Free chapter · Read without an account

.....

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD

BOOK 2️⃣PAGE 1️⃣7️⃣
__________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Cikin tattali da taka tsantsan Mubeen ke bawa  Samha kakkauran tea abaki, duk yanda ta motsa ko ta yamutsa fuska sai Mubeen yace "Sannu, sannu kinji ciwo kike ji ko? insha Allah yanzu zai daina da kinsha magani."

Jinjina ma shi kai kawai Samha ke yi dan sam ba ta da ƙarfin yin magana,ko wace gaba ta jikinta ciwo ta ke ma ta.

Cije baki ta yi tare da dan zamewa kadan za ta kwanta, caraf Mubeen ya rikota tare da kwantar da ita a barin hannunsa na dama ya na jera ma ta sannu.

   Cup cake ya bata amma taki ci sai ma kulle ido da tayi ta na sake lafewa a jikinsa.

Cikin rarraahi da kalamai ma su sanyi Mubeen ya ta da ita tare da bata magani sannan ya sake kwantar da ita.

Shan tea din shima ya yi tare da maganin sannan ya lallaba ya kwantar da Samha shima ya kwanta.

Kallon Samha ya ke cikin martaba ga wani irin shauki da ke fizgarsa ya na tuno moment dinsu na jiya.
Ahankali ya shafa fuskarta tare da fadin "Tabbas kedin hasken alkairi ce a rayuwata, na samu nutsuwar da ban taba samu ba daga gareki, banda bakin da zan gode miki saboda halacinki a gare ni yafi karfin godiya, zan hidimta miki kamar bawan ki zan kula da ke kamar jinjirara zan kula da ke ta yanda ko kuda bazai samu damar rabarki ba bare ya cutar min da ke, Allah ya albarkaci RAYUWAR KI SAMHAD yakika kedin mace ta gari ce wadda kowa ke fatan samu."
Yana fadawa Samha dadadan kalamai a haka barci yai gaba da su makale da juna.








"Hummm kai de bari Mamman ni kaina daga baya ban samu nutsuwa ba musamman yanda na rabu da yarinyar cikin rashin lafiya, kasan daga asibitin da ka kaimu muna dawowa ko gida bamu shiga ba muka tarar da aurunkinta sunzo daukarta nan take aka tafi da ita ko yan gida babu wanda sukai bankwana da shi, kasan yaron tsohon aminina ne na aura ma ta, ai kasan Alhaji Muhammad Bashir karfe ko?."


Wa ta irin zabura Mamman ya yi yana fadi "Kace me? Alhaji Muhammad Bashir karfe fa kace!."

   Kalonsa kawai Abbu ya yi yana murmushi ganin yanda Mamman ya rikice daga fadar sunnan Karfe.

"Haba Alhaji cewa za ka yi yarinya na cikin daula, kaf kasarnnan waye bai san family karfe ba, kasan kuwa irin shaharar da sukai ga tarin dukuya, haba Alhaji kace kana ciki daula ai ka kwantar da hankalinka ka nutsu yarka tana cikin alkairi dumu-dumu damuwa da tagumi ba naka ba ne.


Murmushi kawai Abbu ke yi yana kallon yanda Mamman keta tada jijiyoyin wuya.

Mamman saita kanshi ya yi cikin sigar mutuntaka ya ce " To amma alhaji wani daga dangi kai ko yan uwanta kunje kun duba halin da take ciki kuwa? kasan bai dace ba akai yarinya nesa ace babu mai zuwa yana dubota."

Shiru Abbu ya yi yana jinjina maganar Mamman a ransa dan dama tunanin da ya addabe shi kenan ya rasa yanda zai yi.

  "Ka yi shiru alhaji bakace komai ba."

"To Mamman na rasa abinda zan ce ne shiyasa nai shiru, dan nima wallahi ina son zuwa in duba yarinyar amma ina jin nauyin hakan."

  "To ga shawara manah, mi zai hana ka kira shi Muhammad karfen ka fada masa za ka zo wani  aiki a Abujar, idan kazo za ka shigo ku gaisa."











Mamy tun da Daddy ya korota waje tunaninta ya tsaya cak haka ta tafi dakinta cikin jimamin abinda yai ma ta wanda ya dakula lissafinta. 
Wayarta ta janyo ta lalibo number Maman Nabila, bugu daya Mamman Nabila ta dauka tare da sallama. 

   "Mama akwai matsala gagaruma, gaf muke da rasa komai Mama dan Allah kiyi wani abu akai."

 "Subahanallahi Sarhabila lafiya mike faruwa ne na ji kina wannan maganganun?. "

      "Komai ya faru Mama, gaf muke da rasa komai Muhammad ya dawo hayyacinsa yanzu haka koroni ya yi daga dakinsa ya kulle."

Sosai Maman Nabila ta rikice har ma tafi Mamy rikicewa saboda tsab ar yanda maganar ta daketa, Kallonta kawai Malam Umar ke yi dan tunda ya ji ta ambaci sunan Beela yasan ba wani abin alkairi ba ne.🌹RAYUWAR SAMHAD🌹(Abar tausayi ce😭)

WRITE BY.✍️✍️✍️

MARYAM STAR ⭐⭐

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.