Free chapter · Read without an account
.....
BOOK TWO PAGE 2⃣9⃣
Bayan Samha, Salma, Sadeek sun tsagaita da kukanne kowa ya nutsu saboda maganar da Alhaji Muhammad ya fara.
"Da farko dai muna miƙa godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya bamu iko da dama ya kuma ara manah rayuwa da lafiya har muka zo wannan rana me cike da albarka, bayan jin cikakken rabalin Aishatu matar Mubeen da mu dukkanmu akan kunnenmu akai komai, yanzu ina cikin farin ciki sosai da haɗin kan da kuka samu a tsakaninku."
Sai yai shiru tare da kallonAbbu da ya nutsu yana saurarenshi sannan ya ce.
"Malam Abdullahi ina so da kanka sanar da su halin da ake ciki, sannan ka faɗa masu abin alkairin da ya samume na gano inda ɗanmu ya ke, wanda ya mace shekaru masu yawa."
Jinjina kai Abbu yai tare da gyara zama ya fara rantaɓo jawabi.
"To Alhamdulillah bayan tsayin shekaru da muka kwashe ni da aminina muna cikin wani hali na kaidin mata, da kuma wasu rikitattun al,amurra da ke zagaye da mu wanda mu kanmu bamu sansu ba, to Alhamdulillahi yanzu komi ya zo ƙarshe, yanzu Allah ya haska mamu abubuwanda ke lulluɓe cikin duhu wanda sam bamu san da wanzuwarsu ba, kamar yanda Aminina wato Daddynku ya faɗi, abu biyu ne muke tafe da shi, na farko al'amarine da muka jima muna jiran ranar zuwanshi, na biyu kuma al'amarine me rikitarwa wanda mu kanmu bamu bamusan da wanzuwarshi ba sai da magabatanmu suka haska mamu hanya sannan muka gane lulluɓin da akai cikin duhu.
Abu na farko shine, mungamo inda Abubakat Sadeek ya ke rayuwa, wanda ya kasance ɗana na farko a duniya kuma yayaga ita Aiahatu wato Samha."
Wa ta irin zabura Samha tai jin zancen Abbu, neman tashi take daga zaunen da ta ke amma Mubeen ya ƙi bata damar tashi, dan riƙeta yai sosai tare da faɗa ma ta magana ƙasa-ƙasa ta yanda babu wanda zai ji abinda suke tattaunawa.
Ci gaba da bayani Abbu yai.
"Abu na biyu kuma shine, mungano wani shuɗaɗɗen al'amari me razanarwa wanda ya girgizamu matuƙa, kasancewar babu wanda acikinmu ya taɓa tunanin hakan zai iya faruwa, to Alhamdulillahi da Allah ya bayyana mamu wannan cakuɗaɗɗen lamarin, ba komi bane wannan lamarin face al'amarin mutuwar matar Aminina wato Daddynku Alhaji Muhammad, mungano cewa akwai lauje cikin naɗi akan zancen mutuwar ta marigayiya Aishatu wanda aka ɓoye lamarin ba tare da sanin cewar Ubangiji zai iya bankaɗoshi wa ta rana ba, kamar yanda kukaji labari akan cewa wajen haihuwar wannan yarinyar Salma Aisha ta rasa ratuwarta wannan gaskiya ne, wajen haihuwa Allah ya karɓi rayuwarta amma harda sa hannun wasu mugan mutane wanda bamusan abinda ta tare masu ba, kasancewar kowa yasan Marigayiya Aishatu kamilalliyar mace ce, amma duk da irin kirkinta aka samu wasu marrasa iymani suka san yanda sukai wajen ganin tabar masu duniyar gaba ɗaya.
Bazan ja zancen da nisa ba tunda bamuda wasataccen lokaci yanzu haka baƙi nakan hanyar zuwa, ba kowa bane aka zargi wajen kashe Marigayiya Aishatu face kishirya abokiyar zamanta kuma yaya ga Aminiyarta wato Salhabila Mamynku, itace tai sanadiyyar barin Aishatu duniya."
Sak Salma da Sadeek sukai, hawayen da ke gudana a fuskarsu ya tsaya cak, kwanyarsu ta tafi hutun wucin gadi, Mubeen da Samha kuwa kallon juna sukai tare da girgizawa juna kai sannan kuka ya kufce musu a tare.
Daddy ma hawaye ya ke sharewa a fakaice yayinda Abbu ke jimanta girman lamarin.
Kusan mintuna goma aka ɗauka kowa na jimanta lamarin kafin daga bidani Abbu ya ɗora musu da nasiha me kashe jiki,
Tofah masu karatu, anya kuna gano ƙurar da nike hangowa a cikin labarinan, shin wai dama Saddek Yayan Samha ya na raye duk tsayin shekarunan amma shine ya ɓoye kanshi ba'asan inda yake ba?😳, Hummm mamy kenan duk ki gama tseren gudun ki dawo ƙarshenki ya zo dama hausawa sunce rana dubu ta ɓarawo rana daya tak tame kaya.
KU BIYONI DAN JIN YANDA ZA TA KAYA.
TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKAIRI 🙏🙏🙏.