Free chapter · Read without an account
KUSKURE 26
*KUSKURE*
By Maman Shaheed
Shafi Na Ashirin d shida
SAFWAN be farka ba saida yaji Ana kiraye2 sallah sanan ya tashi ya tafi masallaci bayan yayi alwala.
Su twins sun shirya tsaf ,hidaya tacema Ammy zata itama ,Ammy tace musu " adawo lpy"
iyaa ma tace "Adawo lpy" su Noor da haneef da Janna karamar Babar su Noor sunata murna zasu unguwa kunsan yaro da son yawo .
Indo ashiga cikin doguwar Riga yaluwa (yellow color) Mai adon wasu golden Stones ta rolling brown veil ,tayi kyau matuƙa tare da taimakon hidaya tasa flat shoe d'in ta fuskar ta d'auke da fara'a wacce ta yalwata fuskar ta ,tayi make-up d'in ta wala'ba'asa light one tayi kyau matuk'ar kyau da kaganta kasan Tana cikin farin ciki bayanane
Duk suka fito sukama Ammy sallama ,Ammy tabada sako a Leda taba hassana tace su ba Inna suce Tana gaishe ta .
Suka karba , Indo ta farama Ammy godia da Addu'a ,Ammy ta dakatar da ita ta hanyar "ba komai Kar ki damu ,kuje kuyi maza ku dawo"
Har sun Fara tafiya Ammy ,tace "hassana ya baku yima huzna magana ba ,kartaga kamar kun ware ta" gaban Indo sai da ya bada daram!
Hassana ma tasan ba zuwa zatayi ba , ussaina ce tace "Ammy bacci fa takeyi Kuma tace in aka tashe ta Tana bacci kanta ciwo yake Mata shiyisa muka kyaleta"
Ammy tace "ok, haka wani yake Kam bayaso a katse Mai bacci sai kansa ya Sara ,toh kuyi maza sai kun dawo ku nemi driver, kuce yayi tuƙi da nutsuwa"
Kafin su twins su fita Janna ta dawo da gudu Tana cewa "driver baya Nan wai ankirashi Kiran gagawa a gidan Shi"
Ussaina aka zuciya aka nufi hanyar fita don Jin dalilin da baze fada musu uzirin shi tun wuri ba har ya riga ya amsa musu ɗazu.
Ammy Ce ta dakatar da ita da cewa "tsaya nace uwar masifa kamar ita yake ma aikin" Ammy ce ta saka hijab suka nufi wajen baba Mai gadin da kanta.
Mai gadi na ganin Ammy ya Fara Mata barka da yamma , ta amsa cikin sakin fuska hade d tambayan shi uzirin driver .
Baba Mai gadi ,yace "wlh muna tare tun d'azu su kawai yake jira ,yanzu aka kirashi wai yaron wajen sa ne me babur ya Kaɗe shi kamar Ana zargin ya Sami gocewar ƙashi ,shine yace bari yaje ya gani yanzu ze dawo na baku hakuri kafin ya dawo"
Amman barin kirashi naji, YA d'aga waya zai Kira .
Safwan ya shigo gidan ya dawo dg sallah .
Ammy ta dakatar da baba Mai gadi da Kiran da zema driver, tace, "ai babban uziri ne dashi gara da ya tafi"
Atake ta ummarci SAFWAN da ya taimaka ya kaisu su.
Yace "Ina zan kaisu?"
Noor d haneef suka bashi amsa da "gidan Inna wacce take bamu Aya da gyaɗa me kirkin Nan da kace itama kakar muce Inna aunty Aishatu (Indo) Dady Dan Allah ka kaimu kaji?"
Ya gane inda zancen ya dosa ,Amman yace ma Haneef "wace Aunty Aishatu Kuma?"
Janna tace "lndo Ammy tace mu dinga kiranta da anti Aishatu shine sunan tana gaskia" Jin sunan yayi har cikin jinin shi da ɓargon shi da ya rasa dalilin hakan.
Ammy ce ta katse su da cewa "Dan Allah kayi ka kaisu ba jimawa zasuyi ba sai ka dawo dasu matuk'ar hakan ba'a shiga sabgogin ka ba driver ne wlh yaron saya gamu da tsautsayi kaga Kuma tsautsayi Yana Kan kowa"
Bashi da zaɓi ga su Haneef nata Mai nacin ya kaisu , haka ya haƙura kodan su Noor yace "kumuje na kaiku Amman karku ɓata min lokaci"
Sai a lokacin ya hango Indo cikin wata mayar doguwar rigar da ya shiga tantama shin Anya shi ya siyo da hannun sa kuwa ? To ai shi daukowa yayi ba zaɓa ba kawai ,Amman sune sukayi kyau....can kuma ya kwaɓi tunanin shi da Kar ya zarce yaje inda ba'a tura shi ba ,Yana Kara Satan kalon ta.
Itama Indo ajiyar zuciya ta sauke da taji ya amince zai kaisu kodan Kar farin cikin ganin Inna ya koma ciki.
Su twins baya suka shiga har hidaya ,Indo Tana Shirin shiga bayan ganin Haneef ya shiga gaba kusa da dadyn shi , hassana ce tace Mata "Indo gaba Zaki shiga Dan kece kikasan gidan ke Zaki nuna hanya da layin da gidan tunda mu ba sani mukayi ba"
Safwan beso hakan ba ,Indo ma ji tayi wani iri wani banbarakwai namiji da suna hajara l Amman Bata d zabi Jin muryar safwan na cewa "kefa muke jira" da sauri ta shiga Tana sunkuyar da Kai k'asa ,Haneef nata murna ya matsa ta zauna ya jinginu da jikin ta Yana Mata Hira .
Mai gadi ya buɗe musu gate ,suka Cinna hancin mota sai hanyar gidan Inna.
Suna tafiya Haneef yaga Mai sai da Apple, mango,banana, fruit dai komai Akwai a gefen titi ,Haneef yace a siya Mai har yanama dadyn shi magiya .
Dadyn nashi yayi dariya yace "Kai kaɗai za'a saima Banda su Aunty Janna da sis dinka Noor?"
Da sauri Yace "harda su Amman nawa yafi yawa ,ko Dady?" Yace "Kai Haneef Banda son Kai fa"
Noor tace" barshi Mana yaro na girmeka nawa ne zefi yawa"su twins nata musu dariya har Indo d hidaya .
Safwan parking yayi ya ce Haneef din ya fito suje asiya ya nuna Abin da yakeso ,Indo ta Miƙa Mai shi har hannun su na gogan na juna ,wani bahagon sak'o ya shiga sasan jikin su indon da safwan din duk suka rasa gane kome hakan yake nufi ,yasa Haneef agaba suka tafi .
Leda 3 yayo Niƙi Niƙi da kayan fruits
ya miƙama su twins Guda biyu ya mik'ama Indo ɗaya batare da ya cemata komai ba ,itako ganin cewa Akwai waje a gabanta ne yasa ya Miƙo Mata ta ajiye Mai ,Dan haka ta ajiye da niyar in suka sauka ta cemai ga ledar Shi.
Suka shiga sukaci gaba da tafiyar ,tare da taimakon Indo suka Isa har ƙofar gidan Inna.
Suna Fara fitowa sukaci Karo da nawara kawar Indo ,tanata bin su da kalo Tana Shirin shiga gidan Inna ,ganin Indo a cikin su yasa nawara dawowa da baya ,Aiko indon itama ta ganta da gudu nawa tazo ta rungume Indo Tana cewa" ƙawar zuwa ba sanarwa? "
Indo tayi murmushin farin ciki tace" wlh zuwan ne yazo min kawai "
Indo Ce tace ma su Haneef da su twins su taho su shiga Tana kamo Janna da Noor Haneef dama Yana hannun ta.
Safwan na cikin mota idon sa ƙirrr....Akan Indo ya kaleta ya Kali yaranshi da farin ciki ya bayyana a fuskar su Yama rasa gane murnar me sukeyi da zuwa gidan su indon ,can Kuma yace "Koda yake shimfidar fuska ai tafi ta tabarma" Yana Kara binsu d kalo ..
Su twins sunyi gaba har hidaya ,safwan ne ƴa Kira Indo da sunan Aishatu Wanda shikansa besan sanda yayi Amfani da Abin da zuciyar sa ta ayyana Mai ba ya jefar d Abin d harcen sa yaso furtawa wato (Indo)
Ba Indo ba kowa sai da ya waigo Dan ya tabatar Kiran sunan daga bakin shi ya fito ,Aiko kowa y tabatar shine ya Kira ,sunan ya zauna a bakin shi kuwa ga iya fitar da sunan da yayi ,Indo dai ganin tabas da ita yake gudun Kar ta bada shi yasa ta zuwa tace" naam dadyn su Noor "cikin wata kasalaliyar muryar
Muryar ta sakar Mai da saƙonni da dama a jikin shi ,da wata irin murya Yana Mata wani irin kalo, kalon da Saida ta shiga firgici.
Yace" wa Kika barma ledar Nan?"
Cikin sanyin murya Tace" au inace takace ai"
Ya Mata wani kalo Kafin ya firta "ai Dole ta zama tawa tunda ga biri natacin wanan uwar ayabar zuwa Nan da sati biyu na cinye" dariyace ta kusa kubcema Indo Amman Kar yace ta Raina shi Dan ba kowa ne yakeson dariya ba in yayi magana , Dan haka tace" in d'auka in shiga dashi Ne? "
Ya d'auke kanshi gefe Yace" in kinyi ra'ayi ba , inko Baki yi ba ki Bari har asamu Mai d'auka ya shigar Mata dashi"
Jin kalaman shi yasa ta gane na Inna ne ,Dan haka Kar maganar tayi tsayi gashi Ana jiranta yasa ta d'auka ta Fara jero Mai Addu'a....har Saida ya dakatar da ita da wani salon kalon da NAWAL kawai yakema irin kalon, dan Har so yayi da ace daga bakinta addu'a ta fito.
Shiko besan ma yayi ba ,itako Jin wani Abu baƙo atare da ita yasa tayi saurin barin wajen ta nufi inda su twins suke jiranta .
Da sallama suka shiga ,Inna na ganin su ta karbe su hannu bibiyu tanata murna Tana cewa su Noor su matso kusa d ita.
Aiko Nan su twins suka Fara gaishe da Inna cikin kulawa da fara'a take amsawa .
Sun Sami gidan tsaf tunda ba yarane da ita ba komai ƙalƙal tanata tuyar wainar filawa wai tayi sha'awar ta.
Dan haka tace ma Indo tazo ta Kara kwaba ƙulin wainar ga filawa a roba tayi maza ta soya musu Dan gidan ya gauraye da ƙamshin wainar taji Albasa Mai ganye da attaru Tana fita gwanin sha'awa dan kaskon ya horu.
Hassana ce tace" laa Inna da Kin barshi akoshe muke"
Inna tace "haba 'yar Nan ai abar sha'awa ce kwa maida yawu ga ƙamshi duk ya cika gida saidai ko in bakwa iya cin girkin mu na yaku bayi" Jin haka ussaina tace "laa wlh aa Inna ko ɗaya Ai duk ɗaya muke atoya zamuci" dan Dai su kwantar ma da inna hankali.
Inna tace "toh yanzu naji Batu ga filawa ga yaji dazu Yar Albarka nawara taxo ta daka min shi Ashe Kuna hanya"
Indo da nawara da hidaya nata hada kayan wainar wani na toya sauran ƙulin wasu Kuma na kwaɓa sabo wani na yanka Albasa.
Bayan hassana ta mikama Inna ledar da Indo ta ajiye batare da tace Mata komai ba ,tace"gashi inna inji Yaya safwan yace abaki "
Aiko Inna tayi ta shimai da Albarka ,Tana ma iyayen shi Addu'a sunji Daɗi sosai.
Noor ko da Hannah da Haneef Inna ta cikasu da ɗata da karass sunata ci suna nishad'i .
Nan da Nan aka Fara soya wainar nawara ce Mai suyan Tana mik'oma su twins sunata ci cikin Jin Dadi da nishad'i Abin su Nan da Nan suka Saba da Inna wata shak'uwa ta shiga tsakanin su ,kamar ba yau suka Saba ganin juna ba.
Sunci sun ƙoshi sanan suka wanke manjan hannun su da omo, Inna ta Basu su kantu Mai siga da Mai gishiri da Aya da gyaɗa har su hanjin ligidi ,su Noor sunata murna zasu sha Dadi in sun koma gida.
Sukama ,Inna sallama da godiya bayan sun Bata sak'on Ammy Nan ma addu'a tayi Tama Ammy da Abban su ,tamusu fatan Isa gida lpy , har Tana cewa agaida uwar d'akin Indo hajiya NAWAL ,sukace "zataji"
Suka doshi mota Dan komawa gida , safwan na gaban mota yanata Danna wayar shi wai har yaje wajen abokin shi yanzu shima ya dawo , Indo da nawara badon sun so ba suka rabu da Alk'awarin Indo na Nan zuwa bayan an kwana biyu .
Yadda suka Zo haka suka koma suna baya Indo da Haneef na gaba .
Koda suka koma gida suna shiga ,huzna na zaune a parlour ta gama baccin asara ,tanata Shan ƙamshi .
Taji haushin fitar su da Kuma zuwa inda sukaje ,Tana ganin hakan kasƙanci ne da zubarwa Kai da kima su rasa inda zasu wai sai gidan su Indo Mai Aiki wahalaliya boyiboyi su, ita ta rasa gane irin zuciyar su twins.
Harda safwan da take kalon kamar ya waye yasan kanshi, ƴar aikin shi Ashe soko ne ?.
Harda su Noor sai kace zasu wani irin outing dinan irin zasu yawon zaga gari dinan ...tir ...!
Bata ƙara firgita da shiga ɓacin Rai ba sai da tayi tozali da Indo da rigar da tafi so acikin kayan da taketa so da sanin na waye acikin gidan.
Ɓacin Rai da takaici ƙarara babu sayawa a fuskar huzna ,gaba ɗaya kwanyarta ta shiga rud'u da firta "shin indon Ce wai ? Kuma dama kayanta ne? Safwan ya siyo Mata? Kodai Ammy ce ta bashi kuɗi ya shiyo Mata? Dan NAWAL ko Indo zata tafi tsirara tasan bazata sai Mata wanan zuƙa-zuƙan rigunan ba sadai ta tafi tsirara" a fili yadda babu mai jinta.
Kai Ina badai safwan bane ya siyo Mata kayan Nan , indon ? To ai daga wajen shi aka taho da kayan Kuma ance na sako NE kamar yadda hassana ta shaida Mata .
Kai Aiko sai ta tabatar sanan zata yanke hukuncin Dan haka ta d'auke idon ta d'aga Indo Dan samun sasauci .
Suko sunata ba Ammy labarin karamci irin na Inna da Abin da ta Basu ,twins hidaya Indo duk su suka Fara yima huzna magana ta amsa na hassana da ussaina Amman Taƙi amsa na hidaya da Indo .
Hidaya dai yatsina Baki tayi ta tafi wajen iyar ta ma .
Indo ko waje ta nema ta zauna tanata gayama Ammy sak'on godia da Inna ta Bata ta faɗa ma Ammy.
Ammyn nata cewa" ba komai yima Kai ne " huzna nata Jin haushi yadda suke ma indo da iyayen ta suna d'aukan kansu ɗaya salon ta Raina su ,Anya Indo Basu mallake su Ammy ba da asirin su irin na matalauta ? Wanan shine tunanin huzna .
Shiko safwan masalaci ya nufa ganin magriba ta yi.