Free chapter · Read without an account
Page2
Duk diri dirin da Ummul take yi me nafef bai gajiya ba,dan shi duk zatonsa wasu manyan kudi zata dauko ta bashi, har wani sosa hannunsa yake dan yasan tabbas yau akwai sa a agareshi, Ummul kuwa zuciyarta cike take da barazanar fashewa da wannan tsananin abun kunya da yake shirin faruwa da ita,kamar daga sama ta tsinkayi murya ana cewa a" Hajiya Barka da zuwa ya kuma na ganki a dan sahu ina driver din naki ? Bai tsaya sauraren amsarta ba,ya debo kudin da bai tsaya irgasu ba ya mikawa me nafef din yana cewa "ungo kudinka wuce ka tafi"cikin sauri me nafef yaja yana washe baki tare da zuba godiya dan a yadda yaji nauyin kuɗin zasu kai wajen 5k, tuni saurayin nan ya shiga mamaki wanda hakan yasa yayi saurin dakatar da me nafef din tare da bashi kudi masu yawa ya sauka yana cewa "nima anan zan sauka karbi ka kara da wannan,"yau ranar tawa ce me nafef ta fada yana bawa mashin dinsa wuta.
Kallon mamaki kawai Ummul take bin saurayin da shi, kafin ta bude baki zata yi magana yayi saurin tare ta da cewa, "dalla rufe mana baki da kika samu ma yau an yi mana sallama na fidda ki shan kunya, tun daga majalisa na hango yadda kike ta zabga gumi kina laluben jakar da babu ko sisi saitarin karya a ciki"amma yaya mufty ina ka samu wannan kudin da yawa haka,hala ma kudin sallamar ne ka haɗa ka bawa me nafef gaba ɗaya?"hakan ma zata iya kasancewa amma dai ba duka na bashi ba,saboda yau me gida me gidansa ya lullube shi da abin arziki shine muma ya bamu wani abu,amma ba dan haka ba yau da wata tasha kunya a titi a gaban samarin layi"ya fada yana tuntsurewa da dariya,gaskiya yaya baka kyauta min ba a maimakon ka bashi dubu biyu amma sai ka kwashe har 5k ka bashi, ai ko tsiren na kan tukuba ma ci mu dan rage zafi"daidai suka karaso kofar gidansu da yake dan madaidaici irin na gargajiya me dakuna biyu a zauren gidan.turuss suka yi gaba dayansu saboda ganin koshashshen saurayin da tun fara zamansa kofar gidan nasu ba zasu tantance kamanninsa ba,sai dai yanayin zatinsa da tsayinsa da yake nuna jarumtarsa a nazarce,"muje mana yaya mufty ya fada bayan ya dauke idonsa daga kan mutumin,kasa wucewa Ummul ta yi tare da cewa "yaya yau fa sai na yiwa mutumin nan magana akan me zai zo kofar gidan mu ya dasa sana a ba tare da ya nemi izinin masu gidan ba,ko yana tunanin haya muke yi ne?"ke dalla muje yar neman magana ina ruwanki kika sani ko ya gayawa baffa"ta ina zai ga baffan da ba kwana yake a gida ba?"kafin mufty ya bata amsa ya ji an riko rigarsa ta baya ana cewa "yauwa zo ka biya Ni kudin hayar wayar da ka yi, dan wulakanci saboda bukatarka ta biya da ka tashi sai ka aiko min da wayar ba tare da kudin ba"cikin sauri mufty ya janyo matashin suka shige gidansu yana cewa haba abokina ya zaka yarfani a gaban wannan me gyaran takalmin da yake dauka ta wani kusa".kaga Ni kawai bani kudi na na ware bana son surutu"dubu daya mufty ya zaro a cikin aljihunsa ya manna masa a hannunsa yana cewa "nima ita kenan ta ragen ka rabani da ita ka ji dadi"tunda ka bani ai shike nan"jamilu ya fada yana fita daga zauren gidan,sai da ya kalli gentle me gyaran takalmi ya ce"an jima zan aiko takalmina ka wanke min"kamar yadda ya saba da rashin yin doguwar magana yanzu ma jinjinawa Jamil kai kawai yayi, yana ci gaba da abinda yake kansa akasa rabin fuskarsa rufe da pasingcap ba ka hango komai sai kasumbarsa kwantacciya wadda ta saje da bakin fuskarsa da yake wani shainin kamar an shafa masa.
Ummul tana shiga gidan ta samu yaya Ali ya dage yana ta faman gugar riga daya da wando,ummi kuma na yan shige da fice a tsakar gidan da dan madaidaicin kitching dinsu wanda ya nuna alamar sanwar dare ta dora,duban Ummul din ta yi kana ta ce"ke kuma yau haka da yammar nan ko kunyi fadan ne?"zama ta yi gefen tabarmar da ya'ali yake guga tana cewa "ke ma ai kin san halin wannan zezeen in dai bata bata min rai ba ba jin dadi take ba,yau saura ka[10/15, 9:51 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*