Free chapter · Read without an account
Pg16
Numfashinta har wani daukewa yake saboda tsananin razanar da ta yi,dan idanunta sai suka gane mata kamar Dr Bilal rungume yake da Ummul ikram,hakan ya janyo ta kasa rike kanta har sai da ta karasa ta fizgo kujerar da ikram take kai ,take ta yi baya zata wuntsula, cikin zafin nama Dr Bilal ya sanya dogayen hannunsa ya janyo ta daga kan kujerar ta fada jikinsa kujerar kuma ta tafi ta yi baya ita kadai,cike da tsananin tsoro Ummul ta kamkamesa kanta cikin wadataccen kirjinsa idanunta a rufe, dan ita sam bata san bata san zezee ta shigo ba bare har tasan ta karaso inda suke shi yasa ta yi matukar razana,zezee kuwa kallon Ummul dake kwance saman kirjin Dr take tana jin numfashinta na kai kawo a kirjinta, idanunta cike da kwalla,babu abinda yake ɓata mata rai da sanyata cikin tashin hankali sama da ta ga Ummul ta raɓi Dr ,gashi kuma yanzu har ta kai ta kawo ta fara shiga jikinsa har da biyo shi office,cikin sanyin muryar da take dauke da wani irin kunci da bacin rai,zezee ta ce"dan Allah Ummul ki rufa min asiri kar ki kasheni saboda bana son na rataya a wuyan kaskantancciya kamarki"da sauri Ummul ta kwace jikinta daga na Dr tana zare ido tare da mamakin ganin zezee din kamar wata aljana,shi ko gogan ko ajikinsa hasalima duban Ummul yayi da wani irin kallon gargaji na kar ki sake aikata abinda kika yi, daga haka ya yi mata nuni da ta tafi,aiko babu wani jinkiri ta fice da gudu gudu sauri sauri ba tare da kuma gangancin kallon fuskar zezee ba.
Wani irin mamaki ne ya kuma kashe zezee a tsaye saboda ganin yadda Dr yayiwa Ummul magana da ido ta kuma fahimta ba tare da magana ta fatar baki ba,durkushewa ta yi a wajen tana rasa abin yi,ganin zai fita ne yasa ta yi saurin matsawa ta rike ƙafarsa tana cewa"dan Allah Bilal ka yi min afuwa idan ma kana yin duk wannan abinne dan ka huce laifin da na yi maka,to wallahi na horu kuma na yi nadama,amma dan Allah ka bar komai ya wuce mu fuskanci abinda ke gabanmu domin gyara rayuwar auren mu da za mu fuskanta a nan gaba kaɗan"ta karasa maganar tana sakin wani dan marayan kuka,janye ƙafarsa yayi yana ci gaba da takunsa a nutse dan fita daga ofishin,sai da ya kai bakin kofar sannan ya ɗan dakata tare da cewa babu ruwana da rayuwarki dan haka babu wani abu da nake ko zan yi dan na bata miki rai, daga yau ki dinga sanin irin maganar da zaki yi min?"daga haka ya ficewarsa dama ko jiyowa bai yi ba har ya gama maganarsa.
Zezee kam rasa ma me zata yi ta yi, dan wannan wulakancin na Dr ya fi gaban ta yi masa kuka,mikewa ta yi tana cewa"kaje amma wallahi daga Kai har Ummul din sai kun zama bayina alkawarina ne sai ka zo ka rissina min, zan yi duk abinda zan yi dan na sa ka kasoni irin son da baka taba yiwa wata ya mace ba a duniya ba"wayarta ta fito daga jaka tana ficewa daga office din tare da sanya wayar a kunnenta,bely kina ina"?ok gani nan zuwa yanzu",ta fada tana maida wayar tare da nufar motarta,da wani matsiyacin gudu ta fice daga asibitin kamar wadda take shirin tashi sama.
Ummul kuwa tana samun damar ficewa bata tsaya a ko ina ba sai bakin titi,ko tunanin komawa ciki ma bai zo mata ba,nafef ta tare kai tsaye ta wuce gida,tun daga nesa ta hango dan anacenta tsaye jikin motarsa yana ta bazawa gentle dake aikinsa cikin kwanciyar hankali kallon banza,tana shirin bawa me nafef kudinsa taga anzuro hannu an mika masa sabuwar dubu guda biyu,tsaki ta yi ta wuce ta barsa da me nafef yana zuba masa godiya,zata shige gida kenan ta ji muryarsa tamkar saukar a radu a tsakiyar kanta,"babu batun a tambaye ki lafiyarki dan ga dukkan alamu tasamu tun da har kin samu kafar yawo",tabbas ba dan lokacin da ya fara maganar tsayawa ta yi tana kallon keyarsa da kansa yake a kasa ba da cewa zata yi ba shi yayi maganar ba,dan haka sai kawai ta yi masa harar kasan ido tana cewa"da sannunka ce zata sani na warke da sai dai na mutu da ciwo,dan haka kuwa babu dalilin da zai sani na kwanta ina zaman jiran ya jikinki ko sannu daga bakinka"tana maganar tana fari da ido hadi da dan mummurguda karamin bakinta, sannan ta kada kai ta shige gidan bakinta dauke da sallama fuskarta kuwa tana bayyana wani boyayyan farin ciki da ke can karkashin zuciya da ba wanda yasan da shi sai mahaliccin zuciya.
Shi din ma Binta yayi da wani irin kallon da har sai da sukaiman da yake tsaye yana kallon su kusan faduwa, da bai fadin ba sai da ya dafe kirjinsa da yake barazanar fasowa ya fito,har zai je wajen getle din amma yasan idan yayi hakan karawa kansa damuwa zai yi dan haka gwara masa ya je yayi tunanin hanyar da zai bi ya samu Ummul a matsayin matar aurensa,dan yayiwa kansa alkawarin tsayawa tsayin daka ya samu Ummul ko ta wane halin.
******
A can asibiti kuwa jin shurun ummul yayi yawa ne yasa Ummi ta shiga nemantaz karshe dai wata nouse ce ta sanar da ita ta ga fitar Ummul din daga cikin asibitin,dan haka sai kawai ta yiwa mommy sallama ta kama hanyar dawowa gida,tana zuwa gida ko shiga bata yi ba ta tambayi gentle ko ya ga dawowar Ummul amsa mata yayi da "ta dawo tun dazu Ummi"kwafa Ummi tayi ta re da shigewa ciki tana faɗa bakinta bai yi shuru ba har sai da ta dangana da Ummul da tasan bata da gaskiya,dan tuni ta kammala mata aikin gidan miya ka dai ya rage bai karasa ba,jan kunnenta Ummi ta yi tare da kai mata rankwashi tana cewa "dole ki gudo mana tunda kin san baki da gaskiya wallahi ko kaffara ba zan yi ba nasan wannan ciwon cikin na Alhaji ke ce sila,dan Ni dama tun da naga kin yi girkin nan wai zaki kai masa na san cewa ba dan a Allah kika yi ba dan ki shuka tsiyarki kawai kika yi"dan runtse idanunta ta yi tana cewa"don Allah Ummi ki yi hakuri ki daina dukana kinsan fa bani da lafiya gashi na yi girma yanzu ya ci a ace na wuce duka a wajenki" Ummi ta ce"ke ai ba ki san baki da lafiyar ba har kike diban jiki kina zuwa neman magana, ai dan nasan baki da lafiyar ne ma yasa jikinki bai gaya miki ba tun a asibiti da na fahimci abinda kika aikata"tashi Ummul ta yi tana tura baki a ranta tana cewa "Ummi sai dai da hakuri amma ko yanzu na kuma samun dama akan Alhaji da wannan dan itopian yasin sai na ci zalinsu".
*****
Sulaiman yana tafiya kai tsaye gidan saluhu abokinsa ya nufa,inda matar saluhu ta cika gabansa da kayan ciye ciye,amma ya kasa shan ko ruwa,ganin sa cikin damuwa ne yasa matar saluhu ta basu waje,kamar dama jira yake ya yi sauran gyara zamansa yana fuskantar saluhu da yasan matsalar abokin nasa,"saluhu ka bani shawara akan yadda zan bullowa lamarin ikram dan abin ya fara bani tsoro, dan gantakarta da me gyaran takalmin nan kullum abin ƙaruwa yake na rasa yadda zan yi ta tsaya ko na minti biyar ne ta saurareni bare nasan ta yadda zan kamo bakin zaren"dafa kafardarsa saluhu yayi yana cewa "haba calm down mana me yasa idan yar karyar nan ta motsa maka kake kasa control din kanka ne, kullum ina gaya maka ka dinga bin komai a sannu hanzarin ka ko damuwarka ba shi zai sa ka samu yadda kake so ba,dan haka ka ci gaba da bin yan uwanta da mahaifinta da kyautatawa kamar yadda na gaya maka a baya in sha Allah zaka samu zuciyar masoyiyarka yar karya"ya karasa maganar da dariya,harara sulaiman ya watsa masa tare da ture hannunsa daga kan kafadarsa yana cewa, "bana son iskanci saluhu haka zan aureta ka zo gidan mu kana ce mata yar karya?"bai saurari abinda saluhun zai ce ba ya ci gaba d cewa ,saluhu har yanzu abinda ka kasa ganewa shine ba fa yan uwanta zan aura ba soyayyar su nake nema ba soyayyar ikram nake nema, kuma suna matukar son Ikram, ba zasu taba yi mata dole akan ta aure Ni ba,kaga kuwa dole hankalina ya tashi"saluhu ya ce "na fahimta amma dai ka yi hakuri ka bi abin a sannu, haka dai saluhu dinga karfafa shi har ya ɗan samu sukunin cin wani abu ...
A bangaren zezee kuwa ita din ma gidan kawarta bely ta nufa,zezee bata da wata kawa da ta wuce bely duk da cewa bely ba ta tare da iyayenta kai hasalima zaman kanta take yi, gida ne sukutum guda gareta,zezee babu ruwanta duk sanda ta yi niya zata je gidan bely kai tsaye ,bata taba tunanin cewa hakan na iya bata mata suna ba,kawai abinda ta yi believing da shi ubanta yana da kudi dan haka babu wani abu da ya isa ya taba mutucinta haka kuma zamanta da bely bai isa ya sa ta koyi ɗabi unta ba,haka kuma bata ganin wani aibi a rayuwar da bely ta sa kanta, dan acewarta mutum in dai yana da kuɗi to yana da cikakken 'yancin yin yadda yaso a rayuwarsa, dan haka bata da matsala da rayuwar bely ita dinma rashin ra a yi ne yasa bata yi,lokacin da ta isa gidan kai tsaye ta shige falon belyn,inda ta samu wasu kosassun mata hajiyoyi da su,zaune cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya,bata kula ko wacce daga cikinsu ba ta samu waje gefe guda ta zauna tare da makala Bluetooth a kunnenta,ko zaman minti biyu bata yi ba sai ga bely ta fito daga daki sanye cikin wasu shegun kayan da basu da maraba da babu, sai wani gamjejen mutum dake biye da ita yana ta dashare baki kamar gonar auduga,tana ganin zezee ta washe baki tare da daga mata hannu,kallon mutumin ta yi tana cewa "to Alhaji bashari kaje ina da bakuwa sai mun yi waya"sannan ta kalli wannan matan suka ta basu excuse aka sa dawo gobe"cikin kankanin lokaci gidan yayi shuru ya zamana daga zezee sai bely.
Zama bely ta yi a gefen zezee tana cewa"ya dai kawata na ji ki a zafafe haka ko ke da Dr naki ne?"iska zeze tafesar daga bakinta tare da duban belyn tana cewa"bely ina ga zan dauki shwararki ta farko na gwada ko zan dace idan haka bai yuwu ba sai mu dauki ta biyun"shewa bely ta yi tare da tafa hannayenta saman cinyarta,kafin ta ce"lallai na tabbatar da cewa abinda kika gani yau me girma ne da har ya saki mika wuya akan shawarar da na baki,tun da haka ne kuwa na miki alkawarin samun cikar burinki a nan kurkusa"bely duk ba wannan ba yanzu yaushe kike ganin zamu tafi nijer ɗin?"ko gobe a shirye nake da mu tafi Ni da tafiya bata min wuya bare kuma a lafiyayyar mota"mikewa zeezee ta yi tana cewa "shike nan karfe bakwai zan fito na daukeki"daga haka suka yi sallama ta fice daga gidan,tana ji kamar ta janyo goben.
*****
Washe gari kuwa karfe shida da arba in tana dokawa zezee ta bar gidan ba tare da ko momy ta sanarwa ba, ranar ne Kuma da karfe hudu aka yi discharged din Abba Dan gaske, wanda shi kansa ya ji dadin hakan ko dan ya dawo ya ci gaba da gwagwarmayar neman abu guda biyu da suka tsaye masa a kahon zuciya.
*****
"Ummul Ummul kina ina ne sai ka ce kurma ina ta doka miki kira kina jina?"cewar Ummi kenan dake zaune a cikin ɗan madaidaicin kitchen dinta tana tuka lafiyayyen tuwon shinkafa da yayi wani irin laushi kamar kaci shi a haka,"na am ummi gani nan mayafi nake daukowa"Ummul ta fada daidai lokacin da take fitowa daga dakin tare da zura dan silifas dinta me kyau cikin kafarta da kamar bata taka kasa da ita,karasawa ta yi gaban ummin tana karbar kudin da take mika mata,"maza ki karbo min farar leda wajen hamisu me kanti kafin tuwon nan ya sulala nake so ki dawo,idan kuma kika tsaya jan magana Ni dake ne"karbar kudin Ummul ta yi tana cewa"haba Ummi wane irin jan magana sai ka ce wata yarinya"fita ta yi Ummi ta bita da kallo kafin ta ci gaba da abinda take tana dan girgiza kan mamakin shirmen Ummul ɗin.
Tana fita ko kallon inda gentle yake batayi ba, sai dai ita d taji kaifin idanunsa a kanta,wanda hakan yasa ta juyawa bata shirya ba,sai dai ga mamakinta yadda ta fito ta sameshi haka ta ganshi babu wata alama da ya nuna mata cewa ya kalleta,hakan yasa ta ɗan bubbuga kafarta a kasa tare da tura baki tana fadar maganganu akansa,har ta je ta dawo aiki yake sai dai saɓanin ɗa zu da yake shi kaɗai yanzu wata budurwa ce a tsaye sanye cikin fararen uniform, ummul tana can tana tunanin ko wacece wannan din? bata sani ba har ta karasa kofar gidan, sai ji kawai tayi budurwar na cewa "wa nake gani kamar sister din Dr Bilal ƊAN ITOPIA?"sai a lokacin Ummul ta ankara har ta dawo hayyacinta,duban budurwar da akalla zata yi sa a da zezee ta yi tare da dan ware manyan idanuta akanta tana cewa"Yes nice sai dai na manta inda na sanki?"Ummul ta fada tana wani gyara tsayuwar ta tare da boye ledar kwasar tuwon da ta siyowa Ummi ,a ranta tana godiya ga Allah da yasa bata fita a haukace, dan ita dsma ko a gida ba zaka shiga ka ganta da kayan da basu da ce ba,"cikin zakuwa da son lallai sai Ummul ta tunata ta ce"kawar sister mariya(wadda su kayi hira da ikram ta zan bada mata kariyar ita kanwar Dr ce ita kuma ta je ta bazawa ragowar nouse din irin su wannan dake gaban Ummul)ba tare da Ummul din ta tuna fuskar matar ba ta waske da cewa"oh ke ce sannu dai ya kike ya aikin?"lafiya kalau kema gyaran takalmin kika kawo ne duk da cewa na san irin ku so daya kuke sa takalmi ku bayar"matar ta fada tsakaninta da Allah kuma dan banbaɗanci dan tasan yau din kakarta ta yanke saka tunda ta haɗu da 'ya guda ta ɗan itopia,ko kunyar idon gentle da yasan komai akanta bata ji ba ta gyara tsayuwarta tare da cewa"ayya ai dake mu din ba mu da girman kai idan gyaran ne ma ya kama ai sai na yi tunda lalura ba ta bar kowa ba,shigowa na yi kawo taimako wani gidan marayu shine fa na ce da driver ya tafi ya dawo sai na gama zazzaga gidan takawanmu sai ya dawo ya dauke Ni,to ina cikin shiga gudanjen ne fa na ci tuntuɓe da dutse igiyar takalmin ta cire,kin ga kuwa ai yau dole zan yi gyara amma daga na koma gida ya zama na bayarwa".
Alamun idanunsa ta ji a jikinta da yanayin bugun zuciyarta da ya sauya hakan yasa ta ɗan dakata da zubar da take yi,matar kuwa caraf ta ce"to hajjaju idan an cire ina so tunda kinga ni dai fama nake da gyara kullum abinka da me zuwa aiki kayansu basa lasting"wani dan kakkauran miyau Ummul ta hadiye kana ta ce"kar ki damu har gida zan kawo miki ko na bawa yaya Dr Bilal ya kawo miki"zaro ido matar ta yi har da dafe kirji tana cewa dan Allah ki rufa min asiri wace ni da karbar sako hannun Dr ina maaifin ki ce na zo na karɓa"tabe baki Ummul ta yi tana cewa wai me yasa kuke tsoron yaya Dr ne haka sai ka ce wani mala ika? KO dan baya murmushi ne yasa kuke ganinsa kamar wani kumurci?"tsaki ta ɗan yi tana satar kallon gentle da yake mikawa matar takalminta,matar zata zaro kudi ta bashi Ummul ta yi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa"ki barshi kawai zan bashi dama shima akwai sakon taimako daga yaya Dr duk zan hada na bashi"godiya matar ta shiga yi kamar an an bata kujerar hajji gata dai budurwa amma kwadayi yasa ta zage tana ta banbaɗanci, Ummul da take ji kamar ta hankada keyarta saboda haushi ta ce"kije ba damuwa zan hada miki da sako a cikin takalmin mu ba wani abu ba ne a wajen mu yin kyautar miliyan"take Ummul ta kara tashin hankalin baiwar Allah ta tafi tana zabga godiya da sanya rai akan kyautar kudi me tsoka wata kila ma sanadin haka ta bar aiki...........
Cikin sauri Ummul ta daga kafa zata shige gida amma sai ta ji an riko hannunta, juyawar da za ta yi wa zata gani sulaiman ne rike da hannunta yana zabga uban murmushi, cikin tsiwa ta bude baki zata yi magana,sai dai kafin ta fadi abinda zata fada tuni wani dogon hannu da ban, ya dauke hannun sulaiman daga nata tare da jin wani irin sauti kamar na an balla abu......
Tofa Allah yasa ba hannun Ummul aka balla ba,
Wai me kuke zato ne?
Wannan karya ta Ummul dai yau da alama ta kusa karewa dan gashi dai ta yi alkawarin abin da ba ta dashi,
Zahran ku ce dai har kullum ina muku sonso,
Wannan pg kuma sukutum na bawa fans din gidan yan karya ku yi yadda kuke so da shi , idan ma yagalgalashi zaku yi, babu ruwana Ni dai ba ku😂😂😂
Zahra✍️i daidai da shigowar zezee ofishin.......✍🏽
***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....