Free chapter · Read without an account

PART 26

by Hussain Yusuf · AMRAH

AMRAH

<<PART 26>>

Hamrah tana zaune a kan gado, ta sanya kanta tsakanin gwiwowinta, tana kuka mai cin rai. Ji take kamar rayuwarta ta tarwatse, rashin sanin abin da Daddy yake ɓoye mata ya sanya ta ji kamar an ci amanarta.

A wannan lokacin ne, Hajiya Laila ta shigo ɗakin. Ta ga halin da Hamrah take ciki, sai hakan ya karya mata zuciya. Da sauri ta zauna a gefen gadon, ta ɗago Hamrah, ta rungume ta a jikinta.

"Shhhhh…ya isa haka, ƙaunar Mummynta. Ki daina wannan kukan, saboda ba zai warware komai ba," in ji Hajiya Laila, tana shafa bayan Hamrah.

Hamrah ta ɗago idanuwanta da suka cika da hawaye. "Mummy, me ya sa Daddy ya ƙi faɗa min gaskiya? Na gaji da tsoron abin da ban sani ba."

Hajiya Laila ta yi ajiyar zuciya. "Ƴar albarkata, ina so ki sani ba wani abu mahaifinki yake ɓoye miki ba, kuma ba sonki ne ba ya yi ba, yana ba ki kariya ne, daga sharrin Alhaji Sambo." Cike da mamaki Hamrah ta kalli Hajiya Laila ta ce, "Mommy waye Alhaji Sambo?" 

"Alhaji Sambo wani babban ɗan kasuwa ne, kuma mutum ne mai hatsarin gaske. Matuƙar ya sa abu a gabansa sai ya cimmasa zai iya yin komai a kan ya mallaki duk abin da ransa yake so,  barazanar da yake yi mana ta wuce tunaninki. Ya taɓa zama abokin Daddynki na kasuwanci, shi tamkar baƙin aljani ne a siffar ɗan Adam. Wai wata rana ya  ganki a wani supermarket kin je siyayya, tun daga ranar ya ji ya kamu da sonki, ya saka aka yi masa bincike a kanki, sai ya gano ke ƴar wajen Daddy ce, shi ya sa yake so ya tilasta wa Daddy ya aura masa ke koda ba kya son shi. Shi kuma ya ce ba zai aura masa ke ba, saboda ba zai yi miki auren dole ba, kina da wanda kike so, wannan dalilin ne ya sa yake ta yi wa Daddy barazana a kan dole sai ya aura masa ke. Shi kuma baya so ya faɗa miki, don kada ki firgita, ki rasa natsuwarki, har hakan ya shafi karatunki.."

Hamrah ta ɗan natsu. Ta kalli mahaifiyarta, ta ce, "Mummy nagode da kika faɗa min gaskiya."

Hajiya Laila ta rungume ta, ta ce, “Maza ki je ki yi alwala, ki yi salla ki natsu. Muddin muna raye, babu abin da zai same ki."

A tashar mota, saurayin nan ya ci gaba da bin Amrah duk inda ta shiga. Ya takura mata da yawa, a kan lallai sai ta bi shi ya kai ta masauki, tsayawa ta yi tana tunanin abin da yakamata ta yi...

"Kin ƙi yin magana. Kin ƙi bi na. Tun da ba za ki bi ni ba, zan ɗauke ki da ƙarfin tsiya na kai ki masauki ƴar ƙauye kawai." Ya faɗi haka da zafin rai, ya miƙo hannunsa ya jawo buhun da yake hannunta, sannan ya riƙe hannunta da ƙarfi.

Hannun saurayin na taɓa hannun Amrah, sai ta ji wani zafi mai zafi, ta ji kamar an tsikare ta da garwashin wuta. A wannan lokacin ne, ta tuna da kalaman Hisham da suka yi tasiri wajen hana ta mugunta a ƙauyensu. 'Wannan kyakkyawar zuciya ba ta dace da damuwa da takura ba.' Tsoron Hisham ya sanyaya mata zuciya a ƙauye, har ta zo birni ba ta sake aiwatar da mugunta a kan kowa ba, amma kuma wannan saurayin ya taɓa inda ya fi yi mata zafi wato wulakanci, ta tsani wulaƙanci ko ya yake.

Amrah ta rufe idanuwanta, ta ja wani dogon numfashi. Da ta buɗe su, wani irin ƙarfin iko ne wanda ba irin na mutane ba suka mamaye su.

Nan take, iska mai sanyi, wacce ta fi ta hunturu, ta fara kaɗawa a inda suke tsaye. Amrah ta tsaya cak, jikinta ya fara fitar da wani haske mai launin shudi mai duhu, wanda ya mamaye fuskar saurayin. Kuma gashinta, wanda tuni ya zubo har gadon bayanta, ya tashi sama, yana kaɗawa cikin iskar.

Saurayin ya cika da tsoro. Ya kasa motsa koda yatsansa. Ya ji wani irin bugun zuciya mai sauri wanda ya daskarar da shi a wajen. Ya ga wani ƙarfi irin na aljanu a idanuwan Amrah, wanda ya nuna masa cewa ta fi ƙarfin duk wata mugunta da ya sani

Amrah ta dawo ainihin siffarta. Iskar ta tsaya. Gashinta ya sauko. Ta kalli saurayin da ke rawar jiki a gabanta. A hankali ya faɗi a ƙasa, yana kukan tsoro, yana bai wa Amrah haƙuri, nan idanun mutane suka dawo kansu. Cikin hanzari Amrah ta ɗauki buhunta, ta juya ta tafi, ta fice daga tashar motar..

Alhaji Kabiru yana zaune a babban falonsa yana hutawa. Sai Maigadi ya shigo, ya ɗan rusuna ya gaishe da shi, sannan ya ce, "Alhaji, wani mutum ne ya zo, yana son ganinka. Ya ce sunansa Alhaji Sambo." 

Kafin Alhaji Kabiru ya ce wani abu, dogon mutum, sanye da shadda mai tsadar gaske, babu alamun fara'a ko sassauci a fuskarsa, ya shigo cikin falon. Cikin yanayin izgili, Alhaji Sambo ya tsaya a gaban Alhaji Kabiru... Alhaji Kabir ya kalli Maigadi ya ce, "Kallah za ka iya tafiya." Da sauri ya fice yana waigen Alhaji Sambo..

"Alhaji Kabiru. Na san kana nan, kuma na san cewa kana ƙoƙarin guje min ne shi ya sa na shigo ba tare da izininka ba." Alhaji Sambo ya faɗi haka, a lokacin da ya zauna a kan kujerar da take fuskantar Alhaji Kabir.

"Alhaji Kabiru na dawo gidanka ne, don na yi maka gargaɗi na ƙarshe, saboda na lura ka ɗauki batuna da wasa. Na yi haƙuri mai yawa. Amma yanzu, ina mai sanar da kai cewa haƙurina ya ƙare ka fara kai ni bango." Alhaji Sambo ya ci gaba da cewa, "Dole ne ka aura min ƴarka Hamrah, kafin ƙarshen wata mai zuwa. Idan ka ƙi, to ka sani, zan aure ta da ƙarfin tsiya..."

Hankalin Alhaji Kabiru ya tashi ya cika da tsananin firgici, ya kasa magana. Ya kalli Alhaji Sambo da idanuwansa cike da tsoro da fargaba...

Hussain Yusuf✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.