Free chapter · Read without an account

Pg8

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Ali ya tareshi da cewa "muftahu ba mafarki ka yi ba,arziki ne ya same mu har gida amma muna ji muna gani ana shirin maida shi"salati ummi ta saka yayin da baffa bai ce komai ba sai tattare kudin da yayi ya bar musu wajen ransa cike da takaicin ya'yan nasa, Ummul kuwa abin dariya ya bata sai da tayi mai isarta sannan ta dubi ummi ta ce"ummi wallahi kin yiwa su yaya ta leko ta koma da wannan shawarar ta ki"dakuwa ummi ta yi mata, sannan ta watsawa su alin harara tana cewa "Wallahi dai kun ji kunya tunda kuke jiran arziki ta wannan hanyar , wato kuna zaune zai zo ya same ku ko?"cikin share hawaye muftahu ya ce"ummi babu ta inda Allah ba ya ikonsa tunda gashi yayi amma kiri kiri kun maida Ni imar da Allah yayi mana"tashi ta yi kawai ta bar musu wajen dan tabbas idan ta ci gaba da zama tana jin sakarcin zantukansu zata iya zage karfinta ta jibgesu dan ba fin karfinta suka yi ba,ummi na barin wajen suka matso kusa da Ummul ikram suka kama kunnenta da karfi yayinda Ali yakai mata rankwashi a goshinta yana cewa "wallahi akanki zamu huce da ace kin fara samun mu da maganar nan duk da haka bata faru ba"dan Allah yaya ku yi hakuri kunnena zai tsinke"sakinta suka yi suna shurinta da kafa da gudu ta mike ta shige dakinsu tana cewa "Allah da na yi niyar yi muku wani abu amma tunda kuka ci zalina na fasa"tana gama fadar haka ta fada daki ta rufe tare da saka sakata ganin duk suntaso sun yo kanta,gaba daya ranar kwanan takaici da bakin ciki Ali da mufty suka yi Kai hatta da Safwan da Hamza sai da suka kira suka sanar dasu hakan yasa suka hadu suka jajantawa junansu.

*

Washe gari ummi taga ummul bata da niyar zuwa aiki sai kawai ta yi mata zuru taga iya gudun ruwanta,wajen misalin ƙarfe goma Ummul tana zaune tsakar gida tana cire kunbarta,Ummi dake kokarin dora sanwar rana ta kalleta tare da cewa "wai ikram ba zaki je gidan Alhaji Musa ba ne?"tura baki Ummul ta yi kana ta ce"Ni Wallahi ummi yau ba zanje ba har sai na huce daga haushin yan gidan"girgiza kai ummi ta yi tare da cewa "to Allah ya sauwaka amma dai kin san wannan tsohuwar me aikin ba abinda zata iya yi musu naci dan haka ko kin zauna ma zasu biyo bayanki kin sani"tashi ta yi tana kunkuni akan ko sun biyo bayanta ba zata je ba yau sai sun gane kurensu sai sun gane cewa talaka ma yana da amfani,tana shiga dakin aka yi sallama wanda hakan yasa ta saurin fitowa tana kallon kofa da tunanin muryar wadda ta ji tana sallamar,aiko da wani irin tsallen murna Ummul ta dane me sallamar tana dariyar farin ciki,ummi ta ce "dan Allah ki saketa kar ki karyata"kallon bakuwar wadda bata wuce sa ar ta ba Ummul ta yi tana dariya kamar yadda itama budurwar take yi, "Ummi ta ce"A'isha saukar yaushe haka?"bakuwar da Ummi ta kira da A'isha ta kurkusa tana gaida ummin tare da cewa "Wallahi ummi saukar dare mu kayi shi yasa ban shigo ba"Allah sarki to madalla sannu da dawowa ai na dauka ma Kaduna ta rike ku saboda shirun da muka ji"kamo hannunta Ummul ta yi tana cewa "taho muje ki bani labarin kd"suna shiga daki suka zube kan katifar Ummul, sannan A'isha ta dubi Ummul ta ce"ikram sai naga kin kuma yin kyau ko da ike kullum makerin budurci kara kera ki yake shi yasa kike canzawa"ikram ta ce"Ni dai ki bani labari yaya kd wane irin capacity kika baza a can?"harara ta ɗan watsawa ikram din kafin ta ce"ke dai bari ikram ai Ni da naje kd sai naga ashe gidan na tarar dan mazan kd sun fi kowa iya karya da suwaga shi yasa na ajiye duk wani shirmena sai na dawo gida kuma dake lamarin babu ke shi yasa ya kuma fita a kaina",mikewa ikram ta yi tana cewa "bari kiga na sa kayana mu fita dama yau ba zanje wancan gidan ba",rufe bakinta ke da wuya ummi ta shiga kwalla mata kira,bata jira amsawarta ba ta ɗora da cewa maza ki fito ki tafi aiki gashi nan Alhaji ya kira baffanki dan haka sai ki fito ki tafi"buga kafa ta shiga yi tana hawayen shawagaba, Aisha kuwa sai dariya take mata,shiryawa ta yi tana cewa "zamu fita a matsayin zan je amma wallahi yau ba zanje gidan nan ba shawagi kawai za mu yi a gari mu dawo"A'isha ta ce "ni dai babu ruwana gaskiya, idan asiri ya tonu fa?"sai dai idan ke zaki fada" Ummul ikram ta bata amsa tana surar karamar jakarta ɗaya daya,tare da ficewa tana cewa idan kin ga dama ki fito mu tafi".

Ummi ta bi ikram da ido zuciyarta na fada mata cewa Ummul fa tunda bata yi niyar zuwa gidan nan ba to fa ba za ta je ba musamman ganin dawowar A'isha,hakan yasa ta dakatar da su daga shirin fita da suke yi tare da cewa"ikram fada min tsakani da Allah ina zaku je idan kun fita nasan bakya yi min karya dan haka bana so ki fara duk da nasan cewa sana'ar ki ce karyar"kai Ummi,sana a fa kika ce?",ey mana ko karya na yi,?sai dai ina rokon Allah da ya sauya ki daga Ummul ikram yar karya zuwa me gaskiya ya sauya gidan nan daga sunan gidan yan karya zuwa gidan buzaye kamar yadda sunansa yake a da,kafin ku sa mutane su canja shi, yanzu dai fada min ina zaku je?"dan sosa keyarta ta yi sannan ta ce"ummi gidansu A'isha zamu je"dakuwa ummi ta yi mata tana cewa gidanku gidan su A'isha ko yawan wajen cin abinci da store kuna bi kuna karya da gidan kusoshin gwamnati wallahi ikram ki fita daga ido na, ki kama hanya ki tafi neman halak na gaskiya idan ba ki je ba wallahi sai ranki ya ɓaci fitinanniyar banza da wofi",jiki a salube suka kama hanya suka fice, Ummul na cewa "Wallahi kuma ko na je ba zan yi musu komai ba sai dai su cire a albashina jarababbun mutane kawai,ni wallahi har na fara jin rayuwar masu kudin ma ta fara fita a raina in dai halinsu ɗaya da su zezee"dariya A'isha ta yi tare da cewa "ki bani labarin abinda wannan shegiyar zezee me katon kai ta yi miki"jinjina kai Ummul ikram ta yi,tana cewa "zan baki labarin sai mun zauna"daidai lokacin suka fito waje ,tuni idanun Ummul suka sauka akansa yana zaune a mazauninsa as usual kansa sanye da p cap,yana fama da wani takalmin mata, sai a lokacin ta dubi budurwar da ke tsaye ta tsaresa da ido tana jiran ya gama mata gyaran,tsaki Ummul ta yi tare da zabga musu harara kana ta yi gaba zuciyarta na cunkushewa,ba su kai ga barin kofar gidan ba,wata bakar mota ta yi fakin kofar gidan nasu wanda hakan yasa suka yi burki dan ganin wanda ke cikin motar,suna tsaye amma ita Ummul hankalinta yana kan gentle da budurwar nan da har yanzu aka kasa kammala gyaran takalminnata wanda hakan ke sanya ta jin wani irin bacin rai da haushin gentle din,daidai nan kuma sulaiman wanda shine a cikin motar nan ya fito cikin kyakkyawar shiga fuskarsa dauke da murmushin farin cikin ganin Ummul a ransa yana jin cewa shi din me sa a ne da zuciyarsa ta zabi Ummul matsayin matar aure,"sannu ko ya ce da A'isha dan ita Ummul gaba daya hankalinta ba akansa yake ba, sai da A'isha ta zungureta sannan ta dube su,idanunta na arba da sulaiman ta dafe ƙirjinta tana jan innalillahi kafin ta ɗora da cewa "dan Allah bawan Allah me kake nema dani bayan fallasa da tonon sililin da ka jawo aka yi min shine sai ka kuma biyo ni har gida ka kuma kure ni?to idan baka sani ba ka sani a yanzu ba wanda na tsana a duniya sama da kai domin da baka biyo ni ta wannan hanyar ba da baka jawowa iyayena zagi da cin mutunci ba"sannan ta juya a fusace tana kallon budurwar da aka gama gyara mata takalmin tana gwadawa, fuskarta dauke da murmushin da ta ke ta haske gentle dashi,take ta kuma jin zuciyarta ta wani irin tsukewa da bacin ran da bata san daga ina yake tasowa ba,bugawar zuciyar da bata san mene dalilinsa ba,dagowar da gentle yayi ya ɗan dubi budurwar da kuma sabuwar dubu dayan da take mika masa yasa ta kuma jin tsinkewar zuciya, bata jin tun da gentle yake ƙofar gidan su ya taɓa dago Kai ya kalleta duk tsayuwar da zata yi a gun kuwa,rufe idanunta ta yi hankalinta na kasuwa biyu,bangare daya maganganun so da take karɓa daga bakin mutumin da bata kaunar sake bude ido ta gansa a gabanta,bangare daya kuma gentle da budurwa me takalmi da take cewa yarike kudin ta bar masa sannan idan ba damuwa ko zai bata nomber sa saboda gyaransa yayi mata kyau idan ta je gida zata hada wasu ta kawo masa.

Shi din bai ce komai ba domin dama in dai magana ce bata tsammanin cewa zata sameta a gurin gentle sai dai ga mamakinta gani ta yi yana kokarin lalubo aljihunsa kamar zai dauko waya,sai dai tun kafin taga abinda zai dauko idanunta suka rufe numfashinta ya shiga wani irin kai kawo a kirjinta,ba su sankara ba sai ganin Ummul suka yi ta tafi luuu tana shirin zubewa, cikin sauri sulaiman ya nufeta dan tare ta sai dai kafin ya kai ga karasawa wanda yafisa zafin nama yayi mata kyakkyawan masauki a kirjinsa,cikin tashin hankali A'isha ta bi bayan gentle da ya nufi cikin gida da Ummul ikram dake jikinsa bata san inda hankalinta yake ba,sai ga sulaiman shima a cikin gidan hankali ta she,ummi kam rasa inda zata sa kanta tayi dan gaba daya ta rude cewa ta ke"lafiya kalau fa suka fita ko dai damuwar abinda ya faru jiya ne yasa ta shiga wannan yanayin?"duk cikin mutanen da suke wajen babu wanda yake da amsar tambayarta,dakyar ta iya jagorantar gentle zuwa fallen dakin da ya kasance falo a gidan me dauke da doguwar kujera daya, dan haka anan gentle ya kwantar da Ummul ikram kana ya ja gefe ya tsaya yana mai dora kaifafa idanunsa akanta,sulaiman kuwa tuni shima hankalinsa ya kasu ga tashin hankalin halin da Ummul take ciki ga kuma na daukar Ummul ikram da gentle yayi, duk da cewa bai san matsayinsa a gunta ba, To shima din dai jan tunga yayi ya tsaya yana tunanin ta inda zai fara bada umarnin cewa a kaita asibiti tunda babu wanda yasan shi a gidan sai baffa shi kuma baffa baya nan,ita kanta ummi gaba daya a rude take Dan ta rasa wa ma zata fara kira cikin mazan uku,A'isha kuwa tana zaune saman kanta tana ta shafa mata ruwan da suke tunanin cewa zai iya farfaɗo da ita.

Gentle da ba a iya karantar zuciyar sa kuwa babu wani abu da na hanga a tare dashi,to ina ma ya bada damar kallon fuskar tasa bare har ka karanceta,ta bakin Ummul ta ce ko dai bakar fuskarsa yake jin kunyar nunawa mutane,tunda ita dai bakin fuskarsa kawai zata iya dorarwa a cikin halittar fuskarsa,dan ko yanzun ma da yake tsaye kansa a sunkuye yake.

A'isha ce ta katse musu shurun da cewa "ummi ki daina kuka abinda ya kamata a yi shine kawai muje asibiti tunda ruwan yaki yin aiki"Sulaiman da ya samu damar tofawa yayi saurin karbewa da cewa "abinda ya kamata kenan Ummi ga mota can a waje mu tafi kawai",ya fada yana kokarin sanya hannu ya dauki Ummul, amma sai yaji an dakatar dashi ta hanyar rike hannunsa, ba kuma tare da ya tanka ba ya dubi ummi cikin muryarsa me nutsuwa da ba a fiya jinta ba,ya ce"zan iya Kaita motar?"ummi ta ce ai kai kamar yaya kake a wajen ikram dama kai ka kawo ta shi kuma sha anin lafiya ba a tsayawa tantance wani abu dan haka muje kawai sai na rufe gidan",ko gama rufe bakinta bata yi ba gentle ya kuma sunkutar Ummul ikram yayi waje da ita yayin da sulaiman ya bishi da harara saboda sanin cewa shi din ba kowa ba ne a wajen Ummul, a kofar gida suka ci karo da baffa da Alhaji Musa wanda ya zo bikon Ummul ikram da kansa, hakan kuma ba karamin mamaki ya sanya baffa ba sai dai yayi kokarin kawar da mamakin ta hanyar sanyawa ransa cewa alhajin ya sauya daga yadda ya sanshi, dan haka gaba daya hankalinsu ya dawo kan gentle dake rungume da Ummul,ummi ce ta yi musu bayani a takaice ,take kuma Abban zezee ya umarci gentle da ya sanya Ummul a motarsa su tafi a asibiti wanda hakan bai yiwa sulaiman dadi ba,amma ba yadda ya iya tunda sune masu iko da ita.

Dake driver ne yake jan motar sai ya shiga gaba Ummi da baffa suka shiga baya tare da Ummul ita kuma A'isha tabi motar sulaiman, gentle kuma dama bai nuna ma zai bisu ba, dan yana sanya Ummul a mota ya koma wajen aikinsa ya zauna.

Suna fara tafiya Alhaji Musa ya ce da driver "ƊAN ITOPIA SPECIAL HEALTH CARE zaka kaimu"ok sir"daga nan ya dauki wayarsa yana cewa bari na yiwa surukina waya ko da baya asibitin ya haɗamu da wanda zai ganmu"yana maganar yana wayar sai dai har ta karaci ringin dinta ta gama ba daga ba,ajiye wa yayi yana dan sauke numfashi tare da cewa" surukin nawa ne wani irin murdaddan mutum dama bana zaton zai daga kai tsaye,muje kawai idan mun yi sa a mun sameshi shike nan,idan ma bamu sameshi ba zamu samu likitoci,su dai baffa da ummi babu wanda yake da bakin magana dan gaba daya hankalinsu yana kan autares dinsu da take fidda numfashi sama sama kamar me ciwon asma.

******

Lokacin da suka karaso hadadiyar asibitin da take tamkar a kasar turai,ba tare da wani jinkiri ba nos suka garzayo da gadon daukar marasa lafiya aka dora Ummul a kai,cikin hanzari suka wuce da ita emagency, wata nos ce ta ce bari a sanarwa da Dr saboda wannan tana cikin critical condition an yi sa a ma yana nan"daga haka ta wuce ta ɗane jikin matakalar lipter, ajiyar zuciya Alhaji Musa yayi yana cewa "to mun yi sa a sirikinnawa yana nan in sha Allah komai zai zo da sauki,to wai me ya janyo mata wannan matsalar ne?"ummi dake share hawaye ta ce" yau dai ban san me ya janyo mata ba,amma lokuta da dama kura ko yaji shi yafi sanyata cikin wannan halin sai mun yi fama sosai kafin ta dawo hayyacinta wannan karon ne dai abin yayi tsauri da yawa?"cike da mamaki abban zezee ya ce"kuna nufin kuce ba yau ta fara yin hahan ba?"baffa ne ya amsa masa da cewa "haka ne yallabai sai dai bamu taba tunanin zuwa asibiti ba"jinjina kai kawai yayi ba tare da ya iya kuma furta wata kalma ba,sai a lokacin ne ma baffa ya lura da sulaiman amma dai bai ce masa komai ba dan baya cin yanayin da zai iya sauraren kowa,daidai lokacin nos din ta dawo tare da wuce su cikin sauri tana dauke da abun janyo numfashi hannunta saye cikin Safa,tana kokarin wucewa ummi ta tare ta tana cewa "baiwar Allah lafiya dai ko?"ba tare da ta tsaya ba nos din ta ce "ku kwantar da hankalinku tunda Dr BILAL ya shiga komai zai daidaita, hakan ya sa suka koma suka yi jugum jugum suna jiran tsammani........✍️

[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💞

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol