Free chapter · Read without an account
Pg7
Duk da cewa zeze taga abinda ya kawo Ummul amma hakan bai sa ta daina jin zafin kasancewarta a gurin ba,dan wani irin kishin Ummul din take ji kamar ya kasheta,dakakkiyar muryarsa me cike da kamala da nutsuwa ta ji na yawo a tsakiyar kanta,"abinda kika yi ya nuna min cewa ba zaki taba Kasancewa a karkashina ba,domin Ni bana mu 'amala da mutane irinki wanda Basu san darajar dan adam ba,so dama mahaifina ne yasa Ni zuwa kuma nazo dan bani da hujjar kafa masa aka ro da dama na kin amincewa da zabinsa,amma yanzu ina da hujja me kyau akanki?"dan shiru yayi yana cije lebensa na kasa tare da shafo tattaunawar sumansa wanda yake nuna alamun cewa ya gaji da maganar,a tsanake ya kai dubansa ga Ummul da take shirin tserewa dan jin abinda yake fada ta san akanta zezee zata huce,amma sai ta ji maganarsa da ke fita a rarrabe cikin ginshira ya ce "ke dawo ki kwashe wannan da kika zube a nan"ya fada yana maida dubansa kan kudin da ta zubar a wajen,cikin saurin baki Ummul ta ce" me?Ni wai?"harara ya watsa mata yayinda zezee ta gama yin mutuwar tsaye a gurin kafafunta banda rawa babu abinda suke yi,da sauri Ummul Ikram ta girgiza kanta idanunta na cika da hawaye ta ce"Ni bana so baffa da ummi duka na zasu yi, dan dukan Ummi na jiya har yanzu bai dena min zafi ba"tana gama fadin haka ta kwasa da gudu ta yi cikin gidan.
Gard dinsa ne ya kwashe kudin ya mikawa zezee tare da cewa Madam zaki iya shiga mata da su ciki, dan idan oga yayi kyauta ba a dawo masa da ita"wani mugun kallo zezee ta bisa da shi ba tare da ta iya motsawa daga inda take ba,tana nan tsaye aka rufe motar da Bulal yake ciki a lokaci daya duka motocin suna tashi, baba me gadi tuni ya wangale musu gate, jiki na rawa ya karasa jikin motar da aka ya fito shi, damin kuɗi aka mika masa ya sa hannu ya karba jikinsa na rawa,daga nan suka fice da mugun gudu.
Dakyar zezee ta iya daga kafarta ta bar wajen ba tare da ta iya daukar kudin da suka sauka a jikinta ba,ganin haka yasa Ummul da ke kallonta ta window ta yi saurin fitowa ko kallon zezeen bata yi ba ta wuce ta kwashe kudin tana cewa "kudin marin da nasha aka biyani, to amma ya zan yi da kudin nan?"ta tambayi kanta, barin wajen ta yi tana cewa Gara na kaiwa baffa da ummi na fada musu gaskiya su zasu san yadda za a yi da kuɗin",karon da ta ci da zezee a bakin kofar falon shi ya sanyata cin burki,cikin wani irin huci da yake fitowa da gudu, zezee ta nuna Ummul da yatsa tare da cewa"ki gaya min wajen bokan da kika je dan kawai kiga bayana"da sauri yi ikram ta girgiza kanta tare da cewa Allah ya tareni da zuwa wajen boka, kuma Ni me ya dame me Ni da rayuwarki da har zan wani tsaya bata lokacina akanki,ke dai da nake gabanki sai kije ki ta yi tunda kinga zaki iya"hannu zezee ta kai zata kuma marinta a karo da na biyu, Ummul ta yi saurin rike hannunta tare da yarfar dashi tana cewa, wancan ma da kika yi shammatata kika yi amma da hakan bazata faru ba,dan ina muku aiki kuma biyana ba shi ne zai sa na zuba ido na zama jakarki ba,dan haka ki tsaya a iya zantukanki wanda wannan ba zan hanaki ba".
Kai wai me yake faruwa ne?"cewar momy tana fitowa daga corridon da zai kaika zuwa dakinta,kuka zezee ta saka tare da rungume momyn tana cewa"momy ya ce ba zai aure Ni ba saboda wannan banzar"inna lillahi wa inna ilaihi raji un"momy ta fada tana kallon Ummul da ta sunkuyar da kanta tana wasa da kudin hannunta,ta ce"ikram gaya min me ya faru?"momy ta tambaya cikin yanayin damuwar da ta bayyana a saman fuskarta.cikin nutsuwa Ummul ikram ta sanar da ita duk abinda ya faru, janye zezee ta yi daga jikinta tana cewa "Wallahi zezee muddin ubanki ya san cewa kina shirin janyo masa babbar asara da mugun halinki sai kinga ne baki dawo, dan duk wannan son da yake miki ba dubansa zai yi ba, dan ina da ya kini yafi son wannan auren ya tabbata akanki"daga haka ta wuce cikin sauri zuwa ɗakinta,itama Ummul wucewa ta yi nata dakin ta adana kudin sannan ta fito ta ci gaba da aiyukanta ba tare da tasan ya zezee ta kare da damuwar zuciyarta ba.
[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***
***
💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....