Free chapter · Read without an account

.....

by MARYAM STAR · RAYUWAR SAMHAD

BOOK TWO PAGE 2⃣7⃣



Bayan nakai shekara ashirin cif, na ƙara girma da hankali sai matsin da Anty Zee da Hajiya Adama kemin ya ƙara daɗuwa, domin kuwa yanzu na girma gashi Allah ya wadatani da tsnanin kyawu da surar jiki me ɗaukar hankali, wanda ke ƙara tadawa Anty Zee hankali aduk sanda ta kalleni, yanzu an rage aikena musamman kasuwa acewar Hajiya Adama wai acan ne nike haɗuwa sa samari su na ƙara buɗemin ido, nikam hakan ba ƙaramin daɗi yaimin ba dan dama bason shiga kasuwar nike ba saboda mazan da ke takuramin, kulllum naje sai nasamu wanda zai biyoni da zancen soyayya.



Ana haka wata rana Anty Zee ta ce inzo inrakata unguwa, ban musa ma ta ba tunda banda abinda zanyi alokacin na gama duk ayyukana, kasancewar anyi hutun isilamiya, shiryawa nai cikin koɗaɗɗiyar atamfata wacce ta jeme saboda tsabar wanki, sannan na saka farar hijabina wacce takaimin har ƙasa, nasaka safa da plate ɗin takalmina na fito tsakar gida.

Iske Anty Zee nai ta ci kwalliya sosai kamar me shirin zuwa biki, tayi kyau sosai, cikin nutsuwa muka fice daga gidan muka hau  kwalta muna jiran me adaidaita, mun daɗe atsaye bamu samu ba, zuwa can sai ga wani me mota harya wucemu sai kuma ya dawo dare da tsayawa saitinmu ya buɗe glashin motar fuskarshi ɗauke da murmushi yake tambar inda zamuje bayan mun gaisa, cike da kwarkwasa Anty Zee ta faɗa ma shi inda zamuje.

Tun da muka shiga motar nai tsit ban kuma maganaba dama iya gaisuwa ce kawai ta shiga tsakanina da shi, muna tafiya a hanya ina lura da yanda ya ke kallona ta mirro ita kuma Anty Zee dai wani janshi take da fira kamar damacan sun saba, shikuwa biye ma ta kawai yai amma sam hankalinshi ba akanta yake ba.


Bayan ya saukemu ne ya nemi number Anty zee, bashi tai tare da yi ma shi kodiya muka wuce ranta fari ƙal.

Bayan kwana biyu da haɗuwarmu da wannan matashin ya kira wayar Anty Zee, inda ya nemi yana son yazo gida zasuyi magana me muhinmanci.
Ba bare da ja ba ta amince mishi tare da bashi address, lokacinda ya zo ina makarantar  dare bansan da zuwanshiba, ashe zuwa yai ya sanar da Anty Zee yana so na, aiko ba ƙaramin tashi hankalinta yaiba dan ko rikicewa tai dajin wannan batun nashi.

Ko tsayawa ta gama saurarenshi batai ba ta shiga gida da mugun gudu ta na kuka, direct wajen Hajiya Adama ta nufa cikin tashin hankali ta warware ma ta dukkan abubuwanda ke faruwa, nan Hajiya tai tsalle ta dire tare da shan alwashin koya min hankali akan abinda ni sam bansan da faruwarshi ba, ina kwance a ɗakin da aka ware min ni kaɗai kamar mayya ina tunanin duniya, bansan yanda akai ba kawai se jin saukar suka nai ta ko ina ajikina, cikin firgici na tashi ina kuka tare sa tare da ƙaƙatin tare dukan amma ina Hajiya Adama ta rufe idonta bata ji bata gani dukana kawai take kamar Allah ya aikota, ihun da nike haɗi da magiya sam baisa ta sararaminba sai da ta gaji dan kanta sannan ta kyaleni ta na huci ta jefar da bulalar ta fice ta na ta faman sababi wanda ni sam ba fahimtarta nike ba, jikina yai ruɗu-ruɗu saboda azabar dukan da naci, ko ina yai jajir jini duk ya kwanta a fatata, ranar naci kuka sosai saboda bayan duka Hajiya  bata sararaminba sai da ta haɗa ni da aiki me tarin yawa wanda kafin ingama shi na wahala sosai.

Bayan Hajiya ta rarrashi Anty Zee ta saka ta kira saurayin me suna Abdul ta faɗa ma shi ƙarya da gaskiya akaina, bai ja da nisa ba ya bar zancena ya koma wajen Anty Zee, yanzu kusan kullum se yazo gidanmu fira wajenta, kuma basu tashi yi firar sai da daddare sannan kuma acikin mota suke firar.

Ana haka ne wa ta rana Hajiya ta aikeni siyen magani na fito daga gida kenan na hangi motar Abdul parke daga nesa kaɗan, dayake ta hanyar zanbi ina zuwa wucewa ta wajen tsautsayi ya aikeni na ɗaga kaina na kalli cikin motar daidai lokacin da wa ta mota ta shigo shigo layin ta haske motar Abdul, runtse idona nai cikin rawar jiki na ja ƙafafuwa ina maimaita salati a zuciyata, yayinda tashin hankali ya bayyana akan fuskata domin kuwa tar idona ke maimaita min hannunnAbdul dana gani a saman jikin Anty Zee wacce ta sauke rigarta.


Ina miƙawa Hajiya aiken nai saurin shigewa 
ɗaki ina sakin kukan daya tahomin lokaci guda,
Ina tsaka da kukana sai ga Anty Zee ta faɗo ɗakin cikin tashin hankali, dan ita ta ganni lokacinda na gansu, hakan ya saka ta kasa nutsuwa tai sallama da Abdul ta biyo bayana.

Zazzafan worning ta shata min tare da yimin albishir inde na saki wani yaji wannan zancen bashakka ƙarshen rayuwata yazo dan kasheni za tai kowa ya huta.

Bayan ƴan shekaru, yanzu naɗan samu salama a gidanmu saboda na riga na saba da wahala, aikine kullum se nayishi koda banda lafiya, sannan ina zuwa makarantar isilamiyya dan na gama secondary, yanzu wani lokacin Abbu na zama yai fira tare da ni har unguwa yakanje tare da ni wani lokacin, yanzu na girma sosai sai de banda ƙiba ko kaɗan, farace ni doguwa mai ƙirar jijin manyan mata, inada sassanyan kyau, idanuwana manya ne farare tas masu yalwar gashin gira, bakina ɗan ƙaramin me ɗauke da pink lips, inada diguwar fuska me kyau, ataƙaice duk inda ake neman kyakkyawa to za'aganni wajen dan ni kaina nasan inada kyau, ga wata irin lallausar farar fata wacce Allah ya azurtani da ita, wa ta baiwa da Allah yaimin itace duk wahalar duniyar da nasha, fatata sam bata nuna hakan, ko ciwo naji baya daɗewa tabon ke bacewa ɓat, wannan shine abinda ke ƙarawa Anty Zee tsanata.


Wata safiyar juma'a ina zaune a ɗakina ni kaɗai na rasa abinda kemin daɗi, sam banijin daɗin zuciyata, gashi gabana sai faɗuwa yake akai-akai, sam babu kuzari a jikina dan ko aikina dakyar na gama, ina zaune a ɗaki nike jiyo ƙus-ƙus ɗin Hajiya da Anty Zee, dana nutsu sai naji ashe Anty Zee ce taiwa Abbu laɓe da ta ga yayi babban baƙo sun shige ɗaki su na tattaunawa, ji nayi ta na faɗin.

"Wallahi Allah Mommy da kunnena naji Abbu na faɗin yanzu shi Mubeen ɗin haka ya lallata rayuwarshi sa shaye-shaye, yaro nutsatstse, au ranar naka se naka, Mubeen ɗana ne yafi ƙarfin alfarma awajena, kuma karka manta wannan alƙawarine nai ma shi tun lokacinda aka haifi ita Aishar, tabbas lokacin cika wannan alƙawarin yayi, na yanke hukunci za'a ɗaurawa Samha da Mubeen aure a ranar juma'a me zuwa, Allah ya sa hakan ya zama sanadiyyar shiryuwarshi."


Saurin jan hannun Anty Zee Hajiya Adama tai suka bar wajen jin alamun za'a buɗe ƙofar.

Sosai gabana ke ɗukan tara-tara jin wannan zancen na su Hajiya, sai kuma wa ta zuciyar ta gargaɗeni akan kar in kula maganarsu ba gaskiya bane.

Ban gasgata Abinda ya faru gaskiya bane se sanda sati ya zagayo da kunnuwana naji sanarwar ɗaurin aurena a masallacin unguwarmu, wanda ban gasgata ba sai da aka fara shigowa gida anayiwa Hajiya fatan alkairi, ina cikin wannan tashin hankalin Anty Zee da Fauzy suka shigo ɗakina suka sake tabbatar min da anyimin aure kuma wai ɗan daba gaggararre Abbu ya auramin, sanadiyyar baƙaƙen maganganun da suka yayyaɓamin ya saka zuciyata ta kusa bugawa jinina yahau na faɗi na suma har saida aka kaini asibiti."


CI GABAN LABARI.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.