Free chapter · Read without an account

Page5

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Kafin kace kobo gida ya turnuke da hayakin barkono me dan karan yaji,gashi dama barkonon tsidugune me irin yajin nan,cikin sauri ya Ali ya kama hannun ummi ya Kaita daki ya rufo,baka jin komai a gidan sai tari da atishawa,idanun baba batula gaba daya ya rufe laluben hanya take ta bar gidan amma hakan ya gagara dan duk inda ta nufa sai taji ba hanya ba ce,cikin azabar da ta ishe ta ta fara cewa"dan Allah ikrama ki yi hakuri ki saita min hanya kar ki kashe gawar da bata ki ba"Ummul me zata yi ba dariya ba,duk da cewa itama tari da yaji bai barta ba, amma bata damu ba saboda burinta bai wuce taga baba batula ta shiga taitayinta ba" Wallahi babu inda zan nuna miki ai lokacin da kika shigo babu wanda ya nuna miki hanya,cewar Ummul tana ficewa daga gidan saboda ta samu iskar shaka,su Musa kuwa ai tun farkon al'amarin yayi takansa, ya Ali kuwa da ya muftahu suma tuni sun fice daga gidan suna kyalkyala dariyar mugunta,daga karshe dai baba talatu danta Anas da tuni yayi kakansa shine ya dawo ya fito da ita daga gidan,idanun nan sun yi luhu luhu makogaranta kuwa babu abinda yake sai makakin yaji,suna fitowa Ummul ta kallesu ta shekar da dariya tare da cewa idan Allah ya kaimu da safe ku dawo karbar kayan ku"da sauri Anas ya ce"a'a Ummul Ni dai na yafe"harara ta watsa masa tare da cewa dalla rufe mana baki ban hanaka fadar sunana haka gatsal ba, koda kwana daya na girmeka ai dai na girmeka balle kwana dai dai har bakwai na baka"shi dai Anas bai kulata ba ya ci gaba da jan babarsa da ta zama makauniyar karfi da yaji.

A hankali ta waiga inda yake tattara kayansa na gyaran da ya gama, kallonsa ta tsaya tana yi, duk da cewa yana kallonta kuma yana jin idanunta akansa,amma hakan baisa ya dago ya kaleta ba,"ina son za a gyara min takalmina"ta fada tana ware kunnuwanta dan sauraron abinda zai ce,amma ga dinbin takaicinta sai kawai gani ta yi ya jinjina kansa tare da cewa "ok sai kin kawo" can karshen magoransa ya yi maganar kai idan baka kasance me tsananin ji ba to ba zaka san me ya fada ba bare ka tantance Muryar da aka yi maganar da ita,wai kai baka magana ne?kuma a haka kake rayuwarka?baka jin bakinka yana maka nauyi saboda rashin magana?anya kai ba kurma ba ne kayi basaja dan kar ka rasa me aurenka?"duk abinda take fada babu wata alama da ya nuna cewa yana sauraren ta,ji ta yi wani uban haushi ya kuma kamata take taji tsanarsa me girma a ranta,wucewa ta yi tana kunkuni da cewa"karyar banza da wofi mutum shi ba kowan kowa ba sai tsananin girman kai,ai dai da ba a san asalin balbela ba sai a ce daga Maka ta zo",wani uban tsalle ta yi tare da komawa gefe saboda saukar tsimagiyar da ta ji a jikinta ba tare da zato ko tsammani ba.

Kuka tasa tana sosa bayanta inda tsumagiyar ta sauka,Ummi kuwa kanta ta kuma yi zata kuma kai mata dukan, hakan yasa ta juya ta fita da gudu tana kuka, daidai lokacin gentle ya kawo kayansa na gyara cikin zauren saboda anan yake ajiyewa kullum,bai ankara da ita ba kawai jinta yayi a bayansa ta makale shi tana ihun kukan a taimaka mata,da wani irin speed ya runtse idanunsa saboda yadda gangar jikinta ta hade da bayansa,"wayyo Ummi zata fasa min fata ku taimaka min, ummi yanzu fa na wuce duka dan Allah ki daina dukana"a hankali yasa dogayen hannayensa ya banbareta daga jikinsa, sannan ya kama hannunta suka karasa cikin gidan, tana ganin ummin a tsaye a bakin hanya ta yi saurin komawa bayansa tare da cukwikwiye rigarsa jikinta har wani karkarwa yake saboda tsananin tsoron dukan,Ummi ta ce"ai ke Ummul ba za ki wuce duka ba dan ina tunanin a gidan mijinki ma sai naje na bugeki saboda rashin jinku daga ke har masu tayakin"a hankali gentle ya ce "ummi a yi hakuri dai kin san akwai Kuruciya"tsaki Ummi ta yi tare da cewa jeka abinka kaji?"kara rikesa Ummul ikram ta yi tana hawaye,ummi ta ce ba zaki sake shi ba ko sai na kuma zuba miki?"da sauri ta sake shi tare da yin daki da gudu,tana jin ummi na ci gaba da mita har bayan fitar gentle, su ma su alin ba su tsira ba dan Ita dai Ummul bata san ya su ka kare ba har bacci ya dauketa.

Ji ta yi ummi na tashinta, daƙyar ta iya motsawa,kana cikin magagin bacci ta ce"waye ne"ummi ta ce "nice nan ki tashi ki Sallah"ummi har asuba ta yi ne?"a a bata yi ba amma dai ki tashi ki yi sallar dare"dan Allah ummi ki rabu dani sai gobe kin ga gobe zan fita da wuri"dole fa sai kin tashi ikram, kina nufin a haka kike so Allah ya baki arzikin da kike ta faman karya da na wasu?"da sauri ta tashi zaune tare da mutsike idanunta tana cewa "kuma fa haka ne Ummi"ummi ta ce yauwa ko kefa idan kika yi sallar sai ki roko Allah ya baki arziki me albarka da kuma alheri"tashi ta yi ta nufi hanyar fita tana cewa a'a ummi me albarkar da amma alheri ai na gama rokarsa kuma Allah ya amsa",girgiza kai kawai ummi ta yi tare da fara nata sallar", wannan shine babbar koyarwar da iyayensu su kayi musu shi yasa a'a kome nasu koda karyar za su yi su kan sa Allah cikin lamarinsu,dan kuwa tabbas iyayensu sun yi musu babban gata saboda sun basu ilmin addini sosai da sosai.

******

Washe gari da kyar ummi ta tashi Ummul daga bacci saboda kwanan sallar da suka yi.cikin gaggawa ta Gama shiryawa,ta sanya wata lafiyayyar atamfa me shegen tsada cikin irin kayan da momy take bata idan ta faki idon zezee, dan zezee bata son bawa Ummul kaya, acewarta koda bata son kayan muddin Ummul ta saka su sai ta ji sha'awar kayan da jin inama a ce kirar Ummul kirarta ce,dan sosai suke wa Ummul kyau fiye da ita, idan ta sanya kaya kamar dan ita aka yi su.kasancewar doguwar riga ce yasa ta zauna ajikinta daram, jeccyveil ta ɗora kana ta dauki jakarta da kudin ta fito tana yiwa ummi sallama.

Bata sa a ranta zata gansa ba saboda tasan ta yo sammakon fitowa, shi yasa koda bata samesa ba bata damu ba, sai dai ta watsawa mazauninsa harara tana mai takaicin ganin hawayenta da yayi a daren jiya ko ta ce kukanta da bata cika son dan adawa ya gani ba.

Kai tsaye wellcare me dan sahu ya ajiyeta,lokacin karfe tara na safe ne,shi yasa babu wasu yawan jama'a a wajen,shiga ta yi wajen tana wani taku daidaya kai kace diyar shugaban kasa ce,su kansu security's din wajen cikin hanzari suka bude mata kofa ta wuce, dan kuwa Ummul ikram din kalar masu kuɗince, idan ba karyarta ta shiryo maka ba ba zaka taba fahimtar ko wacece ba, Kwando ta dauka ta fara zagaye wajen tana kallon komai sama sama a haka ta fara diban abinda take ganin ya dace da abinda take son shiryawa a kitchen ɗin, saboda tsananin son baza capacity irin na Ummul ko ficika bata rage ba dubu darin nan tas ta karar da ita a wajen wani abun ma bata san amfaninsa ba amma haka ta dinga duba dan duk kawai a ga ta yi siyayya da yawa,sai dai kuma ana buga lissafi akan ga kudi sun haura dubu dari, kudinta ya kama dubu dari da ashirin, zubawa matar ido Ikram ta yi tana rasa abin cewa, dan kuwa tabbas ta girgiza ga shi layi ake bi wani ne a bayanta yana jiranta,cikin basarwa ta sa hannu a cikin jakarta ta zaro bondle na dubu dari ta mikawa matar tare da kuma maida hannunta kamar zata dauko wani kudin,cikin yar damuwar da bata son nunawa ace ba ta kai ba,ta dubi matar tare da cewa"sorry ina tunanin an zare min bondle biyu na 100k"zaro ido matar ta yi tare da cewa "kai Madam amma ba a nan ba ko?"cikin yar fusata Ummul ta ce "to da a gidan ubanwa kina nufin zan yi miki karya ne akan abinda kina kallona kin san na fi karfinsa?"sorry Madam kawai ina mamaki ne"ki ajiye mamakinki waje daya, ki saurareni"ok ma matar ta fada cikin maida hankalinta kan Ummul ɗin,yayin da Ummul ta fara magana da cewa, kudi kawai na dauko da zan fito ban dauko waya ba kuma ban dauko atm ba, dan haka ki kwashe kayan 20k ki bar na iya kudin da na baki"ok Madam"matar ta fada tana rage kayan, amma saboda kar na bayanta da har wasu sun canja gun biya su fahimci wani abu sai ta yi saurin karbar kayan da dama ba sanin amfaninsu ta yi ba tana cewa ajiye wannan idan kin zuba a leda bari na je na maida su inda suke"daga haka bata jira kome ba ta kwashe kayan ta mayar kwandon kana ta kara gaba ba tare da ko juyawa ta yi ba.

A ankare ta mayar da kayan kana ta dawo ta dauki nata bayan ta karbi rasit, ta yi gaba abinta hankali kwance ta fidda kanta ba tare da ji kunya ba,tana fitowa harabar wajen ta ware manyan idanunta akan dan kara dan karan motocin da suka yi jere reras a jarabawar wajen gaba dayansu iri daya sai guda daya da ta kasance ta musamman kuma fara kal a cikin ragowar motocin,burki Ummul Imram ta yi tana mai jan lahaula,kafin ta taka a hankali ta karasa jikin farar da duk tafi daukar hankalinta,zagaye motar ta shiga yi dan gaba daya ma ta manta a inda take,a bayan motar taga an rubuta Dr BILAL ƊAN ITOPIA. 1.hangame baki ta yi tare da jan numfashi kafin ta ambaci masha Allahu lakuwata illabillah" a hankali ta dinga bin bayan motocin tana kallon sunann guda daya sai canjin nombobi har zuwa nomber ta 10,jinjina kai ta yi kana ta koma wajen farar motar ta jingina a jikinta tana cewa wato dai yau ta tabbata Ni din itopias family ce,wayarta ta zaro a haka tana cewa ai dole na zuba salfi a jikin sunan motar nan ko dan na ci gaba da zuba capacity na akan itopias family wata rana koda an ƙaryata ni ina da sheda"daga haka ta fara zuba selfi ajikin motocinnan sai da ta gama sannan ta dawo kan ta tsakiyar ta cigaba da yi, kasancewar wayar tana yin pic shi yasa bata samu matsala ba,wani me sai da apple a wajen ta kira ta bashi wayar ya dauke ta sosai ta yadda za a ke ganinta a tsakiyar motocin, sai da ta gama tsaf ta karbi wayarta ta mayar jaka, tare da sunkuyawa dan ɗaukar ledar siyayyarta,dagowar da zata yi taga an bude bakaken motocin gaba daya a lokaci daya, wasu dirka dirkan gerd ne masu kwanji jikinsu sanye da bakaken cot fuskar nan a hade babu alamun rahma, wa innahu sulaimanu,kuke ganinmu bamu muke ganinku ba yau garin neman capacity na jawowa kaina pacacity, yau Ummul ta shiga hannun yan sari"da sauri taga sun karasa gaban farar motar sun wani kame kamar sabbin gumaka, sai kuma aka bude farar motar wani gerd din ya kuma fitowa tare da bude bayan motar ta saitin da Ummul take tsaye kamar andasata baki bude hanci bude, bata ankara ba sai jin wani uban kamshin da duk zagayenta da rakiyar gidan yan gayun da takewa zeezee bata taɓa shaƙar makamancin sa ba,bude ido ta kuma yi tana kallon kafar da aka zuro waje sanye cikin takalmin da bata san me zata ce akansa ba,dan babu abinda ta fahimta sai kyalli da shekin da yake,abin mamaki koda aka zuro kafar ba a fito ba sai da aka ɗauki kusan mintuna biyu kana ya zuro gangar jikinsa gaba daya cikin wani irin dan zafin nama me hade da salon burgewa.

Idan na ce muku numfashin Ummul ikram bai yi balaguron wuccin gadi ba to na muku karya,tabbas Ummul ikram ta shiga shock da ganin wannan bawan Allah,tunda take a duniya ko a labari bata taba ganin irinsa ba, Ummul na can sake da baki har ya wuce bata sani ba,sai juyawa ta yi taga wayam,sai a lokacin ta tuna da kashedin momy hakan yasa ta kwashi kayanta ta bar gurin tana mai mamakin wannan mutumin,mutum sai kace shi yayi kansa duk da cewa kuwa ba wai fari ne tas ba,amma kalarsa ta asalin yan itopian dinne,ga wani irin kwarjini da tsananin muskilanci fuskar nan akwai kyau amma babu annuri ko kadan sai na ibada, dan goshinsa har da tabon sallah,da wannan tunanin ta tare dan sahu.

Lokacin da ta iso gidan baffanta baya nan,malam isa da suke duty tare ya canjesa ahi kuma ya koma gida sai bayan kwana uku zai kuma dawowa,hakan yasa ta wuce ba tare da dari dari ba,da momy ta hadu a falo tana ta tattaba wayarta alamun kira zata yi,tana ganin Ummul ta ce yauwa alhamdulillah ina kika tsaya ne haka har gashi bakon ya kusa karasowa?"Ummul Imran ta ce momy gosulo ne"to maza muje dan Allah ga baba atine can ta taimaka miki ku yi komai cikin tsafta saboda ba karamin mutum ne zai zo gidan nan ba,na gaya miki ubansa uban gidan abban zeze kuma ya nema masa auren zezee ne saboda yarda da amincin da ke tsakaninsu,kuma yau din nan zasu fara ganin juna,kinga dole hankalinmu ya tashi dan bamu san makomarmu ba"tabe baki Ummul ta yi a ranta tana cewa "ko ina ruwana da wannan zan can kuma oho?"wucewa ta yi daki ta cire kayanta ta saka na aiki, sannan ta fito ta nufi kitchen din dan fara girkin tun kafin waccan yar bala in ta fito.

*****

Kasancewar Ummul akwai himma yasa cikin kankanin lokaci gidan ya hade da kamshin girkinta wanda yake dauke da spices din meenat cuisine Corry powder, Wanda shine sirrin girkin Ummul dan ko a mafarki aka ce ta yi girki to tabbas sai ta nemo meenat cuisine spices and Corry powder,hadadden falon da abban zeze ke karbar manyan bakinsa na musamman anan Ummul ta jere delicious food's din cikin tsari da tsafta, daga nan ta tafi wajen gimbiyar da har yanzu bata gama shiryawa ba, dan duk kayan da ta sanya da ta tuna da Ummul sai taga bata yi kyau ba ta cire ta kuma canjawa,a haka Ummul ta yi sallama dakin,wata uwar tsawa ta daka mata tare da nuna mata hanya akan ta fice,juyawa Ummul ta yi ta fita a ranta tana cewa matar nan ashe zaki mutu da bakin ciki na".

Tana fitowa suka jiyo alamun bude gate da kuma shigowar motoci harabar gidan,da sauri Ummul ta leka ta window dan ganin me babbar sa ar da zai dauke musu zezee,dafe kirjinta ta yi tare da foddo manyan idanunta waje tana mai bin motocin da kallo.....✍️

Wai yaya ne😂dan ta tsige min gashi na muguwa kawai shi yasa na yi taho wata sai dai su shafa s[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHANw²

ƳAR GIDAN YARBAWA

WeMATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol