Free chapter · Read without an account
RAYUWAR SAMHAD
PAGE 1️⃣8️⃣⭐1️⃣9️⃣
___________________________________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحمن.
Bayan cikin Aisha ya shiga wata na takwas ta matsa akan tanason ta koma gida, Muhammad bai musaba ganin yanda tayi juri,ar zama a kasar bata taɓa cewa tanason zuwa gida ba sai wannan karon.
Waya yayi da Alhaji Bashir ƙarfe akan zasu dawo dan matarshi ta haihu a gida, fafur Alhaji ya hana yace saidai idan ita zata taho shiya tsaya saboda aikin da suke yanzu yake kai yana buƙatar nutsuwa.
Badan Muhammad ya so ba yasaka Aisha a jirgi ta dawo ƙasar haihuwarta ita kaɗai ba tare da shi ba, sunsha kukan rabuwa da juna dan tunda sukayi aure basu taɓa rabuwa ba dai-dai rana daya ba sai yanzu.
Bayan isowarta Alhaji Bashir ya tura driver ya ɗauko ta ya kaita har gidansu tare da kayanta.
Sosai Mubaraka tayi murna da da ganin yanda ɗiyarta ta chanza tazama matar manya kaida ka kalleta kasan hutu da kwanciyar hankali sun ratsata sosai.
Bayan ta huta sosai tayi waya da mijinta ta tambayi ina Nabila har yanzu tana zuwa ko ta daina zuwa tunda batanan.
Murmushi Mubaraka tayi ta ce "tana zuwa sosai ko jiya nan muka wuni atare tana bani labari har na faɗa mata kina hanya zaki zo".
Murmushi tayi tare da cewa "Allah sarki ƙawata ni kaina nayi kewarta sosai" sai kuma tace "Umma wai ina ina yaya Beela halan ta kusa aure?"
Shiru Maman tayi mata kafin tace "Allah dai ya shirya zuri'a amma sam ba ta jin magana yanzu bakiga yanda ta maida kanta farar ƙarf da yaji"
'Shiru Aisha ta na tunano irin yallayar Beela damacan tana shafe-shafen ta amma dai tunda har mamanta ta maganta akan abu to tabbas abin ya munana'
Cigaba da fira sukayi cikin nutsuwa dan kamar yanda Aisha batason magana da hayaniya haka mamanta take itama idan ka ga suna fira ahankali suke magana cikin nutsuwar da Allah ya azurtasu da Ita.
Sai bayan kwana biyu da dawowarta sannan ta shirya ta je gidansu Nabila dan su gaisa.
Nabila tayi farin cikin ganin yanda Aisha ta koma ga tsohon cikinta a gaba wanda ya ƙara mata kyau.
Aisha ba ta daɗeba gidan ta yiwa Nabila sallama ta tafi gidan dan tuda dazo ta lura da kallon da Maman Nabeela ke jefa mata sai duk tasha jikin jikinta.
Bayan tafiyar Aisha babu jimawa saiga Beela ta dawo daga yawon gantalin da ta saba, Maman Nabila ta sakata ɗaki ta gaya mata zuwan Aisha da yanda ta koma kamar wata Hajiya, sosai Beela ta rikice ta na ɗurama Aisha zagi ta uwa ta uba ta na faɗin shienan ta cuceta ta yaudareta tunda taji ance tana da ciki.
Dakyar Maman Nabila ta rarrashi Beela tare da gaya mata wasu maganaganu da suka sanya ta ɗan nutsu dukda a zuciyarta kobara ce ke ci ta tsananin ƙiyayyar Aisha.
Da marice suna zaune a parlo suna fira saiga Beela kamar an jefo ta faɗo musu, tsit sukayi suna binta da kallon mamaki, sosai ƙeya tayi ta gaida Maman Aisha a takaice ta koma kan Aisha tana ta yi mata tambayoyi harda tambayar tare da mijinta tazo da tace "A,a" sai ta kuma tambayar yaushe zai dawo.
Khaleel ƙanin Aisha ne ya ja uba tsaki ya tashi yana yiwa Beela maganar miye ruwanta da mijin Aishar.
Maman Aisha tabason rashin kunya dan haka ta dakatar da khaleel cikin tsawa tace ya tashi ya fice ya basu waje.
Cikin jin zafin abida Beela tayi ya fice daga gidan baki daya.
Beela ganin ba ta samu abinda ta ke so ba yasa ta tashi ta tafi tana sakejin tsanar Aisha na lunkuwa a zuciyarta.
A gidan su Aisha, Aisha kewa mamanta mita akan tambayoyin da Beela keyi akan mijinta.
Murmushi Maman Aisha tayi tana jinjina irin soyayyarda Aisha kewa mijnta da ta kasa ɓoye kishinta akan sa.
A kwana atashi cikin Aisha yashiga watan haihuwa wanda cikin dare suna waya da Muhammad yake faɗa mata zaizo gobe insha Allah Alhaji Bashir ya barshi yazo tunda aikin ya ɗan tsagaita.
Sosai Aisha tayi farin cikin zuwan mijinta wanda saboda zumuɗi ta kasa zaune ta kasa tsaye dukda yau tunda ta tashi takejin ciwon bayan kaɗan-kaɗan.
Bayan saukar Muhammad gidansu ya gaisa da ƴan uwa da abokan arziƙi yasake shiri dan zuwa wajen sanyin idaniyarsa dan yayi mising nata ba sosaiba.
Bayan yaje sungaisa da ƴan uwan Aisha da mahaifanta aka kaushi ɗakin da baban Aisha ke saukar baƙi.
Bayan sun gaisa da Aisha ya lura da yanda take cije baki hakan yasa ya tambayeta ko lafiya?
Bakomai tace mashi amma ganin abin yayi yawa yasa yace kodai haihuwarce? ɗaga mashi kai tayi dan zuwa yanzu dauriyarta ta fara ƙarewa ganin ciwon sai gaba ya ke.
Maman Aisha yasanamawa yace zasuje asibiti akula da ita acan.
Amsa shi tayi da suyi gaba ita zata taho ta kayan buƙatar.
Awa ɗaya shiru awa biyu shiru Aisha ba ta haihuba lititoci sai kaiwa suke suna komowa.
Hamkalin Muhammad yatashi da aka gaya masa haihuwace amma yaron yana kwance abisa bai juyaba dole sai anyi mata CS babu ɓata lokaci Muhammad ya rantaɓa hannu aka shiga da Aisha aiki.
Cikin ƙankanin lokaci aka ciro yaro namiji fari tas kamar uwarsa ƙaton gaske dashi.
Zokuga Murna wajen ƴan uwa da abokan arziki duk wanda ya ɗauki yaron saiya jinjinawa Aisha ganin girman yaron da kuma irin baiwa kyau da Allah yayi mashi.
Labarin haihuwar Aisha ya riski su Beela ahaukace ta tashi daga zaunen da take har tana kifawa tashiga ruwa kuka tana faɗin shikenan ta shiga uku Aisha ta haihu zata mallake dukiyar Muhammad.
Mummunar bugawa zuciyar Nabila tayi jin abinda Beela ke faɗi, kasa tsayuwa tayi ta zauna daɓas tana sakin zafafan hawaye na baƙin cikin halin yayarta kuma ƴar uwarta.
Maman Nabila ce ta lura da katoɓarar da Beela tayi agaban Nabila aiko ta hau naɗe tabarmar kunya da hauka harda cewa idan Nabila taje asibiti ganin Aisha sai ta tsine mata.
Sosai Nabila tayi kukan baƙin cikin halin mahaifiyarta ta ƴar uwarta, ida ba hanata zuwan da Maman Nabila tayi asibitine ya dame ta ba A,a da wane ido zata kalli Aisha baiwar Allah kawarta ta amanah ace wai yayarta ke son mijinta abun sam ba tunani aciki.
Ranar Nabila ɗaki ta wuni tana zubar hawayen baƙin ciki da takaicin abin kunyar da Mama da Beela zasu aikata.
𝑲𝑼𝑩𝑰𝒀𝑰𝑵𝑰 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑱𝑰𝑵 𝒀𝑵𝑫𝑨 𝒁𝑨𝑻𝑨 𝑲𝑨𝒀𝑨 𝑨𝑪𝑰𝑲𝑰𝑵 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑴𝑨𝑰 𝑻𝑨𝑲𝑬𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫, 𝑲𝑨𝑫𝑨 𝑲𝑼𝑴𝑨𝑵𝑻𝑨 𝑴𝑼𝑵𝑨 𝑪𝑰𝑲𝑰𝑵 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰𝑵 𝑻𝑨𝑹𝑰𝑯𝑰𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑴𝑨𝑴𝒀.
𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑲𝑼𝑫𝑰 𝑵𝑬 𝒁𝑨𝑲𝑰 𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑵𝑨𝑰𝑹𝑨 200 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑪𝑰𝑮𝑨𝑩𝑨 𝑫𝑨 𝑩𝑰𝒀𝑩𝑰𝒀𝑨𝑹 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰𝑵.
𝑴𝑨𝑺𝑼 𝑱𝑰𝑹𝑨𝑵 𝑫𝑶𝑪𝑼𝑴𝑬𝑵𝑻 𝒁𝑨𝑺𝑼 𝑩𝑰𝒀𝑨 400 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑨𝑹 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵, 𝑲𝑨𝑹𝑲𝑰 𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑨𝑩𝑨𝑹𝑲𝑰 𝑨 𝑩𝑨𝒀𝑨.
𝑮𝑨 𝑨𝑪𝑪𝑶𝑼𝑵𝑻 𝑵𝑼𝑴𝑩𝑬𝑹 𝑫𝑨 𝒁𝑨𝑲𝑼 𝑻𝑼𝑹𝑨 𝑲𝑼𝑫𝑰𝑵 👇👇👇👇👇👇👇👇
9136291920
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑼𝑴𝑨𝑹
𝑶𝑷𝑨𝒀.
𝑺𝑯𝑨𝑰𝑫𝑨𝑹 𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑻𝑨 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑳𝑨𝒀𝑰𝑵
👇👇👇👇👇👇👇👇
***
𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵✍️
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐⭐