Free chapter · Read without an account
A Flight to the Blessed Land
by NorthernAngel · His Rose
Yau kwanan huɗu kenan da sakin Salma da Zafar yayi kuma daren yau ne jirgin Zara zai ɗaga zuwa Saudi Arabia. Acikin kwanakin nan gaba ɗaya estate ɗin ya ɗauki wani erin shuru kamar anyi musu mutuwa, the heavy atmosphere suffocating the entire estate. Hajiya Mama dai tayi fushi ganin Baffa baice komai ba game da sakin, dan haka kwana biyu da yin abun ta haɗa kayan ta ta koma Abuja. Abbah da Baffa kullum suna haɗuwa a masallaci daga sallar asuba har zuwa isha amma babu wanda ya taba yiwa wani maganar abunda ya faru a cikin su, both maintaining a rigid, prideful silence. Yayin da Baba kuma kullum yana cikin yiwa Baffa maganar, shi kuma Baffa yace masa bazai takurawa Zafar ba akan ya maida Salma ba, sai dai bai gaya masa abunda ke ransa na ganin hakan yafi alkhairi ba. Ga Hajiya Mama kullum saita kira Baba akan jin ya sukayi da Baffa dan sosai tayi fushi da Baffa bata kiransa da kyau, her frustration boiling from a distance. So da Baba ya matsa sai Baffa yace Baban yayiwa Zafar ɗin magana da kansa. So Baba sai ya yanke shawarar zaiyi masa amma sai zuwa sanda ya huce, gwara a bashi space acewar sa. So da wannan shawarar ne aka samu Hajiya Mama ta sararawa mutane. Sai dai abunda kowa bai sani ba shine kiran da Hajiya Mama ke yawan yi tana takurawa itama ba yin kanta bane; Aunty ce da Salma suka sakota gaba da roƙo da magiya ba dare ba rana. Salma kam kamar ta fita hayyacin tama, completely shattered and unraveled, sosai take ba Hajiya Mama tausayi shiyasa ta dage. A ɓangaren Abbah kuwa, a duk sanda Baba ya tada maganar sai rayuka sun ɓaci saboda yace Salma ta gama auren Zafar indai ya isa da ita. Ko da Baffa ne yace a maida auren zai ce a barshi kawai dan shi a ganinsa hakan yafi, kuma a cewar sa Zafar ba erin mijin da yakewa ʼyarsa fatan ƙare rayuwarta dashi ba kenan. Acikin maganganun da ya gayawa Baba da Hajiya da kuma su Salmar, harda cewa marar tarbiya erin Zara itace tafi dacewa da Zafar, kuma shiyasa yafi ƙaunar ta kuma baya ganin laifinta. Babu dai kalar maganganun da baiyi ba kuma ya tabbatar wa Salma ta cire ranta akan Zafar, trying so hard to salvage his bruised ego. Amma yana tashi daga gurin, uwar Salma tace, “Rabu da shi.. yana magana sai kace zai iya nemo miki wanda yafi Zafar ɗin.” Sai kuma tayiwa Salmar wani kallo, her eyes scanning her daughter with sharp disappointment, tana cewa, “Ae zama gidan Zafar yanzu kika fara. Ni dai kawai kin bani mamaki wai ace bai taɓa kusantar ki ba kuma biki gaya mun ba. Ke wace erin shasha ce Salma, sai kace ba mace ba? Ni da yace ya sake ki, inata adduar Allah yasa kina da ciki, ashe ke ko dabbanci kikaje gidan kinayi?” Her harsh words adding salt to Salma's bleeding wounds. Shuru Salma tayi tana goge hawayen ta tana kasacewa komai, her spirit completely crushed under her mother’s harsh words. Babu kalan zagi da tsinuwar da Zara bata sha ba. Yanzu haka duk yan gidan su Salma sun daina yiwa Muazzam da Omar magana har yaran ko sun gansu basa gaishe su, creating an icy, permanent rift within the extended family. Haka yayan mom sosai tsanar Zara ta ƙaru acikin ransu musamman jidda da Aisha. Ita dai mom zuwa yanzu sosai tunanin haɗa Omar da Yusrah ya shiga kanta kuma bata damu da cewa Omar da Noor nada ɗa ba, focusing entirely on her next strategic move. Ita yanzu babban burinta ma kowa ya sani Yemma ta tozarta, so ita duk wannan abun da ake bashi ne a gabanta ba, kawai dai zata yi using chaos ɗin as a perfect shield for her own hidden agenda. A ɓangaren gidan Muazzam kuwa, tun ranar da Surayya tayi abun nan da Muazzam ya tafi gidan amaryar sa cikin tsakar dare ta kasa bacci. Ta kira gidan su tana rusa kuka tana cewa azo a ɗauke ta. Haka aka turo driver gurin karfe ɗaya da rabi na dare saidai sam securities suka hanashi shiga estate ɗin. Har ita ta fito da kanta amma suka ƙi buɗewa suka ce sai sun samu kira daga wani ɗan gidan shine zasu buɗe, executing their strict orders with zero compromise. Haka ta haƙura amma washe gari da sassafe ta shiga motar ta tabar gidan. So tun lokacin bata gidan… Ƙarfe 8:30 na dare Zara ta fito daga cikin part ɗinta tana sanye farin kaya. She looked stunningly elegant, embodying a flawless minimalist, modest look. Gaba ɗaya jikinta fararen kaya ne; a white crewneck top tucked seamlessly into high-waisted, wide-leg linen trousers with a drawstring waist. Sai kuma farin soft cotton kimono dake har ƙasa, adding an ethereal movement as she walked. Sai siririn farin veil saman kanta wanda Miss Dior sunglasses ɗinda ta ɗaura saman kan ne ya danne mayafin effortlessly. Hannunta na riƙe da black quilted Lady Dior mini bag with gold hardware that perfectly broke the monochrome white, sai kuma ƙafar ta dake sanye da black Casadei wedges.Tafiya ƙaɗan tayi ta isa inda akayi ajiye baƙar The hybrid G-Wagon ɗin da aka fito da ita daga parking space. Tana isa dai dai Zafar ya gama sa luggage ɗinta a trunk kennan yana rufewa. Juyowa yayi yana kallon ta, his eyes instantly softening at the pure glow radiating from her. Zara ta saki mai murmushi tana cewa “Muje.” Frowning yayi yana janyo ta jikinsa ya rungume ƙam yana tusa kansa cikin wuyanta. Dariya Zara ta farayi tana cewa “Since when did you become such a baby?” Shuru yayi mata yana ƙara ƙanƙameta jikin sa yana jin ina ma ta fasa tafiyan sai bayan two weeks su tafi tare, completely dreading the distance between them. Da kyar dai Zara ta ɓanɓaro sa daga jikin ta sannan suka nufi mota. Opening the front passenger door for her, ya tsaya kafin ta shiga ta miƙa masa wayar ta tana cewa yayi mata picture.
Bayan yayi mata ta karɓi wayan ta shiga yi musu video, capturing the intimate moment, sai ta gama sannan ta shiga motar shi kuma ya zagaya ya mazaunin driver ya ja motar. Manor suka nufa kai tsaye inda suna fitowa shi kuma Lamidi ya nufi ƙofar gidan Zara da mota dan ɗaukar maid ɗinta da zata tafi da ita. Suna isa manor sukayi parking a cikin wing ɗin Yemma sannan suka fito suka shiga yana riƙe da hannun ta, walking into the lion's den with total dominance. Da sallama a bakin Zara suka shiga second parlour ɗin Yemma, sai dai ɗan turus sukayi ganin waye acikin parlourn. Salma ce da Aunty a zaune; Aunty na kan kujera while Salma na gaban Yemma a zaune a ƙasa tana facing ɗinta kamar almajira. Gaba ɗaya ta rame tayi pale acikin kwana huɗu kacal, looking completely unraveled, stripped of all her usual pride. Ga kumburarrun idanun ta sun jeme sunyi fari kamar nama, her eyes bloodshot from endless crying, hijab ɗin jikinta ma a karkace, showing how badly she had neglected her appearance amid the sudden heartbreak. Daga ita har Aunty bin su Zara da Zafar sukayi da kallo. Cikin sauri ita Aunty ta ɗauke kai bayan ta haɗa ido da Zara, yayin da ita kuma Salma take bin Zafar da wani kallo kamar zata cinye sa, her gaze practical burning with desperation. Wani matsiyacin kallo Zara ta watsa musu ta ɗauke kai, utterly unbothered, kafin ta zagaya ta bayan sofar taje ɗayan gefen Yemma tana gaisheta. Yemma ta amsa shortly sannan ta ɗaga kai tana kallon Zafar daya ƙaraso yayi kissing kanta yana cewa, “Ina suke?” Yemma tace, “Suna sama.” Juyawa yayi ya nufi hanyar sama, tayi saurin cewa, “Hold on, dawo nan. Don’t go rushing my babies. Bari in duba maka su da kaina.” Daga haka ta miƙe tana kallon Salma data sunkuyar da kai wasu hawaye na sake zubota, her quiet sobs cutting through the tense atmosphere, yayin da Aunty ke watsa mata hararar kukan da take gaban Zara, utterly embarrassed by her daughter's public display of weakness. Aunty ce ta ɗago tana cewa, “Zafar ba gaisuwa? Ina wuni?” Yemma ta kallesa ta fara yi masa yare inda take mai bayanin tun ɗazu suke nan sun ishe ta da kuke kuke, expressing her deep annoyance at the endless drama. Ɗan taɓe baki Zafar yayi kafin ya ɗan kalli Aunty ciki ciki, his expression completely blank and emotionless, yace, “Ina wuni.” Washe baki tayi tana faɗin, “Lafiya lau, fita zakayi da yaran ne haka?” forcing a fake smile to hide her desperation. Zafar ya ɗan haɗe rai kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace, “No, airport zan kaisu ne. They're flying out to Saudi with Zara.” Ɗib parlourn ya ɗauki shuru, a dead silence filling the room, babu wanda ya sake cewa komai. Yemma dake tsaye tana danna waya ta ajiye wayar kan sofa sannan ta juya, muryar Aunty taji tana cewa, “Okay toh zamu jiraka in ka dawo. Please, join us here so we can finally sit down and discuss everything as a family, koh?” Ta ƙarasa maganar tana kallon Yemma hopefully. With a completely neutral face, Yemma ta girgiza kai, “No, I already told you, Amina, bazan sa baki ba. Ga Salma ga Zafar, she should swallow her pride and beg him to take her back mana. Me yasa ʼyarki take da girman kai ne haka? You guys crossed the line with him, sai ku bashi haƙuri mana. Ni miye nawa aciki?” Ta ƙarasa maganar tana frowning, daga haka ta juya ta nufi sama tana kwala kiran “Noori” tana magana cikin yare. Ran Aunty ne yayi masifar ɓaci. Ba kuma dan abunda Yemma tace ba, dan tun ba yauba sun saba da erin wannan ƙasƙancin nata; yin da tayi musu a gaban Zara dake zaune tana kallon TV shi ya cima Aunty rai kuma ya muzanta su duka, completely crushing whatever dignity they had left. Salma dai kanta ƙasa tana jin zafin ƙasƙancin da Yemma keyi musu ko da yaushe amma kumma tana ja ta ƙulle a ranta akan zata rama. Zafar shima ya samu guri ya zauna kan two-seater ɗinda Zara ke zauna yana ciro wayar sa daga aljihu. Salma ta miƙe ta dawo kan wata sofa ɗin dake facing ɗinsu, yayin da Aunty ke bin Zara da wani kallon kurilla saboda gani da tayi ta ƙara haske da wani glowing da fatarta ta ƙara. Wani erin faɗuwa gaban ta yayi tana sake ƙurawa mata ido cike da mamaki. Zara ta miƙe tsaye, tayi yar miƙa tana cewa, “Obim, let me go raid that huge freezer.” Zafar ya ɗago yana kallon ta cike da wasa, idanunsa na lighting up with affection amid the cold tension, yace, “Kwaɗayi. You just left the exact same one at home.” Shrugging tayi tana cewa, “Hunger just hit me out of nowhere.” Daga haka ta nufi waje ta shiga cikin hallway ɗin da kitchen yake. Tana zuwa ta shiga pantry ɗin ta buɗe walk-in freezer. Dube dube ta farayi a ciki kafin tasa hannu ɗauki bag of frozen grapes ɗaya na banana ma ɗaya, sai ta ɗauki Cold Fudge Sauce dake cikin wani glass jar. Daga haka ta rufe fridge ɗin ta fito, ƙaramin dessert spoon ta ɗauka sannan ta fito. Parlourn ta dawo dai dai lokacin da Yemma ta gama saukowa tare da Zwar da Imaan. Ƙarasowa sukayi cikin parlourn tare, duk idonsu na kan Salma datayi saurin miƙewa daga durƙushen da take wurin ƙafar Zafar, trying to salvage her desperate attempt at begging. Ga Aunty itama sai magana take mai da alama haƙuri take bashi. Wani kallo Zara ke binsu dashi tana taɓe baki haɗe da wani satisfied murmushi akan fuskar ta. Zwar ne ya nufo inda Zara take yana cewa, “Aunt Zara, aren't you supposed to be wearing an abaya? We’re going to Saudi Arabia, you know.” Ya ƙaraso inda take yana folding his arms da wani erin cute, serious face. Kowa kallon su ya koma yi yayin da Yemma ta wani gyaɗa kai cike da jin daɗin maganar da Zwar ya faɗa, fuskarta na ɗauke da murmushi take kallon Zafar. Aunty ma ta wani taɓe baki tana ɗagawa Salma gira, tana nuna Zara da ido, silently gloating and hoping Zara would get scolded by Yemma. Zara dai dariya ta fara nonchalantly tana cewa, “There’s absolutely nothing wrong with my outfit, sweetheart. I can’t sit on a long flight wearing an abaya.” Sake ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa sannan yayi humming kamar wani babba, sannan yayi shrugging yana cewa, “You look beautiful anyway.” Zara ta matso tana faɗin, “Aw,” ta ɗan duƙa tayi kissing kansa ta ɗago tana faɗin, “Thank you, honey! And you look so handsome yourself.” Kansa ya kalla yana sanye da baƙar jallabiya sak erin ta jikin Zafar, murmushi kawai yayi yana girgiza kai kafin ya juya. Zafar ne ya miƙe yana janyo Zara jikin sa yayi kissing cheeks ɗinta, ignoring the absolute tension from Salma and Aunty, kafin ya kalle su Yemma yana cewa, “Muje?” Yemma ta gyaɗa kai tana cewa, “Imaan je ki duba Noori, let her know we're heading out right now.” Daga haka ta kalli Aunty tana cewa, “Amm, Amina, we’re all heading to the airport now. Let's head out, please.” Da wani erin mugun mamaki Aunty da Salma suka ɗago suna kallon Yemma, shocked by her freezing indifference, dai dai lokacin da Noor ta sauko da Mezyan a hannun ta tana cewa, “I’m here, sorry. Let’s head out.” Maids ne suka fara saukowa da luggage ɗin Imaan da Zwar sukayi waje dashi. Zafar ne yasa hannun sa akan kafaɗar Zara, yana raɗa mata playfully, “Come on, let's go, let's go before I change my mind.” Daga haka suka fice yayin da Zwar da Imaan suka rufa musu baya. Noor kuma ta ɗan kalli Yemma da alamar tambaya tana kallon Aunty dake zaune yayin da Salma ke tsaye. Yemma ta ɗanyi narrowing idonta slightly tana faɗin, “Amina ke fa nake jira.” Miƙewa Aunty tayi a hasale, her face flushed with absolute humiliation, tana ficewa kamar zata tashi sama, yayin da Salma ta tsaya tana kallon Yemma tana cewa, “Yemma dan girman Allah ki—“ Dismissively, Yemma tayi mata wani kallo tace, “Kin dai ga fita zanyi ko?” Juyawa Salma tayi jiki a sanyaye tana fashewa da wani kuka mai ban tausayi. Yemma ta bita da wani kallo, her voice dropping into a cold, hard tone, tana cewa, “Lokacin da babanki ya sa min ɗana a gaba, who stood up for him? Nima I’m done standing up for anyone else’s child.” Daga haka Yemma ta kalli Noor dake ɓaɓɓaka dariya tace, “Ke muje, you just find everything funny saboda hauka.” Daga haka suka bi ta backyard suka shiga wing ɗin Baffa. Anan suka tarar da su Zafar har sun isa dake a mota ne. A tsaye suka tarar da kowa har da Omar, daman Baffa yace dashi za’a raka su airport. Su fitowa kawai sukayi gaba ɗayan su suka nufi mota inda da Omar ne zaiyi driving Baffa. Da sauri Noor ta isa gurin Yemma ta miƙa mata Mezyan. Yemma na karɓar sa bata ma gama processing komai ba ta hangi Noor taja hannun Zwar sukayi hanyar motar Omar. Wani kallon takaici da mamaki Yemma ta bita dashi, completely stunned by her sudden audacity, tana tunanin yaushe Noor ta rainata haka? Imaan ce ta ƙaraso taja hannun Yemma suka nufi motar su Zafar. Yemma dai sai gyaɗa kai take tana ƙwafa. Zafar na tsaye shidai ya buɗe mata backseat. Yemma ta ajiye Mezyan sannan itama ta shiga ta zauna kafin ta sake ɗaukar sa. Tare Imaan da Zafar suka zagaya, Zafar yayi saurin buɗe mata ƙofa itama ta shiga tana yar dariya tana faɗin, “Merci le sang.” Rufe motar yayi sannan ya shiga mazaunin driver. Zara na zaune a mota tana dipping fruit ɗinta cikin chocolate sauce tana ci, completely lost in her own little world. Su Baffa ne suka fara fita kafin Zafar ya rufa musu baya tukunna Lamidi dake bakin gate ɗin manor shima ya rufa musu baya da maid ɗin Zara acikin motar… The ride to the airport was pure silence acikin motar su Zara, ba abunda ke tashi sai ƙira’ar da Zafar ya kunna a motar. Hannun sa ɗaya na riƙe cikin na Zara tana shafawa softly, jikinta na sanyi all of a sudden saboda kewarsa da ta fara ji. A bayan mota ma Imaan ce kwance kan jikin Yemma itama jikin ta a sanyaye dan bata taɓa tafiya ba tare da Yemma ba. Wayar Zara ce ta fara vibrating. Ɗauka tayi tana kallon mai kiran sannan tasa hannu ta rage volume ɗin karatun kafin ta ɗaga wayar. Muazzam ne ya fara bata haƙurin bai dawo gida da wuri ba; baban Surayya ne ya kirasa akan yazo dan Allah, yanzu haka tun ɗazu yana cikin gidan ana sulhu ne. Gyaɗa kai tayi tana cewa, “Its fine Yaya, I understand, kayi mana addua.” Addua ya ringa kwararo mata sannan yace ta bashi Zwar, gaya mai tayi sai dai ya kira Omar, daga haka sukayi sallama ta kashe wayan… Ƙarfe goma saura na dare suka isa MMIA inda kai tsaye suka wuce FBO inda suka shafe minti 40 acikin airport ɗin gaba ɗayan su. Hira suka sha sosai har Baffa cike da annashuwa. Zafar dai na manne da matar sa baya ma jin kunyar kowa, holding her close as if she would disappear, tana jikinsa all the time. Gaba ɗaya ya dawo wani shuru shuru ko hiran bayayi, yana sauraren su kawai. Itama haka Zara duk jikinta yayi sanyi, duk da ita tana sa baki cikin hiran. Baffa ne ya kalli agogon sa, checking the time with a subtle frown, sannan yayi gyaran murya yace ayi addua. Daga haka gurin yayi tsit, the noise suddenly fading, Zafar ya fara addua duk suna amsawa in solemn whispers. Bayan ya gama kuma aka miƙe, shuffling their feet as the departure reality set in. Baffa ne ya fara musu sallama yariƙe da Mezyan sannan ya fita. Yemma itama ta rungume Zwar da Imaan tightly, kafin ta juyo ta kalli Zara ba yabo ba fallasa, her face strict but her eyes softening just a bit, tace, “You are going to a blessed land where prayers are never rejected. Pour your heart into prayers for the little one while you are there.” Zara ta gyaɗa kai tana murmushi softly, tace, “Insha Allah.” Daga haka Yemma ta juya, her elegant abaya trailing behind her, ta fice tare da Noor dake ta faman ɗaga musu hannu with a wide grin. Zafar yabi mahaifiyar tasa da kallo, a small, grateful smile playing on his lips, yana jin daɗin yanda tasa cikin a rai tun daga ranar da ya kai mata result ɗin test ɗinda akayiwa Zara ta tabbatar akwai cikin. Omar ya ƙaraso yana kissing kan Zara affectionately sannan ya isa gurin Zwar, leaning down yana masa magana a hankali da babu mai jinsu. Idon Zara tuni ya ciko da kwalla tana riƙe hannun Zafar dake kusa da ita gam, her fingers intertwining tightly with his as an overwhelming wave of regret hitting her na cewa da tayi ba dashi zata ba. Kallon Zafar tayi wasu hawaye na fara zubo mata, her lip trembling slightly. Shima murmushin ƙarfin hali kawai yake, his eyes scanning her face with deep longing. Ya janyota jikinsa in one swift motion ya rungume, tana fashewa da kuka cike da shagwaɓa da sangarci, clinging to him tightly, burying her face in his chest. Da kyar ya samu ya lallashe ta, stroking her back gently, dan lokacin tashin su yayi. Bayan ya samu tayi shuru, wiping her wet cheeks with his thumb, ya sake ta ya sunkuya yana sumbatar cikin ta cike da so, pressing a long, warm kiss against her fabric, sannan ya miƙe ya sake janyo ta ya rungume yana cewa, “Like Yemma said… Take all the time you need and pray for the baby, yeah?” Zara ta gyaɗa kai tana turo baki tana goge sauran hawayen ta with the back of her hand. Lead flight attendant ce ta ƙaraso inda suke tana gyaran murya, stepping forward politely, wanda hakan yasa su ɗagowa suna kallon ta. Ɗan tight smile tayi tana cewa, “Deeply sorry to interrupt, Mr. Galado. The captain asked me to inform you that we’ve already missed our original departure slot. Luckily, Air Traffic Control just granted us a strict five-minute extension to close the doors, or we'll face a heavy delay.” Giving her a short curt nod, yayi kafin ya juyo ya kalli matar sa. He cupped her face in his hands ya fara showering fuskarta da kisses kamar zai haɗiye ta, kissing her forehead, cheeks, and nose repeatedly, kafin ya ɗan ɗagato yana kallon cikin idonta yace, “Allah ya tsare, barakallahu fiki. Go safely, and call me the moment you guys touch down.” Zara ta gyaɗa kai tana sake kwaɓe fuska kamar zatayi kuka, her eyes welling up again. Da sauri ya juya, turning on his feet without looking back, ya fita dan yasan bazai iya tafiya inta fara kukan nan ba. Karfe 11:05 jirgin su Zara ya ɗaga zuwa Saudiya, roaring into the night sky, inda ta tafi cike da kewar mijinta, shima kuma ya koma gida, staring at the empty passenger seat of his car, cike da kewar matar sa…