Free chapter · Read without an account

Sawun Keke

by Ayeesha Abdulkareem · SAWUN KEKE season 1

Kamar a mafarki idanunta suka yi arangama da Rislan yana takowa zuwa ciki, yana sanye da Fararen kaya na saƙi a samansu ya ɗora baƙar Alkyabba itama ta saƙi, tinda ya doso idanunsa na kanta yayin da ita ma ta kasa ɗauke kallonta daga gareshi.
Adadin kusantota da yake yi adadin ƙaruwar bugun Zuciyarta, zaram! ta miƙe kamar an tsunkuleta cike da kaɗuwa da lamarinsa ta ce "Akhiee?? kai ne ko kuma mafarki nake yi? ni fa dama ban san wanda ya kawoni nan ba kawai ina Ofishin Ƴan-sanda sai na buɗi ido na ganni a nan, gaskiya mafarki ne, wannan ba Akhiee ba ne!" ta ƙarasa maganar cike da bawa kanta yaƙini. Hannayensa dake goye a gadon bayansa ya sauke hakan ya bawa idanunta damar yin arba da Zobukan hannunsa guda tara da kuma jan lallen da ya zamowa yatsunsa tamkar ajali.
Idanunta ne suka ƙara girma ta ƙara matsawa baya ta na zazzaro masa ido, "Akhiee!! to waye ya kawoni nan? kuma ina ne na ɗin??" ta jefa masa tambayoyin a kiɗime "Ni na kawo ki da kaina, kuma nan gidanki ne" ya bata amsa gami da raɓewa ta kusa da ita zai wuce.
Cikin ɗaga murya ta dakatar da shi da cewa 
"Rislan!!" komai naka tsoro yake ban!, don Allah waye kai??? ka faɗa mini gaskiya, shin kana Fashi ne? ko kuma kana Kidnappen?, Akhiee ko dai kana Tsafi da jinin Mutane ne kamar yadda Ƴar uwarka ta faɗa?????" cikin nutsuwa ya juyo yana zuba mata idanunsa da suka koma kalar Golden sun yi wani Zaiba-zaiba sai sheƙi suke yi. "Asma'u na ce ki dena bani dariya domin kinsan idan na yi ta akwai matsala, za ki iya rasa ni ko kuma ki dena ganin ƙwayar idona har na tsawon lokaci" "Dariya kuma?? anya kuwa kai mutum ne Akhiee? me yasa dariya take zamowa matsala a wurinka?? wai kai Rislan wane irin mutum ne??, anya kuwa ba ka Tsafi??, ka gaya mini gaskiya don Allah!!" 
lumshe idanunsa ya yi ya buɗesu gami da ɗorasu akanta, lokaci guda ƙwayar idon nasa suka ƙara canjawa daga Golden zuwa Baƙi wulik farin kuma ya ƙara haske tamkar Madara.
Buɗe mata hannayensa ya yi kafin ya yi magana cikin muryarsa me cike da zarra da tsantsar jin kai "Rungume ni mana! sanyi fa kike ji kina buƙatar jin ɗumina, idan na fita yanzu ba za ki ƙara ganina ba sai ƙarfe 12:00am zan dawo mu koma gidanmu." 
Jikinta na karkarwa ta yi taku biyu zuwa gabansa, har lokacin idanunta na kansa, Zuciyarta na ƙara raya mata abubuwa da yawa game da shi, a hankali ta shige jikinsa gami da ƙanƙame shi ƙam, ya lumshe idanu gami da rungumeta, cikin murya irin ta raɗa ya ce............

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.