Free chapter · Read without an account
Chapter 13
Ya jima yana kallon fuskarta me cike da rauni, ƙuruciya da rashin mafita goshinsa yana shafar nata, a hankali ya janye goshin nasa sai kuma ya sake ɗorawa ya sumbaci goshinta da kulawa kafin ya gyara mata kwanciya ya miƙe tare da fita daga cikin shagon nasa, a dakalin gidansu Ana ya zauna ya yi shiru yana harɗe hannu a ƙirji.
***
A karo na biyu ta sake ɗago kanta daga kan t.v da take kallo, ta juya kaɗan ta kalle shi sai taga ya harɗe ƙafarsa ɗaya kan ɗaya hannunsa ɗaya riƙe da hot coffee yana sha. "Liman ko baka ji me na ce maka bane?" Bai ɗago kai ba, sai ajjiye cup ɗin da ya yi a center table ya ce "Me kika ce Umaimah?"
Wani irin kallo ta watsa masa me cike da gargaɗi kafin ta mai da hankalinta gabaɗaya gare shi ta ce "Ina magana akan yarinyar da zaka aura wacce Alhaji Sadi suka je kai maka kuɗin auren, auren da tunda Baffa yaƙi zuwa kai kuɗin jikina ya bani akwai matsala a tattare dashi bawai baki na yi maka ba Allah Ya tsare" ta ƙarasa maganar tana sauya yanayin fuskarta. Wanda aka kira da Liman kallon ta kawai yake yi, ya ji me ta ce kuma zai iya maimaita kalaman da Umaimah ta ce, amma ko za'a saka masa wuƙa ba zai ce ga abin da take son nuna masa ba. Sai ya zaɓi yin shiru akan bata amsa. "Ya zama last time da zan sake maimaita kaina akan batun nan Liman"
Ya numfashi ya ce
"Me kika ce ne?"
Ta dube shi ta ce
"Ina magana akan yarinyar ne" Da rashin fahimta ya ce
"Who?"
"Why are you answering my question with a question ne Liman? Yarinyar da zaka aura wacce aka kai sadakinka gidansu, ina buƙatar ka kawo mini ita na ganta da kaina" da wani irin yanayin na rashin jin daɗi Liman ke kallon Hajiya Umaimah yafi seconds sha biyar kafin ya iya cewa "Umaimah ina jin I already told you that the girl is visually impaired, so I can’t bring her to Baffas Estate by myself.” da mamaki tace
"She's visually impaired? Mugunta zan mata ko naman jikinta zan dinga yanka ina ci da zaka wani sauya mood kana ce mini wani visually impaired, au daman da gaske kake makauniyya zaka aura Liman? Kana da cikakken hankali kowa? Me ya sa kai ɗin nan abin da ka yi ra'ayi kawai kake mana a cikin gidan nan? Haka kaga Mu'allim yana yi ne?"
Liman ya miƙe tsaye fuska a kame, Hajiya Umaimah ta ce "Zauna ban gama magana ba" daga tsayen ya kalle ta sai ya yi kamar ba zai zauna ba a hankali kuma ya yi baya tare da sake zama akan kujerar daya tashi akai ya fara kallon wani direction daban. "Zan sake magana, ina fatan ta zama ta ƙarshe ina son ka kawo mini ƴarinyar nan gidan nan, domin ba zaka auri wacce zan zo ina kasa nuna ta a dangi ba. Ban ma dai gama gamsuwa da uban nata ba, ƴar waye? Matsayin mahaifinta, mene matsayin karatunta? Ƙasashe nawa ta je? Ta je Saudia? Musaɓaka nawa ta ci, ta Jiha ko ta ƙasa? Sau nawa tana sauke Alkur'ani?"
Ya yi jim a daƙile ya ce
"Ba ko ɗaya"
Murmushi Azizah ta yi ta ce "Stop beating around the bush Liman, ka fito ka ce ƴar talakawa kawai zaka aura, duk kewaye-kewayen naka da gujewa ƴaƴan ƴan'uwa sai ka ƙare akan ƴar talakawa haba Liman?" Tunda ta fara magana yake binta da wani irin masifaffan kallo yana sauke numfashi akai-akai idanunsa sukai jajur ya dunƙule hannunsa dake masa rawa. Hajiya Umaimah ta ce "Ga dukkan alamu Azizah, ki yi shiru kar ya kawo mana duka naga yana rawar ɗari" Azizah ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya
"Ko burkutu yake sha ai bai isa ya taɓa ni ba balle ke Umaimah da kika haife shi ko?" A hankali ya ce
"Bata da iyaye a haka kuma nake son ta"
"Kutumar uba, marainiyya zaka aura?"
Daidai nan wanda ya sako ƙafarsa cikin parlour ya tsaya cak kamar wanda aka yi wa umarnin hakan, ƙafar ta daɗe a yadda ya ɗage ta cikin wani kyakkyawan farin takalmi na saƙi me ɗauke da gashin ɗawisu daya kwanta, sannu a hankali kuma ya shiga yin baya da ƙafar hakan ya bawa wanda yake tare dashi tabbacin ya fasa shiga gidan a yanzu. Ya yi tsaye akan ƙafafuwansa hannunsa ɗaya ya juya shi zuwa bayansa ɗayan kuma ya ɗora a saman goshinsa ya saka yatsu biyu yana murza tsakiyar goshinsa idanunsa a lumshe suke, kamar yadda zara-zaran gashin idanun suka bi fatar wajan suka kwanta, iya idanun daman kawai ake iya gani a fuskarsa da zarar ya saka glasses suma ya yi wa jama'a rowar ganinsu, ilahirin gargasar jikinsa sai data mimmiƙe wani irin sanyi ya shiga ratsa farar fatar jikin nasa, yaja numfashi da saukewa sau babu adadi. Babban yatsarsa na ƙafa sai rawa yake yi shi kaɗai hakan ya faru ne a dalilin zagin da Azizah ta yi a daidai sanda Sayyadi Baffa yake sako kan shi cikin parlourn.
Fuskarsa ta rikiɗe ta yi jajur laɓɓansa yana wani irin rawa da ɓari, a cikin zuciyarsa ya furta “A’udhu billahi minash-shaytanir-rajim” yana kame jikinsa da kyau cike da kulawa ya ɗora da;
“Allahumma ighfir li wa lahum wahdina sawaa’as-sabeel” ya maimaita a zuciya.
Ya ɗauki a ƙalla minti guda tsaye yana addu'ar nemawa Azizah gafara wajan Ubangiji da kuma tsari da neman afuwa wajan Allah akan jin zagin da ya yi. Bai san wacece ta yi zagin ba, bai ɗauki murya ba kamar yadda bai damu da sani ba, ba murya kowa ya haddace ba, yadda jikinsa ke rawa ya sake tabbatarwa Mu'allim akwai matsala. Juyawa ya yi yabar sashin gabaɗaya baya mistake a sauke ƙafa sai ya cire ɗaya yake ɗora ɗaya saboda nutsuwa.
Ta ƙofar baya yabi har zuwa babban sashin da yake mallakin Sayyadi Baffa, a nan ƙofa Mu'allim ya ja ya tsaya yana cewa "Allah ya huci zuciyar Baffa, ya ƙarawa Baffa lafiya" Wannan karan ko zarafin jinjina kai bai samu ba, ya buɗe ƙofa da yatsu biyu, sai da ya yi addu'ar shiga ɗaki kafin ya saka ƙafarsa da Bisimillah ya shiga zuwa ciki.
Mu'allim ya juya kai tsaye cikin gidan ya shiga idanunsa ya sauka akan Azizah dake zaune har yanzu ita da Hajiya Umaimah saboda Liman ya fita.
"Ukhty Azizah me ya sa kike son yi mana zagi a gidan nan ne? Wa kika ji yana yi?"
Ta ce "Mu'allim ban fa san na yi ba?" Al'ameen ya watsa mata fararan idanunsa
"Ko?" Ya tambaya cike da takaici. "To a kunnen Baffa kikai, kuma ya ce ko wacece ya bata minti ashirin ta bar gidan nan, yana da tabbacin ba zuri'ar Hafiz Hafiz Baffa ce da aikata wannan saɓon ba" wani irin sandarewa Azizah ta yi, sunan Baffa ya saka zuciyarta bugawa da matsanancin farinciki har ta kasa ɓoyewa ta faɗaɗa murmushinta tare da lumshe ido ta buɗe. "Da gaske Baffa ya dawo? Yana cikin gidan nan Please Mu'allim ka nema mini iso wajansa, don Allah ina kamon ƙafa da kai"
"Allahumma yahdiki. Is like kamar ba ki fahimci me nake cewa ba ko Ukhty Azizah?"
"No, na ji. Na san bai sanni ba, ka rufa mini asiri idan ya tambaya ka ce baƙuwa ce kuma ta tafi, sai ka nema mini izinin ganin nasa Please"
Mu'allim ya dinga kallon ta ya rasa abin da zai ce mata, yaushe ma zai sake ganin Baffa balle ya nema mata izini a wajansa, shi ɗin wa ma? a hankali ya juya ya nufi part ɗin Mamy yana jin gajiya na saukar masa a jikinsa saboda driving da ya yi daga airport zuwa gida, ba kowa Baffa yake son ya dinga driving jikinsa ba, baya son damuwa, rawar kai a komai, yana buƙatar mutum me nutsuwa da kamala da kuma taka tsantsan, baya son stress ko hayaniyar da ta saka mutum ya yi driving kamar bashi da nutsuwar sanin me yake, hakan yana saukar masa da ciwon kai me tsanani, ciwon kan da baya buƙatar shi ko kaɗan, wata baiwa ce ko kuma haɗuwar jinin da ya yi yawa tsakaninsa da yaransa, muddin ya kwanta ciwo sai Nadiyaah da Diyanah Sayyadi Baffa sun kwanta, shi ya sa yake kulawa da jikinsa da duk abin da zai shafi lafiyarsa ɗin baya wasa dashi. A ƙarƙashin wannan dalilin ya ware mutane biyu da ya yi na'am da nutsuwarsu, duk da a hakan ma cike yake da yi musu gargaɗi da wa'azin babu kyau wasa da kowanne irin rai da Ubangiji ya wanzar a duniya. Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa wato Mu'alim, sai kuma wani babban yaron shi a ɓangaren aikin Hisba me suna Ansar Khamal Khashim. A wannan dawowar ma tun kafin su taso Ansar ya kira Mu'alim ya sanar masa, yana airport ɗin jirgin nasu ya sauka, bashi da tabbacin ko sun yi nasara akan Da'awar da suka je yi bashi kuma da ƙwarin gwiwar tambayar Baffa sai Ansar.
Ansar ɗin kuma tun a airport suka rabu dashi. Sanda ya shiga part ɗin Mamy bayan ya yi sallama sai daya jira izinin shiga daga bakin Hidaya bisa umarnin Mamyn da kanta. A nutse ya sako kan shi cikin parlourn nata da yake ta ƙamshi, bakinsa ɗauke da sallama. Hidaya ce kawai zaune hannunta da riƙe da Mi'ata Hadith tana karantawa. Ya nemi waje ya zauna. Cikin sauri Hidaya tace
"Ahky Mu'alim yaushe zaka kai ni shan Ice cream ɗin, ka yi mini alƙawari fa, shi alƙawari kaya ne cika shi wajibi ne"
Ya dubi ƙanwarsa, wacce take yanayi da late Hafizz Hafizz Baffa, cikin kulawa ya ce "Zan kai ki Hidaya in sha Allah, but not now"
"Than, when?"
Sai ya yi ƙasa da muryarsa domin gani yake a hakan Baffa yana takura da maganar da suke yi. "Baffa is back, da zarar ya ji labarin ina ɗaukan ki zuwa wajan shan Ice cream mun kaɗe a gidan nan, kinga ke little sis ce autar gidan nan, kuma amanar Hafizz Hafizz Baffa, kenan Baffa ba zai taɓa yi miki faɗa ba" Hidaya ta yi shiru tana kallon Mu'allim cikin rashin fahimta ta ce "Baffa baya faɗa ai Akhy"
"And who told you that? Bakya nan ya kwakkwaɗawa Liman mari, wata ƙara da ihu da ya yi wa Liman sai da kowa ya firgita a gidan, don Allah Hida mu ajjiye shan Ice cream a gefe zan siyi na kawo miki, ni aure zan lallaɓa Baffa ya nema mini please?"
Ta washe fararan haƙoranta masu kyau ta ce "Idan baka kawo mini ba, I'll go and tell Baffa everything kana zuwa wajan Ice cream"
Mu'allim ya dafe goshinsa yana murzawa ya ce "Ya rabb, ke ba'a sirri dake ne Hidaya?"
"Ka rasa dawa zaka yi sirri sai da Hidaya Hafiz Hafiz Baffa? Baka san halinsu ɗaya da Nadiyaah Sayyadi Baffa ba? Ai Baffa yana jin komai dake faruwa a gidan nan ta wajan Hidaya da Nadiyaah da Diynaah tas ma kuwa"
"Sannu da fitowa Mamy" Mu'allim yace yana bata girma wajan miƙewa, ta nemi waje ta zauna idanunta akan Mu'allim, tana sanye da baƙar Jallabiya me kyau ta yi rolling kanta da mayafi a nutse ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannunta riƙe da counter da azkar. "Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa" Mu'allim ya ɗaga kai ya kalli Mamy bayan ya amsa cike da kulawa da rashin sakin fuska ta ce "Zaryar me kake wajan nema na haka?" Ya yi ƙasa da kan shi na wani lokaci.
Kan shi a ƙasa ya ce
"Akan yarinyar nan ne"
"Yarinya?" Ta maimaita a fili ta ɗora da "Wacce yarinya? Wani abu ne ya faru?"
"Mamy akan Iftihal yarinyar da aka kawowa su Nadiyaah da Diynaah aiki, da gaske ina son yarinyar nan sosai a cikin zuciyata tun kallon farko da na yi mata na yaba da hankali da nutsuwar da take dashi. Sunanta Iftihal na gaskiya Aysha, a unguwar Kankarofi suke, na sake komawa na yi bincike akan ta sosai" Ta ɗan gyara zama kafin ta ce "Ina fata binciken da ka yi ya yi daidai da tsarin matan da Baffa ya ɗora ku akai wanda suka dace da zama surukan Baffas family. Ba ƴar ƙananun mutane bace"
"E, gaskiya su talakawa ne sosai Mamy"
"Shine me? Kuɗi da talauci mutum ke yin su ko Ubangiji? Mutumci da tarbiyyar gidansu nake magana akai"
Ya yi jim, domin binciken da ya yi ba mai daɗi bane akan gidansu, binciken da shima sai da ya hana shi bacci, da ace yarinyar bata tsaya masa ba, tabbas zai iya haƙura da Iftihal amma me? Ko idanu ya rufe ita yake kallo, idanunta, fuskarta, komai nata sune suke masa gizau a cikin idanunsa. Da wannan muryar tata me sanyi da kamala.
Mamy ta ce "Uhm? Ina jinka?"
Ya girgiza kai, "Mamy ban saba ƙarya ba kin sanni akan gaskiyata ko za ta yi ajalina. Da ina da iko da fara yi miki ƙarya to zan fara a yau ne, a dalilin Iftihal. Mutanen unguwar sun ce mahafinta yana shan giya, yana yin caca, kawai dai ba mutumin ƙwarai bane, mahaifiyarta tana da ilimi sosai ta taɓa koyarwa a makarantar gwamnati kafin sabuwar gwamnati tazo ta sauya ma'aikata. Ta basu tarbiyya sosai, komai na rayuwarsu ita ce. Suna da ƙanin uba sunansa Bala amma ɗan daudu ne.....," tun kafin ya ƙarasa ta ɗaga masa hannunta tana miƙewa tsaye cikin rawar ɗari da kakkarwar jiki ta ce
"Auzubillahi! Ka bincika komai kaga komai, amma baka gamsu ba sai ka faɗa mini? Tun a can unguwar tasu ya kamata ka ajjiye soyayyarta. Irin wannan jinin da tsatson zaka kawo mana cikin zuri'ar Baffas? Al'ameen ka haukace ne me yake going ta cikin kanka daka kasa controlling zuciyarka"
Sai ta yi baya kaɗan tana salati. Ba tare data juya ta kalle shi ba ta ce "Karka kuskura Baffa ya ji wannan maganar hukuncin da zai maka na san ba zaka iya ɗauka ba. Zai nemi wata can cikin matan da suka amshi musulunci ya ɗaura maka aure da ita ne for sure" jikin Al'ameen ya dinga rawa ya zamo daga kan kujerar ya ɗora ƙafafuwansa a ƙasa, idanunsa sukai jajur duk da acn dake cikin parlorn zufa ce ke wanke masa fuska.
"Mamy don Allah.....,"
"Kar ka roƙe ni Mu'allim, tashi ka fita" Ya ce "Ki yi haƙuri. Amma Mamy tarbiyya daman ta iyaye mata ce, yau da mahaifiyarta ke aikata abin da mahafin nata ke yi wallahi ba zan sake ɗaga maganar ba" wani uban kallo ta yi masa, a karan kanta zata iya barin Mu'allim ya auri yarinyar itama ta yi mata, amma hakan ya saɓa dokar ahhalin Baffa. Zai ja musu ƙasƙanci ne a idanun jama'a. Wannan maganar ma ba zata bari Hajiya Umaimah ta ji ba. Ta juya ta kalli Hidaya ta ce "Da kika je kitchen kinga baƙuwar me aikin nan tazo yau ɗin nan?"
"A'a Mamy, bata zo ba"
"Good, ta bar aikin daga yau ɗin" ta nemi waje ta zauna fuska babu walwala "Ko auren za ka yi ma ai ka haƙura a fara na Baffa, tunda na ji Malami ya ce yau za'a saka rana"
Hidaya sai kallon Mamy take yi sai ta ce "Mamy zani wajan Anty Diynaah ta yi mini ƙarin karatu" ta jinjina kai ta fice. Al'ameen da ƙyar ya iya jan jikinsa ya fice zuwa nasu part ɗin, ɓangarensa da yake kusa dana Liman ya shiga babban ɓangare ne me kyau yana shiga ya zube a ƙasa yana riƙe kai.
***
Ruwan daya sauka akan fuskarta shine ya sakata sauke ajjiyar zuciya me ƙarfi, ta ɗan juya kanta kaɗan da ya yi mata nauyi, sannu a hankali ta miƙa hannunta ta ɗora saman ƙirjinta daidai saitin zuciyarta da take bugawa da ƙarfin gaske. Laɓɓanta a bushe ga wani irin ciwo da kan yake mata bata iya ko buɗe ido balle taga mutanen da suke kanta. Ta ware bakinta da take jin ya bushe mata sosai tace
"Yau dai da gaske bani da lafiya mahaɗita, ban san me yake mini ciwo ba, amma ko ma mene Alhamd gaki a kusa dani, na san ciwon da kan shi zai ji kunyar kamani akan idanunki" ta yi shiru sai ta miƙa hannunta.
"Ki ɗora ni a cinyarki mahaɗita, ki rungume ni a jikinki ina jikin kamar Innti ce ina son ki danne mini ƙirjina ki hana zuciyata fitowa"
Jummai ta yi wa Iftihal ƙuri da idanunta, yarinyar ta yi fari fat saɓanin jiya, ga jini sai zuba yake yi a jikinta tunda Baita ya yi mata aika aika. Jummai ta juya kaɗan taga Baita shimfiɗe a saman gadonsa ya ɗora hannunsa a saman cikinsa sai bacci yake yi yana sakin munshari. Hannu ta saka ta maka masa dukan daya saka shi buɗe ido da miƙewa tsaye, ganin Jummai sai ya yi siririn tsaki ya ce "Uwar Kasko ya kai ne?"
"Ya akai kake tambayata? Sakko ka kalli ɓarnar da ka yi wa yarinyar nan Baita"
Alhaji Baita ya kalli Jummai sai ya juya ya kalli inda Iftihal take kwance, ya ƙurawa ƙirjinta idanu ganin da ƙyar take iya jan numfashi da saukewa. "Jummai ke sanda na amshi budurcinki ya kike a lokacin? There's nothing serious, pain ne kawai a bata magani" Jummai ta girgiza kai ya ce "Wannan pain ɗin bana iya budurci bane, hadda na zuciya. Ka faɗa mini ka yi aiki a kanta ne?" Sai ya jinjina kai na wani lokaci.
"E, na yi mana. Kalli can kiga Jummai" Juyawa ta yi sai taga sabbin daloli bandir bandir, kamar kuma bayan su akwai saura.
"Au har kuɗin sun samu shine babu labari? Daman ai saboda aikin nake tausayin yarinyar idan kuma ka yi ai shar dani" Baita ya watsa mata wani lalataccen kallo ya ce "Macuciyya uwar Kasko da Marka. Ki ɗauki yarinyar nan ki mata wanka yanzu zan dawo domin har yanzu a sama nake jin kaina"
"Kasan aiki kuɗi nake, bari na yi mata yanzu na dawo mu tsadance, akwai wasu magungunan ma"ya ce "ki haɗu mini dasu". Fita waje ta yi, shi kuma ya yi shirim yana danna waya, wata number ya kira ana ɗagawa ya ce "Ranka ya daɗe, Allah Ya taimake ka. Aiki ya kammalu a ɗakin da na ce ka ware, yanzu kana shiga zaka ga zakara me abun mamaki" shiru ya yi alamar saurare ya ce
"Ka bada Biliyan goma ya wadatar ai kai ne, dole mu tsaya maka a komai, idan aka kafa ai damu ake komai. Thank you Sir na gode"
Ya kashe kiran yana sakin murmushi.
Jummai ta dawo tana kallon Iftihal dake cikin jini, yarinyar sai surutai take ita kaɗai tana cewa Ana ta rungumeta, ji take yi kamar ana fusgar naman jikinta, ji take yi wata wuta na rura kanta a fatar jikinta, ƙoƙarin buɗe baki take yi wajan yi wa Ana bayanin irin ciwon da take ji, amma ta kasa. Jummai ta tattare hannu ta ɗago Iftihal sama wani gigitaccen ihu Iftihal ta saki tana zabura jini na sake ɓalle mata ta cakume Jummai tana kafa mata haƙori a hannu saboda wani irin raɗaɗi da take ji a ƙasanta. Jikinta ya ɗauki zafi sosai kamar gaushin wuta. Ta shige banɗaki da ita a cikin wani ƙaton ruwan zafi ta saka Iftihal, daga nan kuma bata sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi da wata sabuwar azabar data ninka ta baya. Ɗis haka idanunta ya buɗe ya kumbura sosai kamar zai faɗo, Baita ta gani a kanta yana yi mata abin da ya yi jiya, ta yi masa ƙuri da idanunta, deep down na zuciyarta sunan Allah kawai take kira jikinta ya saki zuciyarta ta tsaya, daga nan numfashinta ya ɗauke bata sake sanin inda kanta yake ba saboda tashin hankali.
Yadda azaba ta sumar da ita, haka wata azabar ta sake farkar da ita. Ɗakin shiru, ba iya ɗakin ba, kusan duka gidanne shiru, Ana take son gani, Anarta take buƙatar kwanciya a jikinta, ta san dole raɗaɗin da take ji a zuciyarta zai ragu, ta shiga kiran sunan Allah guda ɗari babu ɗaya, cikin hukuncin Allah ta samu zarafin yunƙura wa ta miƙe zaune, ta ɗauki hijabin data gani a gefe ta saka, ya saukar mata har ƙasa jikinta ko wando babu, ta shiga daddafawa ta miƙe, taga kuɗi da yawa ta saka hannu ta ɗauki dubu ɗaya, da taimakon Ubangiji ta fito tsakar gidan, tas kamar an share, har zata fice sai taji wata ƙara da ɗan ihu daga gefen ɗakin da take tsaye, ɗaki da akaf mutanen gidan har matan Baita hatta Jummai babu wanda ya taɓa shiga, kodayaushe a rufe yake, yanzu bata san mene ya saka ya zama a buɗe ba. Taja ƙafafuwanta a hankali ta nufi ɗaki ta buɗe ta shiga, sandarewa ta yi kanta ya sara gabanta ya yi mummunan faɗuwa, wata ƙaramar yarinya ta gani tsaye cur an kafeta, tana kyautata zaton Anisa da Baita ya bata labari ce. "Anisa?" Iftihal ta kira sunanta, madadin Anisa ta amsa sai ta shiga ambaliyar kuɗi ta cikin bakinta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Duk wani kira da Iftihal ta yi wa Anisa kuɗi ke zuba, cikin ƙaramin lokaci kuɗi ya taru sosai. Ta shiga ƙarewa ɗakin kallo sosai, da sauri ta juya ta fita jiri na kwasarta haka ta samu zarafin bin wani lungu ta fice daga unguwar. Ina zata je? Ba zata iya komawa gida ba a wannan halin da take ciki ba, tana buƙatar ganin Ana akwai abin da take son faɗa mata akan Alhaji Baita, amma gidan a yanzu ya haramta da ita. Ta tsayar da me napep da ƙyar ta shiga ta ce masa "Mai taɓa sule, Baffas estate zai kaita, please ka kaini har bakin gate ɗin Baba driver ka ji?"
"In sha Allah yarinya" yace yana jan napep ɗin zuwa kan titi hankali kwance. Iftihal taja jikinta kaɗan ta kwanta jikin kujerar napep
***
Yana zaune a saman dakalin yana danna wayarsa ya ji motsi kusa dashi, a hankali ya ɗaga kan shi zuwa gare ta, ya watsa mata idanunsa masu laushi, sai yanzu take farkawa. "Anji daɗin katifata irin bacci haka"
Ta ɗan dube shi kamar za ta yi magana kuma sai ta yi shiru, idanunta ya yi wani irin jirkicewa fuskarta a haɗe babu walwala da wata sanyin murya ta ce "Abbaa yazo?"
Haysaam ya girgizar kai ya ce "Jaheed dai"
"Abbaa bai zo nema na ba?"
"Sure, ai kamar baya nan fa"
Ana ta juya manyan idanunta wanda sannu a hankali suke sake rinewa, ta ɗaga hannunta wajan dafe ƙirjinta ya ce "Ya akai? Ciwo yake miki ƙirjin?" Ta yi tsaida idanunta akan Yaa Sam bata kuma sake masa magana ba ta shige cikin gidansu, sallama ta yi ta shiga Jaheed dake ta aikin kuka ya tusa Jadid dake cinyarsa yana suma ya amsa mata. Da wani irin rawar jiki idanunta na firfitowa ts durƙushe ta riƙo hannun Yas Jadid ta ce "Masoyi, don Allah ka tashi haka nan, ka daina wannan ciwon, ina jin fiye da abin da kake ji, idan na tuna kuna kusa dani sai na ji duk wani ciwona ya yafi. Haba nawan"
Jaheed ya share hawayensa ya ce "Masoyiyar jeki gidan Emama ki kira Innti kar Jadid ya mutu bata nan, nima mutuwa zan yi idan ɗan'uwana baya raye a duniya wallahi"
"A'a......." Ta shiga girgiza kai, gabaɗaya Ana bata san me take ji a ranta ba, tana jin ciwo tabbas, tana jin raɗaɗi tabbas, idan taga sunan Daada a tafin hannunta ji take kamar ta cire hannun ta yar, babu wani abu data tsana a duniya fiye da Daada da kuma hannunta, ta ɗauki alƙawarin goge wannan sunan ta kowacce hanya.
"Abbaa fa?"
Jaheed ya ce "Ban san ina yake ba" Bata sake magana ba, ta miƙe tare da yin waje bata ganin ko gabanta, kamar wacce ta yi wani mugun abu duk inda ta shige sai taga ana kallon ta, a haka ta isa gidan Emama tana shiga ta same su suna cin shinkafa da miya da nama ga lemo a gefe.
Daga tsayen ta ce "Sannu Emama, Innti fa?"
Liya ta ce "Ke don uwarki a haka uwarki ta koya miki yadda ake gaida na gaba dama?"
Tana saukewa Ana ta ce "Ke don uwarki a haka uwarki ta koya miki yadda ake yi wa mutum gyara dama?" Liya ta juya ta kalli Hanna da wani irin mamaki ta ce
"Ni yarinyar nan take zagi da mayar wa da magana Hanna? Ni yaushe aka haifi Ana?"
Hanna ta ce "Ki bar shegiya da idanu irin na Aljanu, mugun duka za mu yi mata wallahi"
Ana ta juya sosai sai ta saki dariya ta ce "A haba? Ƙarya kike wallahi Hanna, sai dai mu daku kuma kar ki yi kuskuren taɓa Ana, don wallahi ko wannan bugaggen yayan naku a yanzu ya ce zai taɓa ni sai ya san ni ƴar wahala ce, sai ya san ni cikakkiyar ƴar halak ce gaba da baya. Idan kina ganin ƙarya ne bisimillah try me za ki gani a fayyace" Liya ta miƙe tsaye tana yin ɗamara, cikin azama Ana ta cire hijabin jikinta ta cire ɗankwali ta yi ɗamara, gashinta da Babban yaya ya yi mata gida biyu dasu suka sauka har baya, wasu kwantattun suma ne daga gaban goshinta masu ɗaukan idanu, gefe da gefen fuskarta sumar ce ta kwanta gwanin sha'awa. "Ƙashi ɗaya ne dani, idan kun fasa baku haifo cikin Emama ba dukanku"
Kanta suka yo, Hanna ta shaƙe wuyan Ana, Liya kuma ta shiga jan gashin kan Ana. Idanun yarinyar ya yi jajur jijiyoyin kanta suka firfito waje, wani ihu da kururuwa Ana ta yi saboda azama ta kai wa nonon Hanna cafka ta matse, azaba ta saka Hanna sakin wuyan Ana, tana sakinta Ana ta juya ta buga Liya da ƙasa da wani irin ƙarfi daya zo mata, idanunta rufe ta shiga dukan Liya da naushi ta fasa mata baki. Hanna ta ɗakko taɓarya zata makawa Ana a kanta ta ji an kwarfeta ta baya, ta yunƙura zata miƙe ta sake jin an kwarfeta ta zube a wajan wanwar a ƙasa.
"Innalillahi, Muraad uban me ya kawo ka cikin gidana? Kashe mini ƴa za ka yi?"
Babban yaya bai ko kalle ta ba, ya ciri wayar caja daya gani a tsakar gidan ya shiga zararawa Hanna tana ihu da birigma ya farfasa mata jikinta, ganin ta yi laushi ya kalli Ana yaga har yanzu tana kan Liya hannu ɗaya ya saka cak ya ɗauke Ana, ta ɗauka Hanna ce da ihu ta juya zata dake ta ya yi saurin riƙo hannunta. "Abbaa....," ta ce da rawar murya.
Rungumeta ya yi sosai yana jin tana sauke ajjiyar zuciya, ya ɗauki ɗan kwalin ya saka mata ya zura mata hijab, idanunsa zube cikin ƙwayar tata idanun. "Abbaaa...
"Ina ka je na dinga nemanka..,"
"Shhhh" ya ce yana ɗora yatsarsa a bakinta alamar ta yi shiru yana ta shafa kanta.
Emama ta ce "Shegu haihuwar asara, uwar taku tana can wajan police sun garƙame shegiya a can" dam! Zuciyar Ana data Yaya ta buga lokaci guda, cikin sauri ya riƙe hannunta suka fice daga cikin gidan Emama.
***
BIYA.
Shatu na gaba Innar Ramu na biye da ita, ta riƙo Ramu a hannunta a haka suke tafiya, har suka shiga cikin dajin sosai kafin suka isa inda bukkar take. Innar Ramu ta ce "Shatu kin tabbatar me bada magani ce? Yama sunanta kika ce mini jiya da yammaci?" Shatu ta murmusa sosai ta ce
"Bokayan karaba sunanta"
Ta ƙarasa jikin bukkar a hankali ta ce "Muna gaisuwa zuwa ga karaba, muna muki jinjina yake bokanyan rugar Biya da kanta gamu"
Daga cikin bukkar Batty ta kumbura murya ta ce "lalle, ga Ramu da Innarta, ga Shatu ƴar rakiya, ga ciwo nan da mutuwa suna binki Ramu, ga lahira nan dab dake Ramu"
Ramu ta ƙanƙame Innarta tace "Inna kin ji ko mutuwa zan yi, daman na faɗa miki Batty ta ce bani da lafiya kin ƙi yadda dani gashi yanzu bokanya karaba ta faɗa sai ki yarda"
"Yanzu Bokanya mene abin yi?" Batty ta maƙale murya
"Kin san ciwon Taifot? Shine yake damun Ramu hanjinta ya fara taɓowa yana fashewa kuma shikenan. A samu tafashasshen gayen zogale ko neem (dogon yaro) ta dinga shan ruwan akai akai sai a dinga yi mata surace, in sha Allah zata samu waraka magani sadidan daga wajan Bokayan karaba" Innar Ramu ta ce "Na gode sosai, na gode Bokayan karaba mene kuma abin sadaƙa" Batty ta yi shiru ta rasa me zata ce, cikin sauri Shatu ta ce "Dubu uku ake bata ai" jikin Innar Ramu na rawa ta ɗauki kuɗin ta tura ta ƙasa, ta riƙe Ramu suka tafi. Suna tafiya Shatu ta yi wuf ta faɗa ciki ta ce
"Mutuniyar....
"Na'am, masoyiyar"
Batty ta amsa tana cire ganyen kanta ta ce "Wash Masoyiyar yunwa nake ji sosai wallahi" Cike da damuwa Shatu ta ce "Yau ma su Lami basu sammiki abinci ba? Suke barinki da yunwa haka?" Batty ta jinjina kai ta ce "Ai don fara cin mutane ba, da sai na lashe kurwarsu tas. Jira nake kaɗo ya dawo mu yi aure irin wanda za'ayi wa Hawwa tunda kin ce mijin mutum yana bashi abinci"
Shatu ta ce "Sosai ma. Amma waye kaɗo?"
"Wani fari, dogo kyakkywa, me gashi a gefen fuska, me suma har wuyansa shine mijina shi nake so ba Saleh ba, kyakkywa ne sosai don ki ji" shiru suka yi, Batty ta lumshe idanunta tana hasaso yadda taga mutumin.
"Ya sunansa?"
"Kaɗo.....
"Ke sunan gaskiya za ki waɗe mini?"
Sai Batty ta watsa hannunsa alamar rashin sani. Daidai nan Hawwa ta ƙarasu da sauri tana hakki ta ce "Ke Shatu maza zo, Mado ne ya mutu gashi can an cika a gidan Moddibo ana ta kuka, duka abokan Mado na birni sun zo har da Sambo" jikin Shatu ya ɗauki rawa, domin tana da alaƙa da gidansu Moddibo. Jikin Batty ma ya ɗauki rawa sosai da ɓari hawaye ya ɓalle mata a fuska ta ƙanƙame jikinta tana jin kamar ta fasa wani irin gigitaccen ihu haɗe da birigma. "Wallah bani na cinye shi ba, bani bace...," Hawwa ta ce
"Batty me kika ce?"
Cikin sauri Shatu ta ce "Babu komai, mu je mu gani" Batty taƙi yadda ta je gani take kamar asirinta ne zai bayyana. Sanda suka je, shirin yi wa Mado jana'iza ake yi, Shatu ta hangi Sambo yana alwala a hankali ta ce.
"Laa ashe da gaske dai Hawwa take yi?"
Idanun Sambo akan abin da yake yi ya ce
"Da gaske me?'
"Da gaske ka zo binne Mado"
Ya ɗago idanunsa a hankali, ganinsa ya sauka akan Batty, ya ƙura mata idanunsa da suka sha farin ƙwalli ya jima yana kallon ta kafin ya zame idanunsa ya ce "E, babu jimawa" Shatu ta ce "Allah sarki, ya aiki kuma?"
"Kazo da Lemo da biredin yau ma?" Kafin ya ce komai Batty ta ce "Nima ka bani idan ka zo dashi, zaka bani ko yaya ne ko?"
Sambo ya sake juyawa ya kalli Batty can ya ɗauke kai yana miƙewa ya ce "Ina dawowa"
A hankali Batty tabi bayansa da kallo.
***
Anty Jiddah ce ta tura handle ɗin ƙofar ɗakin Ahlam magana za ta yi sai ta fasa, ta zubawa bayan Ahlam idanu ganin yadda faffaɗan waist ɗinta ya zauna a riga da skirt ɗin data saka, ya yi mata wani irin kyau sosai atamfar, ta murza ɗauri na gaban goshi, fat fat haka ƙirjin Anty Jiddah ke bugawa. Sai ta ƙirƙiri murmushin dole ta ce
"Golden voice da kanta, kwaliyyar tarbar mijin ce har yanzu bata ƙare ba?" A hankali Ahlam ta juyo idanunta ya yi jajur saboda kukan da ta yi, ba ta yi kwaliyya ba, amma skin ɗinta ta yi fresh ta goge hannunta ɗaya maƙale a hammata. "Kuka kike Ahlam?"
"Kuka akan me subuhanallahi!"
Ta ƙarasa tana kama Ahlam zuwa jikinta ta ce "Haba kakata, mene abin kuka a aure? Na ɗauka za ki fi kowa farinciki, kin san a duniya bayan ganin kin samu nasara akan aikin ki, babu abin da Engineer yake so irin ya ganki a ɗakin mijinki. Haba Hali dubu, kakata ta kaina ya isa haka daina kukan" Ahlam ta narke tana shagwaɓe fuska ta ce "Anty Jiddah wanene shi? Ki faɗa mini ko sunansa ne, Allah tsoro nake ji bana son fita, bana son auren, na amince saboda Yaya ne kawai, fargaba da faɗuwar gaba nake ji idan na tuna ina da aure. Burina, farincikina, nasarata duk za su rushe fa Anty Jiddah, ɗaukakar da nake son yi fa?" Anty Jiddah ta share mata hawaye ta ce "Haba Babyn yaya, aure ai ni'ima ce kuma ba zai hanaki cimma burinki ba, idan bakya son ran yaya ya ɓaci maza tashi ki sami mijinki yana parlour" da rawar ɗari Ahlam ta ce "Yazo ne? Innalillahi!"
Anty Jiddah ta fashe da dariya tana sake fesawa Ahlam turare, taja hannunta suka sakko ƙasan bene daga nan Anty ta juya.
Yana tsaye a tsakiyar parlourn, ya bata baya sanye yake da yadi kaftan brown wanda ya haska fatar jikinsa, ya ɗora wula a saman kan shi, hannunsa ɗaya sanye cikin aljihun wandonsa. Kan shi a sama ya zubawa photon Ahlam dake manne idanu baya ko ƙiftawa. Ya ji sanda ta tsaya a bayansa nesa dashi, kamar yadda gabanta ke faɗuwa haka shima nasa yake yi, bai sani ba ko zata amince masa, zata karɓe shi a matsayin mijinta, ya aureta ba tare da amincewarta ko neman soyayyarta ba. Amma bashi da iko da kan shi, kamar yadda bashi da control da zuciyarsa akan soyayyarta. She loves her so much. Sannu a hankali ya shiga juyawa zuwa inda take, wata ajjiyar zuciya ya sauke sanda ya ɗora idanunsa a kanta, a yanayin da bai taɓa ganinta ba. Kanta yana ƙasa bata son ya juyo ba, bata san ya ƙarasu inda take ba. Sai nunfashinsa ta ji yana sauka a fuskarta. Kadin ta yi motsi ya zaga hannunsa biyun zuwa bayanta daidai ƙugunta ya ɗora ya janyota kaɗan ya sakata a tsakiyarsa. Wani irin rawa jikinta ya fara.
"Assalamu Alaiki Halimatul Sadiya.....
"Hello my Ahlam Abdallah Kurmi....
"Fine baby, my wife"
Ahlam ta sandare ta kasa motsin kirki zuciyarta ta fara gaza ɗaukan yanayin, tsigar jikinta ya shiga tashi, dum haka take jin saukar muryarsa kamar dalma kamar kuma ruwan sama, ta kasa yadda da abin kunnenta yake jiye mata a yanzu ɗin.
"Mrs Asad....
"Matar MD da kanta"
Ya saka yatsu biyu ya ɗago kanta, idanunta da yake zubar da hawaye ta watsa akan fuskar Md wani abu na cakin zuciyarta. "Md ne mijina?.....
"Md yaya ya aura mini? Me Md zai yi da ƴar iska matsoraciyya? Anya Md take gani?" A zuci take wannan maganar jikinta duka rawa yake ta kasa furta komai, ji take kamar ba Ahlam ba, yau ita Md kewa dariya? Bata dawo daidai ba ta ji ya jata jikinsa ya rungumeta kaɗan, ta rasa dalilin daya hanata hana shi, ko yatsa ta kasa motsawa ta yi wani irin hooking gabaɗayanta.
Ya sumbaci goshinta ya riƙo hannunta ya ce
"Let's go.....
"Mu je" ya jata suka fita har inda ya yi parking motarsa ya buɗe mata tare da sakata, ya zagaya ya shiga. Tafiya suka yi me tsayi hannunta yana cikin nasa, ta kasa motsi, ta kasa magana, ta kasa daina zubar da hawaye. Daidai Napep na tsayawa a bakin gate ɗin daidai lokacin da motar Md ta ƙarasu, aka buɗe masa gate ya shiga, itama a dai-dai lokacin ta sako ƙafafuwanta da babu ko takalmi a cikin makeken gidan.
Md ya buɗewa Ahlam ƙofa ya riƙo hannunta, Ahlam kuma ta juya sai kallon wacce take tsaye dafe da cikinta ta kasa motsi take yi. Ya ja hannun Ahlam zuwa babbar ƙofar shiga gidan daidai nan Mu'allim ya fito saboda saƙon Mamy da zai amso, na magani, idanun Nadiyaah ke ciwo sosai tun jiya sun jajur. Mu'allim ya dakata.
"Finally, ni ne wanda ya fara ganinta" in ji Mu'allim
Md ya kalli Mu'allim ya yi shiru.
"Ahky Liman, Allah Ya sa Albarka ashe staff ɗinka ka ɗakko, wannan ai na sha ganinta a Bright Fm idan na je wajanka, Am right?"
Md ya ce "Al'ameen, ina zaka by this time?"
"Nadiyaah Sayyadi Baffa zan amsowa magani a asibiti wajan family Doctor"
"Sayyadi Baffa?"
Ahlam ta maimaita a zuciyarta, Md yaja hannunta zuwa ciki shi kuma Mu'allim ya yi gaba. Har yazo daidai inda take bai lura ba, sai da ya ji ta cakume shi kamar daman wani take jira, ya ɗago kai gabansa ya faɗi ya ce "Iftihal? Me kike a nan wajan?"
Bata iya buɗe ido, bata ko ware laɓɓanta ta kifo jikinsa, nan take kuma jini ya ɓalle mata, a firgice ta ce "Ana.......
"Ana, kai ni wajan Ana zani gida" Laɓɓanta ne kawai ke motsawa idanunta a rufe suke. "No bari na kai ki asibiti"
Ta damƙe hannunsa tana girgiza kai "Don Allah ka kai ni wajan Mahaɗita don.....
Gabaɗaya jinin ya ɓata shi, ya sunkuce ta gabaɗaya ya saka a mota suka nufi Kankarofi. Ana ta kira magariba sanda ya isa, ya ci sa'a Babban yaya yana shirin shiga Masallaci, suka gaisa cikin kulawa, Mu'allim ya yi wa Muraad bayanin komai, har yadda yake son Iftihal ya shirya aurenta, Yaya ma ya yi wa Al'ameen bayani har batun cacar, nan take ya ce zai biya miliyan ashirin ɗin a bawa Alhaji Baita, zai turo Mahaifinsa gobe a ɗaura masa aure da Iftihal ɗin. Yaya ya yi na'am da hakan sukai exchanging number.
Ya ɗauki Iftihal a hannunsa zuwa gida, Innti ta dawo gida da ƙyar bayan alƙawarin da yaya ya yi zai biya Bala Sukunbiya kuɗinsa.
Sanda Innti taga Iftihal bata san lokacin ta saki wani irin kuka ba, ta riƙe Babban yaya jikinta na wani irin rawa da kakkarwa kamar mazari. "Na shiga uku Yaya, me na aikata wa Iftihal? Me yake damuna ne, me ya sa nake biyewa Daada wajan saɓon Ubangiji? Ba haka na yi niyya ba, abin da nake niyyar yi daban abin da nake aikatawa daban, ina jin kamar narasa kaina yaya. Na yi asara a matsayina na uwa, na yi saɓon Ubangiji"
Wani irin kuka take yi har da shassheƙa, idanunta kamar za su fito waje. "Na rusa rayuwar yarana, wani ciwo nake ji a ƙirjina Yaya" gam yaya ya rungume Innti a jikinsa idanunsa sun yi jajur wani irin ruwa ya taro a cikinsu ya kasa cewa komai. Ana ƙuri haka ta zubawa Iftihal ido, zuciyarta na buɗewa haka ƙirjinta, idanunta na soyewa na rashin sanin dalili ko hawaye ya kasa fita daga cikinta. Wanka Innti ta yi wa Iftihal ta gasa mata jikinta, data duban jikin yarinyar bata san sanda ta sake sakin wani ihun ba tana rungume Iftihal. Ta bata magani ta kwantar da ita bacci ya ɗauke ta.
Cikin dare Iftihal ta riƙe Ana saboda a jikin Ana ɗin take, ta shiga bata labarin abin da Baita ya yi mata, ta ɗauki wani abu ta damƙawa Ana a hannunta. Ana ko tari bata yi sai ƙanƙame Iftihal kawai ta yi a jikinta.
Wajejen ƙarfe uku na dare ya banko ƙofar ya shigo, hannunsa riƙe da kwalbar giya yana layi da tangaɗi, kamar yadda ya saba yau ma ɗin tsirara ya shigo, yana shigowa gaban Innti ya yi mummunan faɗuwa. Tana zaune akan ladduma tana istigifari, jin shiru ya saka Innti juya wa dam! Ƙirjinta ya buga jikinta na wani irin rawa da ɓari ta miƙe tsaye, ganin Daada ya gurfana a gaban Ana ya yaye rigarta yana ƙarewa ƙirjin yarinyar idanu, maganganun da sukai da Alhaji Baita yake tunawa, ya faɗa masa hanyoyin da zai bi idan yana so ya yi kuɗi ya shahara ya nemi duniya, dole sai ya kasance da Ana.
"Daada!" Ta kira sunansa da ƙarfi. "Innalillahi raji'un mene haka?"
Kafin ta ƙarasa ya saka hannu ya damƙo ƙirjin Ana da suke tubarakallah, bata saka rigar mama saboda ciwon ƙirji take yi.
Duk abin da yake faruwa akan idanun Iftihal data farka ta yi sallah ta dinga yi wa Daada addu'a domin har zuciyarta tana ƙaunarsa.
"Innti ina son na kasance da Ana" ya sake faɗin "Zan kasance da Ana a wannan daren ina kwaɗayinta, zan yi arziƙi idan na kasance ta"
Kau! Kau! Kau! Kau! Innti ta jerawa Daada maruka huɗu a fuskarsa lokaci guda, tana wani irin huci ta ce "Wannan ya zama na ƙarshe, hatta Iftihal ba zata koma inda ta fito ba, idan ka shirya na shirya shege kafasa" ya ji zafin marin har wuta ya gani.
"Muddin ina raye sai na kusanci Ana!"
A firgice Iftihal ta fito daga ɗauki ta yi wa Daada wani irin kallo, hijabi ne a jikinta wanda ta yi sallah, duk irin masifar da ake Ana bacci take sosai. Ga wani duhu a tsakar gidan babu nepa, "Sai na kusanci Ana!" Shine ya dinga yawo a zuciyar Iftihal.
Yadda ta kasance me shegen tsoran duhun dare da abin da yake cikinsa, hakan bai hanata fitowa tsakiyar tsakar gidansu ba, ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa tana jan wani irin ƙarfaffan numfashi daga baki ya sauka a ƙirjinta, jiki na rawa ta zube a ƙasa bayan ta kalli gabas ta yi Sujjada ta ɗago, hannunta ta miƙa zuwa sama idanunta na kallan sararin samaniya gangar jikinta na fuskantar Alƙibila cikin sarƙewar harshe ta fara magana. "Allah Ya tsinewa babana, Allah ka yi sanadin mutuwarsa yau, Ubangiji ka haɗa shi da ajalinsa a cikin daren nan, idan ya yi tsayin rai, Allah ka hana babana jin daɗin rayuwa, ka yi masa farraƙu da farincikinsa, Allah ka sanya babbar mota tirela ta yi awon gaba dashi yadda ko ƙashinsa ba za'a gane ba, Allah ka sanya bilo inci goma ya faɗuwa babana a kan shi idan yana bacci, Allah ka haɗa babana da ƴan daban da za su sassara naman jikinsa, Allah ka ɗorawa babana ciwon zuciyar da zai ajalinsa, Allah ka hana babana shiga Aljanna, ka yi masa iyaka da walwala, farinciki, da jin daɗin rayuwa...," bata ƙarasa faɗa ba, Daada ya sunkuci Iftihal baya ganin ko gabansa bai zarce ko'ina ba sai cikin rijiya, cumdum haka ya cilla Iftihal a cikin rijiyar.....