce komai ba, gyaɗa masa kai kawai ta yi kafin ta ce, “Sai ka shiga ka gaya ma Salmar, dan har ta fara shiri.” Gyaɗa kai ya yi, feeling a slight pang of awkwardness, daga haka ya miƙe ya yi mata sai anjima ya fice. Gida ya koma, yana zuwa ya wuce part ɗinsa. Kaya ya canza, inda ya fito daga shi sai shorts da singlet, ya ɗauki laptop ɗinsa. Daga haka ya fito daga part ɗin nasa ya wuce na Zara, inda yana shiga ya hau elevator so bai haɗu da maids ko ɗaya ba. Yana zuwa ɗakin ta, ya tarar tana ta baccinta peacefully. Cheeks ɗinta ya yi kissing softly, sannan ya koma ɗayan side ɗin ya hau gadon ya fara aikinsa, yana janyo wayarsa yana kiran EA ɗinsa to reschedule his entire week. Haka ya zauna a ɗaki throughout ranar yayin da Zara kuma take bacci peacefully, the IV fluid dripping steadily into her system. Daya ƙare kuma kamar Omar ya daidaici lokacin ne dan sai gashi ya kira Zafar yace yana parlour, bayan yayi masa iso kuma ya shigo ya cire mata duk tana bacci.. Sai cikin dare ta farka, inda ya taimaka mata ta yi sallolin ta, sannan kuma ta koma bacci. Ko ruwan da ya kawo mata ba ta karɓa ba, completely knocked out by the heavy medication… Zafar sai da ya yi four days a gidan Zara yana jinyar ta, bai fita ko ina ba sai masallaci da gida. Salma na ganinsa da safe bayan ya fito daga masallaci da kuma da daddare kafin ya shige gida yana zuwa ya yi mata sallama. Sometimes a wurinta ma yake dinner and their relationship is getting a lot better saboda Salma is now playing the perfect, understanding wife. Normally, in ya shiga za ta mai tayin abinci; in ya ci a gurin Yemma ya ce mata ya ƙoshi, in baici ba kuma ya je dining ta yi serving ɗinsa tana masa hira cikin kwanciyar hankali har ya gama, sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sosai ta ji daɗin samun kansa da ta ga tana yi, dan har a kan jikinsa tana zama kuma yana rungume ta. Sai dai kiss ne da ta taɓa gwada masa, kafin ta kai bakinta ya hana ta instantly; daga ranar kuma ba ta sake gwadawa ba. Duk abun da ta san ba ya so, avoiding ɗinsa take yi tsaf. Da ta ƙara ce masa tana so su yi fulfilling marriage duties ɗinsu, ya ce mata in Zara ta warke zai dawo gidanta. Sai dai abun da kowa bai sani ba shi ne, lafiyar Zara ƙalau! Fluids drip ɗin da ake saka mata ne kawai ya sa ta wani yin sanyi, kuma kwana uku aka yi aka gama. Yau na huɗu, kuma washegari ne mazan za su je Abuja ɗaurin auren Mu'azzam. Sai dai ba kowa ne ya sani ba; daga iyaye maza, sai matan Baffa, sai Hajiya Mama da yayanta. Amma ko su Ummi ba su sani ba. Ƴan uwan Maamah kuwa da yawa sun koma, waɗanda ba su da ƙananan yara ne kawai suka zauna—wanda Anne da Aunty Hannah na cikinsu—kuma suna Abuja a gidan Maamah ko ince gidan Zara suke zaune. Umma Deeza ba ta yi wani biki na azo-a-gani ba dake Amrah ba mai son hayaniya ba ce. Wani small dinner kawai Umma Deeza ta haɗa wa family and close friends ɗinta, the wedding was very private. Har kamun amarya da aka yi ma ba mutane da yawa ba ne. Sai dai auren ya dinga yawo a social media, rumor ɗin Mu’azzam Galado zai ƙara aure ya dinga tashi sama-sama ba sosai ba, wanda Allah bai sa Surayyah ta gani ba. Ƴan gidansu kam, sisters ɗinta sun gani, amma duk ba su ba abun mahimmanci ba, sai ma Rahama da ta yi live video tana ƙaryata maganar gaba ɗaya. Gidan Amrah yana jikin gidan Surayyah. Omar Galado ne ya yi mata komai na hidimar auren, irin yadda iyaye ke kai yayansu da shi, wanda Umma Deeza ba ta so ba amma ya dage shi ne yayan amarya shi zai yi komai. Daman a cikin yayankan Maamah, Amrah ta fi shaƙuwa da sakewa da Omar, yayin da Mu'azzam kuma ko iya haɗa ido da shi ba ta yi. A ɓangaren Zara kuwa, ranar ta kwana da murna saboda washegari ɗaurin auren Mu'azzam, kuma a goben za’a kawo amarya cikin estate ɗin. Shi yasa da daddare da Zafar ya nemi haƙƙinsa, ba ta yi masa musu ba, kuma ta sakar masa jiki ya yi komai son ransa. Bangaren sa ya ja ta suka je. Ai kuwa ba ƙaramar gajiya ya tara mata cikin daren nan ba! Dan duk kewarta da ya yi da rowar da ta dinga masa, sai da ya fanshe a cikin daren nan. Ko kaɗan bai sarara mata ba, kuma shi kansa ya san ba ƙaramin juriya ta yi ba. Haka washegari ma, sai da suka ɗaura daga inda suka tsaya with intense passion, sannan around 9:00 AM ya shiga wanka saboda kiran da Mu'azzam ke ta masa a waya ba ƙauƙautawa. Bayan ya fito daga wanka, to his greatest surprise, ya ga Zara ta cire sheets ɗin kan gado ta shimfiɗa wani tana ƙoƙarin gyarawa, daga ita sai silk robe ɗinta a jikinta. Sosai ya ji mamaki ganin tana ta ƙoƙarin gyara gadon, duk da ba daidai ta shimfiɗa ba ma. Cikin murmushi ya ƙarasa inda take. Kissing ɗinta ya yi sweetly, sannan ya hau cire zanin gadon gaba ɗaya ya saita shi, yana mata bayanin yande za ta yi tsaf. Taya sa ta hau yi suka gyara gadon tass, sannan ta hau tsince kayansu dake zube a ƙasa, clearing the beautiful mess from their wild night. Inda yake sa kayan wankinsa ta kai bedsheet ɗin kuma ta saka a cikin washing machine, sannan ta koma bedroom ɗinta ta kunna incense tower burner ɗin dake ɗakin bayan ta sa turaren wuta. Nan da nan ɗakin ya hau ƙamshi mai daɗi, filling the space with a rich, luxurious aroma. Daga haka ta bi shi cikin closet ɗinsa; yana tsaye yana shafa mai, ta ƙarasa ta fara taya shi suna wasansu da dariya cike da soyayya da nishaɗi. Zafar bai taɓa jin hankalinsa ya kwanta ba irin yau, ji yake ina ma zaman lafiyar nasu zai ɗore a haka. Haka ita ma Zara, she finally felt settled and at home, and they are both extremely happy. Kaya ta zaɓar masa, inda ta fito masa da espresso brown shadda sabuwa da hula ta ajiye yayin da yake combing kansa. Cikin sauri ta nufi bathroom ɗinsa ta faɗa wanka. Lokacin da ta fito, ya shirya tsaf, yana zaune kan sofa a bedroom yana waya, looking incredibly sharp and putting off absolute billionaire vibes. Ba ƙaramin kyau ya yi ba, kamar shi ne angon! Zara na ɗaure da towel ta ƙarasa gabansa tana cewa, “Obim, baka yi breakfast ba.” Ɗan muting wayar ya yi yana kallon ta, his eyes sweeping over her fresh post-shower glow. Playfully ya jawo hannunta yana cewa, “Matata ba ta ba ni ba.” Daga haka ya ci gaba da wayarsa yana zaunar da ita kan cinyarsa. Ɗan frowning ta yi tana tunanin me ta iya da za ta yi masa. Kallon sa ta yi ta cewa, “Zaka sha milk tea? Or should I make you some oats?” Kissing cheeks ɗinta ya yi cikin sauri ya ce, “Tea is fine, princess.” Gyaɗa kai ta yi tana tashi. Shi ma miƙewa ya yi, ta kama hannunsa suka sauka ƙasa. A parlour ya yi zamansa har lokacin yana waya, ita kuma ta wuce kitchen ɗinsa. Wani garlic bread da Yemma ta yi ya taho da shi jiya ta gani a foil cikin fridge. Fito da shi ta yi, ta nufi Slot Toaster ta saka a ciki ta kunna, daga haka ta koma gurin espresso machine ta hau haɗa masa Assam milk tea. In 5 minutes ta gama komai, ta fito ta ajiye a dining table. Zafar da ya ga wucewarta, ya juya yana kallon ta da mamaki, dan ya zata tea kawai za ta haɗa masa ta ba shi. Miƙewa ya yi yana murmushi, har lokacin yana waya, ya isa inda take tsaye ya ja ta jikinsa yana kissing kanta, daga haka ya zauna. Kitchen ta koma cikin sauri ta ɗauko white truffle butter a cikin fridge, ta ɗauki spreader knife ta fito. Shi dai Zafar binta kawai yake da kallon mamaki, his heart full of contentment at her sweet effort. Zama ta yi ta fara shafa masa truffle butter ɗin a jikin bread ɗinsa. Gama wayar ya yi ya kashe, daidai tana gamawa ta tura masa plate ɗin gabansa. Tana turo baki cikin shagwaɓa, ta fara magana: “Obim, I’m sorry.. I give you my word, I’m going to practice and get better in the kitchen, trust me.” Ɗagowa ya yi yana kallon ta da mamaki yana frowning. Hannunta ya janyo ta dawo gabansa, dan zama ta yi kan table ɗin tana kallon sa. Zafar dake kallon ta shi ma, cikin soft voice ya ce, “What do you think we have chefs in this house for? I married you for you, not to turn you into a cook. The only reason I don't eat their food is because my tastebuds are strictly used to Algerian dishes, kin gane?” Zara ta ɗan yi frowning tana gyaɗa kai. Ita daman ganin ta yi bai taɓa cin abincin da ake jere wa a dining ba kullum, sai dai in ya dawo daga masallaci ya ce mata ya ci a gurin Yemma; toh a tunaninta abincin chefs ɗinta ne ba zai ci ba. Zafar ya sake cewa, “Here’s the plan: I'll have Noori send over one of Yemma’s personal chefs. They will provide the kitchen staff here with a complete guide to my likes and dislikes. That solves it, yeah?” Gyaɗa kai ta yi tana sakin cute smile ɗinta, hankalinta na kwanciya. Daga haka ya fara shan tea ɗinsa da bread, ita kuma ta juya da sauri ta hau sama. Closet ɗinsa ta shiga inda ta ga wasu kayanta a ciki. Wata beige abaya ta ɗauka irin mai zip ɗinnan a gaba, ta fito da ita. Daga haka ta saka innerwears ɗinta sannan ta saka abayar. Jiƙaƙƙen gashinta ta yi packing, sannan ta yafa mayafin, ta saka flip flop wedges ɗinta ta nufi gaban mirror. Fesa turaren sa ta yi, sannan ta fito fully ready to see him off. Ko da ta sauka ƙasa, yana kan shan tea ɗin, wayarta ce ta fara ringing. Ta kalli screen ɗin kafin ta ɗago tana cewa, “Obim, Ya M ne.” Zafar ya miƙe yana cewa, “Pick up, kice masa I’m on my way out.” Zara ta ɗaga, ta gaya wa Mu’azzam dake faman faɗa cewa gashi nan zuwa. Daga haka ta ƙarasa inda Zafar ɗin yake, hannunta ya kama ya yi kissing. Yana kallon ta cike da so ya ce, “Thank you for the breakfast, princess.” Washe baki ta yi tana cewa, “Anytime, Obim. I’ll do better next time, I promise.” Pointed look Zafar ya ba ta yana cewa, “Don’t you dare. I married a queen, not a cook. Just stay beautiful and let the chefs do their job.” Sake washe baki ta yi cike da jin daɗin maganarsa, duk da ta saka a ranta ko ba ta girka ba, za ta dinga kula da girkinsa in ana yi—za kuma ta dinga jerawa da serving ɗinsa da kanta. Fita suka yi daga part ɗinsa, suna tafiya tana masa hira har suka iso bakin gate ɗin gidan. Haka suka fito suka hau titin estate ɗin, hannunsu sarƙe cikin na juna; tana ta masa surutu shi kuma yana murmushi. Duk inda suka wuce kallon su ake yi, har suka tsallaka zuwa gate ɗin manor, inda Baffa, Mu’azzam, Ahmad, Omar, da Zwar ke tsaye suna jiran su. Kowa da murmushi a fuskarsa, hatta Omar dake waya shi ma murmushi yake yi yana kallon su. Duk sun yi kyau, kowa ya sha farar shadda har Zwar. Suna ƙarasawa, Zara ta yi sallama duk suka amsa. Ta isa gaban Baffa tana gaishe sa da murmushi a fuskarta. Shi ma ya amsa cike da fara’a da kuma jin daɗin yadda ya gansu ita da Zafar ɗin, da kuma farin cikin da ya gani a fuskar duka yayansa yayin da suka hango su suna tahowa. Tambayar ta ya hau yi ya ƙarfin jiki, sannan ya kalli Zafar yana cewa, “Shikenan kuma kun yaye zuwa breakfast ko?” Ɗan murmushi Zafar ya yi yana sosa kai, ya ce, “Baffa za mu fara zuwa InshaAllah.” Baffa ya gyaɗa kai yana cewa, “Ya fi kam.” Daga haka ya yi gyaran murya, yana cewa, “Sallu alan nabiyyil kareem!” Kowa ya amsa da, “Sallallahu Alaihi Wasallam!” Daga haka gurin ya ɗauki tsit aka fara salati. Bayan an gama kuma, Baffa ya ce a karanta Al-Ikhlas, Al-Falaq, An-Nas, da Al-Quraysh. Shi ma sai da suka gama tass, sannan Zwar ya yi gyaran murya ya fara karanta Ayat al-Kursi, kowa na kama masa har da Zara. Bayan sun gama kuma, ya fara addu’ar tafiya: “Subhanal-lazi sakhkhara lana hadaza wa ma kunna lahu muqrineen. Wa inna ila rabbina lamunqaliboon.” Duk suka amsa, sannan Baffa ya juya ya nufi mota yana cewa, “Zwar muje.” Zwar ya ƙarasa gaban Zara, ya ɗauki hannunta ya yi kissing, ita ma ta sunkuya ta yi kissing kansa, kafin ya ɗaga mata hannu yana bin bayan Baffa da sauri ya faɗa motar da yake. Nan da nan driver ya ja sukayi gaba. Mu’azzam ne ya ƙaraso gaban Zara, ya yi hugging ɗin ta fuskarsa cike da wata irin fara’a da ta sa Zara dariya tana cewa, “Ah ah, Angoo.. See the way you are glowing.” Shi ma dariyar ya yi sosai kafin yayi kissing kanta yana cewa, “Sai mun dawo.” Gyaɗa masa kai ta yi, daga haka ya juya ya shiga mota. Zafar ya kalli Ahmad yana cewa, “Su Abbah fa?” Ahmad dake buɗe front seat ya ce, “Yanzun nan suka wuce airport.” Gyaɗa kai Zafar ya yi, kafin ya juyo ya kalli Zara dake tsaye a gabansa. Ya janyo ta jikinsa, suna kallon juna suna murmushi. Ya ja hancinta yana cewa, “Take care of yourself, sit pretty, and don't let nobody disturb you, alright?“ Gyaɗa kai ta yi tana ɗan shagwaɓe fuska. Cikin lallashi Zafar ya ce, “We’ll be back by 3:00 PM Insha Allah.” Nan ma ta gyaɗa kai, kafin ta sa hannunta akan fuskarsa tana ɗan kissing lips ɗinsa lightly, sannan ta ce, “Wish you journey mercies. May Allah guide your footsteps and bring you back safely to me.” Zafar ya yi kissing kanta yana jin kamar ya yi zamansa, ya ce, “Amin... thank you, princess. Allah yayi miki albarka. Make sure you get some proper sleep, yeah?” Zara ta gyaɗa kai tana murmushi. Daga haka ya shiga motar yana kwalawa Omar dake can gefe yana waya kira. Omar ya kashe wayar ya ƙaraso. Gaban Zara ya je yana ɗan taɓa kanta, ya ce, “Ya jikin? Kina cin abinci yanzu?” Zara dake murmushi ta ce, “Only prepped cold meals.” Omar ya gyaɗa kai yana cewa, “That's exactly what you need. Small, chilled portions are much easier on your stomach right now. You'll get through this, InshaAllah.” Zara ta gyaɗa kai tana maimaitawa, “Insha Allah.” Daga haka ya juya yana cewa, “Sai mun dawo.” Hannu Zara ta fara ɗaga musu har aka tada motar suka wuce, Zafar na mata murmushi da waya a kunnensa, ya ɗan ɗaga mata hannu shi ma. Bayan sun wuce, Zara ta juya ta nufi hanyar gida, sai dai wayarta ta yi vibrating. Ganin Zafar ne ya sa ta ɗaga da mamaki. Tana kai wayar kunne, ta ji muryarsa yana cewa, “Princess, I forgot to mention—go inside and greet Yemma, kinji?” Ɗan shuru ta yi kafin kuma ta amsa, gabanta na faɗuwa, ta ce, “Tohh..” Cikin lallashi ya ce, “Don’t worry, ba komai. Kije kinji?” Nan ma ta sake gyaɗa kai tana cewa, “Okay.” Daga haka ya yi mata sallama yana kashe wayar, leaving her to face Yemma alone. Juyawa Zara ta yi ta shiga cikin manor ɗin, daidai lokacin da Surayyah ta fito daga gida, her steps erratic as she walked like someone who had completely lost her mind. Ko ganin gaban ta ba ta yi, blinded by sheer rage and panic. Daga ita sai ɗan kwalin ta da ta ɗaura a kai. Wani irin sauri take zabgawa ta nufi hanyar manor ɗin. Tana zuwa ta tsallaka za ta shiga gidan Zara, securities suka dakatar da ita da cewa ba kowa a ciki. Tambayar Zara ta yi cikin tsawa, ɗaya ya nuna mata manor yana cewa, “Yanzu ta shiga ciki.” Ai kuwa ba ta yi wata-wata ba ta juyo, tana wani irin sauri har da gudu ta tsallaka ta shiga ciki. Idanunta sun kaɗa sun yi ja, bloodshot and fierce, kana gani kasan ba ta cikin hayyacin ta. Tana shiga manor ɗin, ta ƙarasa ciki da gudu tana wuce driveway ɗin. Amirah ta gani—wato autar gidan. Cikin sauri ta isa inda take tana ƙoƙarin shiga mota, da alama fita za ta yi. Surayyah na zuwa ta finciko ta, gripping her arm tightly, cikin rawar murya take cewa, “Ina take? Ina Zara?!” Amirah da ta gaba ɗaya ta tsorata, cikin sauri ta nuna mata wing ɗin Yemma tana cewa, “Yanzu naga ta shiga.” Tura ta Surayyah ta yi roughly, kafin ta juya da gudu ta nufi wing ɗin Yemma. Zara na tsaye cikin foyer ɗin Yemma tana zullumin yadda za ta shiga, ta ji an turo ƙofar da wani irin ƙarfi, the heavy wood slamming against the wall. Da sauri ta ɗaga kai tana kallon ƙofar. Sai dai kafin ta yi processing komai, ta ji an cafko rigarta. Kwalar abayarta Surayyah ta kama da ƙarfi, trapping her against the space, tana cewa, “Gaya min ina mijina ya je?! Me kuke ƙullawa dangi munafukai?! Ki gaya min ko in kashe ki in kashe banza wallahi!” Cike da wani irin mamaki Zara ke kallon ta. Calmly ta ce, “Sake ni.” Cikin tsawa Surayyah ta ce, “Bazan cika ki ba, tsinanniya! Tell me, what are you guys planning behind my back?!” Kafin kace me, maids ɗin Yemma sun fara taruwa, watching the unfolding drama in hushed shock. Cike da rashin arziki, Surayyah ta sake cewa, “Wallahi in mijina ɗaurin auren sa ya tafi, sai na kashe ki yau kafin ya dawo! Sai dai in matacciyar uwarku ce za ta dawo ta haifi wata ƴar!” Kafin Zara ta yi magana, suka ji muryar Yemma tana cewa, “Me yake faruwa ne?” Sai gata ta fito tare da Imaan cikin sauri. Da mamaki ta tsaya kallon Surayyah da ta maƙure Zara da rigarta tana ta sarfa ashar ta uwa ta uba, completely losing her home training. Yemma ta ƙaraso gurin, tana kallon su cikin mamakin me ya kawo su ɓangarenta. Cikin ɓacin rai ta kalli Surayyah tana cewa, “Ke, sake ta!” Ƙin sakin Zara Surayyah ta yi tana fashewa da kuka. Cikin ɗan ɗaga murya Yemma ta sake cewa, “Baki da hankali ne ko kuwa gidan ku ba manya ne?! Sake ta nace!” Cika Zara Surayyah ta yi, kafin ta yi snapping fingers ɗinta tana nuna Zara cikin kuka, “Wallahi yau mijina ya auri wata, sai dai wata ba ke ba! Nice ajalinku wallahi, sai dai in ba za ki fito daga nan ɓangaren ba!” Daga haka ta juya ta fita, storming out as abruptly as she had arrived. Zara ta bi ta da kallo cikin mamaki, kafin ta girgiza kai ta juya. Suna haɗa ido da Yemma, ta ɗan ɗauke kai. Yemma dake mata kallon tsaf, coldly ta ce, “Me kike yi a nan?” Zara ta sunkuyar da kai tana cewa, “Gaishe ki nazo yi.” Yemma ta watsa mata wani kallo tana cewa, “Gaishe ni kika saba zuwa yi? Kin yi tsokanar ki, shi ne za ki zo nan salon wani abu ya sameki ɗana ya ce a wing ɗina abun ya sameki?” Daga haka ta nuna ƙofar shiga cikin parlourn ta tana cewa, “Wuce.” Sum-sum Zara ta wuce ta gabanta, tana shigewa cikin parlour, feeling the heavy, tense silence following her. A second parlour ɗin Zara ta tsaya har Yemma ta shiga, ta nufi sofa ta zauna. Imaan ma ta shiga, tana ɗan nunawa Zara sofa alamar ta zauna. Zama Zara ta yi tana ɗan ɗar-ɗar, tana kallon Yemma da ko kallon ta ba ta yi. Imaan ta zo ta zauna a gaban Yemma, yayin da Yemma ta ci gaba da mata gyaran gashin da take yi, acting as if Zara wasn't even in the room. Suna nan zaune har 30 minutes, idon Zara na kan TV, sai hamma take yi saboda ba ta yi wani baccin kirki ba jiya. Miƙewa ta yi, wanda hakan ya sa Yemma kallon ta. Zara ta ɗan sosa kai tana cewa, “Bacci nake ji, zan tafi.” Dan shuru Yemma tayi kafin ta saki kan Imaan tana cewa, “Habibty, take her to Zafar’s room.” Gyaɗa kai Imaan ta yi, ta miƙe tana cewa Zara, “Muje.” Daga haka ta nufi hanyar sama. Ita dai Zara ta bi ta tana ɗan turo baki, dan gidan ta take son komawa, missing her personal comfort zone. Bedroom ɗin Zafar dake wing ɗin Yemma ta kaita. Tsaf ɗakin yake, immaculate and smelling faintly of his cologne. Imaan ta kunna mata AC sannan ta fito tana rufo mata ƙofa. Tana fita, Zara ta hau cire kaya. Daga ita sai bra da panties, ta hau gadon ta yi kwanciyar ta. Kafin kace me, baccin gajiya ya ɗauke ta, leaving all the family drama behind…