Free chapter · Read without an account

Pg9

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Nos din na shiga room din da aka kwantar da Ummul ikram ta sanar da ragowar nos din da ta samu akan Ummul ikram suna kokarin janyo numfashinta, tana shirin sanar da su zuwan Dr BILAL ta ji takunsa daga wata kofa dake kallon gabas,kafin ya bayyana gaba dayansa a dakin,bai ce musu komai ba ya nufi gadon da Ummul take kwance tana kokawa da numfashinta,kirjinta sama da kasa kawai yake yi tamkar zai ɓullo,hannunsa ya dora kan kirjinta yana dannawa a hankali,idanunsa akan fuskarta,kafin zuwa dan wani lokaci ya dauki abin janyo numfashin da yake kan try ya shiga hadashi ta hanyar jonasu da mahadinsu,cikin kankanin lokaci ya tsaida harbawar numfashinnata,bayan gwaje gwaje da tasha,a ƙalla ya dauki kusan awa daya akan Ummul ikram,ba shi ne ya fito daga dakin ba har sai da ya tabbatar ya gano abinda yake damun ikram,fita yayi ta hanyarsa da yake shiga duk wani room da ya kasance v i p a hospital ɗin,hakan yasa su baffa basu san wainar da ake toyawa ba.

Nos din dazu ce ta fito daga room din, hakan yasa duk suka zabura suka yo kanta, abin mamaki Alhaji Musa ma har yanzu yana asibitin bai je ko ina ba, nos din ta ɗan dakata tare da kallonsu daya bayan daya sannan ta ce"waye mahaifinta?"cikin barin jiki baffa ya ce" gani nan"gaba ta yi tana cewa "biyo ni Dr nason ganinka"bin bayanta yayi kamar zai kifa,ummi ma kasa hakuri ta yi hakan yasa tabi bayansu,nos din ba ta bi da su ta lifter ba dan bata ga zasu iya ba,shi yasa suka bi ta saman kai tsaye,dakatar da su ta yi ta fara shiga sannan ta fito ta basu izinin shiga,yana zaune cikin kujerarsa kansa sunkuye yana rubutu akan wani fayal,nuni yayi musu da wajen zama, hakan yasa baffa ya zauna a kujerar da take kallonsa ita kuma ummi ta zauna a doguwar kujerar da ke girke a office din tana baza ido cikin office din wanda da damuwar da suke ciki bai hanasu yin tunanin ko a aljanna suke ba,tsawon mintuna biyar yana rubutu akan fayal din nan kafin ya dago kansa yana dan kallonsu a karance,kafin cikin maganarsa dake fita daidai a kuma ɗan kausashe ya ce"tun tsawon yaushe ne take fama da wannan daukewar numfashin?"baffa ya ɗan yi jim alamun tunani kafin ya magantu da cewa tun tana shekara goma"girgiza kai Dr Bilal yayi tare da dan cizon lebensa kana ya ce "amma me yasa tun da ta fara ba ku kawo ta asibiti ba?"wannan karon ummi ce ta amsa masa da cewa "Wallahi Dr ba mu dauki abin da muhimmanci ba ne dan mun dauka ma aljanune shi yasa muka fi karkata da yi mata turare da addu o in korar shedanu"shiru yayi na kusan minti ɗaya kafin ya fesar da huci daga bakinsa kana ya ce"gaskiya kun yi sakaci bai kamata idan yaro yana rashin lafiya a dinga barinsa a gida ba ko kuma a dora cutar zuwa wani bigiren da bai shafe ta ba"shiru yayi yana duba takardar dake gabansa kafin ya dauke ta ya mikawa baffa yana cewa"wannan shine sakamakon gwaje_gwajen da muka yi mata"karbar takardar baffa yayi yana juyata dan bai san komai a ciki ba bare yasan me take nufi,ganin haka yasa Dr Bilal yi masa bayani da cewa"yarinyar ku tana dauke da ciwon asma wanda hausawa suke kira da ciwon daukewar numfashi, likitoci kuma suna kiransa da a asma wanda yake tashi a duk lokacin da mutum ya shaki yaji ko kura wani lokaci har da damuwa takan kawo toshewar numfashi daga nan sai mutum ya samu kansa cikin wannan halin da take ciki,to gaskiya da ace tun farko kun yi gaggawar Kaita a asibiti to da abun ba zai kai matakin da yake a yanzu ba,dan yanzu ta kai matakin da dole sai ta yi rayuwa da inhela wadda ita ce taimako na farko da take bawa me irin matsalar su,dan haka yanzu zata ci gaba da karbar magani har zuwa nan da kwanakin da komai zai daidaita amma dai yanzu ma jikin da sauki sosai dan ko gobe za a iya discharged nata"jiki a salube suka mike dan sun rasa abin cewa, dan sun ɗorawa kansu laifi kacokan.

Suna fitowa ummi ta fashe da kuka tana cewa yanzu baffan ikram shike nan mun yi sanadin saka rayuwar ikram cikin kila wakala?kasan yadda masu lalurar nan suke cikin jarabta,duk lokacin fa da ta tashi idan har babu wannan abar shaƙar a tare da su kuma aka yi jinkirin kaisu ga likita komai fa na iya faruwa da su,yanzu ikram ma wannan rayuwar zata yi?innalillahi wa inna ilaihi raji un" karasa maganar tana share hawayen da suka ki tsaya mata,baffa kuwa ya kasa cewa komai dan shi kansa zuciyarsa suya take yi,to amma ya suka.iya da jarabtar Ubangiji a haka ma su tasu me sauki ce dan haka godiya zasu yi masa kawai tare da nemawa ikram sauki a wajensa, dai-dai lokacin suka karasa reception din inda suka samu A'isha sulaiman da kuma baban zezee sai muftahu da Aliyu da suka karu,cikin tashin hankali suka nufi iyayen nasu suna tambayar su abinda likita ya ce,baffa ne yayi musu bayani a takaice,sai ga Ali da muftahu suna kuka kamar wasu kananan yara, A'isha ma kukan take yi, sulaiman da Alhaji Musa ne suka dinga basu baki sannan suka nutsu,an basu damar ganin Ummul ikram amma ba a tare za su shiga ba,da bibbiyu suka dinga shiga, daga na Alhaji Musa ya tafi tare da alkawarin zai dawo da dare,sulaiman kuwa yana nanne da su muftahu duk sallar da zasu je tare suke zuwa har baffa,A'isha kuma suna tare da Ummi a falon da daga shi sai room din Ikram wanda yake kamar ciki da falo,sai da suka yi sallar Isha sannan aka barsu suka kuma ganin Ummul wadda har lokacin bata tashi ba,daga karshe aka ce duka su tafi gida akwai masu kula da ita wanda haka ne ƙa idar asibitin, ba dan ran ummi ya so ba ta tafi gida,a'isha ma taso a ce an barta tare da kawarta sai dai ba damar hakan.

A waje suka hadu da Alhaji Musa ya dawo,To shima dai sai komawa yayi dan yasan halin surukinsa baya alfarma bare ya sa ran zai barsa ya shiga ganin ikram din dan haka sai kawai su kayi sallama daga nan, baffa yana ta masa Godiya saboda sun ga babu wanda yake tambayarsu kudi komai sai dai suka an shigar wa da ikram shi,kuma sun san ba me yin hakan sai Alhaji musan,kashe gidiyarsa yayi yana karfafa musu gwiwa akan su kwantar da hankalinsu zuwa safiya zasu dawo su tarar da Ummul sumul kamar ba ita ba, sulaiman shine ya ɗebe su a motarsa ya maida su gida,yana faka motar yayi saurin fitowa ya budewa bangaren da baffa da ummi suke suka fito baffa na shi masa albarka,tare da yi masa Allah ya huta gajiya,shi kuwa sai wani sussunne kai yake yi,siyayyar da ya tsaya yayi ba tare da sun gane su yayiwa ba ya debo yana rakasu da Ita,baffa yana shirin yin magana muftahu ya amshe yana cewa"an gode suruki Allah yayi albarka"harara ummi ta zabga masa tare da yin kwafa, suna kokarin shiga gidan gentle ya karaso tare da yi musu barka da zuwa da yi musu ya me jiki,cikin kulawar da a koda yaushe ummi take bashi ta dubesa tana cewa da sauki jafaru har yanzu baka tafi makwanci ba ba kenan?"dan murmushi yayi me sanyi kafin ya ce"ina jiran dawowarku ne dan naji ya me jikin"Allah sarki to maza shigo da kayan ka karbi abincin ka wuce kar dare ya kuma yi"gaida baffa yayi shima tare da yi masa ya me jiki,daga nan suka shige gidan, muftahu kuwa tuni sun shige gida da ledoji suna faman hura hanci dan su sam wannan gentle din bai damesu ba, hasalima haushi yake basu dan dai kawai ba su iya wulakanci ba ne shi yasa suke rabuwa da shi, amma dai babu wata mu amala ta kirki a tsakaninsu.muftahu baffa yasa ya raka A'isha gida, bayan an diba mata kayan kwalam din da sulaiman ya bayar,duk da cewa sun san me yake faruwa tun a waya amma dai wannan kyautatawa ce da karamci.

Cikin sauri sauri muftahu ya rakata ya dawo, dan gaba daya tun da ya fita hankalinsa yana kan kaza da youghot din nan,su baffa kuwa da ummi dakyar suka dan ci kadan shima maganin yunwa, amma gaba daya hankalinsu yana kan autarsu burinsu kawai gari ya waye su je su ga idanunta biyu.

******washegari

Washegari da sassafe Alhaji Musa ya sanya momy a gaba da kanta ta shiryawa Ummul breakfast, hakan ba karamin takaici ya bawa zezee ba, bata gama shan takaici ba sai da abban nata ya umarce ta da ta shirya su tafi dubiyar ikram ɗin,tana buɗe bakinta kuwa sai cewa ta yi"ni babu inda zani ku dai da kuka ga zaku iya sai kun dawo"cikin rarrashi ya dubeta ya ce"ko baki je dan Ikram ba ai kyaje dan abin kaunarki Dr Bilal"ai ko cikin sauri ta mike tana cewa "da gaske Abba?"to zan yi miki karya ne,ko nima duk abinda kiga ina yi ina yinsa ne dan yana cikin shirina, dan ina son gyara abinda kika ɓata, na tabbata idan yaga yadda muka damu da yar aikinmu zai sauya tunaninsa a kanki,kuma kema wannan babbar dama ce a gareki da zaki gyara barnar da kika tabka"da gudu ta nufi daki dan shiryawa zuciyarta cike da dokin ganin fuskarnan tasa me kyau da kwarjini.

******

Tun cikin dare ikram ta farka, nos din dake tare da ita ta taimaka mata ta yi wanka sannan ta rama sallolinta,sosai taki dadin jikinta sai dai a dame take ganin babu kowa nata,dan haka ta dubi nos din ta ce"wai ina yan uwana da su ummi na ne kije ki shigo da su tunda safiya tayi"a wannan karon kai tsaye nos din ta bata amsa da cewa ba anan suka kwana ba,amma nasan zuwa anjima zaki gansu"tayi zaune ta yi tana yiwa nos din kallon uku ahu kafin ta ce"to wane shafaffe da man ne ya hana su kwana?"bude kofar da aka yi tare da sallama da wani irin masifaffen kamshi ne yasa su maida hankali kan kofar,dafe kirji ikram tayi tana zaro manyan idanunta,kafin ta juya ta kalli nos din da taga tana gaida shi cikin ladabi daga nan ta fice daga dakin,wani irin miyau ikram ta hadiye kafin ta marairaice fuska kamar zata saki kuka,karasowa yayi har gaban gadon idanunsa akanta take ta kuma diriricewa babu shiri ta fara tari, cikin zafin nama ya dora hannusa kan kirjinta yana dan dannashi cike da kwarewa irin ta aiki,cikin wata irin murya me dan kauri da taushi da rarrabe kalma, ya ke fadin"ke kina son kashe kanki da shegiyar fitina ko?"ture hannunsa ta shiga kokarin tana cewa Ni ka rabu da ni ka kirawo min ummina"bai saurareta ba ya shiga yi mata wasu gwaje gwaje,wanda ganin yadda ya wani kuma kime fuska yasa ta jin wani irin shakkarsa dole ta tsaya yayi mata duk abinda ya kamata,tsadadden agogon hannunsa ya duba, kana ya ce kin ci abinci?"me makon ta nashi amsa sai ta wani murgude bakin tana faman hararar gefensa, bata ankara ba ta ji ɗal ya sa yatsun hannunsa biyu ya dalla mata su akan yan labbanta da take murgudawa,take ta sanya kuka kuka sosai irin na taɓararrun yara,bai bi ta kanta ba,ya shiga har hada mata magunguna fuskar nan babu alamun wasa.

Su ummi ne suka fara karasowa kafin su Alhaji su zo,sai dai dukkansu a nan falon nos ta dakatar da su saboda Dr yana ciki,zezee jin haka yasa taji kamar ta mangare nos din ta shige taga qaunar da ake toyawa,tunaninta ne ya katse saboda fitowar da, Dr Bilal yayi, sai dai yana jikin kofar bai bawa Kowa damar shiga ba,a dan ladabce ya gaida mutumin da ke amsa sunan surukinsa sai kuma baffa da ummi,daga haka bai kara bawa Kowa damar yin magana dashi ba,zezee ji take kamar taje ta rungumesa sabida yadda yayi mata kyau kamar wani dawisu,sai dai ko kallon inda take bai ba, kai bata ma zaton cewa ya ganeta a dai yadda yayi banza da al'amarin ta a wajen,maganarsa ce ta katse tunaninta,ina abincin da za a bata Muna bukata saboda zata sha magani,ummi ce ta yi suatin mika masa kular dake hannunta, sai momy ma ta mika masa kwandon dake nata hannun tana cewa akai mata duka sai ta zabi abinda zata iya ci"bai ce komai ba ya wuce nos ta bi bayansa da kwandon,yunkuri zezee ta yi zata bisa,abbanta yayi saurin riko hannunta tare da watsa mata harara da yi mata gargadi da ido,ba dan taso ba ta dakata amma fa ji take kamar zata yi a man wuta,ita abinda yake bata mamaki wai shin dama Dr da kansa yake yiwa mata lafiyarsa hidima duk da cewa ga nos ga kuma dangin su"kasa yin shiru ta yi dan haka ta dubi nos din da fitowar ta kenan ta ce"wai nos in tam bayeki mana?"ina jinki nos din ta fada tana maida hankalinta kan zeze,zezee ta ce"wai dama haka Dr yake yiwa duk wani maralafiya ko kuma akan wann6ne ya fara?"kai tsaye nos ta bata amsa da cewa Dr ko magani ba shi ya ke bawa fetien dinsa ba komai nos ke yi dan haka zan iya ce miki akan ikram ya fara".

Ai ba tare da kowa ya a kara ba sai ganin zezee ta shammaci nos din ta shige dakin,zuciyarta na wani irin tafasa tana jin cewa ba zata taba iya actin din da babanta yake so tayi ba ,dan tsaf zata iya tafiyar zuciya ta mutu.

Daidai lokacin Dr Bilal ya dauki cup din shayin da ya gama haɗawa me rai da lafiya ya mikawa ikram ita kuma ta tsaya masa gaddama dan haka sai kawai ya dora masa shi saman bakinta yana zare mata idanunsa da suke saye cikin farin glasses.

ƊAN ITOPIA'S MENTION.........

Tunda ya dawo daga gidansu zezee ya shige dakin Mamma yayi kwanciyarsa, duk da cewa ba bacci yake ba amma ba zaka taba zaton hakan ba.

Duk da cewa gidan cike suke da gajiyar tafiyar da suka shawo daga Abuja zuwa Kanon a daren jiya hakan bai hana gidan cika da al umma ba,dawowarsa ce tasa mamma saurin sallamar ragowar jama ar da suka yi saura, dan sanin yana cikin gidan hayaniyar kan iya haifar masa da damuwa ko ciwon kai,cikin kankanin lokaci gidan yayi tsit baka jin hayaniyar komai sai ta tsuntsayen da suke shawagi tsakanin bishiyun da suke kewaye da tafkeken mention din.mamma bata kusanci inda yake ba sai da ta tabbatar ya sauke duk abinda ya kwaso daga can inda yaje din, sannan ta shiga bangaren nata da sallama dauke a bakinta, yana kwancen a yadda yake kamar me bacci,zama ta yi a gefen gadon kusa da kansa tare da kai hannunta saman tattausar sumarsa tare da cusa yatsunta cikin sumar tana cakuda masa ita,a hankali ya bude idanunsa da suka dan shige ciki sannan ya sakar mata murmushin da ita kadai take iya ganins[10/15, 10:08 PM] fatima y Adam(Zahra✍️): ***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol