Free chapter · Read without an account

Pg6

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

.......Muryar momy ce sa ta saurin ja da baya tana zare ido,zuciyarta cike da fargaba, momy ta ce"me kike yi anan maza kije ki shirya saboda idan ya ɗan huta zaki je ki yi saven dinsa"ware ido Ummul ta kuma cike da mamaki,ta bude baki tana kallon momyn kafin ta magantu da cewa"momy mijin da zata aura ne fa kuma nice zan yi saven dinsa?"ba tare da momyn ta jiyo ba, ta ce"to ai ikram kin san halin mutuniyar ta ki babu abinda ta iya,Ni Wallahi har na fara fargaba ma saboda shi wannan din ba irin kowa ba ne, dan a yadda muka samu labarin dan tarihinsa daga bakin abban zezee ba komai ne yake burgesa ba, sannan yana tsirfa da ka ido ji kai shifa ko wannan gard din da suke binsa ba a son ransa ba ne ,shi yasa babu wanda yasan shi a duniya a matsayin babban yaron ALHAJI AHMED ƊAN ITOPIA hatta da fuskarsa ba kowa ne ya sani ba,shi yasa nake ganin lokaci yayi da zezee zata sauya tun kafin ta jawowa mahaifinta babbar asara"asara kuma?"Ummul ta fada ba tare da tana da yakinin samun amsar tambayar ta ba,ile kuwa hasashenta ya zama gaskiya dan kuwa momy murmushi kawai ta yi tare da cewa "wannan ba huruminki ba ne"yaraf Ummul Ikram ta zauna saman kujerar da ta fi kusanci da ita zuciyarsa na ta jujjuya maganganun momy,shike nan ita kam ta tabbatar ba ita ba arziki tun da ga shi tana zaune zezee zata aure dan gidan Itopian da take ta karya da su,ke nan sabon bauta da wulakanci zasu karu,jinjina kai ta yi tare da cewa Allah babu ruwansa gashi dai yasan zezee ubanta na da arziki amma da ya tashi kawo mata miji sai ya kuma kawo mata wanda ya ninka mahaifinta sau dubu,to amma a yadda aka fadi halinsa tana ganin kamar Allah ne ya Turi shi ɗan ya zama sanadin gyara zezee, to Ni kuma kowa ye zai zama sanadin gyaruwata?"ta fada tana shigewa dakinta dan sanya kaya,koda ta sanya kayanta tsayuwa ta yi gaban mirror tana kallon kanta,take kuma ta saki murmusgi me haɗi da dariya tana cewa "nima fa Allah yana sona gashi ya bani abinda zezee bata da shi har ma take bakin ciki da hakan,to amma me yasa Ni ban ji bakin ciki da arzikin da suke da shi ba?me yasa nake farin ciki da yadda Allah ya barni?duk da bakya bakin ciki amma ai kina karya"wata zuciyarsa ta fada mata,tura baki ta yi kamar wadda take magana da wani tana cewa itama zezee gashi Allah ya kawo wanda zai sanadin shiryuwarta nima Allah zai bani wanda zai sanadin daina karyar kuma ai karyar kawai nake yi saboda rayuwar masu kuɗi tana burgeni dan haka wata rana zan daina, Allah ya shiryemu nida yan uwana",ta kare maganar tana daure dogon gashinta da ya warware fuskarta dauke da murmushin da yake nuni da cewa bata da wata damuwa cikin ranta.

A can bangaren zezee kuwa dakyar ta yadda momy ta zabar mata kaya ta sanya ta gyara mata fuskar ,duk da cewa ta yi kyau sosai amma bata ga hakan ba kuma bata gode Allah ba,dan sai da momy ta yi mata jan ido sannan ta hakura ta fita zuwa hadadden falon bakin abbanta, a yangan ce take taku kamar bata son taka kasar a haka ta shigo dakin ba tare da ko sallama ta yi ba,cikin yanga ta nemi waje ta zauna, duk da cewa ta so bada kanta ta hanyar kure sa da kallo da kuma shiga firgicin ganin irin mijin da ake kokarin aura mata,tabbas in dai har ba mafarki take ba wannan gwarzon mazan dake hakimce a saman kujera kamar basaraken kasar labarawa shi zata aura to tabbas yau Allah ya biyata daga tawayar da take ganin yayi mata.bata san ta yi nisa da kallonsa da tunanin da take ba har sai da ta ji saukar wata irin murya me cike da kamala da nutsuwa tare da wani amon sauti me shiga jiki da ƙwaƙwalwa tana cewa "ke baki iya sallama ba sai kallon mutane ko?"firgigit ta yi tare da diriricewa kafin ta yi kokarin saita kanta wajen furta cewa "ka yi hakuri amma karka ga lefin duk macen da ta kasa sarrafa kwakwalwarta da tunaninta lokacin da ta yi arba da kai,dan haka ka yi min uzuri na rashin sallama domin ganin ka shi ya tafi da duk wani imani na"dan tsuka yayi kadan saboda yadda zantukan nata suka gundureshi, dan bude idanunsa da suke a lumshe yayi tare da jefa kwayar farar idanunsa a kanta yana kallonta, sai dai fa kallon ba na komai ba ne sai na nazarta wanda a take ya gano wasu halaye daga gareta,ba laifi bata da muni sai dai kuma shi ba wannan ne ya damesa ba,hakan yasa ya dauke kansa domin shi bai ma iya kallon kai tsaye ga duk abinda bai damu da shi ba,tunda ya maida kansa ya kwantar sakan jikin karin kujerar ya lumshe idanunsa bai kuma cewa komai ba,numfashi zezee tana tana jin wani irin kaunarsa, sai dai ga dukkan alamu zata sha wahala da mutumin nan dan da ganinsa a juye yake,to amma dai zata jure in dai zata samu shiga gidansa ko da bata kai cikin zuciyarsa ba,katse shirun ta yi da cewa"baka ce komai ba bayan an turo ka ne dan mu ga juna mu daidaita kanmu,Ni dai ka yi min dari bisa dari fiye da zaton mai zato".

Yadda kasan ba da mutum take magana ba haka take kallonsa, sai can bayan da har ta fidda tsamannin cewarsa, ta kuma tsinkayar muryarsa a tausashe a kuma nutse babu hayani ko karfin sauti,yana cewa is ok idan na yi miki daga gareni kuma ba hurumin ki bane",zuba masa ido ta yi tana tunanin ta yadda zata shiga zuciyar Wannan handsome din, Dan irin su sai suna matukar don mace ne kawai zata ji dadin zama aure da su,fuskarta ta shan shafa tana ji a ranta wata kila da tana da kyau kamar na Ummul ikram wata kila ya so ta fiye da yadda take zato,sallamar Ummul Ikram ce ta katse mata tunaninta tare da saurin waigawa, sai kuma ta maida dubanta kanta B A din sai taga yana nan a yadda yake ko motsi bata jin yayi,harara ta watsawa Ummul din tana tambayar ta da ido me tazo yi?"kai tsaye Ummul ta nufi wajen abincin ta fara kawosu gaban B.A din tana jerawa,sai da ta gama sannan ta kalli zezee din ta ce"momy ce ta ce naso na yi saven ɗinku lunch"kawar da kanta ta yi dan tasan ko ta kori ikram din ita babu abinda zata iya yi, a nutse ikram din ta dubesa kana ta ce?" Me Zaka ci"?a harzuke zezee ta yunkuro tana cewa "ke wai wace irin jakar yarinya ce? abinda zai ci din ma ke zaki tambaye sa meye gaminku da shi?ko kina tunanin dan kina da kyau kin gama cike gurbin da na miji zai so ki?"cikin kunkuni Ummul ikram ta ce"Ni ban ce ina son shi ba kuma ba zan taba fada ba, sannan kuma kudi ba shine so ba kamar yadda kyau ba shi ne so ba dan haka idan ba a soni dan kyau na ba ke ma bai zama dole a so ki dan kudinki ba"daga haka ta zuba duk abinda yazo ranta ta mike ta bar fakon ba tare da ta kuma kallon inda suke ba,kamar daga sama ta ji maganarsa yana cewa ,a haka kike treating na kasa dake?"shiru ta yi yana kokawa da abinda ya tsaya mata na maganganun Ummul ikram,wai me yasa yarinyar nan bata shakkar gaya mata magana ne?"ta tambayi kanta ba tare da ta lalubo amsar ba ta kalli Bilal din a marairaice tana cewa, baka ga yadda ta rainani ba?sam yarinyar nan bata da mutunci, idan bata raga min saboda girman ta da na yi ba ai ta raga min saboda aikin da take a karkashina?"bai zama dole ba tunda kin yada girman"ya fada kamar bashi yayi maganar ba, ganin ba zai goyi bayanta ba yasa ta yi shiru tare da ɗaukar plet din da Ummul ta shake da lafiyayyar sakwara da miyan egushi ta ji uban naman kaza da ganda ko kalla ka yi a ido sai ka hadiyi miyau,dakatar da ita yayi daga shirin ɗora masa akan karamin Centre table da take yi,hakan yasa ta dakata tana kallonsa, gani ta yi ya sauko kasa daga kan kujerar tare da sanya hannunsa cikin ruwan da Ummul ta ajiye na wanke hannu,karba yayi ya sa a gabansa tare da tsoma hannunsa cikin sakwarar,tsayawa kawai zezee ta yi tana kallonsa cike da dinbin mamaki, tunda Ita dai bata taɓa zaton zai ci abincin kai tsaye ba ma bare akai ga abubuwan mamakin da ya gabatar kafin ya fara cin abincin,a saninta dai yana daya daga cikin halinsa baya cin abincin kowa sai na mahaifiyarsa sannan yana da matukar tsantsani wanda shine dalilin da yasa bai sakin jikinsa a ko ina,amma sai gashi a karon farko na haduwarsu ya ƙaryata hakan duba da yadda yake cin abincin cikin nutsuwa kamar wanda dama ya saba da texting din abincin.

"Yana daya daga abinda yake sani jin tsanar mutum wato yawan kallo dan haka ki kiyaye"cikin mutuwar jiki ta koma ta zauna tana kawar da kanta daga garesa.

A bangaren Ummul ikram kuwa tana fita bata tsaya a ko ina ba sai a harabar gidan inda gard dinsa suke tsaye jikin motocinsu kamar an dasa su ko kwakwakran motsi ba wanda yake yi,ba tare da ta damu da su ba ta gyara tsayuwarta ta shiga kafta selfi ,hatta da gard din sai da ta fito da su cikin hotunan,tana shirin barin wajen bayan ta gama selfinta ta ji ana hon, juyawa ta yi tana kallon baba me gadi da ya bude karamar kofa dan duba wanda zai shigo saboda motocin Bilal Ahmad Dan itopia sun cika harabar gidan, hakan yasa Ummul ta tsaya tana jiran ganin me hong din,baba me gadi ko da ya leka sai yaga wata matashiyar budurwa cikin wata kyakkyawar mota, kallo daya zaka yi mata kasan cewa ita din yar gidan wani kusa ce a gwamnati,yana kokarin karasawa inda take sai yaga ta fito dan haka sai ya koma ciki wajen aikinsa yana jiran karasowarta,ganin macece kuma.matashiya ta shigo gidan yasa Ummul saurin karasawa bakin gate din , daidai lokacin da suka gama gaisawa da baba me gadi,tana tambayarsa ko nan ne gidansu muftahu?"dan jim baba me gadi yayi yana tunanin waye muftahu tunda shi a iya saninsa gidan nan mace daya ce tal da ake ji da ita uwa tsoka daya a miya a gidan,ganin yana tunani yasa budurwar ta bude wayarta tare da nuno masa hoton wanda take neman,sai dai kafin ya karba Ummul ta wafce wayar tana kallon hoton yaya mufty akan allon wayar kai kace dan gidan masu dashi ne saboda yadda ya baza capacity a hoton abinka da me kyau, washe baki Ummul ta yi bayan ta gama kallon hoton tare da mikawa budurwar wayar ta tana cewa ey nan gidan yayansa ne dan yanzu ma yaya mufty din yazo kinga ma motocin sa da gard dinsa a tsaye, sai dai ba zaki samu ganinsa ba saboda suna miting da wasu turawa ne a ciki bana tunanin zai fito da wuri"tuni fuskar budurwar ta nuna farinciki dan sosai ta yadda da Ummul dan ta gano kamanninsu da muftahun sosai,yauwa amma ke kanwarsa ce ko?"budurwar ta tambayi ikram fuskarta a sake"ey Ni kanwarsu ce Ni ka dai ce mace a cikinsu babban yayanmu shine BILAL AHMED ƊAN ITOPIA shi kuma muftahu Ahmad Dan itofiya Ni kuma Ummul ikram Ahmad Dan itopia"ayya uwar karama ke nan amma shi yayanki bai taba gaya min cewa shi ɗan gidan dan itopia ba ne?"dan sosa kai Ummul ikram ta yi tare da cewa "ai dake kin san ba sosai muke son fito da kanmu ba saboda duniyar ba gaskiya da an sanmu da yanzu ba wannan labarin ake yi ba,da tuni yan kiddnappin sun samu babbar sana a"budurwar da Ummul ta gama tafiya da ita saboda ganinta take wata yar cut baby da ita gwanin sha'awa,ta muka mata hannu tare da cewa nice to meet you and my name is farida wakili",mika mata hannun ta yi itama tana cewa "nice to meet u too"daga nan ta juya tana cewa amma dan Allah da ya fito ki fada masa nazo nemansa amma an jima idan yayi free mu hadu Tahir restored"to baki da damuwa zan gaya masa "cewar Ummul tana raka ta har zuwa bakin motarta,sai da taga ta shiga sannan ta ce amma baki da nomber ne?"dan jim Farida ta yi, kana ta ce wayarsa bata shiga amma shine ma dalilin biyosa gida"daga haka tana motar ta tafi Ummul kuma ta koma gidan, shi dai baba me fadi Binta da kallo kawai yake yana tarkake Ubangiji a ransa saboda tunda yake bai taba ganin wanda ya iya karya irin wannan yarinyar ba.

Tana gab da shiga falon ta ga sun fito daga ɓangaren bakin,yana gaba tana binsa a baya, duk da yadda take ta kokarin ganin ta daidaita dashi sun jera, sai dai hakan ya gagara a wajen zezee wanda hakan ya dinga bata mamaki dan a ido dai ba zaka taba cewa yana sauri ba kuma ba zaka ce yana yanga ba,sai dai kawai tsantsan natsuwa da kamewa hadi da dan hanzari irin na jaruman maza,har zata shige sai kuma ta fasa ta nufesu dan komawa ta dauko kayan abincin,ko kallo su ba ta yi ta wucewarta, tana shiga falon ta ga yadda aka ci abincin sosai dan kamar ma an dada akan wanda ta zuba,sai ta yi tunanin ko zezee ce ta ci to amma ganin plet daya aka bata yasa ta shiga shakku,ganin zata batawa kanta lokaci akan abinda bai shafeta ba yasa ta tsuguna ta fara tattare kwanunkan da fulasan, tana daga babban tiren taga bodles din dolas sun fado,a fitgice ta mike tana kallon damin kudin wanda ko a mafarki ba ta taɓa ganinsu ba,cikin sauri ta dauka ta maida su gefe sai dai tunanin da ta yi na anya ko ba shi ne ya manta ba yasa ta ajiye babban tiren tare da ɗaukar kudin ta fita da gudu.

Daidai yana shiga motarsa gard dinsa na kokarin rufewa zezee kuma na tsaye tana wani lanlangabewa akan sai ya gaya mata yaushe zai dawo, tunda ya hanata lambar wayarsa,tunda a cewarsa lambarsa bata shiga wayoiin mata, ganin haka yasa Ummul ta kara karfin gudunta tare da kwalla masa kira da "yallabai yallabai"gaba daya sai hankalinsu ya koma kanta duk da cewa bai fito daga motar ba amma kofar a bude take kuma ƙafarsa daya tana waje,cikin haki ta karaso tana maida numfashinta sai dai tun kafin ta ce komai zezee ta dauke ta da wani matsiyacin mari wanda har sai da Ummul ikram taga tar tsatsin wuta na gifta mata, sannan ta dora da nunata da yatsa tana cewa "ke dai idan mayyace sai dai kici kanki wai ke Ummul kasheni kike son yi? idan ba kasheni zaki yi ba ta yaya ina kokarin kafa soyayyata ke kuma kina kokarin rusata ta hanyar kawo kanki ga masoyina?yanzu da kika taho kina masa girgiza kina tunanin zaki jawo hankalinsa ne sabida kin ga kyanki bai ɗaɗa shi da kasa ba? To wallahi a hir dinki kuma Ni nafi karfin wanda ya so Ni ya so ki,kuma.har abada baza ki taba cika burinki akaina ba dan ko driven ba zaki samu ba barantana kuma matukin jirgin sama, haka zaki kare rayuwarki a bauta min kina ci gaba karya da fafa da gidanmu".

A fusace Ummul ikram ta mike daga durkushewar da ta yi tana kuka me taba zuciya, duk da cewa bata so gazawa ba sai dai fa ita indai kana son ganin hawayenta to ka taba jikinta dan bata da juriya akan wannan,kudin dake hannunta ta watsa a kasa tana ji kamar ta bi ta kansu ta tattaka sai dai ba zata iya hakan ba tunda tasan cewa almubazzaranci babu kyau ba ranta na kuma.ga su da bashi ne da su ba,sai kuma.gaba daya suka bi kudin da ido kafin a hankali ya dago kansa da lumsasssun idanunsa da suke cike da gajiya da kuma wani boyayyan al'amari yq zuba su kan Ummul ikram da take sheshshekar kuka........✍️

UMMUL IKRAM

BILAL

ZEZEE.

GENTLE.

ROMANCE

COMEDY'S

RICH

LIE

[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHANw²

ƳAR GIDAN YARBAWA

WeMATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol