Free chapter · Read without an account

Pg12

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Duk wanda ke wajen babu wanda ya ji dadin marin nan,dan hatta sulaiman sai da yaga zakewar Alhaji dan gaske,muftahu kansa sai da jikinsa yayi sanyi,bare Ummi da take jin kamar Ummul dinta aka mara,shi kuwa gogan yana tsaye ƙyam a wajen bai motsa ba, yayin da Ummul ke gefensa kamar zata shige cikinsa babu inda take kallo sai fuskarsa inda aka mara ji,baffa ta ne ya girgiza kansa cikin tsananin damuwa ya ce"ashsha Alhaji har abin ya kai haka?ai shi yaro hakuri a ke dashi,musamman ma irin su hafaru da basu da fitina gaskiya abin bai yi dadi ba"ya kare maganar yana tafiya dan shiga gidan zuciyarsa babu dadi dan har ya kasa kallon gentle din saboda tsananin kunyarsa da ta rufe shi,ummi ba bin bayan baffa ta yi dan ita din ma ba za ta iya fuskantar gentle ba,shi kuwa uban gayyar Alhaji dan gaske ko akwalar rigarsa, sai ma kallon gentle din da ya kuma yi ya nuna shi da yatsa yana cewa"wallahi in dai ka cika gaba da shiga gonata to zaka yi nadama domin fada dani baya karewa, kuma ni bana yafe lefi ko mai kankantarsa musamman irin wannan da ake son rabani da wani abu me muhimmancin a gareni,dan haka idan kana son kanka da arziki ka kiyaye"juyawa yayi kan Ummul da ta ki sakin hannun gentle tare da cewa"sake shi ki wuce gida"wannan maganar da ya kuma yi mata ita ta sanya ta kara harzuka jin zuciyarta take na mata wani irin suya, yayin da ta ke kallon gentle da idanunta da suke cike da kwalla bakinta yana rawa hannunta na rawa har zuwa gangar jikinta,ganin yadda take neman birkicewa yasa shi kama hannunta tare da leka idanunta kafin cikin dan karamin murmushinsa da bata taba gani ba wanda ya tsaya a iya kan fatar bakinsa ya ce"ikramm"shi kansa yadda ya kira sunanta sai da ya daki zuciyar duk wanda kunnensa yake kansu,ya haka kuma me kike shirin yi ne?kin manta matsalarki ne, a yanzu babu wanda yake bukatar damuwarki sai wanda bai sai muhimmancinta da darajarta ba, ikramm na yi hakuri saboda darajar lafiyarki da muhimmancinta dan haka kema ki taimaka min ki yi hakuri saboda lafiyarki"ya karasa maganar yana dan dage mata gira, ikram bata san lokacin da ta sanya murmushi saman fuskanta ba har sai da kumatunta suka lotsa,hakika ta samu farin ciki da wannan yanayin fiye da zaton mai zato,kama hannunta yayi ya shiga da ita gidan ba tare da ya nuna alamun yasan da tsayuwar wasu a wajen ba.

Wannan abu da ya faru ba iya Alhaji dan gaske ya taba ba,hatta da sulaiman sai da ya ji zuciyarsa zata sare, hakan yasa shi juyawa cikin sanyin jiki ya bude matarsa ya shige,muftahu ne ya leka ya bashi kwarin gwiwa da cewa "kar ka damu da wannan nasan yayi ne saboda ya rama abinda Alhaji dan gaske yayi masa tunda duk akan ikram din yayi masa abinda yayi masa"jinjina kai kawai yayi kana yaja motar ya tafi, shima mufyahun tafiyarsa yayi ya bar Alhaji dan gaske a nan, cikin ciwon rai dan gani yake da wannan cin fuskar da gentle yayi masa wallahi gwara yayi masa mari goma a jere,wata irin kwafa yayi tare da shigewa motarsa yana cewa"lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka,idan har ka zabi yi wasa da ni to kuwa zasu shiga cikin ukuba dan wallahi akan ikram tsaf zan sa a batar min da kai mara galihun banza da wofi".

Gentle kuwa bai bar ikram ba har sai da ya danka hannunta a hannun Ummi, sannan ya juya zai fice,"dan Allah jafaru ka yi hakuri da abinda dan gaske yayi maka"Ummi kar ki damu sai da safe"Allah ya bamu alkhairi ta fada tana jan Ummul zuwa daki.

*****

Wannan dare ya zamarwa Ummul ikram daren farin ciki wanda ta san dalilinsa amma bata san tushensa ba,yau ita ce gentle yayi magana da ita me tsawo kuma yana kallon cikin idanunta,kuma kalamai na musamman wanda bata taɓa tsammanin jin irinsu daga bakinsa ba,wani irin juyi ta yi tana mai kankame fulo a kirjinta cikin yanayin da ko bindiga a ka saka mata baza ta fadi na meye ba,sautin mutuwarsa ka dai ke amsa kuwa cikin kunnuwanta da bugun zuciyarta,da wannan tunani bacci me dadi ya saceta,to asuba ta gari ummgent.....

******

Tun a daren jiya yake kaiwa da kawowa shi kadai cikin daki, babu abinda yake yi masa kai kawo sai gentle da abinda ya wakana,har zuwa wayewar gari abin ya ki fitar masa aka,shi kansa bai san ya aka yi dattijuwar zuciyarsa take neman komawa karamar yarin ba,ey to karamar yarinya mana tunda gashi ta fada son yar cikinsa wanda idan da ace ya samu 'ya'ya da yawa ma zai iya sanya ta a matsayin 'ya ta ƙarshe ko kuma jikar farko,da farko bai yi zaton son da yake mata na gaske ne ba,dan ya sanya shi a matsayin sha awa da son yin karayi bayan ya samu duniya ta hanyar zamowa suruki ga babban mutum kuma biloniya a kasar nan,sai dai lokaci daya abin ya zanja daga karami zuwa babba,dan kuwa a yanzu ji yake zai iya yin komai domin samun Ummul ikram matsayin mata, sosai yake ji ta zama duniyarsa da duk wani farin cikinsa, a farko bai dauka cewa samun ikram zai zama wata barazana ko abin wahala a garesa ba,duba da yadda ubanta da ita kanta suke karkashinsa da kuma duba da rayuwar yarinyar na karya da son zama daya daga cikin mata masu aji wanda suka ci suka kwanta akan arziki,a baya yana tunanin cewa bashi da matsala da Imran3dan da zarar yayi amfani da dukiyarsa tsaf zai samu hadin kanta,to amma yanzu ya fara shuga wasi wasi akanta,anya yarinyar nan son abin duniyarta ba a iya baki yake ba,idan har ba a iya baki ba ne to tabbas ba zata fifita wani matsiyaci akan su ba,domin idan shi ta ƙi shi dan girmansa ai Sulaiman shima matashi ne kuma da kudi sannan kyakkyawan da ko wace mace zata yi alfahari da shi,komawa yayi ya zauna a bakin gado tare da hade hannayensa biyu, zuciyarsa na gaya masa ikram akwai abinda take nema wajen gentle amma ba so ba,domin idan yayi la a kari da duk abinda ƙwaƙwalwarsa ta zano masa tabbas babu abinda ikram za ta yi da gentle, na farko dai gashi ba kyau ba fuska kamar an saka shuni sannan shi ba kudi ba hasalima yana daga cikin sahun farko na manyan matsiyatan da ake kwatance da su a duniyar talauci,dan haka ikram ba son shi take ba,kai wata ƙila ma ta yi abinda ta yi ne saboda sulaiman ya ji haushi dan ya fahimci bata son ganin yaron, idan haka ne kuwa shike da nasara,wani dan numfashi ya sauke tare da murmushin samun mutsuwar da ya kasa samun ta tun jiya, sai a lokacin ya samu karfin tashi ya shiga wanka.

A can bangaren zezee kuwa har yau tana fama da ciwon zuciyar da Dr Bilal ya da ikram suka saka mata,gashi abbanta yayi mata banza ya daina kulata sabgigoginsa kawai yake yi,bare ta samu hanyar ganin Dr ta bangarensa, ita da kanta ta ji a ranta fa dole ta canja in dai har tana son samun Dr Bilal a matsayin mijinta,dan haka da yau ta ji cewa ta daura aniyar bin hanyar gyara domin ceto soyayyarta da kuma burin mahaifinta da ba yasan wane iri ba ne.

******

Alhaji Ahmed dan itopia ne zaune cikin Ni Im taccen falonsa tare da uwargidansa kuma uwar yayansa Hajiya madina,shayi take zuba masa a dan karamin cup din tangaran, yayinda shi kuma idanunsa dake saye cikin galass suke kan tv da ake labaran BBC a bangare daya kuma da karamin kur ani a hannunsa,kamilin mutum ke nan wanda bai dauki duniya da komai ba,sauƙaƙƙa ne kuma kaifaffa ne akan gaskiya da jajircewa akan iyalansa,an ce hatta shi kansa bai san yawan adadin dukiyarsa ba,duk da cewa kullum cikin kyautar da ita yake wala lokacin Zakka da ba lokacin Zakka ba, Allah ka dai yasan yawan mutanen da su kayi arziki a karkashinsa,a salinsu yan Itopia ne sha'awar zama ne ya dawo dashi Najeriya,daga shi har hajiya Madina Asalinsu da tushensu daya ne,kusan arzikin su na gado ne, dan kaf yan uwansu babu talaka kuma ta wani bangare sun gaji sarauta, haka kuma shi mutum ne me zumunci shi yasa ko da ya baro cikin yan uwansa ya dawo zaman Nigeria basu damu ba, saboda babu wani abu da ya ragu ta bangaren zumuncinsu,duk sanda suka so zasu shigo jirgi su zo, haka shima duk abinda ya kama ko.ya tashi zai dauki iyalansa takanas su tafi wannan halinnsa shi yake kara masa soyayya a wajen yan uwansa na kusa da na nesa,haka Hajiya Madina macece me kirki da sanin ya kamata su din dukkansu masu addinine shi yasa kaf ƴaƴansu babu wanda bai kai wani matsayi ta fannin addini ba,domin shi har ya fi bawa ilmin addini muhimmanci fiye da na boko,a cewarsa wannan shine zai taimake su a gobe kiyama shi kuma wannan na zamani iya duniya ne kawai, duk da cewa shi din ma bai tauye su a fannin sa ba.

Duniya sunan dan itopia kawai ta sani amma ba ta san fuskarsa ba kuma bata san ahlinsa ba,sanin bakin ma da aka yi masa an yi masa ne saboda kadarorinsa, har yanzu akwai wanda su kayi arziki ta sanadinsa ba tare da sun san haka ba,saboda shi ka'idarsa ce yin kyauta hannun hagu bai sani ba,sai da kuma duk yadda ya so ga hakan sai da abin arzikinsa ya bayyana wanda ta dalilin haka ne ya kuma yin suna a bakin al umma,saboda shi alheri danko ne kuma yaɗuwa yake duk yadda ka kai ga boye shi wata rana sai ya bayyana, saboda bayyanar tamkar wata hamya ce da Ubangiji ya kawowa mabukata, tunda ko wane abu akwai silarsa wani abun duk yadda kakai ga nemansa idan ba kasan inda zaka samu ba dole ka hakura, shi yasa Allah ya bayyana Alhaji Ahmed ga duk wanda arzikinsa yake tare da shi.

Cikin nutsuwa Hajiya Madina ta mika masa shayin tare da dan rissinawa, kana ta koma ta zauna,sai da ya shanye shayin sannan yayi mata addu'a ya dora da cewa"ina yaronki yake ne?yana leƙawa wajen yarinyar Alhaji Salisu dan gaske kuwa?"murmushi ta yi irin nasu na manya kafin ta ce"ai kasan halin dannaka in dai ba cewa aka yi da shi ya je ba ba zai taba zuwa ba,kum....sallamarsa ce ta katse Hajiya daga abinda take shirin fada, amsawa ta yi tana ɗorawa da cewa "kaga dan halak"fuskar nan tasa babu yabo ba fallasa ya karaso gabansu ya zauna tare da gaishe su cikin girmamawa irin ta cikakkun yayan da su ka yi riko da fadin Allah da manzo,cikin SOYAYYA me tsafta suka amsa masa, daga nan baban ya dora masa da tambayar da yake yiwa hajiyarsa, ɗan rufe ido yayi kafin ya bude yana amsa wa da cewa"bana3tun ranar ban kuma zuwa ba"duban Hajiya baban yayi yana cewa "kinga Ni Ko?"kafin ya maida subansa kan Dr yana cewa to me yasa?"a hankali ya sanya hannunsa saman tattausar sumar kansa yana shafawa kana cikin rashin son yin maganar ya ce "baba aiki ne ya ɗan yi yawa amma zan je ko zuwa jibi ne"Hajiya ta sanya baki da cewa to dama ba dole aiki yayi maka yawa ba tunda ka ƙi tsayawa akan daya,kai ne tuƙin jirgi kai ne riƙe allura"murmushi baba yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba, ganin haka yada Dr mikewa yayi musu sallama ya tafi, ba tare da ya damu da mitar hajiyar ba, dan idan da sabo ya saba da wannan in dai akan ya ki ya ajiye aiki daya ne saboda ya dinga samun hutu.

******

Ko da ya je asibiti bai jima ba saboda yau din yana da tafiya zuwa dubai kuma a yau zai juyo,shi yasa ma bai sanya kayan asibiti ba ya sanya kayansa na tuki inda ya fito tsaf a cikakken pilot dinsa,damarar nan ba karamin kyau ta yi masa ba, haka mutane suka dinga binsa da kallo a sace saboda yadda ya zama wani tauraro abin burgewa,sai dai fuskar nan ce kamar me saboda hadewa idan aka rantse maka akan bai taba yin dariya ba sosai mutum zai yadda dan a yanzunma iyayensa da yan uwansa mata ne kawai suke dan ganin murmushinsa sama sama shima.

*******

A bangaren sulaiman shima dai ya kwana ne cikin wasi wasi da tsoron kar dan Hakim da ka raina ya tsole maka ido,dan shi kansa al amarin gentle ya tsaya masa a rai, to amma shima ta wani bangaren yana da nasa kwarin gwiwar har da hujjojin da muftahu ya kawo masa,wanda sune suke dan kwantar masa da hankali,ya so komawa a yau din amma wani bangare na zuciyarsa ya haneshi akan ya ɗan saurara zuwa gobe sai ya koma,dan haka sai kawai ya shirya ya fito,da zaliha suka ci karo cousin sister dinsa da ake so ya aura,yana ganinta ya hade fuska dan dama can bai wani aminta da aurenta ba bare kuma yanzu da ya samu ikram dinsa,"lafiya zaki shigo min kai tsaye?"yatsina baki ta yi tare da cewa to yaya sulaiman meye laifina dan maso duba lafiyarka bare ma mama ce ta ce na zo na duba ka ko lafiya baka fito da wuri ba yau"wuceta yayi yana ci gaba da daura agogonsa ba tare da ya tanka mata ba,bin bayansa ta yi ba tare da ta damu da halin ko in kula din da ya nuna mata ba.

***********

A bangaren hajja Ummul me pacacity kuwa, wayewar garin safiyar ta tashi garau da ita,har aiki ta fito taya Ummi,tana bakin kitchen tana barewa Ummi doyar da baffa ya siyo da safen saboda Ummul din,ta ɗan kalleta kafin cikin takaicin jiya da bata jin zai sake ta idan har ba daukar fansa ta yi ba,ta ce"wai ummi me mutumin nan me katon kai yake nufi da ni ne?"duk da cewa Ummi ta fahimci wanda take nufi amma sai ta jefa mata tambaya da cewa waye take nufi?"ummi dan gaske man mutumin da ya zage kwanjinsa ya faskawa gentle Mari, kuma wallahi bai ci banza ba,to ma wai meye hadinmu da shi dan kawai muna aiki a karkashin su?duba fa kiga maganganun da ya dinga fada masa sai ka ce shi arzikin shi yabawa kansa meton kai kawai"kafin Ummi ta ce wani abu sallamar baffa ta katseta, shigowa yayi yana cewa "maza ikramm tashi ki dauko abin shimfida mun yi bako"ta shi ta yi ta dauko tabarma,Ummi kuma ta dauko hijabi ta sanya a jikinta,Ita kuwa ikram daki ta koma,wanda tana shiga ta ji Muryar dan gaske yana sallama,wai ashe shine ya zo kara duba jikinta,hamdala ta yiwa Allah kana ta suri hijabi ta zura tare da fitowa daga dakin,baffa na shirin kiranta sai ganinta su kayi kamar an jefota,tsugunawa ta yi ta gaishesa cikin fara a da girmamawa, shi kuwa sai washe baki yake.

Tashi ta yi ta fice tana cewa yau zaka gane kurenka zaka san cewa ba ko wane kudi ne suke kwatar mutum ba",

Jimawa ka ɗan sai gata da dawo daidai lokacin Alhaji dan gaske ya mike tare da yi musu sallama, har da ajiye wa ikram kudi wai a siya mata kaza,godiya kawai ummi ta yi amma ba wai dan kudin sun burgeta ba ko kuma me kuɗin,kai tsaye ya sa kai ya fita zuwa wajen motarsa ba tare da yasan tanadin da Ummul ikram ta yi masa ba..........✍️

Me kuke zato Ummul ta yiwa Alhaji dan gaske oya mu wasa ƙwaƙwalwa.

Masu comments ina godiya

Zahra✍️

***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol