Free chapter · Read without an account

Pg15

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Washe gari da sassafe Ummul ta fito ta fara gyaran gida, dan ko bacci bata koma ba tun asuba,haka ta fito ta bar ummi a daki tana lazimi tana gyangyadi,shayi ta fara dafawa yana ta kamshin kayan kamshi,daga nan ta fere ragowar doyar jiya da baffa ya siyo saboda ita ta soya wata wata kuma ta yi yamvols, cikin kankanin lokaci ta gida ya turnuke da kanshi,wanda ya tashi Ummi daga dan baccin da yake figarta daga zaune,fitowa tsakar gidan ta yi tana ware idonta akan gidan gaba ɗaya,kafin ta maida kallon nata kan Ummul da ta fito daga wanka mijinta daure da zanin aramfa jikin nan sai wani glowin yake kamar fatar tarwada,gashinta kuwa duk ya zuba a bayanta wani kuma ya manne a goshinta, "ajiye bokitin ta yi tana cewa ummi lafiya naga kina ta kallona haka kamar na yi wani abu sabo"?kin bawa kanki amsa" Ummi ta fada tana karasawa kitchen inda ta hangi kulolin da suke rufe har guda biyu,sai kuma fulas din shayi a gefe shima,budewa ta shiga yi ta ne cewa "Ummul me yake damunki ne yau?ko dai aljanun ki ne suka so yin abin arziki ko dai da abinda kika taka?"dan sosa kanta ta yi sannan ta ce"ummi abinda na san zaki ne na yi miki,dan haka albarka kawai ya kamata kisa"jinjina kai Ummu tayi tare da cewa"to Allah yayi albarka amma shi kuma wannan da na gansa daban na waye?"wucewa ta yi tana nufar daki sannan ta ce"ummi na Abba dan gaske ne,kinga dai yadda ya dinga hidima damu a asibiti shi yasa naga ya dace mu yi masa ko da bai kai rabin abinda yayi mana ba"ey lallai kin yi tunani to bari mu karya sai mu tafi gaba daya tunda dama nima ban je ba"a'a ummi ki bari na fara zuwa idan na tsaya jiranki abincin zai huce saboda fulas din ba wani rikon zafi yake ba"buta ummi ta dauka tana cewa "shike nan sai kin dawo"da sauri Ummul ta shige daki ta shirya cikin gaggawa dan kar ma ta yi jinkiri su zo su yi daidai da ummin.

Ita kanta ummin sai da ta yi mamakin saurin shirin Ummul ɗin,bata ce komai ba dai, hakan yasa Ummul din ta dauki fulas din tana cewa "to ummi na tafi sai Kun taho" ko jira ummin ta amsa bata yi ba ta fice fit kamar walkiya,

Bata jima da fita ba,su yaya mufty suka tashi,yana fitowa ya ci karo da karin kummallon da Ummul ta haɗa, bai yi wata wata ba ya je yayi brosh ya dawo.yayi zaman dorshen a gaban kwanukan da ummi ta jere,sai ga Ali shima ya fito yana zuba yamma3kamar wanda zai ci babu,shima din cikin sauri ya yo brush ya dawo ya yi joinin da mufty,harara Ummi ta watsa musu tare da cewa,"babu abinda kuka sani sai karya da ci a nan ne kuka fi kauri"sai da muftahu ya cika bakinsa da doya sannan ya fara magana da cewa"ummi wai me ye tsakanin ikram da wannan me gyaran takalmin ne?"Ali da ya haɗa shayinsa yana shirin kaiwa baki ya harareshi kana ya ce"ina ruwanka dan shishshigi"malam ba da kai nake ba"mufty ya fada yana yin kwafa,"nima da kake da Ni ba amsa zaka samu ba, sai ka bari ita wadda take da amsarka ta dawo sai ka tambaye ta "dakin su Ummul din ya kalla yana cewa "to ina ta tafi da sassafen nan sai yanzu ba takwas da rabi ta yi?ko har ta koma aikin ne?"asibiti ta tafi kaiwa Alhaji abinci"Ummu ta fada tana hade rai dan kar ma ya kuma yi mata wata tambayar,dariya suka tuntsure da ita shi da Ali har da tafawa, kafin Ali ya ce"Allah sarki Ummul tamu ai akwai tunanin manya yanzu haka ta haɗa masa da dan wani guzuri"Ita dai Ummi bata kara bi ta kansu ba ta ci gaba da karyawar ta,dan tun jiya baffa ya karbi duty dan haka yau bai kwana a gida ba, haka suka gama shiriritarsu suka tashi ba ta tanka musu ba.

Karfe takwas da arba'in Ummul ta yi sallama a kofar dakin da aka yi admitting din Abba,zezee bata nan sai momy ta samu tana shirin haɗawa Abba abin karin kumallo,"a'a Ummul ce da safen nan haka ke da baki da lafiya"dan rissinawa ta yi ta gaida momyn sannan ta kalli Abba da yake ta washe baki tun shigowarta,"Abba ina kwana ya jikin naka?"baki kamar gonar auduga ya amsa da "lafiya kalau ikram ya naki jikin?"da sauki Abba ta fada tana turawa momy kular da ta shigo da Ita,tare da cewa momy gashi na kawo saboda nasan babu me yin girki a gidan shi yasa?"to masha Allah aiko kin kyauta dan take away aka yi mana kin gan shi nan"cikin zumudi Abba ya ce"Hajiya maza bani girkin ikram kin san kwana biyu ba a hadu ba dan ke kanki na san kun yi missing ɗin abincinta"murmushi kawai momy ta yi ba tare da ta ce komai ba,sai da ta zuba masa doyar da yamvols din ta ɗora masa miyar sos din da take ta zuba kamshi, sannan ta mika masa ta koma gefe tana kallon yadda yake ta fara a da rawar jikin cin abincin kamar wani mayunwaci.

Hira suka shiga dan tabawa da momy lokaci lokaci yana sa musu baki, Ummul kuwa murmushi kawai take ta dokawa tana jiran sakamakon aikinta ya bayyana,sai da Abba dan gaske ya cinye abincin nan tas ya kora da ruwan shayin da momy ta haɗa masa yayi gyatsa da goge bakinsa da tisue,yatsune fuska ya ɗan fara yi kadan kadan, Ummul na kallonsa ta gefen ido zuciyarta fal farin ciki, tun Abba na daurewa har ta kai ga ya fara rike cikinsa da yake wata irin juyawa,dubansa momy ta yi tare da tambayarsa ko lafiya?"girgiza mata kai kawai yayi saboda baya son bada kansa a gaban Ummul dan shi a yanzu jinsa yake kamar saurayi dan shekara talatin da biyar a gaban Ummul dan haka baya son yin abinda zai barar da soyayyar da yake ta kokarin dasata, Ummul kuwa tana hankalce dashi, hakan yasa ta ɗan muskuta tana cewa "Abba lafiya dai ko a kira likita ne?"wani irin mugun murmushin yaƙe ya sakar mata yana waskewa ta hanyar shafa sankon kansa tare da girgiza kansa yana cewa"babu wani abu kar ki damu"so yake ya ce Ummul din ta tafi amma kuma ta wani bangaren baya son tafiyar tata sannan kuma baya son yin abin kunya a gabanta,dan bil hakki cikinsa karta yake kamar ana karta masa reza,can dai basu ankara ba sai jin wata irin kara su kayi, "subhanallah momy ta faɗa tana duban Abba dan gaske dan tantance abinda ke faruwa,dan dai ita idan ba jin kunne ba sai ta ce kamar karar tusa ta ji,idanunsa ta gani a rufe yana ta zuba uban gumi wallahi idan ba a gabanka yake ba sai ka ce ruwa aka watsa masa,da sauri Ummul ta zaburo tana cewa"Abba idan da matsala ka yi bayani a kira likita"ta fada tana toshe hancinta saboda warin da ya bugeta'momy ce ta ce"tsakani da Allah Alhaji da bakinka da komai kai ba yaro karami ba amma ka dage ka sakar mana k......haba momy baki bashi da lafiya ba ai lalura ce babu wamda bata kamawa"cewar Ummul tana kunshe bakinta

Saboda dariyar dake neman fin karfinta.

A takaice dai a cikin mintinan da basu wuce biyar ba Alhaji dan gaske ya bata dakin nan da zawo gashi me shegen wari, duk yadda suke so daurewa sai da amai ya dinga ta so musu,ba wai ta shi ya kasa ba tsananin yadda cikin ya birkice ne yasa ko tashi yayi kafin ya kai ga toilet din ya zubo,to a ganinsa da jin kunyar tsaye ai Gara ta zaune shi yasa kawai ya suburbuda abinsa a zaune,nouse ce ta shigo tana tambayarsu ko lafiya amma tun kafin ta rufe bakinta ta fuskanci abinda ke faruwa, to Ita dai dake nouse ce bata nuna kyama ko toshe hanci ba, cikin sauri dai ta fita ta kira wani nouse namiji ya zo dan gyara alhajin kafin a dubasa,fita su kayi gaba daya daga momy har Ummul din suka zauna a falin room din,mommy duk ta yi wani iri da ita, Ita kuwa Ummul sai ta faki idon mommy ta ci dariyarta daga bisani ta juyo da fuskar tausayi tana jimanta al amarin,sai da suka gyara shi tsaf sannan nouse din ya danna kiran Dr Bilal saboda sanin yana da alaka dashi.

Suna nan zaune a falon, Ummul ta ki tafiya saboda son ganin kwakwaf, sai ga ummi ta zo, hakan ya kuma bawa Ummul damar yin zaman dirshen dan ganin karshen Film din da shirya ta kuma bada umarni,momy ce ta sanar da Ummi halin da ake ciki da kuma musabbabin abin,dan jim ummi ta yi tana kallon Ummul cikin tsananin zargi,kafin ta ɗan saki ajiyar zuciya tana cewa"to Allah dai yasa ba doyar nan ba ce kin san sabuwar doya akwai bata ciki"mommy ta ce"nima Abinda nake ta tunani kenan tun dazu"aiko Ummul ta yi zakal tana cewa "ashe shi yasa nima jiya na kwan ina gudawa dan har na yi tunanin ruwan jikina ma ya kare.....wani mugun kallo ummi ta watsa mata wanda yasa babu shiri ta rufe bakinta,tana muzirai nq rashin gaskiya.

A can cikin dakin kuwa bayan shigowar Dr Bilal ,ya fara duba lafiyar Abba cikin kwarewa, sai da.ya tabbatar ya bashi taimakon da zai ji dadi sannan ya tambayesa abinda ya ci na karshe da ya sashi cikin wannan yanayin,kai tsaye Abba ya nuna masa doya da sos din da ya ci sai kofin ruwan shayin da mommy ta haɗa masa,Dr Bilal bai ce komai ba ya ce da nouse ebele ya dauka ya je lab ya yi masa test dinsu,cikin girmamawa ebele ya dauka duka ya fita zuwa lab, ba tare da ɗaukar wani dogon lokaci ba ya dawo masa da sakamakon dan Dr din yana nan bai fita ko ina ba,karbar takardar da ke dauke da sakamakon yayi ya duba, sai kuma ya maida dubansa kan abba da bacci yake son daukarsa,kana ya ce "waye ya kawo abincin da ka ci?"Abba cikin yanayin magagi saboda allurar da aka yi masa akwai ta bacci a ciki,ya ce"ikramm daga haka ya langaɓe sai kace matacce, a nutse ya maida dubansa kan ebele kana ya ce"ka taho min da ikramm office yanzu"daga haka ya fice ta kofar da yakasance akwai ta a ko wane room da ya kasance vip.

"Waye Imran?"ebele ya fada bayan fitowarsa zuwa restroom din,harara ikram ta watsa masa tare da cewa "kaji wani sabon rainin wayo nice na koma Imran din kuma?"bumm Ummi ta buge bakinta sannan ta dubi ebele tana cewa "ko ikram kake nufi?"take ya shiga gyada kai kamar tsohon kadangare yana cewa "yauwa yauwa mama haka nake son fadi"Ummi ta ce to gata nan"tana mai da dubanta kan ikram din da take ta tunzura bakin da aka buge,ba zaki tashi ba ko sai na biki da duka ne eye shashashar banza wadda bata da girma sai na jiki"Ummi ta fada tana kai mata mangari da kafa,da sauri ta mike ta bi bayan ebele tana zabgawa keyarsa harara,ta lifter ya bi da ita kamar yadda kowa yake bi, suna zuwa kofar ya dan kwankwasa kadan ,sai da aka bashi umarni daga ciki sannan ya bude ya sa kai Ummul na binsa a baya tana tunanin gidan uban wanda zai kaita,kansa kawai ebele ya ɗan rusunar sannan ya juya ya fita, wanda sai a lokacin Ummul ta samu damar karewa office din kallo tana wani yatsine baki da jinjina kai,sai da ta gama tsaf sannan ta waiga bangaren da take tunanin cewa akwai mutum musamman kamshin da ya garwaye hancinta yasa ta tunanin inda ta taba jin irin kamshin.

Ware manyan idanun ta ta kuma yi saboda yin arba da mutumin da bata taba zato ba,dakewa ta yi tana wani cin magani, kafin ta ce"me yasa kasa aka kira ni?"dago kansa da yake durkushe tun shigowar ta yayi ya watsa mata razanannun idanunsa da suke firgita me lefi,tare da dora Mata da tambayar da ta sanya ta zama a kujerar da ke gabanta ba tare da ta shiryawa hakan ba,"me kika zuba masa a cikin doyar nan?"hannu ta sa ta share gumin da ya fara yi mata tsartuwa a saman goshinta,a ranta tana cewa" innalillahi yau na gamu da maye me gani har hanji"zuba mata ido ya kuma yi saboda jin abinda ta ke fada wanda ita kuma bata san cewa a fili ta yi maganar ba,har sai da ta ga kallon yayi yawa sannan ta ankara ta yi saurin toshe bakinta tana zare ido kamar an tsamo mage a garken kura,"uhm ina sauraren ki amma ni ba maye ba ne sai dai ina gano marasa gaskiya irinku,kinga ta shin farko na gano cewa ke barauniya ce wannan kuma maketaciya,kin san cewa wannan abun da kika yi idan ya zo da ajali yana nufin kin yi kisa ke nan?"to fa a nan ne idon Ummul ya raina fata har ya ciko da hawaye,kallonsa ta yi tana niyar fashewa da me karfin tare da cewa"wallahi Ni ba kasheshi zan yi ba,dan sumogal fa kawai na dan zuba masa a cikin yamvols din da sos saboda cikinsa ya juye ya yi ta sunturin toilet,dan na ramawa gentle Marin da yayi masa jiya"tafi ya shiga yi mata kafin ya tsagaita yana cewa"oho to shi wanda kika ramawar shi ya sa ki?"girgiza kanta ta yi tana hawaye kamar an bude famfo," ok ina jin ki me ke hadinki da shi?"shiru ta yi anan tana tauna amsar da zata bashi, "saurayi na ne"ta fada ba tare da ita kanta tasan abinda bakinta zai fada din ba kenan.

A nutse ya zare glass din idonsa yana cewa"ke yanzu yar mitsitsiyarki da ke kin san meye saurayi har da rama masa mari ta hanyar da bai dace ba?"kuka ta fashe da shi tana hade hannuwanta biyu waje daya,mai da glass dinsa yayi yana cewa ki tashi kije da iyayenki zan yi magana saboda na kamaki da laifi biyu sata da kokarin yin kis.....tun kafin ya karasa ta durkushe kasa tare da kama kafafunsa tana kuka kamar idan aka rabu da ita gobe ba zata kara ba,ta ce dan Allah ka yi hakuri ba zan kara ba,kuma ni ba barauniya ba ce kudinka suna nan babu wanda ya taɓa?"janye ƙafarsa yayi ba tare da ya ce mata kome ba,dan kukan nata ciwon kai yake ba shi,sai da yaga tana neman kwanta masa a nan, sannan ya bata umarnin tashi,tashin ta yi tare da komawa ta zauna kamar yadda yake nuna mata cikin aiyukansa, saboda shi baya doguwar magana, share hawaye ta shiga yi duk da cewa yaki tsayawa har yanzu dan bata san makomarta ba"da baki ya kuma nuna mata ta yi shiru,dole ta sanyawa bakinta linzami ta wani sauya lokaci daya kamar ba ita ba,ga tsoro ga ban tsoro?"ta ji ya fada can kasan makoshinta,dan da bata kasance me karfin ji ba, tabbas ba zata ji shi ba,kasa kasa ta yi gunguni tare da watsa masa harara,fata take kawai ya sake ta ta zuba masa kalar ramuwarta.

"Kina tunanin ta inda zaki min illa idan na hakura ko?"ya fada kamar bashi yayi maganar ba,kallonsa ta yi tsoronsa na dan shigar ta,amma sai ta dake a wannan karon ba ta nuna masa kasawar ta ba,dan kawar da kanta ta yi tana cewa"dan Allah ka barni in tafi"ai ban rike ki ba ya kuma fada kansa tsaye yana ci gaba da aikin gabansa,laɓɓanta na kasa ta cije tana kallon sumarsa da take ta sheki kamar ta jaririn da aka haifa yau, kasancewar kansa yana kan tulin takardun da suke gabansa,kuka ta kuma saka masa me wani irin sanyi tamkar tama rera waka,dago kansa yayi tare da mikewa ya zagayo ta inda take a zaune sannan ya rankofo da kansa ya dafa teburinsa hakan yasa yayi mata rumfa ko hango ta sai ka yi da gaske za kayi, hakan kuma yay***

💞GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol