Free chapter · Read without an account

Chapter 15

by Na'ima sulaiman Sarauta · HIYAAM

Liman ma sak ya yi ganin an fito da makara da gawa a ciki daga gidan da Mu'allim yazo neman aure, ya yi baya kaɗan yana ƙoƙarin basu waje cikin sauri jikinsa na matuƙar rawa da ɓari Mu'allim ya tari gaban Babban yaya da Yaa Sam, ya kasa magana sai kallon makarar yake a zauce yana riƙe kan shi.

Yaa Sam ne ya samu ƙwarin gwiwar kallon Mu'allim a hankali ya ce "Lafiya dai ko?"

"No, aa". Shine kawai abin da Mu'allim ya iya furtawa. Liman na tsaye yana kallon su.

"Mene ya faru?"

"Sunana Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa, ni ne wanda ya nemi auren Iftihal a wajan yayanta Muraad, kuma ya bani izinin zuwa da iyayena domin ɗaura auren a yau ɗin duka" da ƙyar yake haɗe laɓɓansa wajan yin maganar, tsoro yake ji sosai, ba tsoron mutuwa yake yi ba, tunda ya san raɗaɗi da ɗacinta, ya san yadda take saka kaɗaici da mayar da mutum maraya abin tausayi. Ya rasa mahaifinsa Hafizz Hafizz Baffa, yana jin duk wani rashi da za'ayi wa mutum a bayan ta iyaye take. Bai sani ba, amma ya samu kan shi da tsakanin tsoron abin da zuciyarsa ke raya masa, da fargabar jin wanda yake cikin makara ɗin. Yaa Sam ya juya kaɗan.

Tsakanin Yaa Sam da Babban yaya aka rasa mai tankawa Mu'allim maganarsa sbd tsoro.

"Yawwa, na ce zan iya wa Baffa magana?"

"Allah Ya wa Iftihal rasuwa jiya da daddare"

"What!" Mu'allim ya ce da ƙarfin gaske.

Hakan ya janyo hankalin Malami da yake jingine a jikin mota, shima yana mamakin cikar da aka yi a unguwar ta Kankarofi ɗin. Jin sautin muryar Mu'allim ya saka Malami ƙarasawa wajan ya kalle su ya ce "Menene?"

"Abba, wai cewa sukai ta rasu"

Ya runtse idanunta numfashinsa na kakkatse masa a ƙirji ya ce "I couldn't believe, wai ce mini sukai ta rasu, wai ta mutu, ko dan kar su bani aurenta ne? Ko ban cancanci zama mijinta bane? Ko ina da wani aibu ko mummunan hali ne Abba?" Abba Malami ya riƙo Mu'allim, Liman ya ƙarasu yana dafe kafaɗar Mu'allim ya ce

"Please Al'ameen, ka nutsu"

"Ahky Liman ya zan nutsu? Jiya nina kawo Iftihal gidan nan da kaina, kuma yau sai ace ta rasu? Ai data rasu da na ji hakan a jikina da kuma zuciyata. Aurenta ne kawai basa son bani. Me ya sa ba ku faɗa musu ni jinin Hafiz Baffa ne, ni ɗaya daga cikin zuri'ar Sayyadi Baffa bane, bani da mugun hali" idanunsa ya yi jajur jikinsa na rawa, Liman ya saka hannunsa ya riƙo shi sosai da ƙoƙarin janye shi domin ya basu waje a yi mata sallar Jana'iza kamar yadda addini ya tanadar. Abba Malami ya kalli Mu'allim ya ce "Dawa kukai magana a jiya ɗin Al'ameen?"

Ya nuna Babban yaya ya ce "Yayanta"

Abba Malami ya kalli Yaya ya ce "Bawan Allah mene gaskiyar magana? Yarinyar da Al'ameen ya kawo mu domin nema masa aurenta ne ta rasu ko wata ce a cikin gidan daban?" Kallon su kawai Babban yaya yake yi, zuciyarsa ta masa nauyi laɓɓansa sun bushe. Da wani irin yanayi kuma ya ce "Eh"

"Ina nufin da gaske ta rasu jiya da daddare"

"Mene ya same ta? Jinya ta yi?"

Yaa Sam ya ce "Tana da mutanen ɓoye ne, ta fito zata banɗaki shine suka tashi ta faɗa cikin rijiya, sanda aka shiga ceto ta, already ta rasu a cikin rijiyar, ka yi haƙuri, tunda har yayanta ya amince da auren to kamala da mutumcinka ya kai har ya yi yawa, ai babu wanda bai san sunan Baffas family ba"

"Abba ban yadda ta rasu ba, ba Iftihal bace ta rasu. Don Allah Yaa Muraad ka bani auren Iftihal, wallahi ina son ta zan kula da ita sosai" Babban yaya baya buƙatar sabon tashin hankali da hayaniya, duk abin da zai saka ya yi magana a yanzu baya buƙata, a birkice yake jin kan shi sosai. Ya juya kaɗan ya kalli Yaa Sam ya kalli Jaheed dake baya yana riƙe da hannun makarar sai mahaifin Haysaam. "Ku ajjiye makarar ya gani" sannu a hankali suka sauke makarar a ƙasa, jikin Mu'allim na rawa ya durƙushe a wajan da farar shaddarsa ta angwanci, ya miƙa hannunsa kaɗan ya yaye likkafanin. Kyakkyawar fuskarta me cike da annuri ce ta fara yi masa sallama a cikin idanunsa. Ita ɗin ce dai, yarinyar da zuciyarsa ta so a lokaci guda, son da yake jin ba zai sake samun wacce zai yi wa irinsa ba. A hankali ya ja idanunsa ya lumshe, da tunanin mafarki ne, da tunanin zai farka ya ji shelar an ɗaura musu aure, da tunanin zai farka ya ji ta amsa sunan Mrs Al'ameen Hafizz Baffa.

Ya buɗe idanun da ƙyar da nauyin zuciya ya ce "Allah Ya yi miki rahama Aysha, Allah Ya ji ƙan ki, Ubangiji Ya sa mutuwa hutu ce a gare ki, Allah Ya haskaka miki makwancinki"

Luu idanunsa suka fara lumshe.

Liman dake tsaye shima yana kallon fuskar yarinyar domin tabbas ita ya gani sanda suka zo shi da Ahlam gidan. "Take heart"

Ya ce yana ɗan bubbuga kafaɗarsa.

Ya ja likkafanin ya rufe mata fuska, Liman ya ɗago shi tsaye yana miƙawa ya faɗa jikin Liman shi kuma ya yi saurin rungume shi cike da soyayya yana bubbuga bayansa.

Abba Malami ya juya zuwa motar da Sayyadi Baffa yake ciki, ya yi knocking ya ɗauki wajan 10 seconds a tsaye kafin a sauke glasses ɗin ƙasa, yana kishingiɗe a bayan motar idanunsa rufe, farar shadda ce a jikinsa, ya zagaya scarf a samanta wanda ya sake fito da martabarsa ta kasancewarsa shugaban Hisba, malamin addinin Islama, me zuwa yaɗa Musulunci gari-gari, ƙasa ƙasa yana yin da'awa. Kamar kodayaushe ya yi rawani a fuskarsa, hatta idanunsa ya saka su cikin glasses ba zaka taɓa sanin wanene ba, hannunsa riƙe da ƙaramin littafi yana dubawa, ɗaya hannun ƙaramar counter ce yana tasbihi da ita. Luf luf haka gargasa ta lulluɓe farar fatar hannunsa, ba zaka taɓa kallon Sayyadi Baffa ba ka ɗauka ya yi shekarun da suke jingine da rayuwarsa, jikinsa gabaɗaya bai nuna shekarun ba.

Ba kuma zaka taɓa yadda ya haifi tagwayen yara mata masu shekaru har sha bakwai ba.

Abba Malami ya yi ƙasa muryarsa ya ce

"Yarinyar da aka zo nemawa Al'ameen aurenta Allah Ya yi mata rasuwa, yanzu haka Jana'izarta za'ayi ba, shine ka ga taron jama'a" A nutse ya juya kamar zai kalli Malami sai ya fasa, ya ajjiye azkar ɗin hannunsa bai ce komai ba ya ɗauke kai. Abba Malami ya juya zuwa inda aka ajjiye gawar za'ayi Jana'iza, jama'a duk an hau jam'i ana jiran liman, Mu'allim da Liman suna sawun gaba. Malami ya san Baffa ba zai taɓa fitowa ba. Bisa mamaki sai ya ji saukar kamilalliyar muryarsa me cike da kamala da zallar kwarjini ta sauka a kunnen ɗaruruwar jama'ar da suka samu jana'izar Iftihal. A kabbarar da ya yi ta farko wajan ya yi tsit, muryar Sayyadi Baffa na dukan kunnawansu suka samu kan su da yin wata sabuwar nutsuwa bayan wacce suke ciki.

Shi da kan shi ya yi wa Iftihal sallah, kuma ya sunkuya aka ɗauki makara dashi aka saka a mota, ya koma cikin motarsa. Babu wanda ya san waye shi, amma muryarsa na tunawa jama'a da babban malamin nan.

Wato Sayyadi Baffa. Sai suka yi tunanin ko wani ne yake kwaikwayon Sayyadi Baffa ɗin.

Bayan an kai Iftihal, Baffa ya buƙaci a kira masa mahafiyarta zai mata gaisuwa. Babban yaya ya shiga gidan yaga taron jama'a sosai, daman Jadid na asibiti duk da likitocin sun ƙi taɓa shi sai an kawo kuɗi, Ana kuma tunda ta yanke jiki ta faɗi a jikin Babban yaya har yanzu bata farko ba, tana ɗakin su Babban yaya a kwance ita kaɗai. Innti da kanta ta buƙaci kar a tonawa Daada asiri, duk wanda ya ce shi ne ya cilla Iftihal a cikin rijiya bata yafe ba. Tunda ta yi wannan furucin ko tarinta ba'a sake ji ba, bata ko motsi idanunta rufe zuciyarta ta yi mata wani irin nauyi a cikin ƙirjinta, tunaninta ya rarrabu, ga rashin Iftihal, ga halin da Ana take ciki ga tunanin inda zata samo kuɗin da za'ayi wa Jadid wankin ƙoda, Babban yaya ya buga ko'ina rancan kuɗi ba'a samu ba. Haka Jaheed bashi komai, Yaa Sam ma babu kuɗin a hannunsa wannan ya zama babban dalilin daya saka Innti cewa bata zaman makoki, har wasu suka fara ɗan zancen wai babi abin da za'a bawa masu zaman makokin ne na abincin ci da sadaƙa.

Babban yaya ya ƙarasa kusa da ita dab da kunnenta hankali ya ce "Za'a yi miki ta'aziya"

Ta juya ta kalle shi sai ta ce "A ina ne?"

Da yatsarsa ɗaya ya yi mata nuni da waje.

"Maman Haysaam ina zuwa"

"A'a babu komai ai"

Tare suka jera kamar ƙawaye ita da Yaya yana riƙe da hannunta, jikinta sanye da hijabi kanta a ƙasa, domin bata yadda ta ɗago kai ba. Ta ja ta tsaya kaɗan sai ya ce "Yana cikin mota, babban mutum ne shi" ta ɗaga idanunta ta kalli Yaya kamar za ta yi magana kuma ta fasa, ta ƙarasa jikin motar kanta a ƙasa. Abba Malami ne ya fara yi mata ta'aziya ta jinjina masa kai kawai tana ɗora hannu a ƙirjinta. Mu'allim da yake kwance a jikin Liman ya ɗago da ƙyar ya ce

"Ya ƙarim haƙurin Iftihal? Ubangiji Allah Ya yi mata rahama ya kyauta makwancinta"

Shima ta jinjin masa kai alamar ta gode.

Za ta juya kenan, daga cikin motar ta ji kamilalliyar muryarsa me cike da nutsuwa da haiba da wani zallar kwarjini ya ce

"Rabbi rahamhuma" ya ɗora da faɗin;

إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ، أَعْظَمَ اللَّهُ أَجْرَكُمْ، وَأَحْسَنَ عَزَاءَكُمْ، وَغَفَرَ لِمَيِّتِكُمْ، وَأَلْهَمَكُمُ الصَّبْرَ وَالسُّلْوَانَ.

Ma'ana: "Lalle mu na Allah ne kuma gare Shi za mu koma. Allah Ya ƙara muku lada, Ya kyautata ta'aziyyarku, Ya gafarta wa mamacinku, kuma Ya ba ku haƙuri da juriyar wannan rashi" a hankali ta ɗago ta kalle shi, sai taga hankalinsa yana kan azkar ɗin hannunsa, ba zata iya magana ba, ko yaya ta buɗe baki sai ta ji kamar zuciyarta ce zata fito waje, sai ta jinjina kai ta juya.

"Ga wannan ayi sadaƙa, wataƙila ba za mu samu damar dawowa ba" ta dubi kuɗin, sam ba ta yi niyyar amsa ba, amma data tuna ciwon Jadid sai ta saka hannu biyu ta amsa ta nufin cikin giani. Daada yana ganin abin da yake faruwa da kuɗin da aka bawa Innti ya yi zumbur ya miƙe ya nufi cikin gidan, kamar zai kifa saboda saurin da yake.

***

Abba Malami ne ya amshi driving ɗin, saboda Mu'allim har yanzu baya cikin hayyacinsa tun bayan suman da ya yi a can maƙabarta sanda ake saka Iftihal a gidanta na gaskiya. Liman yana buƙatar zuwa wajan Ahlam domin ya yi mata text akan zashi, a kuma yau za'ayi Annual Media Excellence Awards 2025. Ban da an ɗan jirkinta da tuni an yi ɗin. Yana buƙatar ya tafi tare da ita.

2:05 ya ƙarasu unguwar Kurmi a hankali ya yi parking da motarsa a harabar gidan Engineer Abdullah Kurmi, ya jima yana kallon wajan kafin ya ɗauki wayarsa ya yi masa text na zuwan nasa. Sai da ya shafe minti wajan goma ta fito tana cika tana batsewa, fuskarta babu walwala ko kaɗan, a hakan ma sai da Anty Jiddah ta ce zata haɗata da Engineer sannan ta saka wani dakakken lace wanda Engineer ya yi mata da kansa, ta yafa mayafin da ya yi dai-dai da lace ɗin, abinka da Kanuriya wani irin sassanyan ƙamshi me sanya nutsuwa ne yake tashi a jikinta. Tun kafin ta ƙarasu ya zubawa fuskarta idanu yana kallon dukkan wani moving da jikinta yake yi, a hankali yaja idanunsa ya lumshe zuciyarsa na buɗewa da tsananin ƙaunarta me girma.

"Rest of my life....

Ya furta a ƙasan zuciyarsa. "My beloved wify" ya ce sanda take buɗe murfin motar ta shiga ta zauna kanta a ƙasa, ta shiga wasa da fingers ɗin hannunta, gabanta na faɗuwa. Ya miƙa hannunsa ya riƙo nata ya ɗora a cinyarsa da rashin kuzarin jiki ya ce

"Do you want me to greet you?"

A kumbure ta ce "Ina yini Liman?"

"What!" Ya ce yana bubbuɗe idanunsa, don mai tsammaci ko da wasa ta ji sunan ba.

"Say it again"

Ahlam ta yi masa banza.

Ya murza tsakiya tafin hannunta ya ce.

"Say it again, again again and again"

Wani irin takaici ke kama Ahlam kamar ta daddage ta ƙunduma masa ashar haka take ji a ranta, duk irin rashin mutuncin daya dinga yi mata? Da wulakanci kala-kala? Shine zai zo yana mata wani abu kamar wani ɗan iska ko wanda ya sha wata ƙwaya ta daban? Me ya sa sometimes maza masu data ido ne? Most of them akan mace? Ta yi ƙwafa kawai tana share shi. Ya ɗan matsa hannunta da yake cikin nasa kaɗan yana matsar da fuskarsa dab da tata, kwantaccen sajensa ya shafi gefen fuskarta. Yar yar haka ta ji tsigar jikinta yana tashi. "Ɗan is.....,"

Saurin saka hannu ta yi wajan rufe bakinta, saboda subucewa da kalmar ta yi a bakinta.

Md ya jinjina kai ya ce "Ɗan iska"

"To kai ma ba ce mini kake ƴar iska ba, kullum kana aibata ni da hattarata a cikin jama'a, kana mini kallon mara kamun kai ni da Anee..," bai bari ta ƙarasa faɗar sunan Anees ba ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakinta ya ce "quiet" ta tura masa bakin.

"To mene tsakaninki dashi da har kike kiran shi in the middle of the night? Haka daman kike? Kiran wani ƙatoto a tsakiyar dare eh?"

Ta murguɗa masa baki ta ce.

"Abin da yake tsananinka da Yussy, shine yake tsakanina da Anees da kake magana"

Ya yi poiting ɗin kan shi da yatsa ya ce

"Kike haɗani da ƴar iskar nan?"

Ahlam ta waro ido, ta ce "Oh! Ƴar iska ce?"

A daƙile ya ce "Halimatu!"

Yanayin kiran da ya yi mata ya saka ta shiga hayyacinta sai kuma ta fashe da kuka tana ɗora kanta a cinya ta ce "Haka kawai kamar wata wacce ta rasa saurayi sai ka sallaɓo kamar ɓarawo ka nemi aurena, without my knowledge, ina na taɓa jin wannan gadara da ikon? Ina kuma aka taɓa yin haka? Bayan kowa ya san ka tsane ni baka so na, wulaƙantani kake saboda kaga ni marainiyya ce kuma ina da naƙasa, komai a Bright Fm sai ace ban iya ba sai Yussy, duk ƙoƙarina, haka ina ji ina gani ake cire sunana a saka na Yussy duk don na haɗiye zuciya na mutu kuma burinku bai cika ba" ta sake sautin kukan jikinta duka rawa yake yi. "Har da cewa wai Anees ya ɗauke ni ya kai ni hotel, ko ka ɗauka alaƙar dake tsakaninka da Yussy ita ce muke yi da Anees? Anees kawai yana taimakona a aiki ne, yana fahimtata da bani shawara. Me na yi maka haka da zafi har kazo ka nemi aurena don ka baƙanta mini, ai na san cusguna mini kake da ainiya" ta ɗago fuskarta sharkaf da hawaye ta haɗe hannunta biyu da me lafiya da maƙalallen ta ce "Please, ka sake ni..,"

Wata tsawa Md ya daka mata ta yi saurin runtse idanunta ta ce "Ni dai bana son ka, ka sake ni don girman Allah, ina da buri akan aikina yadda ake mini kallon wulaƙantaciyya, nakasasshiya, wacce yin bara ne ya dace da ita, na ci burin sai na nemawa duk wani me nakasa ƴan cinsa"

"Please Liman, ka sake ni"

Idanunsa da suka sauya kala ya zuba mata, yana mamakin yadda ta ƙware a zuba surutu don bai yi expecting nata haka ba.

A hankali ya ce "Kike cewa na sake ki?"

Ta yi masa shiru.

"Saboda ba ki son yadda nake son ki ba, yadda nake nake faɗa akan ki ba, har kike da courage na kallon idanun Md ki ce wai na sake ki? Wacece ke Please? Who are you?"

Ahlam ta ce "To ni bana son ka?"

"Than, kalli cikin idanuna ki faɗan haka"

Ta murtuke fuska ta ce "Idanun duk kwantsa" Md ya ware ido, ya miƙa hannun to make sure haka ɗinne ko a'a, bai yadda ba, ya buɗe madubin motar yaga idanunsa fresh farare tas dasu. Ya shammace ta ya riƙo ta, zata ƙwace gabaɗaya ya fusgota ta faɗa jikinsa ya rungumeta sosai a ƙirjinsa.

Ya ɗora bakinsa a kunnenta, ya hura mata iska kaɗan, kafin ya yi kissing ƙasan kunnen.

"Wannan na rashin kunya ne"

Ya sake kissing kumatunta ya ce "Wannan na hana zuciyata sukuni da tunaninki ne"

Ya yi kissing tsinin hancinta ya ce

"Na kishin Anees ne wannan"

Sai ya jirkituta cinyarsa, jikinta duka rawa yake yi da ɓari saboda taɓa jin hakan ba iyaka cin rayuwarta. Ya dinga kallon bakinta da yadda laɓɓanta suke rawa, ya yi baya kaɗan yana lumshe idanunsa, hannunta ɗaya ya riƙe ya ɗora lips ɗinsa a nata.

Slowly ya yi kissing na ƙasan sosai.

"For all the love I have for you"

Ya ja hancinta kaɗan ya ce "Ina son ki Halimatul Sadiya, ina son ki Ahlam ɗin yaya, ina son Babyn yaya, ina son Golden voice. Ina son ki tun ranar dana fara ganinki Ahlam, na zuba idanu ne naga yanayinki da tarbiyyarki, duk abin da nake miki tsakanin kishin Anees ne ya ja, domin da ace na furta ina son ki ko bakya so na, yake shige miki ko ban karya ɗan mutane ba, jikinsa zai faɗa masa. Sannu a hankali na fahimci kema kina ra'ayina. Kar ki mini musu ke kin sani nima na sani, Yussy kuma bani da business da ita, ina barinta ne ta yi abin da taga dama akan idanunki saboda na kunna ki, kuma Alhamd ina yin nasara" ya yi shiru yana sassauta riƙon da ya yi mata, kanta a ƙirjinsa tana rera masa kuka ya shafa kanta kaɗan ya ce "Ni ba zan tauye ki akan aikinki ba, zan barki duk abin da kike so ki yi muddin bai saɓawa koyar war musulunci ba, zan tayaki aiki wajan cimma burinki"

Cikin sauri ta ce "Za ka yi inviting Sayyadi Baffa na yi Interview dashi don Allah?"

Md ya yi shiru yana kallon ta.

Ta daki ƙirjinsa ta ce "Please Liman"

A hankali ya ce "Ƙarewa ki ce Asad Hafiz Baffa" ya ɗora da "Ba zan miki ƙarya don ki so ni ba, Md ne ni a Bright Fm, Bilal ne Founder a Bright Fm, shine me rediyon, kuma muddin yana nan Sayyadi Baffa ba zai taɓa zuwa nan ba, ke ko bashi bane i don't hakan zai faru, even Nadiyaah da Diyanaah ba ki da zarafin hira dasu" ya kalli cikin idanunta yana goge mata hawaye ya ce

"Tunda kika amsa sunan Mrs Asad Hafiz Hafiz, dole ki yi Interview da Sayyadi Baffa"

Ahlam ta ce "Yaushe?"

"Not now"

Ta zame a jikinsa ya tayar da motar ya jata suka fice daga cikin gidan gabaɗaya.

***

Bayan azahar jama'a duk suka watse a gidan Innti, da an shigo an yi gaisuwa mutum yake komawa gida. Jaheed ta bawa kuɗin aikin da za'ayi Jadid a asibiti ta ce ya je ya zauna kusa dashi, saboda kada a shigo ba'a same ta ba daman shi ai namiji ne, gwara ya saba da jinyar ɗan'uwansa tun yanzu. Ita ta kewa Jadid komai, hatta wanka da alwala idan ciwon ya tashi, bata jin nauyinsa kamar yadda shima yake jin bashi da kamar Innti a duniya kuma uwa ce, labulen sirrinsa ce. A hankali ta miƙe tun bayan dawowarta daga waje babu wanda ta cewa komai, komai da idanu take binsa dashi. Duk yadda zata faɗi raɗaɗin da take ji a zuciya ba kowa zai fahimce ta ba, nauyin da zuciyarta ta yi mata ita kaɗai ma sai ta saka ta jinya, ga tijarar da Daada ya yi a cikin jama'a akan kuɗi, Emama tazo ta tusa.

"Wai ai ita ce ta kai Iftihal gidan masu kuɗi, kuma idan Innti ta bata kuɗin sadaƙa za'ayi"

Hanna ta ce "Ta ina kike zaton zata ba ki kuɗi, tana kallo mugun abin da take jifanmu dashi, da kuma Daada ya fara komawa kanta, gashi nan ƴarta ta faɗa rijiya ta mutu"

"Ai shi sharri kan me shi yake bi, kuma alhaki ɗan tsako ne" ita kanta ko karin maganar bata gama iyawa ba. Innti da idanu kawai take bin su dashi, bata ko tari.

Maman Haysaam ta ce "Haba bayin Allah, wanne irin tozarci ne wannan? Ɗiyar cikinta ta rasu saboda baku da lissafi ku dinga binta da waɗannan munanan malaman? Shi ɗan'uwan naku me ya tare mata da har zata yi asiri saboda shi? Wallahi baiwar Allan da tana jin shawara ta da tuni ta jima da kashe aurenta ta rungume ƴaƴanta ta rufawa kanta asiri. Banda gantalallen ɗan'uwan naku yana yi mata yadda yake so, saboda tunanin tana masa biyayya ko wani dalili nata can mara tushe, ai tuni Innti ta sha kwana ta zama abar data zama. Jaheed yana shago, duk wata ana masa albashi ko babu yawa ne, Muraad yana zuwa farm centre ko babu yawa dai yafi zamam gidan, matar nan tana koyarwa a makaranta, tana ɗaukan albashi, ga ɗinki ta na yi, ga ƙananun sana'a ta hannu da mata suke yi. Ita kenan faɗi tashi wajan ganin ta rufawa kanta asiri bata bar yaranta cikin yunwa da datti ba. Motsi kaɗan sai ya sace kuɗi ya shiga caca, komai na Innti a sace yake a wajan ruɓaɓɓan mutumin can, ga shegen bin mata kamar uwa ɗaya ta haife su da ɗan taure, tunda ta daina koyarwa ta shiga matsin lamba, ga ciwon Jadid dake lashe kuɗi, ɗaukin nawa kika taɓa kawo mata a matsayinki na uwar mijinta, kuma jininta? Wanne tallafi kikai mata?" Maman Haysaam ta ƙare maganar tana miƙe tsaye idanunta na zazzagowa kamar zata hau iska jikinta sai rawa yake.

Daada ne ya ɗaga hannu zai mare ta, Emama ta riƙe hannunsa ta ce "Rabu da ita"

"Basshi ya taɓa ni, wallahi da sai na masa sanadin da zai koma bakin titi da yin bar"

Ta juya kan Emama ta ce "Ke kuma ba wayo kike dashi ko dabara ba, tunda ga ƴaƴa mata nan kina dasu, tun a nan duniya za ki fara ganin HUKUNCIN ALLAH, Saboda kin riga da kin zama INUWAR GIGINYA mara tsoran Allah da son zuciya, a halin da matar nan take ciki ga yaro can a asibiti ba'a san ina kan shi yake ba, shine nan kuka wanko jiki a baku kuɗi, daman ba jana'iza ta kawo ku ba. Jarrabawa ce kawai irin ta aure amma Innti ba tsaran Daada bace in sha Allah farincikin da kuke baƙincikin ta yi kuna ji kuna gani za ta yi yaranta za su zama zama abin sha'awa ga jama'a. Ƴan wahala kawai"

Tana faɗin hakan ta saka kai ta fice, zuciyarta na yi mata raɗaɗin rashin hankalin jama'a. Suma ɗin juyawa suka yi tare da ficewa. Daada ya kalle ta ya ce "ƴar daba kika kawo mini cikin gidana ashe bani da labari? Har tana iƙirarin zata sabauta ni ko?"

Ya jinjina kai, yau fes yake cikin hayyacinsa tsaye akan ƙafafuwansa ya ce "Ina jin igiya ɗaya ta rage tsakanin auren da bashi da wata ma'ana a wajena, face ni na rufa miki asiri kamar yadda mahaifinki ya nema ko?"

A hankali ta ɗago ta kalle shi, ta zuba masa rinannun idanunta bata ce ci kan ka ba.

Ya ce "Tunda babu abin da za ki yi dani kuma kina da wanda zai iya aurenki, ki je na sawwaƙe miki. Nima yau zan yi sabuwar amarya. Na yanke sauran igiyar da ta yi saura" yana faɗin hakan ya juya ya fice da takun isa da ƙasaita. Ta zubawa bayansa idanu, a hankali ta ɗora hannunta a ƙirji ta danne sai kuma ta saki yalwataccen murmushi. Duk abin da yake faruwa Babban yaya yana ɗakinsu kusa da Ana wacce har yanzu babu inda yake motsi a jikinta, kanta a cinyarsa yana shafa sumarta a hankali hannunsa ɗaya ya damƙe nata hannun dashi. Bai sani ba, amma ya samu kan shi da hamdala bayan sakin da Daada ya yi wa Innti ɗin, ya ji wani sanyi na musamman, ya ji relief na musamman a zuciyarsa yana sauka a hankali, hakan ya yi masa daɗi shi ya shirya, daga Ana har Innti yana da inda zai kai su da baza su ta gayyara ba. Yana wannan tunanin Jaheed ya kira shi a waya, ya zubawa wayar ganin number da baya so a kira shi da ita yana yawo a screen ɗin wayar bayan katsewar kiran na Jaheed, ya kuma fahimci filashin daman Jaheed ɗin ya yi masa. Don haka numbers ya kira kai tsaye yana ɗagawa

Ya ce "An fito da Jadid yanzu daga wankin ƙodar" Babban yaya ya yi shiru for a while

Sai kuma ya kashe kiran.

Innti na zaune har yanzu ta kasa motsi, ita da kanta bata san meke damunta ba, duk abin data furta kusan zata iya cewa ba shine ainihin abin da yake mata yawo a zuciyarta ba, carbi kawai take ja tana istigifari, a ranar sai da suka saukewa IFTIHAL Kur'ani ita da Yaya da Jaheed, ta san da idanun Ana biyu ita kaɗai zata iya sauke Kur'anin da kanta cif. A nutse ya shigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, ƙamshinsa me sanyi ya mamaye tsakar gidan, yana sanye da yadi me laushi ash colour ya ɗora a akan shi.

Ya durƙusa ya ce "Ina yini ya ƙarin haƙuri?"

"Allahamdulillah Haysaam" ta ce da ƙyar.

Ya yi shiru kan shi a ƙasa, ta dube shi ta ce

"Ya aka yi ne Haysaam?"

"Daman Offer ɗin aiki da gwamnati ta raba Allah Ya yi na samu, yanzu ma daga can ma'aikata ilimi nake, an sake tantance mu wajan Hamsin akwai wani interview da za mu ke Abuja, wannan kuma shine Finally Interview da za mu yi, shine na ce a tayamu da addu'a mu tsallake idan da rabonmu"

Innti ta ce "Khairan in sha Allah Haysaam, Allah Ya taimaka ya basa sa'a isa rabo ne"

Ya ce "Amin Ya Allah"

"Amma yaya bai san da Offer ɗin ba, link aka cike ko e-mail ne? The offer is still available?" Ya girgiza mata kai kafin ya ce

"A Redio aka sanar, kuma masu first class"

"Yaya ma first class gare shi. Babu rabo ina maka murna ƙwarai da gaske. Yau za ka tafi?"

"Nan da 2 days masu in sha Allah"

"Ma sha Allah" ta ce a nutse.

Ya yi jim kafin ya ce "Nanaah ta farko?"

Da hannunta ta yi masa nuni da ɗakinsu yaya, ya miƙe gently hannunsa ɗaya cikin aljihu da nutsuwarsa ya ƙarasa cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, bai da tabbacin ko Muraad ya amsa, ya yi cak a bakin ƙofa ya zuba musu ido, Ana na jikin Yaya ya rungumeta kanta a ƙirjinsa yaja idanunsa ya lumshe, ƙirjinsa na ɗagawa a hankali, alamar shima bacci yake yana jingine da bango, Yaa Sam ya harɗe hannayensa a ƙirji idan ya kalli Babban yaya sai ya kalli Ana, sai kuma ya kalli yadda take rungume a jikin yaya, ya ɗan runtse idanunsa, ai yayanta ne, bai kuma ci ya ji abin da yake ji a yanzu ba.

Ya jima yana kallon su kafin ya juya ya fice daga ɗakin ya yi wa Innti sallama jikinsa a sanyaye, zuciyarsa ta yi masa nauyi.

***

BIYA.

Batty na zaune a bakin gaban ruwan ta yi shiru tana wasa da ruwan da ƙafafuwanta data saka a ciki, idanunta ya kaɗa ya yi jajur kamar an wasa mata gaushi a cikinsu, barkonon da take ci idan ƙanƙarar maitar ta motsa a ƙare bata san kuma inda zata samu wani ba, ta yi kuka sosai da birigma duk a gaɓar kogin ita kaɗai idanunta suka kumbura. Daga bayanta ta ji an dafata cikin sauri ta juya sai taga Shatu ce, wata ajjiyar zuciya ta sauke tana jan numfashi ta ce "Shatu kin bani tsoro, ki ce na yafe miki"

Shatu ta marairai ce fuska ta ce "Shatu kika ce mini fa? Haba mutuniyar, ba masoyiyar?"

"To ai ki maitata ce ta motsa, bani da lafiya bana jin daɗi, mutum nake son ci Shatu"

Shatu ta waro idanu waje ta ce "Ke Batty mutum fa, ai ba'a cin mutum wallahi"

"In ji wa? A na ci Mado ma cinye shi akai, ba mutuwa ya yi ba, kurwarsa aka kame wlh"

Jikin Shatu a sanyaye tana kallon Batty ta ce

"Shatu ya ake cin mutum to? Mece maitar nan, a ina take ɗakko ki nuna mini ita" Batty ta girgiza kai idanunta ya kawo ruwa ta yi saurin goge hawayen ta ce "Nima ban san mece maita ba, amma kafin a kashe Innata, ita ce ta bani maitar, ina jin ƙanƙarar maitar na mini yawo a ciki babu daɗi Shatu. Kekam kin ji daɗi Innarki ba'a kashe ta ba, kuma tana son ki, ana ba ki amince da yawa, kina yin wanka kina sauya kaya, ina jin kamar ina wari fa" ta yatsuna fuska ta ce "Shanshanani fa ki ji Shatu wari nake yi, ɗoyin dauɗa nake" Shatu ta girgiza kai cike da damuwa.

"To yanzu wa za ki ci? Ke kika ci Mado?"

Batty ta ce "A'a Yaaye ce ta cinye Mado, ai ni ban taɓa cin kowa ba, amma an taɓa yankawa an soya an bani na ci" sai ta yi saurin kara bakinta a kunnen Shatu ta ce

"Kuma wallahi naman mutum akwai daɗi"

"Ce Allah Batty? Nima zan ci"

Yanayin Batty ya sauya ta ce "A'a, ai ba kyau tunda ke ba mayya bace babu ruwanki, kuma idan kika je gidan mutanen da ba ki sani ba, aka ba ki abinci kar ki ci, kar ki yi kwaɗayi Shatu, idan kikai mafarki ana ba ki ɗanyen nama ki ci, to kar ki ciki, idan ba haka ba, kina ci watarana za ki wayi gari kina kallon kayan cikin mutane. Ki dinga addu'a kina neman dafa'i na sharrin mayu"

Ita dai Shatu bata ce komai ba, domin kamar almara haka take kallon abin, bata ma san mene maita ɗin ba, ta kuma gaza gane maganar Batty. Sai ta ce "Jiya da daddare na ganki Batty, ina kika je?"

"Maitar dare. Nima ai na ganki a jiyan wajan ƙarfe uku na dare kin fito shan ruwa a kogi"

Shatu ta zaro ido ta ce "Ni ɗin?"

"E, nima ai kin ce kin ganni haka ne?"

Shatu ta ce "Ni a mafarki na ganki fa"

"Zahiri ne, da babu Dafa'i a jikinki wallahi da tuni na kama kurwarki Batty, ki daina kwanciya da ƙishirwa, idan mutum yana jin ƙishirwa kuma yaƙi shan ruwan har ya kwanta bacci, to kurwarsa bata jurewa, tana tashi cikin dare duk inda ruwa yake ta nema, a wannan tafiyar tana haɗuwa da kurwa kala-kala, muma mayu muna fitowa, kuma duk kurwar da babu Dafa'i a jikinta nan take ake kame ta, madadin mutum ya farka da lafiya kamar yadda ya yi kwanta sai ya tashi cikin jinya. Shatu duk mutuwar da ake yanzu ta farat ɗaya wallahi mayu ne da yawa, sharrinmu yana da yawan gaske"

Idanun Batty ya kawo ruwa ta ce "Shatu ke kamar jinina ce bana son na rasa ki, zan ba ki magani sosai, idan kina tare da maye a cikin gida ko maƙwafta ne ku, muddin kikai wannan wallahi sai dai maye ya ganki ya barki, daga ƙarshe ma ko inuwa ɗaya ba zai iya haɗawa dake ba. Ki samu Igiyar yaɗiya, sai ki bubbuga da dutse, sai ki samu sassaƙin maɗaci amma da dutse ake sassaƙe wa, ba da adda ko gatari ba, ko magirbi ba. Ki haɗa su waje ɗaya ki zuba a babbar roba ko ƙwarya sai a zuba ruwa akai, sai ki samu ɗanyen tafarnuwa ki zuba a ciki, sai ki rufe ruwan, ya yi awa ashirin da huɗu ki dinga sha kina wanka, idan mayen a cikin gidanku yake ki dinga wankan safe da yamma, idan a maƙwafta ne da yamma kawai za ki dinga yi, ba maye ba ko Inna Badakuwa ce nan gani nan bari Shatu sai ta Allah bata mutum ba" Shatu ta yi shiru tana sauraran Batty. A hankali ta miƙe ta ce

"Bari na koma cikin gari kar Innata ta ji shiru" Batty ta jinjina kai kanta a ƙasa.

***

BAFFAS ESTATE.

Tunda ta zauna a hadaɗɗan parlourn kanta a ƙasa yake, tana jin yadda idanu wajan huɗu suke kallon ta, Azizah, Hajiya Umaimah sai kuma Mamy, da Hajiya Kaltum ƙanwar Hajiya Umaimah. Mamy ta kalli Ahlam a hankali ta ce "Allah Ya nuna mana lokacin Nikkah da alheri, ya saka mutuwa ce zata raba tsakaninki da Liman" ita dai bata iya cewa komai ba, kanta yana ƙasa abinta.

Liman ne ya kame fuska ya ce "Amin Mamy"

Ta miƙe tana faɗin "Idan zata tafi ka yi mini magana Please Asad" nan ma ya ce "I'll"

Azizah zuciyarta a cunkushe tabi bayan Mamy da kallo ta ce "Mikirar mace, wallahi ina zargin idan ba ita ta rusa aurena da Baffa ba, kuma wallahi indai ina raye Baffa bashi da wata mace a duniya sama dani"

Hajiya Kaltum ta ce "Ko ba Hajia Ni'ima ba? Ai na jima da fahimtar kamar tana da saka hannu a ƙin auren Baffa, hatta hatsarin Baffa wallahi ita nake zargi ke har mutuwa Hafiz Baffa ma ina saka ran ita ta tsara komai, saboda ta samu gado me yawa, ba tana taƙamar zaratan yaranta maza har biyu ba, ga ƴar auta Hidaya da late Hafizz Hafizz Baffa ya ɗauki son duniya ya ɗora a cikinta tun kafin ma yaga zuwanta duniya, da yana raye aka haife ai ƴar kallo za ki zama a gidan" Hajiya Umaimah girgiza ƙafa kawai take yi, ba tare da ta ce komai ba.

Liman ya kalli Hajiya Kaltum ya ce

"Is this the right time da za ku yi wannan maganar? Haba Ummy" ta kalle shi.

"Ni na mance wai matarka ka kawo ashe Liman. Ke yama sunanki kika ce ɗazo?"

Kanta a ƙasa ta ce "Ahlam sunana"

"Ke dilla bana son iyayi, sunan gaskiya"

Slowly Ahlam ta ɗago kai ta kalli Azizah, shigar alfarma ce a jikinta wuyanta ya sha daham, ta yi kamar ba zata yi magana ba sai ta ce "Halimatu sunana" Azizah ta taɓe baki

"Hajiya Halimah kenan ko?"

"No" kawai Ahlam ta ce.

Azizah ta ce "Kan uba, uban mene no?"

"Ina nufin ko airport ban taɓa zuwa ba, ban kuma san ranar zuwana ba, amma ina da rufin asiri dai-dai gwargwado in sha Allah"

Hajiya Umaimah ta ɗago kai ta kalli Ahlam sosai, taga gabaɗaya lace ɗin jikinta bai fi 150k ba, ɗan kunnen ba gold bane, ta kalli hannunta a maƙale da ya yi yaushi ta taɓe bakinta ta ce "Ok, ashe ke nakasasshiya ce?"

Wani abu ya daki zuciyar Ahlam ta ɗago a hankali ta kalli Liman sai ya yi saurin runtse idanunsa yana ɗauke hawaye ya fara cika idanunta. Azizah ta ce "Disable kenan ko?"

Hajiya Kaltum ta ce "Ko shi ya sa daga zuwa neman aure aka ɗaura auren? Wannan ai dole Liman ya auri lafiyayyiyar mace gsky"

"Let's go" Liman ya miƙe yana riƙo hannun Ahlam, bai jira ya koma part ɗin Mamy ba, yana da tabbacin ma likita ne yake duba Mu'alim itama tana wajan Al'ameen ɗin. Suna shiga mota Ahlam ta fashe da wani irin raunataccen kuka, wanne irin aure ne wannan, tun kafin ta shiga? Ba zata iya ba, gwara ta nemi ɗaukaka a aikinta akan wannan zaman na aure, babban gida ne sun fi ƙarfinta. Ta kowacce fuska, Liman ya kasa ce mata komai sai hannunta daya riƙe.

Wajejen 8:00 na dare ya sake dawowa ya ɗauke ta, zuwa wajan awards, sabuwar Abaya ya saka me masifar kyau, shi da kan shi ta yi masa kyau, lokacin da suka ƙarasa event ɗin ya cika sosai, ta riga shi fitowa suka hadu da Zainab Alƙali suka yi ciki, Anees tun daga nesa yake mata murmushi ta yi ƙasa da kanta. Waje suka nema suka zauna da Zainab Alƙali, Yussy sai ƙwainane take, ta saka wasu shegun kaya, ɗuwawunta ko motsi ba ya yi ya haɗe da bayanta ya shafe. Zainab Alƙali ta zunguri Ahlam

Ta ce "Ga mutuniyar fa, yau sai Allah"

Murmushi kawai Ahlam ta yi hankalinta akan wayarta, ta samu kanta da yin research akan TIVA. Zainab Alƙali ta ce

"Ke kawai nake jira a bawa award na tafi"

Ahlam ta ce "Wa fa?"

"Wawa" cewar Zainab Alƙali.

"Kefa kin san dole sai an ba ki award, akaf Bright Fm waya kai ki kawo news tell me?"

"Uhm"

Aka ci aka sha.

A hankali aka fara bada awards kamar daga sama suka ji an ce "Zainab Alƙali ta samu Rising Star in Journalism” wani irin buɗe baki Zainab ta yi, Ahlam ta rakata ta amsa.

Aka kira wata Binta Baba aka bata na

"Most Promising Reporter"

Me bada award ɗin ya ce "Award ɗinmu na ƙarshe me taken,Outstanding Journalist Award, wato Lambar Yabo ta fitaccen ɗan jarida. Wannan award zai je zuwa ga, ga"

A tare Yussy da Ahlam suka miƙe.

Md daga nesa yana ta kallon Ahlam yana murmushi, domin tun kafin yau ya san ita ce, haka ma Anees. Deep down na zuciyarta bugawa yake sosai. Daga sama ta ji an ce

"Zuwa ga Yussrah Yassar Yakasai"

A tare Md da Anees suka miƙe tsaye da faɗin "What!" Yussy na murmushi ta je ta amsa cike da farinciki friends ɗinta sukai ca

A ɓangaren maza aka bawa Md da Anees.

Dishi-dishi haka Ahlam take gani ta miƙe ta yi waje tana fashewa da wani irin kuka. Tana tsaye ta ki an sakar mata dariya da ihu ana mata Vedio. Yussy ta ce "To ya akai Ahlam?"

"Yanzu za ki yadda ni ba sa'arki bace? Za ki yadda na fiki ta kowacce fuska? Za ki yadda ki ɗauki shawarar dana ba ki na ɗaukan roba ki bi layin mabarata? Ki haƙura da aikin jarida, bana irinku bane, ba za ki iya ba wallahi" Billy ta ce "Wai Yussy daman wannan ce me yin ƙasa dake tana ɗaukan footstep ɗinki? Ashe naƙasa ma gare ta"

"Wallahi fa Billy, kuma ya zama na farko na ƙarshe da zan ganki tare da Md domin nawa ne, mijina ne in sha Allah. I'm sorry fa, ga Outstanding Journalist Award da sunan Yussrah Yassar Yakasai, yau kam bacci ai babu shi a cikin idanunki na sani wallahi"

Suka sheƙi da dariya Yussy ta ce "lose....,"

Bata ƙarasa faɗa ta ji an ɗauke ta da mari a hagunce, Md na sauke hannunsa Anees ya sake sharara mata wani marin ya ce "Ke Yussy har kina da zummar faɗawa yarinyar da nake so magana? Waye bai san da yadda kika samu Award ɗin ba, waye bai san halinki ba, award indai ta hanyar da kika samu ne bana fatan baby ta samu irinsa"

Md ya kalli Yussy sama da ƙasa ya ce "Ya zama last time da za ki yi wa matata haka, ni sa'anki bane zan iya saka ki a gidan yari har ƙarshen rayuwarki, texci no garage"

Yussy jikinta na rawa ta ce "matarka?

"Yes, Mrs Asad Hafiz Hafiz Baffa"

Yana faɗin hakan ya riƙo hannun Ahlam yana sanyata a cikin mota, suman tsaye Anees ya yi, ji kamar bai ji daidai ba, yau yake shirin faɗawa Ahlam komai na yadda zuciyarsa ke son ta, ya faɗa wa family ɗinsa shi kawai suke jira. Yussy kamar ta haukace

Sanda Md ya kai Ahlam gida ya jima yana rarrashinta kafin ta yi masa murmushi ta ce

"Nothing fa, ya shige ai"

Ya ce "Da gaske kike har zuci?"

Ta jinjina kai. "Ok kiss me idan haka ne"

Ta shawagaɓe fuska "Ai ban iya ba"

"Ni na iya, come closer"

Ya riƙota yana kallon fuskarta ta yi masa murmushi ta miƙa hannunta zuwa sajensa ta shafa kaɗan ta ce "Ina son Liman"

"Ina son Asad Hafiz Hafiz Baffa"

Ta sake shafar lips ɗinsa ta ce

"Ina son Md ɗina"

Wani shock ya kama Md, domin bai taɓa expecting hakan ba, ya san tana son shi, amma bai kawo hakan ba nan kusa, ya dinga kallon ta, ta ce "Ka fasa kissing ɗin?"

"No, I'll try ban iya ba"

Kafin ta yi magana, ya ɗora bakinsa a nata ya shiga kissing ɗinta, cikin sa'a ta shiga yi masa nata kissing ɗinz few seconds ta zare jikinta ta ce "I'm very sorry Md please"

"Sorry? Na mene?"

Ta ce "Just, za ni Abuja please"

Ya ce "Me za ki a Abuja?"

"Wajan Antynmu, kwana biyu zan"

Ya girgiza kai ta ce "No, ki bari zan kai ki"

"A'a don Allah, da Yaya zamu kuma gyaran amarci za'a yi fa" ya dinga kallon ta.

"Am going to miss you Leemah, ya zan?"

"You can call me, and nima zan yi kewarka ai" ya jinjina kai ya lumshe idanunsa.

"Ka amince?"

"Sure, Allah Ya tsare hanya"

Sai ta yi saurin rungume shi, hawaye na cikowa a idanunta, ya yi holding nata back"

Sallama sukai ta shiga cikin gida, ƙarfe 2 na dare ta gama haɗawa duka wasu ID cards nata, atm, wayarta, computer da komai ta saka a cikin jaka, ta yi ɗan note a paper ta ajjiye. Tana da duka maƙulan gidan ta buɗe ta fice, har kuma ta fice daga cikin gate ɗin me gadi yana sharata bacci bai sani ba.

Ta kalli gidan ta ce "I will be back, zan dawo da nasarar da za ka yi farinciki yaya, zan dawo da nasarar da Yussy bata isa ta yi mini dariya ba, zan dawo matsayin cikakkiyar ƴar jarida" ta goge hawayenta. "Zan dawo, dawowar da zata bani nunawa Md so na gaskiya, son da zai yi alfahari dashi, soyayyar da Yussy bata isa ta shiga cikinta ba" ta nemo number Md ta yi masa text da

"I'm sorry sweetheart....

"I will be back soona or later"

***

Washegari ya kama juma'a, Jadid ya dawo gida ya nemi warware sai jinyar zuciya na rashin Iftihal, gashi har lokacin Ana bata farka ba. Suka shirya suka nufi masallacin juma'a, Yaya, Jaheed da Jadid, daga nan suka ƙarasa kabarin Iftihal wajan yi mata addu'a. Lokacin Innti ta yi alwala ta yi sallah ta leƙa ɗakinsu Yaya ta kalli Ana, ta shafi fuskarta tana sumbatar goshinta a hankali.

Innti ta jima tana azkar da yin addu'a ga Iftihal da Ana, ta dinga addu'a Allah Ya bawa Ana haƙuri da juriya Allah Ya bata dangana.

Sallah ta fara, tana cikin sallar kuma su Yaya suka dawo, waje suka nema suna jiran su yi mata sannu da gida, sun san tana jimawa a Sujjadar ƙarshe amma wannan jimawar ya yi yawa. Jaheed ya ce "Sahibarmu a roƙa damu" Jadid ya yi dariya sosai shima ya ce

"Addu'ata duka taku ce ai"

Jaheed ya ce "Kai ni Innti?"

"To ai abin da zata ce na faɗa, ni dai ki roƙa mini ko a mafarki ne na dinga ganin Iftihal"

Suna ta barkwanci. Babban yaya yana zaune sai kallon Innti yake yaga hannunta ya ɗan lamƙwashi ya miƙe da sauri ya dafata, yana dafata yaga ta faɗi, jini ta hanci da bakinta hannunta riƙe da farar takadda, da biro daga can gefe. "Innti...!!!" Suka kira sunanta.

"Ta rasu" shine abin da yaya ya ce yana ɗora kan shi a ƙirjinta ya ƙanƙameta jikinsa ya shiga wata iriyar rawa da kakkarwa da ƙarfi ya ce "Don Allah Innti, Anarki, ni ɗaya ba zan iya kulawa da Ana ba" daidai nan Ana dake cikin ɗaki ta fasa wata iriyar ƙara ta ce

"Abbaaa....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.