Free chapter · Read without an account
A Bleeding Womb, A Severed Bond
by NorthernAngel · His Rose
Shigar Omar ke da wuya gidan Muazzam ya hange su a compound—Salma, Jidda, Hasinah, da wata ƙanwar Salma mai bi mata. Suna tsaye sai cacar baki suke da Surayya ita kaɗai. Tana tsaye ta riƙe ƙofar parlour ta ɗan sunkuya cikin azaba, her knuckles white from the strain, amma duk da hakan bakinta bai mutu ba. Maganar tata ma da kaji kasan akwai rauni a ciki, ɗaurewa kawai take yi tana yin faɗan da kyar. Muryar Salma ce take tashi cikin kuka da zafi, shaking with pure rage, “Kin zata ni wawuya ce dan kinga bana faɗa? Sai in kashe ki in kashe banza Surayya ba abunda za’ayi! Ƙanwar taki ma ki tabbatar mata nice ajalinta in ta shigo estate ɗin nan. Banzaye kawai!” Cikin murya mai cike da ƙarfin hali, Surayya tace, “Bashi kuka ci gaba ɗayan ku wallahi baku daki banza ba! Wallahi yanda kuka mun sanadi, sai nayi muku... shegu dangin asara.” idda ce ta sake yin kanta, stepping aggressively into her space, tana faɗin, "Akwai asarar da ta wuce haihuwar ku da iyayenku suka yi a duniya? Look at you! Just because you managed to crawl your ass into this house, you actually think your cheap sister has a place here? You are both nothing but desperate, low-class gold diggers chasing after men. No matter how hard you climb, you will never belong in a house like this.. You can play your dirty tricks all you want, but you will never be anything more than high-class beggars in this family!" Kafin ta kai ga taɓata, tsawar Omar ta dakatar dasu, booming through the compound like thunder. Cikin sauri duk suka juya suna kallon sa. Kafin kace me, ƙanwar Salma ta kwasa a guje ta nufi gate, not wanting to be caught in the crossfire. Omar ya juya yana kallon ta kafin ya juyo yana ƙare musu kallo. Idonsa ne ya sauka akan Surayya da zuwa lokacin ta durƙusa sosai tana numfashi da ƙyar. Cikin sauri ya ƙarasa inda take yana kallon sage color kayan ta daya yi staining. Inda take durƙushe kuwa jini ne—duk da ba mai yawa ba, amma akwai drops sosai jefi-jefi against the concrete floor. Da razana Omar ya furta, “Subhanallah! What did you guys do to her?” Muzurai Jidda da Hasinah suka fara yi, looking guiltily at each other, yayin da Salma ta ɗauke kai tana share hawayen fuskarta, babu alamar nadama ko ɗar a tare da ita, sai ma raɗaɗin cin amanar da aka mata da yake sata jin abunda tayiwa Surayya kaɗan ne. Daman Jidda ce tace su dakata cikin tsoron ganin jini yana bin ƙafar Surayyar. Cikin tsawa Omar ya sake cewa, "Me kuka yi mata na ce? How can you be so heartless? Are you out of your minds?! Start moving your useless selves right now before I lose my temper and lay my hands on you! Just get out, ku fita gaba ɗayan ku!" Cikin sauri duk suka juya, sai dai basuyi nisa ba muryar Surayya ta cimmusu, her words sharp enough to cut through glass: “Ke Salma har kina da zuciya ashe? Rashin zuciyar naki akan mata ne kawai kenan? Asararriya! Ai kece wadda iyayen ta sukayi asarar haihuwa... kowa na bin maza, ke kina bin mata. Yanzu kuma kinzo kina hasada dan mijin da ya sakeki ya samu saliha wadda ba watsastsiya irinki ba. Ai sai dai duk mai mutuwa ya mutu, amma auren Zafar da Rahma mutu ka raba! Yanzu zai san yayi aure.” Salma wani murmushin baƙin ciki tayi kawai ta juya tayi gaba a kunyace, her face burning with humiliation, yayin da aka bar su Jidda da Hasinah da tunanin abunda Surayyar ta faɗa. Omar kam at that exact moment, ji yayi kamar ya bar Surayyar a gurin yayi tafiyar sa saboda kalamanta na ƙarshe—yasan ba wai da Salma kaɗai take ba, har dashi. Daman kwanan nan indai Muazzam yana gidanta, toh ta ringa maganganu kenan. Omar kuma mostly yanzu tare yake dinner da yayan nasa, so haka zata ringa waya tana faɗin maganganu har in Allah ya yarda sai an bar Rahama daga ita sai mijinta. Jiya kuwa da aka ɗaura auren ba kalar maganganun da batayi ba gaban Omar. Yanzu gaba ɗaya zafin kishiyar da Muazzam yayi mata akan wannan auren take saukewa tana gasa musu maganganu. So at that moment, Omar yaji kamar ya ƙyaleta, amma sai taci darajar auren yayan sa dake kanta. Juyawa yayi fuskar sa a haɗe yana faɗin, “Taso.” Wani dogon tsaki taja, kafin ta miƙe da kyar tana janyo mayafin ta daya faɗi can gefe ta sa a kanta, sannan ta fara tafiya da kyar a dudduƙe ta bi bayan sa. Parking space ya nufa ya ciro key ɗin motar Muazzam daga key box ɗin da ke gurin, sannan ya buɗe motar ya shiga ya tada motar. Da kyar ta ƙaraso ta shiga tana nishin azaba, clutching her abdomen saboda with each passing minute, cikinta ƙara mirɗa mata yake. Asibitin sa ya wuce da ita straight, driving through the estate gates in a blur. Yana zuwa ya miƙata ga emergency team ɗinsa; ko shiga baiyi ba ya juyo. Sai da yayi nisa, ya tsaya ya shiga turawa Muazzam text ɗin cewa ya kaita asibiti, ko yaje ko kuma ya kira wani a gidansu. Muazzam da akayi komai akan idon sa, Omar ne dai bai gansa ba tun farko. Shima instead of responding or showing up, message kawai yayiwa maman Surayya, ya sanar da ita ɗiyarta batada lafiya da kuma asibitin da suke, completely washing his hands off the chaos. Koda maman Surayya ta samu saƙon, magrib ya riga ya yi. Dan haka sai da suka tsaya sukayi sallah, sannan ta fito ita da yayan ta duka su uku. Gidan, jama’a sun riga sun fara taruwa saboda shirye-shiryen bikin Rahama daya kankama with full force—har an fara yi mata gyaran jiki ma saboda sati biyu kawai aka sa na tarewar ta. Koda suka isa asibiti, sosai likitar data dubata ke faɗan an barta ba kowa, expressing utter disapproval, wanda hakan ya ɓatawa maman Surayya rai jin cewa bama Muazzam bane ya kawota kuma bai zo ba. Bayan ta bi likitar office, ta hau mata bayanin cewa ta samu ɓarin cikin wata biyu ne, amma yanzu thankfully bata cikin wani critical condition. Sai kuma likitar ta hau mata tambayar me ya faru, dan sosai taga alamun duka ba kaɗan ba a jikin patient ɗin. Dan ma an ce mata Dr. Galado ne ya kawota da kansa shiyasa ta taɓata hakanan. Hankalin maman Surayyah ya tashi, ta fara tunanin, ‘Toh ko faɗa sukayi da mijin shine ya daketa tayi ɓari?’ Ganin itama maman bata san komai ba, likitar ta sallameta tace zata iya zuwa ta ganta. Koda ta shiga, idon Surayya biyu sai kuka take zubawa ita ƙadai, tears streaming down her face continuously. Ga wata nurse a tsaye tana kallon ta da mamaki because tayi lallashin har ta gaji, amma Surayya har da mata tsawa ta zage ta. Surayya na ganin mahaifiyarta ta shigo, ta ƙara sautin kukan ta tana ƙoƙarin tashi da kyar. “Mommy! Mommy ya sake ni! Ni Muazzam ya saka mommy... wai ni?!” Da sauri nurse ɗin ta isa tana riƙeta dan kar ta sauko daga gadon and risk hurting herself. Mahaifiyar tata kuwa, wani jiri ne ya kwasheta nan take; cikin sauri ta dafe bango, kanta na juyawa mata from the absolute shock. Rahama dake biye da ita ta riƙeta da sauri tana faɗin, “Mommy, calm down. Karki je ki faɗi a banza fa.” Cikin kuka da tashin hankali, Surayya ta ci gaba da faɗin, "Mommy na shiga uku! Please help me, ki faɗa mun what should I do? Wallahi ina son mijina!" Cikin ƙarfin hali maman tasu ta iso tana rungume ɗiyarta, cikin sanyin murya tace, "Addu'a za kiyi Surayya ba ihu ba! Please pull yourself together. Tell me, saki nawa ya miki me kuma ya faru?" Labarin dukan da aka mata ta hau badawa sannan ta janyo wayarta tana kasa ƙarasa labarin saboda kuka da ya ci ƙarfinta ta miƙawa maman ta wayar kawai. Karɓar wayar maman tasu tayi, inda ta fara karanta text ɗin nasa kamar haka: "I was only keeping you as my wife because of the pregnancy. But you see? God is truly great! He knew I was trapped, so He called that forming soul back just to save me from your darkness, and He did it to protect them from a mother like you. Yes, He took it away because He knew a child with my blood shouldn't be raised by a gold digger like you! He freed me from you. It’s over—na sake ki saki biyu!" Wani nannauyan ajiyar zuciya Hajiya Saudah ta sauke cikin tashin hankali tana faɗin, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Tabdi jam.” Sauran yan uwan ma duk jigum sukayi, stunned into total silence, suna kallon Surayya dake wani erin kuka mai ban tausayi. Sake rungume Surayyar maman tayi tana cewa, "It’s okay Surayya, calm down. Ke ma ba kya ji, you never give him any peace of mind! Sam ba kya ba shi peace, and peace is not something a man compromises on; if a husband cannot find rest in his own house, he will eventually look for an exit. Tsakani fa da Allah. I have told you several times, Rayah, when you strip a good man of his peace, you are practically begging for a broken home." Sai kuma ta ƙara kwantar da murya cikin lallashi ta ci gaba da magana, "Yanzu dai wipe your tears, ki daina wannan kukan. It's not the end of the world since it's not a triple divorce—zai maida ki Insha Allah. We just need to give him space ya huce. Da zarar Auta ta shiga, everything will be sorted out. Mark my words, once Zafar divorces that Zara girl and she goes off to marry someone else, everything will go back to normal. It’s not that deep, he just needs time to realize that." Rahma ta saki wani confident murmushi tana gyaɗa kai, cike da iyayi tace, "Exactly, you just need to chill, Rayah. The moment my man gets me and realizes what he’s been missing out on his whole life… wallahi shikenan! It’s going to be just me forever, and you’ll find your way back to that arrogant husband of yours." Gaba ɗayan su suka kwashe da dariya harda maman, wadda ta janyo Rahamar jikinta affectionately tana faɗin, “Baki abun magana, Auta! Allah ya shirya mun.” Kowa ya amsa da amin yayin da ita kuma Rahama ta narke wa mahaifiyar tata cike da shagwaɓa. Ƙanwar Surayya dake binta ce ta tada zancen dukan da akayi ma Surayyar da kuma matakin da zasu ɗauka na ɗaukar fansa. Maman ta katseta da sauri da faɗin kar ayi abun da zai jawoma auren Rahama matsala. Dalili na biyu kuwa, su kansu sun san gidan Galado ya fi ƙarfin ace za’a taɓa wani dake cikin sa, koda ɗan aiki ne balle yayan gidan—their status has always been untouchable. Shiyasa tace musu ba tanan za’a rama ba. Haka dai sukayi ta ƙulle-ƙullen su har ƙarfe 9:00 na dare, tukun yayan suka tafi. Maman su kuma ta kwana da Surayya, inda washe gari da sassafe ta nemi sallama suka bar asibitin, leaving the drama behind for now... A ɓangaren Omar kuwa, ƙarfe goma na dare ya koma gida saboda daga asibitinsa LUTH ya wuce lokacin, the long shift leaving him completely drained. Shi da Amrah ne a cikin motar saboda itama sai yamma ta shiga asibitin. Hirar su suke yana bata labarin abunda ya faru da kai Surayya asibitin da yayi, sannan kuma ya dawo yana complain akan rashin zuciyar Zara akan Zafar, wondering why she keeps tolerating his mother’s excess baggage. Yayin da Sanyi ke ta dariya tana cewa ya ƙyaleta tunda tana son mijinta, and love makes people do the craziest things. Besides, Noor tace mata Yemma ce tace dole sai ya auri Rahamar. Shi Omar ya sani, amma gani yake kawai gwara Zara ta haƙura da irin wannan abubuwan da Yemma ke sa yayi mata, instead of putting up with the constant emotional disrespect. Har suka iso gida suna ta maganar, inda Amrah ke ta kwantar mai da hankali tana fahimtar dashi yanda yake tunanin Zara na cikin damuwa ba haka bane, reassuring him da cewa kullum sai sunyi waya and she always sounds happy in suna waya. A ƙofar gidanta ya tsaida motar, inda Muazzam da ke zaune yana jiran dawowar matar tasa ya miƙe da sauri ya fara buɗe musu gate ɗin da kansa. Amrah dake kallon sa ta yi murmushi tana girgiza kai saboda gate ɗin motorized ne amma tsabar son burgeta ya tashi ya buɗe da kansa. Omar ma murmushin yake har ya shiga yayi parking motar. Cikin sauri Muazzam ya ƙaraso ya buɗe ma Amrah ƙofa, yana matsawa ya buɗe mata hannu; saukowa tayi da sauri daga motar ta faɗa jikinsa, tana rufe fuskar ta a ƙirjinsa, melting into his embrace. Sannu da dawowa yayi mata cike da so yana kissing kanta. Daga haka ya ja hannun ta ya kalli Omar da ya aje key yana mai sai da safe. Frowning Muazzam ɗin yayi yana cewa, "Kunyi dinner ne? I didn't eat anything because I was waiting for you guys." Sighing Omar yayi cike da gajiya kafin ya gyaɗawa yayan nasa kai yana cewa, “Muje toh.” Daga haka suka nufi ciki gaba ɗayan su. Straight dining suka nufa bayan sun shiga ciki, inda bayan Omar da Amrah sun yi sanitizing hannun su suka zauna cin abinci. Anan ne Muazzam ke faɗawa Omar ya sallami Surayya, dropping the heavy news casually over the meal. Omar ya gyaɗa kai, not even surprised, yana cewa, “Better.” Daga haka suka canza wata hirar… bayan sun gama cin abinci, Muazzam ya miƙe yana kama hannun Amrah saboda haka suke kullum bayan sun ci abinci; za su je sama tayi freshing up sannan nan su sauko su samu Omar a parlour su sha tea suna hirarsu kafin wurin 10:00 PM yayi musu sai da safe ya tafi. Amma yau dake dare yayi already, sai Omar ya miƙe shima yayi musu sai da safe yana cewa bacci yake ji. Sai da safe suka mai kafin suka bisa ya fita, sannan suka rufo ƙofar suka wuce sama. Cike da gajiya ya ƙarasa manor da ƙafar sa. Yana zuwa ya nufi wing ɗinsu straight saboda 11:00 PM ta riga ta yi, kuma yasan Baffa ya rufe ƙofarsa zuwa lokacin. Koda ya shiga ɗakin sa, turus yayi saboda abunda yake gani, his exhaustion momentarily vanishing in sheer shock. Noor ce a zaune tsakiyar gadonsa, ga Zwar a gefen ta yana bacci peacefully. Ita kam idonta wasai tana scrolling through her phone. Wani silk burgundy pajama set ne a jikin ta da yayi mata kyau ya haska farar fatar ta, kanta yana sanye da white silk bonnet yayin da fuskarta take fresh ba wani kwalliya—kana gani kasan batayi making wani effort ba saboda haka take baccin ta. Wani long, tired sigh ya sauke kafin ya ƙarasa ciki yana cewa, “Tashi ki fita.” Noor dake kallon sa ta turo baki tana cewa, “Toh yaya, Yemma ta kore ni fa! Ina zanje?” Closet ya nufa, his tone completely unbothered yace, "Ki je sama, ɗakin Zara ko Zafar, or you can even go to Muazzam’s room! Anywhere you like, just not mine.” Banza ta mai kamar bata jisa ba, completely ignoring his instructions. Ta janyo pillow ta kwanta ta hau addua; bayan ta gama ta shafawa ɗanta, ta shafawa kanta. Dai dai lokacin da Omar ɗin ya fito daga close, yana kallonta ta sa hannu ta kashe wutar gaba ɗaya tayi kwanciyar ta, ta barshi anan tsaye in the pitch darkness of his own room…