Free chapter · Read without an account
"A Glance That Changed Everything"
🔥TURƁAYA🔥
Story
and
Written
By
Zainab Bint Abdulrahman
(Zeeyluv💞)
***
*From the most precious Association*
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
YOTA ID/027
YOTA KO DA KUƊINKA SAI DA RABONKA💃🏻💃🏻💃🏻
Page.....................2
Old Cairo.
Old cairo wajen tarihi ne na musamman a ƙasar Egypt, idan kana buƙatar shaƙatawa zaka iya zuwa wajen kai tsaye haka zalika idan kaɗaicewa kake son ka yi domin ka yi ibadah cikin nutsuwa duk za ka samu a wajen domin kuwa yana kusa da masjid Amr ibn Al-as masallacin da ya kasance na farko a Afirka.....
Zauna ya ke ɗauke da jita a hannun shi yara na kewaye dashi yana kaɗa jitar cikin sanyi yana rera waƙar Kahin toh hogi woh na cikin film ɗin Jaane tu ya jaane
"Kahin to, hogi woh, duniya jahaan tu mere saath hai
(Somewhere, there must be a world where you are with me)
Jahaan main, jahaan tu, aur jahaan bas tere mere jazbaat hain
(Where I am, where you are, and where there are only our feelings)
Kahin to, kahin to...
(Somewhere, somewhere...)
Hogi jahaan subah teri, palkon ki kirnon mein
(Where your morning will be, in the rays of your eyelashes)
Lori jahaan chaand ki, sune teri baahon mein
(Where I hear the moon's lullaby in your arms)
Kehti hai fiza jahaan, tere zameen-asmaan
(Where the atmosphere speaks, that the land and sky are yours)
Jaane na kahan woh duniya hai
(Don't know where that world is)
Jaane na woh hai bhi ya nahin
(Don't know if it even exists or not)
Jahaan meri zindagi mujhse, itni khafaa nahin
(Where my life is not so angry with me)
Kahin to, hogi woh...
(Somewhere, it must be...)
Kahin to hai nasha teri meri har mulaqat mein
(There is an intoxication in every meeting of ours)
Hothon se, hothon ko, choomte rehte hain hum har baat pe" Cak ya tsaya da waƙar sakamakon wanda ya hango yana doso shi amma bai daina kaɗa jitar ba.
Asad Shareeq Khan kenan kyakkyawan matashi mai jini a jika wanda ya zama tauraro kuma allon kwaikwayon matasan Cairo har ma da kewaye.
Fitaccen matashin ɗan kasuwa ne wanda ƙasar Cairo ke alfahari dashi, mai riƙo da addini da tsatsaurar ra'ayi kan al'ada. Sam bai son raini ko kaɗan kuma bai shiri da mai rawar kai.
Mutum ne shi mai masifar tsafta don abin ma har ya ɓaci, shiyasa ba su taɓa jituwa da mutum mara tsafta.
Duk wani abu na ji daɗin rayuwa Allah ya mallaka mishi sai dai giɓi ɗaya da ya ke dashi a rayuwa na rashin mahaifi dukda kuwa mahaifin yana nan a raye amma shi ya daɗe da binne mahaifin shi saboda tsananin gaban da ke tsakanin shi da mahaifin wanda ko maƙiyi baka yi mishi irin wannan tsanar..... Wannan kenan a taƙaice.....
Cikin fara'a ya ƙaraso wajen yana murmushi ya miƙa mishi hannu "Afeef" ya faɗa kamar mai raɗa kafin suka tafa ciki da waje cikin wani salo mai ƙayatarwa daga nan kuma su ka rungume junansu cikin so da ƙauna irin na wa da ƙanin da suka fito ciki ɗaya wanda daga za ka san ba ƙaramin alaqa bane mai girma da ke tsakaninsu.....
"Akhy Asad ɗina ɗaya tamƙar da dubu mai abin mamaki" Ranƙwashi Asad ɗin ya kai mishi a kai.
Shafa wajen Afeef yayi yana faɗin "Auch Akhy da zafi fa" Asad ya ce "Eh ai dama zafin na ke son ka ji"
Murmushi Afeef yayi suka samu waje su ka zauna mutane sai kai kawo su ke yi a wajen kasancewar waje ne da baya rabuwa da jama'a. Duk budurwar da ta zo wuce Afeef sai ya bi ta da kallo kamar zai bi ta amma ba mai kula shi.
Tsaki yayi yana faɗin "Ni fah Akhy shiyasa bana son jera hanya da kai, saboda inda kana waje matan ba su san kallona sai kai" Ya ƙarasa maganar yana ɗan haɗe rai.
"Laaaa kalla wancan yana da ta ke ta binka da ido ƙila sonka ta ke yi bari na je na amso numbarta" ya yi maganar yana miƙewa tsaye.
Da saurin Asad ya finciko shi ya ce
"Afeef baka da hankali ko"
Afeef ya ce "Amma ai ina son yaya ta mace ne tun da bani da ita, kai kenan kullum cikin tsare gida baka bawa ƴan mata dama. Wai Akhy na tambaye maka mana! Wace kalar mace ma kake so ne, Allah yasa kar ra'ayin mu ya zo ɗaya, ina fatan ra'ayin ya bambanta don ina tsoron mace ta zo ta shiga tsakaninmu.
Saboda kusan kullum ina ji a raina kamar mace za ta iya shigowa rayuwarmu ta raba mu....
"Ba zaka gane bane Afeef" "me zai hanani ganewa idan ka min bayani" Afeef ɗin ya yi maganar cikin tarar numfashin Asad ɗin.
Ya yi maganar yana bin wata budurwa da ido yana faɗin "Ma sha Allah, ka ga wata halitta" ya bita da ido kamar zai haɗiye ta.
Tsaki Asad ya yi a ran shi yana mamakin halin ƙanin na shi da ko kunyar shi baya ji idan yana iya shegen shi. Da sauri Afeef ya juyo jin tsakin Asad ɗin ya ce
"Emm umm ina nufin ina jinka sosai" Kaɗa kai Asad yayi yana zuba mishi ido ba tare da ya ce komai ba. Afeef ya ce "Ya Akhy tunanin mai kake yi ne?"
Asad ya ce "Kawai ina mamakin yanda ƴan gidanku su ke jure wannan halin na ka ne" Yayi maganar yana miƙewa ya ce "Mu shiga ciki Amr ibn Al-as" Afeef ya ce
"Tamam" Su na tafiya a hanya Afeef ya ce "Akhy wannan abokina ɗin nan faisal ya siya sabon mashin, mashin ɗin yafi na wa gudu da kyau, sai wani ɗagawa ya ke wa mutane wa yayan shi ya siya mishi sabon mashin"
Asad ya ce "To ni yanzu meye na wa a ciki da kake faɗa min?" Afeef ya ce "Laaa ba fa cewa na yi ka siya min ba fa ni, kawai dai mamaki na ke yi ne kamar ni ne na fi kowa talauci a rayuwa,
da sai faman yawo da tsohon mashin da tsohon waya na ke yi a gari abokai na duk sun raina ni.
Ba su san cewa idan na ga dama bama, ni yayana private jet zai siya min na dinga yawo dashi a gari ba"
Asad ya ce "Da ka yi kyaun kai kuwa" Daidai suna ƙarasowa bakin masallacin........
***************************
Gudu ta ke yi suna bin ta a baya, kusan rai goma a kan mutum ɗaya. Cikin ikon Allah ta samu ta faɗa Old Cairo ta ɓuya.
Nan su ka bazu kowa na nemanta, haka ta samu ta dinga kauce musu har ta faɗa cikin cikin masallacin Amr ibn Al-as.
Zubewa ta yi a ƙasa tana maida numfashi haɗe da fashewa da kuka. Kuka ta ke yi tana kai wa Ubangiji kukanta a kan ya kawo mata ɗauki a rayuwarta ya sauƙaƙa mata sannan ya bata ikon cinye duk wani jarabawa da ya jarabce ta a rayuwa har ma da wanda zai yi mata a gaba....
Tun da suka shigo masallaci idon shi ya sauka a kanta yanda ta ke kuka tana addu'a ya sa ya shagala da kallonta...
Fara ce sol da ita, hasken ta irin hasken nan ne mai ɗaukar hankali, duk yanda ya ke jin kanshi da ganin shi mai kyau sai da ya sha jinin jikin sa ganin kyaun yarinyar wanda ka na ganinta ka san akwai waye tattare da ita, don ba ta yi yanayi da matar cairo ba duk da shigan gargajiya ne a jikinta irin na su na ƙasar amma haka bai saka ta saje da su gaba ɗaya ba duk da akwai yanayin jinin ƴan garin a jikinta.
Tun daga kai ya ke kallonta daga nan inda ya ke har ya zo kan idonta da ya ke a rufe gashin idon ya jiƙe da hawaye hakan ya sake ƙawata fuskar sai ya zama kamar wani kwalliya ce ta musamman hawayen ya yi wa idon, hakan kaɗai zai tabbatar maka da yanayi girman idon.
Gangaro da idonsa ya yi zuwa kan hancinta wanda dogo siriri ba mai faɗi ba mai ɗauke da ƴar ƙaramar bari ma mai launin gold da yake maƙale a gefen dama na hancin, yayi daidai da zane fuskarta da yake oval shape.
Sannun a hankali ya sake gangarowa saman laɓɓanta da yake ɗan tsut dashi wanda da gani zai yi tsiwa da jan faɗa mai shape ɗin heart shaped lip, sanya yake da lipgloss da ƙara fito da asalin launin kalar lip ɗin wanda ya ke ƙasa peach sai saman mai ɗan duhu sai sheƙi su ke yi.
Yanda ta ke ɗan motsa bakin a hankali ya ƙara bawa dimple ɗin ta guda ɗaya da yake gefe dama loɓawa. A yanda ta ke a zaune ma kaɗai zaka iya tantance yanayi jikinta.
Dogowa ce ita amma ba sosai ba don ba zata wuce 57" inches ba. "Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" shine abin da ya furta a zuciyarsa yana lumshe ido ya sake buɗewa daidai lokacin da Afeef ya ƙaraso wajen yana zama kusa da shi.
Shima idonsa ne ya kai kan ta, ai tuni ya shagala da kallonta sam ya manta inda ya ke, (kun dai san mutumin na ku da mata.) Shima a sace Asad ya cigaba da kallonta ƙasa ƙasa, ganin ta buɗe ido za ta tashi ya sa yayi saurin rufe idon na shi yana waskewa.
Miƙewar ta yayi daidai da miƙewar Afeef ɗin still idonsa a kanta ba tare da ko ƙyaftawa ba.
Tana fita shima ya bi bayanta amma kamar a mafarki ya neme ta ya rasa ta ɓace wa ganin shi.
Bai haƙura ba ya cika gaba da shiga lungu da saƙo na wajen yana duba ta amma ba ko mai kama da ita.
Ita kuma tana fitowa ta hango masu bin ta nan har yanzu suna nemanta yasa ta yi saurin shigewa wani ɗan ƙaramin lungu suka ƙaraso wajen ma still ba su gan ta ba sai suka yi gaba.
Ajiyar zuciya ta sauke ta bi ta wata hanya daban ta fice tana fita ta jefar da mayafin da ta lulluɓa da shi a wajen ta yi gaba abin ta. Daidai nan Afeef na ƙarasowa wajen yana waiwaigawa.
Idonsa ne ya sauka a kan mayafinta da ke ƙasa yasa hannu ya ɗauka yana jujjuya shi a hannun shi ya ce "Ina da tabbaci wannan ne mayafin da ta rufe jikinta dashi tabbas"
Bin hanyar ya yi yana tafiya yana waige waige daidai nan wayar shi ta fara ruri. Sa hannu yayi a aljihu yana ciro wayar *Qalbi wa Rouhi* shi ne suna da ya ke yawo a kan wayar murmushi yayi ya san dama za'a rina .
Ɗaga wayar yayi yana karawa a kunne "Afeef ka na ina" sautin da ya sauka a kunnan shi kenan tun kafin ya kai ga magana.
Sake faɗaɗa fara'ar da ke kan fuskar shi yayi ya ce "Brother na tuna akwai aikin da zan yi ne shiyasa na fita ban faɗa maka ba saboda bana son na yanke maka addu'ar ka ne, ban sani ba ƙila sister-in-law kake roƙo min"
Dafa goshin shi Asad ya yi kamar yana gaban Afeef ɗin ya ce "Ya Salam, amma abu ɗaya na tambayeka ko?" "Afwan" shine abin da Afeef ya ce yana murmushi.
Asad ya ce "Faɗa min gaskiya na san abin da ya fita da kai" Afeef ya ce "O'o fa ba abin da kake tunani bane sam, karka damu ka je gida ina da mashin, wannan tsohon mashin ɗin"
"Na ji za ka samu sabo, shikenan?" Cewar Asad.
"No brother ba haka na ke nufi ba fa"
Asad ya katse shi ta hanyar faɗin"Yanzu dai ka saurare ni, ka yi tuƙi cikin nutsuwa" Afeef ya ce "Kai ma haka brother bye" su ka katse wayar a tare...
Daidai nan masu neman Hayat su ka ƙaraso wajen su ka gan shi ɗauke da mayafin a hannu.
Ɗaya daga cikin su ne yace "Ku kalla mayafin nan shine wanda ta saka" ɗayan ma ya ce "Eh tabbas shine amma ya aka yi ya zo hannun shi?" Ƙarasawa suka inda ya ke suna faɗin "Hey" tare da jawo mishi kafaɗa.
*************************
SHAREEQ KHAN MANSION🏛️
Aunt Qaylah ce riƙe da waya a kunne sai faman kwantance ta ke wa wani Uncle ɗin Irfan amma ya kasa ganewa ta ce
"Da kun zo Heliopolis tambaye sunan Baban Humairah saboda ba wanda bai sanmu ba a wajen, tamam sai kun ƙaraso" ta yi maganar tana juyowa nan ta ke mutanan wajen suka kwashe da dariya.
Haɗe rai ta yi tana faɗin "Kawun angon ne ya kira, babban lawyern gwamnati ne shi, yana da basira sosai cikina ƙanƙanin lokaci ya ke warware matsala" Ta ƙarasa maganar tana dariya.
Jaddah ta ce "Uhmmm shakka babu, kuma shine ya kasa gane ɗan ƙaramin kwatance, ya kasa bambance tsakanin hagu da dama" Tsuke fuska Aunt Qaylah ta yi yaran kuwa dariya suka sake kwashewa da shi.
Jaddah ta cigaba da faɗin "To Allah ya sa dai yaron ba irin ƙwaƙwalwar kawunshi gare shi ba"
Aunt ta ce "Ammu karki damu kowa a gidan ya yi karatu da ilimin su, kawun fa har masters gare shi" Nudrat ta ce "Hhhhn shine ya kasa gane kwatance sau ɗaya."
Dariya Humairah ta yi Nudrat ta cigaba da faɗin "Da alama ya sha maimaita aji lokacin da ya ke makaranta" ta yi maganar tana dariya suna tafawa da Humairah.
Aunt Arwa ta ce "ohhh kenan daƙiƙi ne ashe" Sake kwashewa da dariya duk su ka yi amma ban da Aunty Qaylah da ta tsuke fuska ta ce "Arwa ki fahimta mana ba haka bane, iyayen Irfan mutanen kirki ne kuma ina tabbatar miki da cewa Hamra za ta ji daɗin zama dasu. Sannan ga Irfan yaro ne mai ƙoƙari."
Jaddah ta katse ta ta hanyar faɗin "To ki bari dai ya zo sai mu tabbatar, cikin ƙanƙanin lokaci zamu gane ko yana da basirar kamar yanda kika faɗa ko shima irin kawun na shi ne"
Aunt Qaylah ta ce "Eh za ku ganshi ai, daga baya ma yi magan...." Maganar ne ya maƙale a bakinta jin wayarta na ringing ɗaukawa ta yi da sauƙi ta kara wayar a kunnenta.
"Tamam, yauwa daga nan masallacin ku tambaya gidan Sheikh Shaheer."
Humairah ce ta zagayo ta bayanta tana faɗin "Mom tsaya tsaya." Ta yi maganar tana amshe wayar daga hannunta ta kara a kunne haɗe da faɗin
"Assalamu'alaikum, yauwa ku miƙo straight za ku ga SHAREEQ KHAN MANSION ya na facing ɗin ku nan zaku shigo tamam!"
Ta na faɗa ta katse wayar ta juya tana miƙawa Mom ɗin wayar da sai faman zabga mata harara ta ke ta yi.
Hannu ta ɗaga alamar "Ban yi komai ba fa" Juyowa Aunt Qaylah ta yi su ka yi ido biyu da Jaddah, kaɗa kai Jaddah ta yi alamar daidai Humairar ta yi ai...........
***************************
Tafiya ta ke yi a tsakiyar titi ba ta ko kallon gabanta bare bayanta, don ma titin ba babban titi bane.
Keeeeeee ya yi saurin jan wani wawan burki. Tuni ta faɗi ƙasa kayan da ke cikin hand bag ɗinta suka watse a ƙasa.
Hannunta ta shiga ɗagawa tana kakkaɓe bayan hannunta daidai nan ya ƙaraso inda ta ke zaune a ƙasar, kafe ta ya yi da ido ba tare da ya iya furta komai ba.
Tsawon minti uku ya ɗauka kafin ya samu da ƙyar ya tattaro duk wasu kalmomi da ke ransa kamar wanda aka fusgo maganar a bakinsa ya ce "Are you okay?" Ya yi maganar kamar mai ciwon baki.
"Yes" kawai ta ce a taƙaice ba tare da ta ɗaga ido ta kalle mai maganar ba. Cigaba ta yi da goge hannun tana hawaye.
Jin ido na yawo a jikinta ya sa ta share hawayen fuskarta tana ɗago fuska. Karaf idonsu ya sarke cikin na junan su.
Shi ya fara janye na shi yana tsare gida ya shiga tattaro mata kayanta da suka zube a ƙasa.
A fusace ta miƙe tsaye tana faɗin "Au haushi ka ji?" Shima miƙewa tsayen ya yi ya ce
"Mene!?"
Hayat ta ce "Eh mana ka so kashe ni Allah bai yi ba"
Asad ya ce "Kamar ya ban fahimce ki ba"
Ta ce "Idan kasan ba ka iya tuƙi ba me ya sa za ka yi?"
A fusace Asad shima ya ce "Idan ba za ki iya tafiya da kyau ba me ya sa ba za ki zauna a gida ba?"
Hayat ta ce "Idan ba ka san yanda ake magana mai kyau ba me ya sa ba za ka yi shiru ba?"
A fusace ya nuna ta da yatsa ya ce "Hey ki iya bakinki ba wanda taɓa min magana cikin irin wannan sigar" Hayat ta ce "Oh! No wonder i see shiyasa ba ka iya magana ba"
"Ke saurara ki ji" ya yi maganar yana nunata da wani ɗan ƙaramin kwalba na ta wanda ya ɗauko a ƙasa.
Saurin fisge kwalbar ta yi tana faɗin "Ba ni pepper spray ɗina, wannan dashi mata ke tsare kan su daga farmakin maza"
Tsaki ya yi yana harararta daidai wani sauri ya zo wuce wa ya kafe ta da ido ai kuwa ta fesa mishi pepper spray ɗin ya kauce da sauri.
Tsugunawa ta yi ƙasa tana cigaba da kwashe sauran kayanta da ke yashe a ƙasa ta na faɗin
"Wallahi Paris ya fiye min na ƙasar nan daɗi sau dubu, na fi jin daɗin rayuwata a can, gaba ɗaya bana son nan ƙasar nan sam, haba duk inda ka shiga maza suna bibiye da kai da kallo kamar za su cinyeka, ta mata za su iya kare kan su"
Cak ya tsaya daga tafiyar da ya ke yi ya ce "Inda matan za su dinga saukar da kansu ƙasa ba su buƙatar wani kariya, idan ki ka fito cikin shigar mutunci babu mai kallonki" ya juya ya nufa motar shi.
Da sauri Hayat ta miƙe tsaye ta ce "Excuse me! Me ya sa duk wani ƙuntatawa ake ɗaura mace ne ita kaɗai?
Me ya kuke jin cewa a koda yaushe mace da laifi ta fannin kare kanta? Me ya sa kuke ɗaura laifi gaba ɗaya a kan mace idan wani abu ya tafi ba daidai ba?
Don me yasa a ƙasar nan za'a ce dole sai mace ta zauna cikin ƙuntatawa? Karki saka wannan kayan, karki ƙawata kanki, karki je waje kaza! Ya Allah what is wrong with this country"
"Abin da kike ɗauka ƙuntatawa shi ake kira da Etiquette wato ladabi, ladabin sanin ya kamata, ladabin iya magana cikin mutunci, ladabin girmama mutane, ladabin sanin yanda ake zama a wurare daban-daban, ladabin cin abinci cikin nustuwa ba tare da hayaniya ba, ladabin bin ka'idojin zamantakewa, ladabin shiga ta mutunci!
Mutanen ƙasar turai su na bayyana jikinsu, wanda mu sam a nan ba haka bane matar ƙasarmu suna rufe ko ina na jikinsu ne, Fatan kin fahimta kanki ba'a doɗe ya ke ba"
"What! Me kake nufi" ba tare da ya juyo ya kalle ta ba ya ce "Abin da kika fahimta, by the way bana son na tsaya ina ja'in ja da ke a yau da ya ke ranar aurenki"
Murguɗa masa baki ta yi tana hararar shi ƙasa ƙasa ta ce "Yau ba ranar aure na bane"
Juyowa ya yi da sauri yana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa ya san dai Amare ne su ke irin wannan shigar ranar auren su a ƙasar Egypt.
Ta ce "Hey ka daina min wannan kallon ƙurillar wai me ke damunku ne a ƙasar nan da shegen kallon ƙurilla wa mace?"
Tsaki ya yi ya ce "To idan ki na da matsala da ƙasar me zai saka baza ki tattara ki koma Paris ɗin ba"
"Oh my goodness what's wrong with you? Meye ruwanka da zaɓar wa mutane inda za su zauna?
And by the way ni kaina ba son zama a ƙasar nan na ke yi ba. Na zo nan ne saboda wani muhimmin aiki da ya kawo ni kuma da zarar na gama zan tafi"
Asad ya ce "That will be a great favour to this country if you definitely leave" waro ido ta yi waje kafin ta kai ga cewa komai har ya shige motar shi.
Hararar shi ta yi tana faɗin "Nonsense". Ita juya ta kwashe sauran kayanta ta yi gaba tana cigaba da takaicin ƙasar a zuciyarta..............
****************************
Ta ɓangaren Afeef kuwa masu neman Hayat ne su ka mishi taron dangi sai duka su ke yi duk da shima bai bar su haka nan ba, sai dai kamar yanda kuka sani sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi hakan ya sa su ka samu galaba a kan shi don a ganin su raina musu hankali ya yi ya san inda ta ke tun da har ga mayafinta a hannun shi.
Ganin da ya yi yana gab da jiyo ƙamshin lahira ya sa ya fake idonsu ya kai hannu kan wayarsa keypad da ya ke yashe a ƙasa.
Dial log ya shiga haɗe da danna lambar Asad saboda dama shine a sama saboda da shi su ka yi waya ƙarshe hakan yasa ba sha wuyar nemowa ba. (Wato ba za ka gane amfanin keypad ba sai ka shiga irin wannan yanayin shine za ka gane amfanin keypad fiye da android wani lokacin...)
Finciko shi su ka yi suna cigaba da dukan shi hakan yasa wayar faɗi ƙasa ba tare da ya san Asad ɗin ya yi picking ba. Sautin duka da nishi da ya ke ji ta cikin wayar ne ya sa hankalinshi ya tashi tuni ya yi tracking location ɗin ta hanyar amfani da lambar wayar....
Ɗaya daga cikinsu ne ya fido da wuƙa ya dosa inda Afeef ke tsaye sauran sun rirriƙe shi gadan gadan ya yo kanshi tuni Afeef ya runtse ido yana ƙwalla ihu haɗe da sadaukarwa ranar mutuwarsa ce ta zo yau.
A hankali ya soma buɗe idomsa jin shiru bai ji saukar wuƙar a jikinss ba. Idon shi ne ya sauka a kan Asad da ke tsaye a wajen riƙe da hannun wanda zai caka wa Afeef ɗin wuƙar.
"Brotherrrrrr!"
Cewar Afeef ɗin cikin tsananin farin cikin ganin yayan na shi wanda ya ke wa laƙabi da Azwati (backbone) ko kuma ya ce Qalbi wa Rouhi wato (my heart and my soul) domin a duk lokacin da shiga matsala sai yayan na shi ya kawo mishi ɗauki....
Nan faɗa ya canza salo tuni wani jarumta ya zo wa Afeef ɗin ganin garkuwar shi a tare dashi.
Faɗa su ke yi cikin ƙwarewa kamar waɗanda su ka samu horo daga wrestling.
Ba su ankare ba wani daga cikin mutanen ya zo ta bayansu ɗauke da wuƙa a hannu. A tare Asad da Afeef su ka sake wani irin ihu...........
Ina sane da ku daga kan Wattpad, Arewapen, Whatsapp da Facebook babu comments ɗin da ya tashi kaina wanda zai nuna min ku na tare da ni😒To ina ankare da ku, ku ci gaba da na ku nima zan yi na wa nan bada jimawa ba eheee kuma kar a ce ban faɗi ba
#ECOTH_TEAM_OF_YOTA
🌹Autar Yota.........✍🏻