Free chapter · Read without an account
KUSKURE 30
*KUSKURE*
BY Maman Shaheed
shafi Na talatin
Ran Huzna iya ɓaci ya gama baci ,daga baya ma tabar musu parlour ta koma d'aki .
Safwan ma ranar kwana yayi Yana tufka da warwara akan shaƙuwar yaran shi da Indo ,ya sake tir da Hali da dabi'u irin na NAWAL da ta jefar da yaranta da bata Basu kulawar da Indo take basu da be Sami matsala kamar haka ba da ta amsa sunan ta na uwa agare su ,Amman yanzu gashi ta raba Mai gida ,inda yaran shi suke samu kulawa daban ,wacce ta haife su daban "wanan wacce iriyar rayuwace da NAWAL ta jefasu gaba daya?" ya firta a fili.
Kwana yayi Yana tunani ,da Jin zafin Abin da NAWAL tayi ga Yabo da yake ma Indo cikin zuciyar shi na kula da yaran shi da takeyi uwa uba Basu tarbiyar ta tsakani da Allah ko uwarsu iyakacin abinda zata musu kenan.
Yana cikin tunanin ,ya tariyo maganganun NAWAL da takecewa ya maye gurbinta da Indo ,atake kirjin shi ya bada wani gajeren sauti , ya rintse Ido tsabar Jin zafin maganar .
Ya tabatar da lalai NAWAL ta boyemai abubuwa a iya sanin da ya Mata ko Kuma ta mugun canzawa daga NAWAL din da ya sani zuwa wata daban ,ya tuno da kalaman da suke sanyayama junan Rai akoda yaushe in suna cikin nishad'i tun kafin Auren su har Auren su .
Sukance ma junan su ɗaya baze iya rayuwa babu daya ba, Dole bazasu iya ba sai suna tare da juna ,to gashi ta ƙaryata abin da take gayamai da kanta Dan ita ta Fara bilo da hakan Har ya zamar mai kamar karatu.
Ya Jima Yana mamaki da tunani akan Rayuwar su ta farin ciki zuwa yanzu da komai ya canza ya Karo tuno zafafan kalaman da ta dinga duban idon shi Tana Gaya Mai ,ya Kara tabatar da cewa lallai NAWAL ta gama rainashi ,ga babban raini da take hadashi da Indo yarinyar da kyakyawan motsi Bata iyayi in Yana wajen tsakanin ta dashi girmamawa da ganin mutincin juna shine zata dinga hada shi da ita Dan ta rainashi?
Shima bai taɓa ganin wata mace ba bayan ita, Amman zata haɗa shi da wata mace kuma ma Indo, badan yana ƙyamarta ba.
Wani sashin zuciyar sa ya tambaye shi "kafi karfinta ko ? Ka wuce sanin ta ?"
Yayi saurin gujema tunanin wani sashin zuciyar tasa da cewa "bance ba dai Amman haɗin ai Bai haɗu bama" sai da yayi da gaske sanan yayi watsi da tayin Indo da zuciyar sa take kawo Mai take ɗorawa akan maganar NAWAL.
***********
NAWAL ta cigaba da gudanar da komai nata ,mu'amalar ta dasu Laila da haneefa sai Abin da ya cigaba ,suna sha'anin su son ransu sun yadda da junan su sosai ga d'aukan shawarar junan su kamar wahayi ko hadisi ,hakan zaman nasu yaketa wakana.
Indo nagabatar da Rayuwar ta cikin kwanciyar hankali da jin Daɗi gata ga Inna ta ga ƙawar ta nawara .
Yaune hidaya ta kawo Mata ziyara ,suka haɗu da nawara sunata ma Indo tsiya akan saurayi da Bata shawarwari ta d'auki na d'auka tayi watsi da Wanda taji wayewa ta shigo irin ta zamani samarin shanminti da lalube,suna Mata hakane Dan ta goge da yanayin zamani da ya canja itako gani take zasu kaita inda Allah Bai kaita ba ,gwanda nawara ma ,Amman hidaya itama ai kamar indon take masu rangwamen gata masu neman na rufama Kai Asiri Dan mamanta ta rasu sai mahaifin ta da take taimaka musu ita d ita Kuma shima ba ƙarfi ne dashi ba ,Dan haka Indo take sata a sahun su Dan kusan jirgi daya ne y d'ebo su .
Sun Sha Hira gab da hidaya zata tafi ta ɗagama Indo hankali da rigimar da su Noor suketayi tun tahowar ta gidan Inna har yau Basu Dena ba Abu kusan sati guda ,Amman Basu haƙura da ita ba .
Aiko duk Indo ta canja taji ba Daɗi ,Kuma dama tanajin yaran aranta haƙuri takeyi kawai Saboda ba Wanda zatama hirar ,haka dai suka raka hidaya ta hau napep suka dawo nawara tayi gida akabar Indo cikin tunanin halin da suke ciki ita da su Haneef na shaƙuwa Daga Allah.
Itama ta Jima Tana tunani akan shaƙuwar su da su Noor gashi ba Abun da suka had'a, tama rasa gano amsar tunani da shakuwar su da su Noor yasa ta karɓi aikin Inna ta k'arasa ta gyara ko Ina na gidan.
Koda dare tayi haka Abin yake ga su Noor kwana sukayi suna rigima ,sai da Alhj su twins yata mafan rarashi Yana Al'ajabin shakuwar yaran da Mai Aikin ,Ammy ma mamakin hakan take ,Amman duba da sanin halayen Indo kyawawa managarta (halinka jarin ka) yasa bataga laifin yaran ba Dan ita kanta tasan yadda Indo take kula da yaran tasan uwar su ma Bata kula dasu haka ga inganta musu tarbiya da takeyi Dan haka yake sake son tarayar Indo da jikokin nasa.
Washegari da wuri dadyn su Noor ya Zo Dan ganin yaran shi ya ga halin da suke ciki akan rashin Indo a tare da su .
Koda ya Zo suka dinga murna da Mai magiyar ya kaisu wajen Indo ,ya dinga musu wayo da rarashi ya samu ze gudu ,Ammy ta kirashi tace ya d'aure ko in ya dawo ne ya kaisu gidan Inna su gaisa da Indo ko zasu barsu suyi bacci yau .
Baya iya musu da Ammy, ya jinjina Abun sosai kafin yace "Ammy ai da su Hassana sun kaisu"
Ammy tace" hassana da hussaina basa Nan anjima sunada bikin Kuma jiya akayi kamu basuje ba yau za'ayi wini da dinner shine zasu Kar dai ace basuje ba tunda an gayyace su"
Ganin ya tsaya tunani ,yasa Ammy magana tace Mai" to saidai idan kwatantama huzna gidan zakayi sai ta kaisu"
Jin an sako huzna yayi saurin ,kawar da zancen yace "aa zan dawo da yamma sai na kaisu kawai"
Ammy tace "ko kaifa ,Allah ya dawo dakai lpy"
Yace" Amin" ya tashi ze fita ,Noor tace "Dady zaka kaimu wajen aunty Aishatu?"
Yace "eh inna dawo daga office ba" Yana musu murmushin sa Mai ƙayatarwa ,Aiko Haneef yasa murna Yana cewa "yeeeee"
Safwan d Ammy ma tsayawa sukayi suna kalon yaran suna Kara Al'ajabi wanan ƙaunar da take gudana a tsakanin su da indo sun tabata inda Tana cutar dasu da bazasu k'aunace ta haka ba.
Da haka dai ya ma Ammy sallama ya tashi ya tafi ,su Haneef nata Mai Addu'ar dawowa lafiya.
************
Safwan a office yanata tunanin zuwa gidan Inna Kai su Haneef ,yace gashi ba waya da da ita da ya kirata ta Zo ta d'auke su , tun tuni yaso Bata waya don in tatafi gidan Inna in suna buƙatar ta su kirata uwar d'akin ta NAWAL Taƙi Amincewa ,ganin ba musu a tsakanin su ya hak'ura ya ƙi Bata suka zauna lafiya .
Around 5:30 safwan ya ƙaraso gidan Ammy daga Ammy sai Haneef da Noor ,huzna ta tafi wajen wata Yar makarantar su ,su twins da Janna sun tafi wajen biki, dole yasa gidan ma baze musu daɗi ba, gashi suma sun sami wajen zuwa.
Ammy tamai tayin Abinci yaci yasha ruwa ,su Noor suka dinga damun shi wai sutashi su tafi gidan su Aunty Aishatu .
Ammy dama ta gama gyarasu , Jin magiyarta su Noor ta dameta ,tace ma SAFWAN "Dan Allah ka tashi ka kaisu Kar su zauce in Basu ga Aishatu ba yau"
Safwan na dariya ya tashi ya d'au makulin motar shi Yana cewa "kuzo mu tafi"
Ammy tace "safwan Kar a tafi musu haka ,duk d nasan ka da Alkhairi da taimakon naƙasa da kai, Allah dai yasa Amizani"
Yana murmushi ya gano manufar Ammy ,yace "Ammin Ammy" yaji dadin yabon da ta Masa Kuma ya kama su Noor suka tafi .
Around 6:15pm suna ƙofar gidan su Inna .
Noor da haneef ne suka fito suna zumud'in shiga gidan su Indo .
Haneef ko tuni ya ruga ya zunduma gidan su Indo da gudu.
Safwan tsayawa yayi Yana kalon su kawai Yana mamaki ikon Allah.
Noor yacema ta Kira indon.....ta tafi da gudu itama kafin ya ƙarasa maganan sa, Baki buɗe ya bita da kallon mamaki.
Indo na zaune kusa da kurfot Tana girka taliya yar hausa ta filawa da taji manja da ataru da Albasa Mai ganye ga Dan kifi da suka watsa Mata sai kamshi takeyi .
Indo sai Jin sallama tayi da ƙaramar murya ,Inna na tabarma suna Hira da Indo Tana ƙula kayan sana'ar ta ,sai ganin haneef sukayi ya dafe bayan Indo.
Yana "Aunty kizo muje gidan Ammy kin taho kin barmu" Koda ta juyo tayi arba da Haneef itama rungumeshi tayi Tana "Haneef Kai da waye?"
Kafin ya Bata amsa Noor ta shigo ta Fado musu tana murna , itama, Indo ta had'a ta rungumo su tana Jin wani Abu na shiga jikin ta son yaran na ƙaruwa aranta.
Cewa Noor tayi "dadyn mu na waje yace ki leƙo wai"
Indo ta ɗan zaro Ido tace" tare kuke da shi? Banda su aunty twins? "
Noor tace" eh mu da dadyn mu ne ,su Aunty suna wajen biki da Janna"
Indo dai ba yadda ta iya ,haka ta zaunar dasu kusa da Inna ta d'auko gyalenta ta saka Dan zuwa wajen dadyn su, taji Ko wani saƙon ze bata.
Noor da haneef ko Fara gaishe da Inna sukayi Tana sakar musu fara'a Tana amsawa ,Tana tambaya su maman su da Ammy da mutan gidan, duk suna bata amsa.
Koda Indo ta sa ƙafa a kofar fita dg gidan inda take hango dadyn su Noor ,tsintar kanta tayi da Jin nauyin ƙarasawa wajen da yake a tsaye jikin motar shi.
Shiko ya duƙufa da latsa wayar sa, Bema san ta fito ba.
Ganin Bata da zaɓin da ya wuce zuwa Kiran nashi yasa ta ,ƙarasa jiki a sanyaye .
Koda ta k'arasa besan ta Zo ba ,kamar mai sanɗa, sasanyar muryar da ta Aika Mai cikin kunen sa ne ya sanar Mai da ta k'araso.
Ya juyo a nutse ya kaleta ,yace "Aishatu kin tashi hankalin jama'ar gidan su Ammy (wato Banda shi) su Noor wai sai kin dawo ko ankawo su gunki"
cikin zazaƙar muryar ta ta Fara gaishe shi ,sai a lokacin ya tuna ko gaisawa basuyi ba Ashe ,yace" lafiya ya su Inna?"
Tace" Inna lafiya take sunata Hira n baro su da su Noor, tace agaishe ka"kanta a ƙasa da girmamawa take mai magana.
Jin haka ya Mai dad'i ko ba komai ya farantama yaran shi cikin lokaci ƙanƙani ,yace" hmmm su Noor bade surutu ba ,dama kawo su nayi su ganki ko sabar su twins yau su runtsa dan kullin da rigima suke kwana"
Indo tace "wai rigima sosai sukeyi?" ita kanta ji tayi maganar ta fito mata.
Yace" eh sosai suke rigima akawo su ko kizo wajen su ,bamuga farin cikin suba sai yau da akace za 'akawo su gunki"shima Yaji Yana doguwar hira da ita.
Indo ta sunkuyar d Kai ,Tana cewa "to rigimar su Noor ta motsa kenan"
Ajiyar zuciya ta sauke.
"Ni da nake Shirin dawowa wajen Inna gaba ɗaya ma Dan sana'a zamu Kama kafin in cigaba da karatuna in Allah ya nufa"
Cikin wata irin murya safwan yace "me?" A zabure dan Har ji yayi kamar ta watsa mai fetur.
Sai da ta maimaita kafin
Yace "aa ki sake tunani su Noor din fa suyi Yaya?"
Shi kansa besan magana daga bakin sa take fita ba , kowa yasan yayi son kai ƙarara a kalaman shi.
Ita kanta Indo tayi mamakin furucin Shi, na fifita buƙatar yaran shi.
Har d'ago wa tayi Dan ta tabatar da shine ke magana haka .
Shine yayi daidai da Ankara da irin kalaman da suke fita a bakin shi kamar da NAWAL yake magana.
Kalon juna sukayi ,Indo tayi saurin ɗauke idon ta shiko kasa kawar da nasa yayi ,sai d azuciyar sa ta tuna Mai Abin da yakeyi sanan ya kawar da nashi Indo zuciyar sa cike da wani irin Abu.
Jin anfara Kiran sallah yace "d'auko min buta nayi Alwala Dan yin sallah a jam'i"
D sauri ta juya zata tafi Dan neman guduwa takeyi dama bayan ta amsa, har ta Fara tafiya ya kirata.
Cikin sanyin jiki ta dawo ,ya buɗe marfin Mota ya ɗauko Leda ya Miƙo Mata ledoji guda biyu da Kaya a ciki na ciye ciye yace "ki kaima Inna"
Jiki a sanyaye ta karba ta Fara jero Mai Addu'ar da ko NAWAL Bata tab'a Mai irin ta ba ,Jin dad'in sauraren Addu'ar kamar karta Dena yasa ya yi shiru Yana sauraron Addu'a sai da ta ankare da lalai sauraron ta yake kamar Mai biya Mai karatu ,sanan ta tsayar da Addu'a tata ta yi hanyar gida.
Ta Fara tafiya tajiyo muryar shi Yana cewa "Amin suma Amin nagode Aishatu" ya farta ahankali dan itama sai tayi da gaske zata iyaji.
Ji tayi kamar ta juyo ta cigaba da Addu'a Dan ya ƙara gode Mata ,ashe taji shi, Amman kunya da nauyin shi Basu Bata Daman hakan ba Amman taji Dadi matuka da godiya da Kiran sunan ta da yayi .
Bayan t a d'auko Mai butar inna da yara basa taɓawa ta Zo ta bashi hanun su ya haɗu da na juna ya bada wani irin sasanyan sanyi mai game dukkan jiki tad'an risina ta Miƙa Mai Yana karɓa ta wuce gida Tana tuhumar kanta "meye wanan abin baƙon yanayin nan da ya ziyarce ta?"
Bata da amsa dole ta haƙura da son sanin ko meye.